Saturday, 4 January 2020

HALASCIN SHAFA AKAN SAFA

*SHIN KO YANA HALASTA YIN SHAFA AKAN SAFA*

MALAMAI SUN KASU GIDA UKU AKAN MATSALAR SHAFA AKAN SAFA

*NA FARKO:* MALIK, SHAFI'I DA ABI HANIFA SUN TAFI AKAN BAYA HALASTA, HUJJARSU SHINE
لأن الجورب لا يسمى خفا، فلا يأخذ حكمه.
SABODA ITA SAFA BA'A KIRATA DA SUNAN HUFFI BA, SABODA HAKA BA ZATA DAUKI HUKUNCIN HUFFI BA.

*NA BIYU:* HASANUL BASRY, IBNUL MUSAYYIB, IMAMU AHMAD BN HAMBAL(Imamu AHLIS-SUNNAH WALJAMA'AH) DA WASUNSU, SUN TAFI AKAN YA HALASTA DA SHARA'DIN SAFAR TA KASANCE MAI KAURI, KUMA MAI TSAWO WACCE ZATA IYA RUFE WURIN DA FARILLA NE A WANKE IDAN ANXO ALWALA

*NA UKU:* YANA HALASTA SHAFA AKAN SAFA KO WACE IRI CE, KODA SHARARA CE(Ba tada kauri), WANNAN SHINE MAZHABIN IBN HAZAM, KUMA SHEIKHUL ISLAM IBN TAIMIYYA YA ZABI WANNAN, QARAMIN IBN TAIMIYYA NA WANNAN ZAMANIN, WATO IBN UTHAIMIN YA RINJAYAR DA WANNAN MAGANA TA IBN HAZAM, HAKA IBN BAAZ DA IMAMUSH SHANQIDY DUK SUNA AKAN WANNAN FATAWA TA IBN HAZAMIN

IBN UTHAIMIN (RH) YAYI WATA MAGANA MAI QAYATARWA, GA ABIN DA YACE:

SHAFA AKAN SAFA HADISAI SUNXO AKAN HAKAN, YA INGANTA CEWA SAHABBAI DA DAMA SUNYI SHAFA AKAN SAFA, DA ACE ZAMU QADDARA CEWA MA BA SUNNAH BANE DAGA MANZON ALLAH S.A.W, KUMA BABU ATHAR DAGA SAHABBAI, YACE QIYASI TSAFTATACCE YAYI NUNI DA HALASCIN SHAFA AKAN SAFA,YA CIGABA DA CEWA: SABODA MU MUN SAN HIKIMAR DA TA SA AKA HALASTA SHAFA AKAN HUFFI SHINE SABODA TSANANI DA KUMA TAKURA A WURIN ALWALA(ace duk zakayi alwala sai ka cire)......... HAR ZUWA INDA YACE: SABODA HAKA MUKE GANIN NASSI DA KUMA DUBO(Qiyasi) DUKKANIN SU SUNA NUNI AKAN HALASCIN SHAFA AKAN SAFA

MUGEERA DAN SHU'UBA (RA) YA RUWAITO DAGA MANZON ALLAH S.A.W: YAYI ALWALA SAI YAYI SHAFA AKAN SAFA DA KUMA TAKALMA
(ABU DAUD, KUMA ALBANY YA INGANTA SHI)

YA TABBATA CEWA SAHABBAI DA DAMA SUNA AIKATA SHAFA AKAN SAFA, A CIKIN *SUNAN ABU DAUD* YA KAWO CEWA SAHABBAI DA DAMA SUNYI SHAFA AKAN SAFA, DAGA CIKINSU AKWAI: ALIYU DAN ABI DALIB YAYI SHAFA AKAN SAFA, HAKA IBN MAS'UD, DA BARRA' BN AaZIB, DA ANAS DAN MALIKU, DA ABU AMAMA ALBAHILY, DA SAHAL BN SA'AD ASSA'IDY DA AMRU IBN HAREETH, HAKA AN RUWAITO CEWA UMAR BN KHADDAB DA ABDULLAHI DAN ABBAS SUNA AIKATA SHAFA AKAN SAFA

ABU HANIFA YA KASANCE YANA HANA SHAFA AKAN SAFA, SAI A QARSHEN RAYUWAR SHI YA DAWO AKAN WACCAN FATAWAR,  YACE: YANA HALASTA SHAFA AKAN SAFA, BAI FI KWANA UKU KO BAKWAI BA KAFIN YA RASU YA BADA FATAWAR HALASCIN HAKAN

IMAMUT TIRMIDHI YACE: DA WANNAN FATAWAR TA HALASCIN SHAFA AKAN SAFA SU SUFYAN ATHAURY DA IBNUL MUBARAK DA AHMAD DA ISHAQ SUKA TAFI

انتهى

*ليهلك من هلك عن بينة ويحي من حي عن بينة*

#ABU_SINAN
+2348064734911

Https://fb.me/abbansinan

HUKUNCIN HADE SALLOLI A LOKACIN SANYI

*MINENE GASKIYAR MAGANA AKAN HADE SALLOLIN AZHR DA LA'ASAR KO MAGRIB DA ISHA'I A LOKACIN SANYI MAI TSANANI???*

Rubutawa: *ABU_SINAN ATS~TSAMAWY*

Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad S.A.W da iyalan gidansa da sahabbansa baki daya.

Bayan Haka:

Yan uwa Yana da kyau mu fahimci cewa ita fa shari'ah tazo mana da sauki a lokacin da aka shiga cikin tsanani, haka tazo mana da saukakawa a cikin ibada a kowane al'amari Wanda a cikinsa akwai wahala da takura wacce take a bayyane. Kamar yadda Allah madaukakin sarki yake cewa:
*يريد الله بكم اليسر ولا يريد بكم العسر...*
Da Kuma inda Allah madaukakin sarki yake cewa:
*وما جعل عليكم في الدين من حرج...*
Duka Wadannan suna nuna Mana cewa addinin Allah sauki ne dashi.
Yazo a cikin sahihul bukhari, Hadisin da Abi Hurairah ya ruwaito, Manzon Allah S.A.W yace: *_"Lallai shi addini sauki ne, babu Wanda zai dauki addini da tsanani face sai addinin ya rinjayeshi...."_*

Allah madaukakin sarki Yana son mu karbi sauki daga gareshi a lokacin da ya saukaka Mana, ko a cikin abubuwan da ya saukaka Mana.
Ya tabbata a Sunnah, saukakawa a cikin ibada a lokacin da ake zaune gida da lokacin tafiya a wani yanayi kebantacce. Daga cikin abin da ya tabbata na saukakawa akwai *sanyi Mai tsanani ga mutane.*

Dalilin hakan shine saboda gudun kada mutum ya kamu da rashin lafiya a rayuwarsa.
Amma sanyi Wanda baya cutarwa baya halasta, hukuncinsa kamar hukuncin sauran sanyi ne na jin dadi da more rayuwa.

*AN RANGWANTA YIN SALLAH A GIDA KAMAR YADDA AKA RANGWANTA HADE SALLOLI A LOKACIN SANYI MAI TSANANI*

An rangwanta ma Wanda sanyi Mai tsanani ya shafa da yayi Sallah a gidansa, ya bar jama'ah a masallaci. Dalilin hakan shine abin da Nafi' ya ruwaito cewa: *_"ibn Umar ya kira Sallah a wani dare Mai sanyi a wani gari ko wuri da ake Kira DHAJNAN, Sannan yace: kuyi Sallah a cikin gidajenku, sai ya bamu labari cewa: Manzon Allah S.A.W Yana umurtar  ladan ya kira Sallah Sannan ya sashi ya fadi cewa: KUYI SALLAR KU A DAKUNAN KU. A dare Mai sanyi, ko lokacin da sukayi doguwar tafiya."_*[Bukhari da Muslim]
Haka Abu Daud yayi babi a cikin littafin shi, sunan babin: *_BABIN DAKE MAGANA AKAN RABUWA DA JAMA'AH A DARE MAI SANYI._*
Haka Babban Malami *Ibn Qudama* a cikin littafin shi Mai suna: المغني yace: *_Anyi uzuri ga barin jama'ah saboda tsananin iska a dare Mai duhu Kuma Mai sanyi._*

Haka Muslim ya fitar a cikin littafin shi, daga Ibn Abbas (R.A) yace: *_"Manzon Allah S.A.W yayi sallar azhr da la'asar a lokaci guda, magrib da isha'i a lokaci guda ba tare da akwai tsoro ba, ba tare da yayi tafiya ba, ba Kuma ruwan sama akayi ba. An tambayi Ibn Abbas: me yasa yayi hakan toh? Sai yace: Yana nufin kada ya tsananta ma al'ummarshi ne."_*

Saboda haka abin da yake ingantacce shine, ana hade sallolin azhr da la'asar ko magrib da isha'i a lokacin da sanyi ya tsananta.

Haka imamu Ahmad ya ruwaito cewa: *_"Abdullahi Dan Umar ya kasance yana hada salloli a daren da ake tsananin sanyi."_*

Abin da yake na dai dai ga musulmi shine ya saukaka ma kanshi da saukakawar mahaliccinshi, kada ya tsananta ma kanshi ko al'ummarshi.

Akwai maganganun malaman mazhabobin Malikiyya da Shafi'iyya da Ahmad da Abu hanifa akan wannan matsalar. Mazhabin Abu Hanifa kadai ne ya sabawa sauran mazhabobin, shi Abu Hanifa ma yana ganin cewa baya halasta a hade wata Sallah idan ba a arfa ba(Azhr da la'asar) ko muzdhalifa(Magrib da isha'i)

Amma sauran mazhabobin guda uku duk sun yarda a hade salloli saboda tsananin sanyi, inda suka danyi sabani shine wasu na ganin cewa ba za'a hade azhr da la'asar ba wasu Kuma sunce har su za'a hade matukar sanyin da ake ya tsananta.

ALLAH MADAUKAKIN SARKI SHINE MASANI.

#ABU_SINAN
+2349030201868

https://fb.me/abbansinan