🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI*
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Wallafar: *Ash-Sheikh Muhammad Sani Liman Tsafe(ABU HURAIRAH)*
_006_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
✅ *ABUBUWAN DA SUKE TAIMAKAWA WAJAN SADAR DA ZUMUNTA*
Akwai abubuwa da yawa da suke taimakawa mutum wajan sadar da zumunta.
Ga kadan daga cikinsu kamar haka:
1. Yin tunanin manya-manyan darajoji da suka tabbata ga mai sadar da zumunta: Lallai sanin kyakykyawan sakamakon aiki da kuma hango kyakykyawan karshe dake samun mai sadar da zumunta yana taimaka maka wajen sadar da zumunta.
2. Nazari akan mummunan karshe ga mai yanke zumunta:
kula da abin da yanke zumunci yake janyowa na bakin ciki da damuwa da hasara, da nadama da sauransu, yana taimakawa mutun ya nisanci yanke zumunta ya kuma sadar da ita.
3. Neman taimakon Allah:
Wannan yana tabbata ne ta hanyar rokon Allah ya datar da kai ya kuma taimake ka bisa sadar da zumunta ga yan uwanka.
4. Maida mummuna da kyakykyawa:
Yana daga cikin abin da yake wanzar da soyayya da kuma kiyaye zumuncin dake tsakin yan'uwa shine musanya mummuna da kyakykyawa. Karbar uzurinsu idan sun yi kuskure da kuma basu uzuri. Yana daga mafi kyawon abin da zan fada acikin wannan shine abin da ya gudana tsakanin Annabi Yusuf da yan'uwan sa, hakika sun aikata abin da suka aikata amma yayin da suka bada uzuri ya karbi uzurinsu ya musu rangwame mai kyau, bama wannan kadai ba, har addu’a yayi musu kuma ya roki Allah ya gafarta musu.
5. Yi musu rangwame da kauda kai daga aibobansu koda basu baka uzuri ba:
Wannan yana daga cikin abin da yake nuna karamcin mutum da kuma girman himmarsa, mai hankali tatacce yana yin rangwame da kau da kai daga ambaton aiboban yan'uwansa, baya ambaton laifukan su ko da kuwa basu bada uziri ba.
6. Kan-kan dakai da saukin ma’amala:
Wannan yana daya daga cikin abubuwan da suke sanya soyayyar yan uwa ga dan uwansu kuma su kusance shi.
7. Nisantar husuma da yawan jayayya da jidali ko fada da yan uwa.
8. Barin yi masu gori da neman sai sun ran kamaka:
ya zama dole mutun ya bar yima yan'uwansa gori idan ya basu wani abu ko ya ziyarcesu, ko ya basu wata kyauta da dai sauransu.
10. Juriya da daukar duk wani aibantawa daga yan'uwa:
Lallai wannan yana daga cikin abubuwa mafi kyau, shine mutun ya kauda kai yayi hakuri da duk wata suka ko tsegumi da yan’uwansa suke mashi, saboda shedan na shige da fice don ganin ya haifar da matsala a tsakanin yan'wa.
11. Gaugawar aikawa da kyauta idan aka samu sabani a tsakanin yan’uwa:
Kyauta tana janyo Soyayya da kaunar juna, sannan kuma tana hana mummunan zato. Saboda Annabi (SAW) yace; ''KUYI KYAUTA KU SO JUNA''
12. Kwadayin kawo gyara da sulhu a tsakanin yan'uwa idan an samu sabani:
Yana daga cikin abin da ya kamata ga duk masu hankali da natsuwa shine su yi sauri su kawo gyara da sulhu idan wata matsala ta taso a tsakanin yan'uwa, domin idan ba’ayi haka ba sharrin yana iya game kowa.
13. Gaggauta rabon gado:
Ya kamata idan aka samu rasa rai a gida na uba ko na uwa a gaggauta raba gado domin kowa ya amshi rabonshi, wannan yana kawar da rigima da yawan neman sai anraba kuma wannan yana kara dankon zumunci a tsakain yan’uwa.
14. Shirya taro na wata-wata ko shekara-shekara:
Lallai ire-iren wadannan tarukka suna dauke da alherai masu yawa domin a nan ne za’a san juna a sadar da zumunta ga juna, a yima juna wassiya da dai sauransu.
15. Kaddamar da gidauniya ko kafa asusu:
Yana daga cikin abin da ke karfafa zumunta, shine samar da gidauniya ko wani asusu da za'a rika tara kudi duk wata ko shekara domin tallafawa yan'uwa. Da wannan gudunmawa da aka bada za'a iya tallafawa yan'uwa idan wasu matsaloli sun tunkaresu.
16. Kwamitin masu bada shawara:
Yana da kyau a samar da kwamito ta wadanda zasu rika bada shawara a karkashin kwamitin zumunta, kamar kwamitin ilimi, Kwamitin sulhu, da sauransu. Ta haka ne kowa zai san hakkinsa da kuma hakkin yan'uwansa a kansa.
17. Kula da halayensu da ba kowa matsayinsa:
Akwai daga cikin yan'uwa wanda yake yarda da kadan daga sadarwar da akayi masa, koda a shekara za’a ziyarceshi sau daya, koda ta wayar salula ne, wani ma ko da sakin fuskane da kuma Magana. Akwai wanda bai yarda da komai sai ziyara ako da yaushe. Duka wadannan a kula dasu saboda zumunta ta tabbata.
18. Sadar da zumunta don Allah:
Zumunta Ibada ce mai girma don haka ana sadar da ita ne don Allah shi kadai bashi da abokin tarayya, kamar yadda Allah (SWT) yake fada: ''KUJI TSORON ALLAH DA KUKE ROQON JUNA DASHI, KUMA KU KIYAYE ZUMUNTA. [Nisa'i aya ta 1]
Hakikanin mai sadar da zumunta don Allah shine mai sadar da zumuntar sa ga yan uwanshi ko sun sadar mashi ko basu sadar mashi ba, kamar yadda Bukhari ya ruwaito cikin sahihin littafinsa, manzon Allah (SAW) yana cewa: ''BAI ZAMA MAI SADAR DA ZUMUNTA BA, WANDA SAI AN SADAR MASHI SANNAN YA SADAR, HAKIKANIN MAI SADAR DA ZUMUNTA SHINE WANDA IDAN AN YANKE MASHI SAI YAYI KOKARIN SADARWA''. [Bukhari 5991]
A NAN ZAMU DAKATA SAI A LOKACI NA GABA INSHA ALLAHU
DOMIN CIGABA DA SAMUN WANNAN RUBUTU KUNA IYA AIKEWA DA SAQON WHATSAPP ZUWA GA: +2349030201868 DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA*
#ABBAN_SINAN
https://fb.me/abbansinan