*YAR UWA KINASON SHIGA ALJANNA???!!!*
*KI KIYAYE DOKOKIN ALLAH!*
```Hadisi ya tabbata daga Abi Hurairah R.A yace; Manzon Allah s.a.w yace: "Mutane guda biyu yan wutane, ban taba ganinsu ba!(babu irin wadannan mutanen a lokacin manzon Allah s.a.w).
Na farko: Wasu mutane ne wadanda a hannunsu akwai bulala, kamar bindin shanuwa, suna bugun mutane da wannan bulalar,(malamai sunyi fassara biyu, na farko sukace ana nufin azzaluman shuwagabanni, na biyu sukace yan fashi da makami da duk wani mai zalunci). Annabi yace suna daga cikin yan wuta.
Na biyu: sune yan mata wadanda suna sanye da tufafi amma a hakikanin gaskiya tsirara suke! Saboda tufafin bai rufe abunda akeson ya rufe ba(wato suna sanya tufafi Wanda ke bayyanar da tsiraicinsu) kamar hijaba dai gyale na zamani irinsu; show me your back, show me your breast, show me your chest, ustazu baida rabo, baba na balaga da sauransu, wannan duk haramun ne a musulunci!
Annabi ya cigaba da cewa karkatattu ne, kuma suna karkatar da wasu( wato masu ketare abunda shari'ah ta gindaya musu, suna ketare iyakokin Allah, kuma suna koyar da wasu matan irin wadannan dabi'u nasu.
Kawunansu kamar tozon rakumi ne Wanda yake karkatacce(ma'ana suna tara gashi sosai, sai su kulleshi wuri daya, a turashi gefe guda! A yanzu ka iya cewa a cuci maza da sukeyi).
Ba nan matsalar take ba, irin wadancan mutane Annabi Muhammad s.a.w yace ba zasu shiga Aljanna ba sannan baza suji kamshin aljannar ba, shi kuwa kamshin aljanna ana jinsa daga Nisan wuri kaza zuwa kaza, a wata ruwayar Nisan tafiyar shekara dari biyar.
[Muslim ya ruwaito]
Yar uwa kinason shiga aljanna???
Na roke ki don girman Allah ki ajiye wayewar turawa ki rungumi addininki na musulunci.
Wallahi ina jin zafi a duk lokacin da naga mata suna wata shiga ta fitsara, hankali na na tashi kwarai.
Yar uwa Allah ya gafarta miki, kada ki yarda shaidan ya rinjayeki har ya kaiki ga halaka!
Soyayya da kauna da son mu gudu tare mu tsira tare shine yasa na rubuta wannan takaitacciyar nasiha.
ALLAH YA KARA SHIRYA MANA YAN UWANMU MATA A DUK INDA SUKE A FADIN DUNIYA.
DAN UWANKU A MUSULUNCI.
BABAN_SINAN```
+2348064734911