🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴
*_IBN TAIMIYYA BAI YARDA DA BIDI'AR MAULIDI BA, HASALI MA YAYI FADA DA ITA..._*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
**
**
**
**
_002 fitowa ta biyu_
_Rubutawa:_ *_Hashim Surajo Uba Tsamiya(ABU SINÃN)_*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
```Godiya ta tabbata ga Allah shi kadai, tsira da Amincin Allah su tabbata ga Wanda babu wani Annabi bayansa, tare da iyalan gidansa da sahabbansa da duk Wanda ya bi tafarkinsa da kyautatawa.
Bayan haka;
Kamar yadda shimfida ta gabata akan wannan posting, yanxu kai tsaye zanje ga maganar ibn Taimiyya wacce ya fada har yan bidi'ah ke ganin hujja ne garesu.
Ibn Taimiyya a lokacin da yake ambaton nau'o'in da suka shafi lokaci ga abin da yake cewa;```
((وكذلك ما يحدثه بعض الناس إما مضاهات للنصارى في ميلاد عيسى عليه السلام وإما محبة للنبي صلى الله عليه وسلم وتعظيما له. والله قد يثيبهم على هذه المحبة والإجتهاد لا على البدع من اتخاذ مولد النبي صلى الله عليه وسلم عيدا، مع احتلاف الناس فى مولده-))
_Ma'ana;_ *_"Haka ma abin da wasu mutane suka 'kir'kira ko dai don koyi da nasara ga kirsimeti ko kuma don son Annabi da girmamawa gareshi, Allah zai iya basu lada akan wannan son da suke yiwa Annabi ba akan bidi'ar bukin maulidi ba, duk da malamai sunyi sabani akan ranar da aka haifeshi..."_*
```Ya kai Dan uwa mai karatu ko kasan ma'anar wannan magana ta ibn taimiyya?
Hakika manyan Malamai sunyi maganganu akan wannan magana ta ibn taimiyya, daga ciki akwai wadanda sukayi Raddi ga ibn taimiyya, kamar sheikh Al-Tuwaijiri a cikin littafinsa(ARRADUL QAWIY) bayan ya kawo wannan magana ta sheikhul Islam sai yace; "Sai na CE: A nan akwai magana".
Haka sheikh Muhammad Ahmad ALFAQIHI-Allah yayi masa rahama- shima yayi irin wannan maganar.
Amma sheikh ibn uthaimin ya ba wannan magana ma'ana mai kyau a cikin littafinsa(ALQAULUL MUFID ALA KITABUT TAUHID) inda yake cewa;```
*((ولو حسن قصد الفاعل: أي إن االبدعة شر ولو حسن قصد فاعلها، ويأثم إن كان عالما أنها بدعة ولو حسن قصده، لأنه أقدم على المعصية كمن يجيز الكذب والغش ويدعي أنه مصلحه، أما لو كان جاهلا فإنه لايأثك، لأن جميع المعاصي لايأثم بها إلا مع العلم، وقد يثاب على حسن قصده، وقد نبه على ذلك شيخ الإسلام ابن تيمية في كتابه[اقتضاء الصراط المستقيم] فيثاب على نيته دون عمله، فعمله هذا غير صالح ولامقبول عند الله ولامرضى، لكن لحسن نيته مع الجهل يكون له أجر، ولهذا قال صلى الله عليه وسلم للرجل الذي صلى وأعاد الوضوء بعد ما وجد الماء وصلى ثانية:"لك الأجر مرتين" لحسن قصده، ولأن عمله عمل صالح في الأصل، لكن لو أراد أحد أن يعمل العمل مرتين مع عمله أنه غير مشروع، لم يكن له أجر لأن عمله غير مشروع لكونه خلاف السنة، فقد قال النبي صلى الله عليه وسلم للذي لم يعد: "وأصبت السنة" [صحيح أخرجه أبو داود ٣٣٨] فإن قال: إني بهذه البدعة أحيي الهمم والتنشيط وما أشبه ذلك. أجيب: بأن هذا الإرادة طعن في الر سالة الرسول الله صلى الله عليه وسلم لأنه اتهام له بالتقصير أو القصور، أي مقصر في الإخبار عن ذلك أو قاصر في العلم، وهذا أمر عظيم وخطر جسيم ولأن هذا لم يكن عليه الرسول صلى الله عليه وسلم ولا خلفاؤه الراشدون. أما إذا كان حسن القصد ولم يعلم أن هذا بدعة، فإنه يثاب على نيته ولايثاب على عمله، لأن عمله شر حابط كما قال النبي صلى الله عليه وسلم: "من عمل عملا ليس عليه أمرنا، فهو رد" [صحيح أخرجه مسلم ١٣٤٤]. وأما العامة الذين لايعلمون، وقد لبس عليهم هذه البدعة، وغيرها، نقول: ما دامو قاصدين للحق ولا علموا به! فإثمهم على من أفتاهم ومن أضلهم...))). {القول المفيد على كتاب التوحيد ٣٨٧-٣٨٥}*
_Ma'ana;_ *_"Bidi'ah sharri ce koda mai aikatata ya kyautata niyya kuma zai samu zunubi idan yasan bidi'ah ce yake aikatawa ko da ya kyautata niyya, kamar Wanda zai halattar da karya da Algusshu da sunan maslaha, amma da bai San cewa wannan aiki bidi'ah bane, to bashi da laifi, domin babu laifi akan aikin da aka aikata akan rashin sani, kuma ana iya ba mutum lada akan kyakykyawar niyyarsa kamar yanda sheikhul Islam ya fadakar a cikin littafinsa(IQTIDHA'UL SIRA'DUL MUSTAQEEM) sai aba mutum lada akan niyyarsa ba akan aikinsa ba domin aikinsa ba na kwarai bane, kuma ba karbabbe bane a wurin Allah, sai dai saboda kyawon niyyarsa tare da jahiltar hukuncin sai ya zama ya samu lada, don haka ne ma Annabi Muhammad s.a.w yace ga mutumin da yayi sallah da taimama bayan ya samu ruwa sai yayi alwala ya sake sallah:'kana da lada biyu' saboda kyawon niyyarsa, kuma asalin aikinsa aiki ne mai kyau, sai dai yanxu da mutum zai aikata wani aiki sau biyu kuma ya San cewa shari'ah bata bada damar aikata haka ba, to bashi da lada saboda ya sabawa sunnah, hakika Annabi Muhammad s.a.w yace ga dayan da bai sake sallah ba; 'ka dace da sunnah' [Abu daud 338]. Da wani zai ce; 'Na aikata wannan bidi'ah ne domin Karin himma da nishadi da abin da yayi kama da haka. Za'a bashi amsa da cewa; irin wannan nufi naka suka ne ga manzancin Manzon Allah s.a.w domin tuhumarsa ne da kasawa ko rashin isar da sako ga wannan aiki, kuma wannan al'amari ne babba kuma mai hadari. Amma idan ya kyautata niyya kuma bai San wannan aiki bidi'ah ne ba, to za'a bashi lada akan niyyarsa amma ba akan aikinsa ba, domin aikinsa sharri ne kuma lalatacce ne kamar yadda Manzon Allah s.a.w yace: 'duk Wanda ya aikata wani aiki Wanda ba umurninmu a ciki an mayar masa [Muslim 1344] amma gama garin mutane da basu da ilimi kuma aka samu wasu suka rudesu akan wannan bidi'ah da waninta da sunan son Annabi ko da sunan abu ne mai kyau to su matukar suna yine tsakaninsu da Allah kuma basu da ilimi to laifinsu yana akan Wanda ya batar dasu..."_*
[ALQAULUL MUFID ALA KITABUT TAUHID, 1/385-387]
```Wannan ya nuna cewa matukar kasan Abu baida kyau, amma kace kai sai ka aikata toh tabbas kana da zunubin aikatawar, ko kuma maluman Sunnah sunyi maka Wa'azi sun fadakar amma ka kiyin amfani da nasihohinsu saboda son zuciya to tabbas karshen Alewa kasa a cigaba da tafiya sai kowa ya fahimci wake kan gaskiya da kuma Wanda yake akan bata.
Allah ka tabbatar damu akan bin sunnar Annabi Muhammad s.a.w da aiki da ita.
SAI MUN HADU A FITOWA NA GABA INSHA ALLAHU...```
Copyright©
*_Hashim Surajo Uba Tsamiya (ABU SINÃN)_*
📞08064734911📞
Https://mobile.facebook.com/hashimusurajo.tsamiya
atstsamawy@gmail.com
Http://hashimtsamiya.blogspot.com