Saturday, 15 July 2017

MEYASA BA'A AMSA ADDU'OINMU???


*MEYASA MUKE ADDU'AH, AMMA SAI MUGA KAMAR BA'A KARBA MANA???*

```An tambayi Ibrahim bn Adham(RH) akan cewa meya samemu ne, muna Addu'ah amma ba'a karba mana??

Sai yace: Zukatanku sun mutu da Abubuwa takwas(8).

NA FARKO; Munsan Allah, amma ba muyi mashi biyayya(ma'ana; munsan hakkin Allah, amma bamu gabatar mashi da hakkinshi).

NA BIYU; Muna karanta Alkur'ani, amma bamu aiki dashi(ma'ana: Bamu aiki da iyakokin da Allah ya gindaya a cikin Qur'anin).

NA UKU: Munce munason Manzon Allah (Salallahu alaihi wasallam), amma sai muka yi mashi tawaye, muka kiyin amfani da sunnar shi.

NA HUDU: Munsan cewa Shaidan makiyinmu ne, amma sai muka sakar mashi akala muna binshi.(Muna yi mashi biyayya wajen sabon Allah).

NA BIYAR: Munsan cewa Aljanna gaskiya ce, amma bamu aiki domin mu shigeta.

NA SHIDA: Munsan cewa wuta gaskiya ce, amma bamu guje mata.

NA BAKWAI: Mun wayi gari mun shagaltu da aiboban(harkokin) mutane, mu kuma mun bar namu aiboban(harkokin).

NA TAKWAS: Kun binne mataccinku, amma Baku lura da kuma wataran za'a binneku.

NA TARA: Mun ce, muna tsoron mutuwa, amma ba muyi mata tanadi ba.

NA GOMA: Muna cinye ni'imomin Allah, Amma bamu gode mashi(muna cinye abincin Allah, abin shan Allah, da sauran ni'imomi amma mun kasa gode mashi).

Wadannan da wasunsu sune dalillan dake sa muke rokon Allah sai Allah ya kyalemu da dabararmu.

Yaa Allah ka bamu ikon gode maka.
Yaa Allah ka karo mana ni'imominka ta hanyar da muka sani da wacce bamu sani ba.```

HAKKIN MALLAKA©
Hashim Sirajo Uba Tsamiya(ABU SINAN)
+2348064734911
+2349030201868

SHAFUKAN SADA ZUMUNTA DOMIN BIBIYARMU.

atstsamawy@gmail.com

hashimusurajo5@gmail.com

I G @ abbansinan

http://hashimtsamiya.blogspot.com/

http://abbansinaan.blogspot.com/

http://shababusunnahtsafe.blogspot.com/

http://masjiduabihurairatsafe.blogspot.com/

https://mobile.facebook/hashimusurajo.tsamiya/