Monday, 27 November 2017

HALASCIN SALLAH DA TAKALMI A MUSULUNCI

```HALASCIN SALLAH DA TAKALMI

Hadisi ya tabbata cewa An tamabayi Anas bn
Malik "shin ko Manzon Allah s.a.w ya kasance
yana SALLAH da Takalminshi???" Sai ya amsa
musu da cewa Ehhh.
Sahihul bukhari [1/494]
A wani Hadisin Annabi Muhammad s.a.w cewa
yayi" Ku saba ma yahudawa, domin su basu
SALLAH da Takalminsu ko huffinsu.
[Abu daud da ibn hibban suka fitar, imamush-
shaukany yace; babu wani abu na suka a cikin
wannan hadisin, domin sabawa yahudawa abune
Wanda shari'ah tayi umurni da hakan a wurare da
dama.]
Amma fa ba wai munce wajibi bane!!!, A'a
Sunnah ce ta Annabi Muhammad s.a.w kuma
Malamai sunce mustahabbi ne yin SALLAH da
takalmi.
Kada wani yace ABU SINAAN yace wajibi ne!!!
Amma ya kamata ka Dan raya wannan sunnar
koda sau daya ne, amma fa kada kaje masallacin
anguwarku Wanda basu san da wannan sunnar
ba kace zakayi musu SALLAH da takalmi!!! Idan
sukayo waje da kai toh laifinka ne kuma kai ka
janyo!!!

Allah ya tabbatar damu akan Sunnah.

ABU SINAN
Hashim Siraj Uba Tsamiya```

KISHIN MATA

.
*MACE BA'A TABA YI MATA KISHIYA*
*TA KIRKI*

1● In ka auro *USTAZIYA,* tace:
Munafukan gari, Allah a baki,
sharri a zuci, in ko ka auro 'yar
gayu tace ta fitsare kafa, ba tada
kamun kai.

2● In ka auro *MAI KYAU* tace
kyalkyal banza, ka auro mara
kyau tace an cuce ka.

3● In ka auro *FARA* tace Sadaka
Yalla ko Hasken Ambi, in baka ce
tace Bayan Tukunya.

4● Ka auro daga *DANGINTA* tace
kana son bata zumunta, in kaje
wani gun tace Tsintattar Mage.

5● Ka auro *yar makota,* tace
wadda ta gama sanin sirrimmu?,
in kaje nesa tace baa san asalinta
ba.

6● In ka auro *Babba,* tace an
kwaso kwashi kwaraf, in ko
karama tace girma ya fadi.

7● In ka auro *KAWARTA* tace duk
matan duniya?, don cin fuska da
cin amana?, in ko ka auri 'yar
aikin gidan, tace Tir !, wai iyakar
wulakanci ke nan, kuma baka da
taste.

8● Ka auro *YAR MANYA* tace: Kuda
wajen kwadayi akan mutu, in
'yar talakawa ka auro tace: Allazi
Wahidin, Allah baku mu samu.

9● In ka auri  *YAR AMININ KA* tace:
Tsohon Banza, yau Baba ya koma
Bobo, in ko abokiyar aikinka a
ofis ka auro, sai tace: Abin boye
ya fito fili.

10● In ka auro mai *ABIN HANNUNTA*, ( wato Business woman)  tace: Kano Jiddah
ko 'yar Dubai, in ko ba mai sana'a
bace, tace an kwaso cima zaune.

11●  In ka auro *YAR MALAMAI* tace
asirce ka aka yi ba yinka bane, in
ko 'yar bata da karatu, sai tace
gidansu ko sallah baa iya ba.

12● In ka auro daga *DANGINKA*
tace ana son a hade kai a ware
ta, in kuwa bazawara ka auro, sai
tace: In kaga godiya da sirdi, to
wani ta kayar kuma wani mai
gigi zata sake kayarwa..........
_
Yaushe kenan zaa auro kishiya ta
kirki?
_
WAI ME YA SA mata basa SON
KISHIYA NE?