Sunday, 25 November 2018

(B) DOMIN MASU HANKALI SUYI TUNANI

⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪
*وليتذكر ألوا الألباب...*

*DOMIN MASU HANKALI SUYI TUNANI...*
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Gabatarwa: *MUKYAUTATA NIYYA*

_PART_ *B*


*KASHI/BAYAN GIDA YAFI MAULIDI A SALI A CIKIN ADDINI...!!!*

*LADUBBAN SHIGA BAYAN GIDA(BIYAN BUKATA)*

Abubuwan da aka so ayi wajen shiga bayan gida don biyan bukata.

*Gasu kamar haka:-*

1. A lokacin shiga, zaka fadi ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﺍﻟﺨﺒﺚ ﻭﺍﻟﺨﺒﺎﺋﺚ . ```ALLAHUMMA INNI A'UZU BIKA MINAL KHUBSI WAL KHABA ISI```
watau [ALLAH INA NEMAN TSARI DAGA GAREKA, KA KARENI DAGA SHARRIN ALJANNU (SHAIDANU MAZA DA MATA)

2. Shiga bayan gida da kafar hagu.

3.sanya gajeren wando lokacin wanka, domin ka kare tsiraicinka idan a fili ne a wajen wankan

4. Fara yin bisimillah

5. Sanya ruwan wanka a gefen hannun dama

6. Amfani da takaitaccen lokaci a bayan gida(kashi)

7. Fitowa da kafar dama

8. Kebewa daga idanun mutane

9. Tsugunnawa lokacin da ake bayan gida

10. Mayar da nauyin jiki zuwa bangaren hagu

Bai kamata ba a shiga bayan gida da abin da ya ke dauke da sunan Allah s.w.t a jikinsa(sai dai domin gudun kada a sace shi), bayan an gama ana son a wanke hannaye da ruwa, ko da sabulu ko kuma tur6aya ko yashi.

Musulmai ya kamata lokacin da za suyi bayan gida ko wanka, su kebe kansu daga inda mutane zasu iya ganinsu.

An kar6o daga jabir yace; "idan muna tafiya tare da manzon Allah s.a.w, ya kanyi bayan gida idan ya kebe daga mutane (wato ya kan sakaya kansa inda ba mai ganinsa.

*ABUBUWAN DA BA'A SON A AIWATAR DANGANE DA BAYAN GIDA...!!*

1. Fuskantar/juya wa Alkibla baya idan a fili ne.

2. Magana ko kuma wa'ka yayin da ake bayan gida

3. Yin wanka a gaban jama'a

4. Karanta ayoyin alkur'ani a ban daki

5. Yin amfani da ruwa mai yawa.

6. Yin wanka, fitsari, ko bayan gida a wajen da ake ibada, misali;
*MASALLACI, COCI,* ko wani majalisi na al'umma.

7. Wanke can cikin dubura

8. Barin wasu mutane su ga tsiraicin dan uwansu.

9. Yin fitsari a cikin rami.

10. Ta6a azzakari ko dubura da hannun dama.

Yan uwa munji kadan daga cikin ladubban bayan gida(KASHI)
Domin karin bayani, ka duba ﺑﻠﻮﻍ ﺍﻟﻤﺮﺍﻡ -ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻄﻬﺎﺭﺓ - ﺑﺎﺏ ﺁﺩﺍﺏ ﻗﻀﺎﺀ ﺍﻟﺤﺎﺟﺔ

*YAN TA MAULIDE MUNA JIRAN NAKU LADUBBAN NA CASHEWA, DAGA HADISSAI INGANTATTU, DA INDA AKA CIROSU.*

*HAATU BURHAANAKUM INKUNTUM SADIQEEN*

HUJJA MUKE BUKATA BA ZAGI BA


✍ *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy ( _ABBAN-SINAN_ )*
+2348064734911

018 MUKOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUPS DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na sha takwas 018_


Gabatarwa: *UMMU SINAN*

*MUSTAHABBAN ALWALA:*
Wannan shi ke biye da mataki na sunnoni, kenan sunnoni sun fi mustahabbai karfi,
wadanda suke dukansu biyun farillai na gabansu, babu daya daga cikin sunnoni ko
mustahabbai da mutum zai yi sakaci da su, domin kowannen mu so yake ya yi ibada
cikakkiya kammalalla, to kuwa tunda hakane bai kamata kace ai wannan mustahabbi ne ka daukeshi kamar wani karamin abu. Su mustahabban alwala suna da yawa, amma yanzu ga kadan daga cikinsu:

1⃣ Ambaton Allah kace *Bismillah* a daidai lokacin da zaka fara alwala, amma idan mutum
ya manta saida yake tsakiyar alwalar ya tuna
ba komai sai kayi a lokacin.

2⃣ Addu'a bayan kammala alwala, itace kuma kamar haka:

*ﺃَﺷْﻬَﺪُ ﺃَﻥْ ﻻَ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺍَﻟﻠﻪُ ﻭَﺣْﺪَﻩُ ﻻَ ﺷَﺮِﻳﻚَ ﻟَﻪُ، ﻭَﺃَﺷْﻬَﺪُ ﺃَﻥَّ ﻣُﺤَﻤَّﺪًﺍ ﻋَﺒْﺪُﻩُ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟُﻪُ، ﺍَﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺍَﺟْﻌَﻠْﻨِﻲ ﻣِﻦَ ﺍَﻟﺘَّﻮَّﺍﺑِﻴﻦَ، ﻭَﺍﺟْﻌَﻠْﻨِﻲ ﻣِﻦَ ﺍَﻟْﻤُﺘَﻄَﻬِّﺮِﻳﻦَ.*

_Ma'ana:_ ```Ina shaidawa da babu abun bauta da
cancanta sai Allah, kuma shi kadai yake bashi da
abokin tarayya, kuma ina shaidawa lalle (Annabi)
Muhammad bawan Allah ne kuma manzonsa ne,
Ya Allah ! ka sanya ni daga cikin masu yawan tuba, kuma ka sanya ni daga masu neman
tsarkaka.```

3⃣ 'Karanta Ruwa;
   Bawai ana nufin mai alwala ya shashshafa gabbansa bane, a'a, ana bukatar yayi amfani da ruwa amma kada ya malalar dasu, domin yana daga cikin tsarin musulunci
tattali da tsimi da tanadi.

4⃣ Gabatar Da Asuwaki:
Bayani kuma dama ya gabata akan asuwaki, ana yi da danye ko da
busasshe, idan bai samu ba sai ayi da yatsa, amma mu sani asuwaki daban kuskurar baki ma
daban. Hakanan kuma ko da mutum lokacin sallah yayi amma yana da alwala to abinda ake so shine ya yi asuwaki.

5⃣ Wuri Mai Tsarki:
  An so inda zaka yi alwala ya zama wurine mai tsarki.

6⃣ Dama Kafin Hagu:
  Abun nufi shine ka fara wanke hannun dama kafin hannun hagu, hakanan ka fara wanke kafar hagu kafin ta
dama.

7⃣ Jerantawa:
  Wato jeranta kowacce sunnah
tare da 'yar-uwarta, kamar fara gabatar da kuskurar baki kafin shaka ruwa.

8⃣ Wankewa Sau Uku:
  Ma'ana wanke wuraren da ake wankewa sau uku, mu sani wankewa sau uku zai zama mustahabbine idan wankewar farko ta game ko ina, amma idan ta farko bata
game ba to ta biyu tananan amatsayin wajibi, haka idan ta biyun bata game ba
to ta uku tana nan a matsayin wajibi. Ya zama wajibi mai alwala mace ko namiji ya kula sosai
ya cuccuda inda ya kamata ya sa ruwa ba tare da barna ba.
Amma shi kai sau daya ake shafarsa, ba'a shafar kai sau biyu ko uku. Sannan kuma mutum ya tabbata a wadannan wankewa da akace yayi sau uku bai kara akan hakan ba, yayi iya kokarinsa ya ga guda ukun sun kammala.

Wadannan kadan kenan daga cikin
mustahabban alwala, kuma wadannan bayanai
sun shafi mata kamar yadda suka shafi maza, sai dai
mata su sani gashin kansu al'aurane, saboda haka bai
halatta su bayyanar dasu ga maza ba, kenan idan zaki yi alwala sai ki sami wuri ki kebance
kanki.

Wadannan bayanai da suka gabata zasu haskaka mana yadda alwala take, amma hanya mafi sauki shi ne a yi maka ita a aikace ka gani domin haka sahabban ma'aikin Allah suka yi, an
tambayi Usman dan Affan dan gane da alwala sai yasa aka kawo mishi butar alawala yayi musu ita a aikace, yace kuma irinta manzon Allah s.a.w yayi.

A nan nake kira ga dukkanin limamai na juma'a dana sauran masallatai da kuma malamai a
jami'oi da kwalejin ilimi da kuma malamai a sakandare da firamare da malaman islamiyyu da malamai masu karantarwa a masallatai da
masu wa'azi da sauran wadanda abin ya shafa kamar kungiyoyin addini
dasu karantar da mutane alwala a
aikace, yadda kowa zai gani ya kuma yi tambaya, kada kaga kamar kowa ya gane da zarar ka yi ta a aikace zaka ga abin mamaki, ni na taba gwada
hakan a *Federal university birnin kebbi,* ita ibada sai an koyawa mutum ba wai daka akeyi ba, kai da ganin
alwalar wani kasan bai je makaranta ba, Allah ya karba mana ibadummu.

A NAN MUKA KAWO KARSHE DANGANE DA BAYANI AKAN ABUNDA YA SHAFI ALWALA, A GABA ZAMU BAYANIN ABUBUWAN DAKE KARYA ALWALA INSHA ALLAHU.

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN;
✍ *Hashim Siraj Uba atstsamawy ( _ABU-SINAN_ )*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

(A) DOMIN MASU HANKALI SUYI TUNANI

*وليتذكر ألوا الألباب...*

*DOMIN MASU HANKALI SUYI TUNANI...*

_Gabatarwa:_ *MUKYAUTATA NIYYA GROUPS*

PART *A*

📌 *WANNAN ITACE HUJJAR MU AKAN CEWA MAULIDI BIDI'AH NE...!!!*

*==============*

▫ Abubakar siddiq(RA) yayi khalifanci tsawon shekara biyu amma baiyi maulidi ba, tare da cewa shi mai gaskiyar wannan al'ummar ne, kuma abokin manzon Allah s.a.w a cikin kogo lokacin hijira..!!
*▪▪▪▪▪▪▪*

🔸 Umar bn khaddab(RA) yayi khalifanci shekaru goma(10), amma ba'a ruwaito cewa yayi maulidi ba, tare da cewa shine FARUQ na wannan al'umma..!

*▪▪▪▪▪▪▪*

🔹Usman bn affan(RA) yayi khalifanci shekaru 13, amma baiyi maulidi ba, kuma baice ayi ba, tare da cewa ya auri yayan annabi guda biyu, kuma yayi hijira guda biyu, Wanda yafi kowa kunya a cikin wannan al'umma..!
*▪▪▪▪▪▪▪*

🔸 Aliyu bn Abi dalib(RA) yayi khalifanci shekaru 4 amma bai aikata maulidi ba, baiyi umurni da ayi ba, kuma shi Dan baffan manzon Allah s.a.w ne, kuma shine ya auri shugabar matan yan aljanna...!
▪▪▪▪▪▪▪

▫Hassan bn Aliyu bn Abi dalib yayi khalifanci wata shida(6) amma baiyi maulidi ba, gashi jikan Manzon Allah s.a.w, kuma shine shugaban samarin aljanna...!
▪▪▪▪▪▪▪

◼ Mu'awiya bn Abu sufyan yayi mulki na adalci a cikin kabilun larabawa, amma baiyi maulidi ba, bai kuma ce ayi ba
▪▪▪▪▪▪▪
◻Daular umawiyya tazo, a cikinta akwai irinsu Umar bn Abdulaziz, daular Abbasiyya tazo, a cikinta akwai misalin Harun Ar-rasheed, amma dukansu basuyi maulidi ba, basu kuma yi umurni da ayi ba..!
▪▪▪▪▪▪▪

🔹 Yanzu ma malaman gaskiya, masoya manzon Allah s.a.w gaskiyar so, basuyi maulidi ba tun daga karnukan nan guda uku, tare da tsananin sanin su akan abunda Allah ya saukar, da kuma girman fahimtarsu ga Qur'ani, ya akayi basuyi ba? Tare da cewa sune suka iso da Qur'ani da hadissai zuwa garemu..?

▪▪▪▪▪▪▪
  Mu dai yanzu zamu ce;  Da maulidi alkhairi ne da sun rigamu aikatashi..!
▪▪▪▪▪▪▪
Zamu fadi Abunda Imamu Malik(RH) ya Fada; ```Duk abunda bai zama addini a lokacin manzon Allah s.a.w da sahabbai ba, ba zai taba zama addini ba har tashin Al-kiyama..!```
▪▪▪▪▪▪▪
➡ Abu sananne kawai shine; Manzon Allah s.a.w bai bar duniya ba sai da ya kammala Isar da sakon da Allah ya aikoshi dashi..!
▪▪▪▪▪▪▪
   ▪ ya tsoratar da sahabbanshi akan kirkirar wani abu a cikin addini, da aikata abunda bai aikata ba..!
▪▪▪▪▪▪▪

▫ Ya kamata kusan cewa; wadancan karnukan masu girma basu San wani biki mai suna Maulidi ba! Shifa Maulidi wata bidi'ah ce da yan shi'ah *(FADIMIYYUNA)* suka kirkira, a karkashin wani shugabansu da suke kira Mai daukaka addinin Allah, sai dai karya suke, shi mai cutar da addini ne..!
▪▪▪▪▪▪▪
🔸 yayi mulki a bisa kafirci, da fasikanci, ta inda ya halasta shangiya, ya halasta kowane  farji na mace, ya tsinewa sahabbai kuma yayi umurni da hakan a saman mimbarorin juma'ah, wannan Dan ta'addan shine ya kirkiri maulidi fa! Ya kasa maulidin gida shida, Na farko; Maulidin Manzon Allah s.a.w, sai na Fadima, Aliyu, Hassan, Hussaini(ALLAH YA YARDA DASU) sai Maulidin kanshi..!
▪▪▪▪▪▪▪

Daga nan sai yan fadimiyyuna suka jahiltar da musulmai akan wannan bidi'ar, ya kamata kusan cewa babu wani dalili a wurin yan tamaulide akan halascin maulidi, kawai hujjarsu wasu nassosi ne suke yim a gurguwar fahimta, ko kuma hadissai na karya koda sun inganta sai ka samu basu nuni akan maulidi amma sai su juyar da ma'anarsu.
▪▪▪▪▪▪▪

◼ *YANZU GA WASU YAN TAMBAYOYI GUDA UKU DA MUKESON MU JEFAWA YAN TAMAULIDE, MUNA NEMAN AMSARSU:*
▪▪▪▪▪▪▪

1⃣ Shin bikin maulidi biyayya ne ga Allah da Manzon Allah s.a.w ko sabon Allah ne??

Idan sunce biyayya ne! Ko kuma sunce Sabo ne, duka akwai tuhuma garesu..!

2⃣ Yawwa, idan sukace biyayya ne ga Allah kuma zasu samu lada akai!
Sai muce Ko Manzon Allah s.a.w yasan da wannan biyayyar?
Ko bai sani ba?

➡ Da zasu ce bai sani ba, da sai muce kaiconku! Yanzu kuna tuhumar Babban malami(Manzon Allah s.a.w) da jahilci, wannan kafurci ne, kuma zindikanci ne..!
▪▪▪▪▪▪▪

🔸 Da zasu ce ya sani, toh sai muje a tambaya ta uku.

3⃣ Kunce biyayya ne, kuma Manzon Allah s. a.w ya sani, shin ya bayyanar dashi ga mutane ko kuwa ya boye???

Idan sunce bai Isar ba, wannan tozarci ne ga Manzon Allah s.a.w, da kuma tuhumar Manzon Allah s.a.w da boye wani Abu na manzanci, bayan a Qur'ani Allah s.w.t ya Fada cewa; ```Yaa kai Manzon Allah ka Isar da abunda ya sauka gareka daga ubangijinka, idan bakayi haka ba, baka Isar da Manzancin ba.```

Idan kuma sunce ya Isar, sai muce; Toh kuzo mana da dalili, ina aikin magabata akai?
Yanzu muna bukatar amsoshi daga gareku.

ALLAH YA NUNA MANA GASKIYA YA BAMU IKON BINTA, YA NUNA MANA BIDI'AH YA BAMU IKON KAUCE MATA

KU WATSA WANNAN A TSAKANIN MUTANE DOMIN AL'UMMA SU GANE GASKIYAR BIDI'AR MAULIDI...

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN;
✍ *Hashim Siraj Uba Tsamiya ( _ABBAN-SINAN_ )*
+2348064734911