Saturday, 23 November 2019

020 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MU KYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa na Ashirin 020_

Gabatarwa: *Farida bintu salis*

*FASALI NA BIYU*

*CIKI NA ZAMANIN HAILA DA GWARGODONSA.*

Zance acikin wannan fasalin yana da matsayi guda 2.

*MATSAYI NA FARKO:*  A cikin shekarun da haila take zuwa acikin su.

*MATSAYI NA BIYU:*  A cikin lokacin Haila.

Amma shekarun da haila tafi rinjaye acikinsu MATSAYI NA FARKO shine: tsakanin
shekara 12 Zuwa shekara 50, amma ana samu sau da yawa mace tana yin haila a kafin
haka ko bayan haka gwargodon halinta da tasowarta da kuma tsufanta. Lallai malamai
sunyi sa6ani akan shin shekarun da haila take zuwa aciki suna da iyaka da aka ayyana ta
yadda mace ba zatayi haila gabanninsu ba ko bayansu. Kuma shin jinin da yake zuwa ga
mace a gabanninsu ko bayansu jinin haila ne ko na cuta? Malamai sunyi sa6ani acikin
wannan.
Darimiy yace: Bayan ya kawo sabanin: dukkan wadannan kuskure ne awajena domai a
baki dayan wannan yana komawa ne izuwa samuwar jinin, duk jinin da ya samu a kowani
hali da shekaru, ya wajaba a sanya shi a matsayin haila. Wallahu a'alamu. (Al-majmu'u
sharhil Muhazzab 1/336)
Wannan abunda Darimiy ya fada shine daidai, kuma shine za6in Sheikhul Islam Ibn
Taimiyyah. Wato duk sanda mace taga haila to ita mai haila ce koda bata cika shekara 9
ba ko kuma ta wuce shekara 50. Wannan kuwa saboda ALLAH da Manzonsa (SAW) sun
rataya hukuncin haila ne bisa suwarsa. Kuma ALLAH da Manzonsa (SAW) basu iyakance
wasu ayyanannun shekaru ba game da wannan ya wajaba komawa zuwa sumuwar jinin
wanda aka rataya hukunce hukunce a kansa. Iyakance shi da ayyanannun shekaru yana
buqatar dalili daga Qur'an ko sunnah. Gashi kuwa babu dalili akan haka.
Amma MATSAYI NA BIYU: Shine gwargodon Haila wato gwargodon zamaninta, haqiqa
malamai sunyi sa6ani mai yawa a kusan zantuka guda 6 koma 7.
Ibnul Munzir Yace: "wata jama'a tace: babu wata iyaka ta kwanaki ga mafi qarancin Haila
ko mafi yawanta"sai nace: wannan magana kamar maganar Darimiy ce wacce ta gabata,
haka kuma shine za6in Sheikhul Islam Ibn Taimiyyah kuma shine dai dai domin qur'ani
da sunnah da kuma abunda ake gani yau da gobe, sun nuna hakan.

ZAMU CIGABA INSHA ALLAHU

https://fb.me/abbansinan