Saturday, 21 December 2019

ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI

ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI

NA

SANI LIMAN TSAFE
(ABU HURAIRA)
07059593000

    BUGU NA FARKO

WANDA YA DAUKI NAUYIN BUGAWA
Alh. Tambaya Tsafe
(ALLAH YA GAFARTA MASHI)

17 /11/1438

ABUBUWAN DA KE CIKI

    GABATARWA
MECE CE ZUMUNTA

DA WANE ABU AKE SADAR DA ZUMUNTA

FALALAR SADAR DA ZUMUNTA

HADARIN DA KE CIKIN YANKE ZUMUNTA

SABUBBAN DA KE JANYO YANKE ZUMUNTA

ABUBUWAN DA KE TAIMAKAWA WAJAN SADAR DA ZUMUNTA

FALALAR SADAR DA ZUMUNTA GA ABOKAN IYAYE

YAYA ZA`A MAGANCE MATSALAR YANKE ZUMUNTA

YANKE ZUMUNCI YANA DAGA CIKIN ALAMOMIN TASHIN AL-QIYAMA

بسم الله الرحمن الرجيم
                          
                             GABATARWA

Godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata'ala wanda ya fitar da sunan zumunta daga sunanshi, kuma ya tsoratar da al'umma daga yanketa, kuma na shaida babu wanda ya cancanta a bautamawa da gaskiya sai Allah(subhanahu wata'la) shi kadai yake ba shi da abokin tarayya.
Kuma na shaida Annabi Muhammad (salallahu alaihi wasallam) bawan Allah ne kuma manzonsa ne, kuma shine wanda yafi kowa sadar da zumunta a duniya. Tsira da amincin Allah su tabbata gareshi da alayensa da kuma sahabbansa da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka dalilin da yasa na rubuta wannan littafi kasantuwar samar da kwamitin zumunta da akayi a gidan LIMAN DAN BAWA TSAFE shi yasa na wallafa wannan littafi domin yan'uwana su amfana da sauran al'ummar musulmi baki daya. Duk abin da aka gani na dai dai cikin wannan littafi, datarwa ce ta Allah(subhanahu wata'ala), abin da kuma aka samu na kuskure daga gareni ne saboda karancin ilimi, muna rokon Allah(subhanahu wata'ala) ya yafe mana.

                                                          MAWALLAFI:
                                                              SANI LIMAN TSAFE
                                                               (Abu Hurairah)
                                                           Zamfara State
                                                          16/03/1441AH
                                                            14/11/2019

MECE CE ZUMUNTA 
IBN ATHEER yana cewa: Zumunta tana nufin taimakawa yan uwa na bangaren dangantaka da sarakuta da kula da halayen su koda kuwa suna zaune a wurare masu nisa koda kuma suna munana maka (a daya bangaren kuma yanke zumunta yana nufin kishiyar abubuwan da aka ambata a baya)
DA WANE ABU AKE SADAR  DA ZUMUNTA  
       Ana sadar da zumunta da al’amura masu yawa kamar ziyartarsu,                                                 bibiyar halayansu, tambaya game dasu, aika masu da kyaututtuka da kuma saukar da kowannensu a matsayin da ya dace dashi, da bada sadaka ga fakirai daga cikinsu, da tausasa ma mawadatansu(Binsu a hankali) da girmama manyansu, da kuma tausaya ma kananansu, da masu rauninsu, da yawan tambayar halin da suke ciki, da kuma ziyartarsu da kanka ko ka aika wasika ko kayi amfani da wayar salula.
Mafi girman abin da ake sadar da zumunta da shi shine yin wa'azi garesu, kamar yadda Allah madaukakin sarki yake fada wa manzonshi cewa: (KAYI GARGADI GA DANGINKA MAKUSANTA) [shu'araa 214]
   Haka kuma Manzon Allah (salallahu alaihi wasallam) ya rinka kiran danginsa domin ganin sun shigo addinin musulunci.
Saboda haka mutum yayi kwadayin kiran yan uwansa zuwa ga shiriya ya umurce su da aiki mai kyau, ya kuma hane su da aikata miyagun ayyuka.
Zumunta tana bambanta gwargwadon  kusanci da matsayi na wadanda ake sadar da zumunta zuwa garesu,  zumunci da yake tsakanin uba da dan-dansa yana da bambanci da dan-dan dan uwa na nesa. 
Bugu da kari, zumunta tana bambanta gwargwadon halayen wadanda za’a sadarmawa suke ciki kamar sadar da zumunta ga marar lafiya da mabukaci ta bambanta da sadarwa ga waninsu. Haka ma sadarwa ga babba ta bambanta da ta karami.
Haka sadar da zumunta yana bambanta ta fuskar bigire, wanda yake zaune a cikin gari ya bambanta da wanda yake zaune a wani gari wajen ziyartar shi, tambayar halin da yake ciki, da yi masa sallama ko aika mashi da sakonni.

FALALAR SADA ZUMUNTA
  Sadar da zumunta yana da tarin falala mai yawa kadan daga ciki sun hada da: 
Sadar da zumunta alama ce dake nuna cewar bawa yayi imani da Allah da kuma ranar lahira.  kamar yadda hadithin  da Abu Huraira ya riwaito daga manzon Allah (SAW) yace: ''Duk wanda  yayi imani da Allah da kuma Ranar Lahira to ya  Karrama Bakonsa, haka nan wanda yayi imani da Allah da ranar lahira to ya sadar da zumuntarsa (Buhari ya riwaito shi 6138”).
Lallai sadar da zumunta sababine na yalwar arziki da kuma tsawon rayuwar dan adam da kuma samun albarka a cikin su.
         An karbo hadithi daga Anas (R) yace manzon Allah, yace:''Duk wanda yake so a shimfida arzikinsa a kuma jinkirta masa rayuwarsa to ya sadar da zumuntarsa'' (Buhari 5986- Muslim 2557)”.
Abdullahi dan Umar (R) yace ''Duk wanda ya kiyaye  ubangijinsa , ya sadar da zumuntarsa  to za’a jinkirata masa ajalinsa, kuma dukiyarsa zata yalwata, sannan iyalansa zasu so shi.” (Tirmizi-1979- Buhari  adabul mufrad-58).
3. Sadar da zumunta yana janyo sadarwar Allah ga wanda ya sadar da ita.
      Abu Huraira ya ruwaito hadithi daga manzon Allah (SWA) yace ''Lallai Allah ya hallicci dukkan halitta bayan ya kammala sai zumunta ta tashi sai tace nan ne matsayin da zan nemi tsari daga wanda ya yanke ni?  Sai Allah (SWA) yace eh; shin ko kin yarda in sadar ma wanda ya sadar dake in kuma  yanke ma wanda ya yanke ki?  Sai tace eh, sai Allah yace haka zai kasance gareki''. (Bukhari -5987- muslim 2554).
4.  Sadar da zumunta yana daya daga cikin manyan sabubban da ke shigar da mutun Aljanna. Abu Ayubal Ansari yace ''Lallai wani mutum; yace  ya manzon Allah ka ba ni labarin aikin da zai shigar dani aljanna kuma ya nisanta ni daga shiga wuta, sai manzon  Allah yace ''ka bauta ma Allah kada ka hadashi da komai a wajan bauta, ka tsaida  sallah, ka bada zakka, ka sadar da zumunta. (Bukhari 1396-muslim 13)
5. sadar da zumunta yin da'a ne  ga Allah da Manzonsa,  Allah (SWA) ya fada a cikin Alqur’ani yana mai yabon masu sadarda zumunta  “sune wadanda suke sadar da abin da Allah yace a sadar dashi (Zumunci) suna jin tsoron ubanginsu kuma suna tsoron mummunan hisabi ”
  (Suratul Ra’ad 21)
An karbo hadisi daga Abu sufyan a cikin hadisinsa mai tsawo a cikin kissar Hirkala yace ma Abu sufyan mine ne Manzon Allah yake umurtar ku dashi sai Abu sufyan yace: yana cewa ku bauta ma Allah shi kadai kada ku hadashi da komai a wajen bauta, kubar ababen da iyayenku ke fada,kuma yana umartarmu da yin Sallah da riko da gaskiya da kamewa, da kuma sadar da zumunta (Muslim 1883)
6. Sadar da zumunta yana daya daga cikin kyawawan ayyuka a cikin addinin musulunci, Allah (SWT) yana cewa: ''kuba ma’aboci kusanci hakkinsa (ana nufin dan'uwa) (Isra’i 26)
Hakanan a wani wurin yace, kuji tsoron Allah wanda kuke rokon juna dashi kuma ku sadar da zumunta (Suratul Nisa’i 1). Ya kuma kara cewa ku bauta ma Allah kada ku hadashi da komai a wajen bauta, ku kyautatama iyayenku da makusantanku (yan'uwanku na zumunta) da marayu da miskinai da makwabci na kusa.
HADARIN  DA KE CIKIN YANKE ZUMUNTA
Hakika Allah (SWT) da manzonsa (SAW) sun tsoratar dangane da hadarin yanke zumunci, suka sanya matsayin yanke zumunci dai dai da Fasadi/barna a bayan kasa.
Allah (SWT) yace to shin kuna fatan idan kun juya daga (umarnin) zakuyi barna a cikin kasa, kuma ku yanke zumuntarku? Wadannan sune wadanda Allah ya la'anesu, kuma ya kurmantar dasu, kuma ya makantar da ganinsu. (Suratu Muhammad 22-23)
An karbo hadisi daga Aisha (R) manzon Allah (SAW) yace zumunta tana rataye da al’arshin Allah. Tana cewa wanda ya sadar dani Allah ya sadar dashi, wanda ya yanke ni Allah ya yankeshi (Muslim 2555)
An karbo daga MUD’IM (R) manzon Allah (SWA) yace mai yanke zumunta baya shiga Aljanna (Muslim 2556)
Haka nan kuma, an karbo  daga Abubakrata, Manzon Allah yace, Babu wani laifi daya can-canta Allah ya gaggauta ma ma'abocin sa uquba tun anan duniya tare da  cewa yayi mashi tanadin uqubar a lahira kamar wanda ya yanke zumunta da kuma azzalimi (Bukhari adabul mufrad 67)
An karbo daga Abu Huraira; lallai wani mutum yace ya manzon Allah lallai ni ina da yan'uwa kuma ina sadar da zumuntarsu amman suna yanke mani, ina kyautata masu amma suna munana mani, ina yin hakuri dasu amma suna jahiltata? Sai Annabi yace, idan har ka kasance kamar yadda ka fada to lallai kamar kana zuba masu toka ce mai zafi, Allah ba zai gushe ba yana taimakonka akansu matukar ka dauwwama akan haka (Muslim 2558) Ma’ana: kamar kana ciyar dasu toka mai zafi saboda abin da suke haduwa dashi na laifi.
Haka nan kuma an karbo daga Abdullahi ibn Amru binul As, Manzon Allah (SAW) yace, bai zama mai sadar da zumunta ba wanda yake so aranka mashi, sai dai mai sadar da zumunta shine wanda idan an yanke mashi, shi yana sadarwa (Bukhari 541)
An karbo daga salmanu ibn Amir, Manzon Allah yace, yin sadaka ga miskinai sadakace kamar sauran sadakoki, amma yin sadaka ga dan'uwa tana da darajoji biyu (2) ladar sadaka da kuma ladar sadar da zumunci (Abu Dawud 2555-Tirmidhi 658)
An karbo daga Abu Hurairah yace, lokacin da wannan ayar ta sauka,,, kayi gargadi ga yan'uwanka makusanta, Annabi (SAW) ya kira Quraishawa, suka hadu gaba dayansu, yayi musu wa’azi gaba dayansu kuma yayi ma dai-dai kunsu yace ya Fatima ki tsamar da kanki daga wuta, lallai ni bani wadatar daku a wurin Allah da komai sai dai lallai kuna da wata zumunta da sannu zan sadar da ita (Muslim)

8. SABUBBAN DA KE JANYO YANKE ZUMUNTA.
Idan kayi nazari akan sabubban dake janyo yanke zumunta zaka samu cewa akwai sabubba masu yawa. Ga kadan daga cikinsu
1. JAHILCI: Jahiltar mummunan sakamakon da mai yanke zumunta yake samu anan duniya da lahira, ko kuma rashin yin aiki da abin da mutum ya sani. An karbo daga Umar (R) ya kasance akan mimbari yana cewa: ku nemi sanin dangantakarku, sannan ku sadar da zumuntarku wallahi! Lallai zai kasance tsakanin mutum da dan uwansa wata rigima ta hadasu saboda rashin sanin juna, da yasan akwai zumunta tsakaninsu da wannan dalilin na alakar zumunta ya hanashi cin mutuncinsa (Bukhari, Adabul mufrad 73)
2. KARANCIN TSORON ALLAH; Idan tsoron Allah yayi rauni sannan addini yayi saku-saku ba zai damu ba idan ya yanke abin da Allah yayi umarnin asadar, kuma baya kwadayin ladar da ake samu idan an sadar da zumunta kuma baya tsoran mummunan sakamakon da zai same shi a dalilin yanke zumunta.
An karbo daga sa’id bn sam’an, yace: Naji Abu Hurairah yana neman tsarin Allah daga shugabancin yara da wawaye (jahilai) sai aka ce masa mine ne alamar yin haka? sai yace dan za’a dinga yanke zumunta a kuma dinga yin da’a ga mai halakarwa a saba ma mai shiryarwa (Adabul-mufad 66)
3. GIRMAN KAI; Sashen mutane idan mutum ya samu wani matsayi babba ko ya samu wata daukaka ko kuma ya zama babban dan kasuwa sai yayi girman kai ga yan'uwanshi, ya kyamaci ziyartarsu, kuma ya kyamaci zuwa garesu, yana ganin shi ke kan gaskiya kuma shi ya can-canta a ziyarta.
4. YANKEWA MAI TSAWO; A nan akwai wanda yake yanke ma yan'uwansa lokaci mai tsawo al’amarin ya dore akan haka har ya kai ga yanke zumuntarshi dasu gaba daya, har ya saba da yankewa sai yayi nesa dasu. An karbo daga Mikdam, lallai yaji manzon Allah (SAW) yana cewa lallai Allah yana maku wasiyya da iyayenku mata sannan yana maku wasiyya da iyayenku maza, sannan yana maku wasiyya da yan'uwanku (Adabul mufrad 60).
5. AIBANTAWA MAI TSANANI; Sashen wasu mutane idan dan'uwansu ya ziyarcesu bayan a baya ya yanke zumuntarshi dasu lokaci mai tsawo sai su yawaita zar ginshi har zargin yayi tsanani wanda wannan sai yasa shi kaurace masu saboda tsoron mummunan zargi da suke mashi.
6. DORA MA RAI NAUYIN DAYA WUCE QA’IDA; A nan akwai wanda idan dan'uwansu ya ziyarcesu sai su dora ma kansu yin hidindimu da suka wuce karfinsu domin su ga cewa sun karrama dan'uwan nasu sama da karfinsu ko karancin abun hannunsu, wannan shi ke sanya yan'uwan nasu su dinga takaitawa da ziyartarsu domin tsoron kada su dora masu ire-iren wadannan nauye-nauyen. Saboda Annabi yace mafi karancin sadar da zumunci shine sallama mafi girman zumunta shine  sadarma wanda ya yanke maka.
7. KARANCIN KULA DA WADANDA SUKA KAWO MAKA ZIYARA; Akwai daga cikin mutane wanda idan yan'uwanshi suka ziyarceshi baya bayyanar da farin cikinsa akan ziyarar, bai tsayawa ya tattauna dasu ko ya sakar masu fuska, sai dai za ka ga yana bata rai yana kyamarsu, wannan yana zama sanadin yan'uwa ba zasu kara ziyartarshi ba dan tsoron irin wannan wulakancin.
Manzon Allah yace, kada ku wulakanta wani abu na alkhairi ko da sakin fuskane idan ka hadu da dan'uwanka.
8. TSANANIN ROWA; Wasu daga cikin mutane idan Allah ya azurtasu da dukiya mai yawa ko wani matsayi zaka same su suna gudun yan'uwansu, ba wai dan girman kai ba a'ah! Domin jin tsoron kada yan'uwan suyi amfani da wannan damar domin bayyanar da bukatunsu zuwa garesu, ko kuma domin kada ya temakesu. Maimakon ya basu dama idan sun ziyarceshi yakarbi bakuncinsu, ya yalwata masu, yayi masu hidima gwargwadon halinsa,ko kuma ya basu uzuri akan abin da ba ya da ikon yi masu amma sai kaga yana kauda kansa, yana kaurace masu domin kada su rokeshi kamar yadda yake riyawa. Mine ne amfanin dukiya ko matsayi da mutum zai samu idan har zai haramta ma yan'uwansa amfana da ita.
9. JINKIRIN RABON GADO; Hakika zaka samu wasu daga cikin mutane suna jinkirta rabon gado kodai  domin kasala, ko kuma wani daga cikin magadan yana da wani mummunan kuduri game da yan'uwansa ko makamacin haka.
Duk lokacin da aka jinkirta rabon gado to kiyayya da adawa zata watsu tsakaninsu domin idan wannan yana da hali ko yafi karfin gadon wani shi kuma yana bukatar raba gadon domin bashi na shi kason ya samu ya bude kasuwanci ko makamanci haka.
10. MUTUWAR AUREN ZUMUNCI; Hakika mutuwar auren zumunci yana haifar da matsaloli a tsakanin yan'uwa na bangaren miji dana bangaren mata musamman in akwai 'ya'ya a tsakaninsu ko kuma saboda wasu matsaloli da suka shafi sakin auren.
11. NISAN WURIN ZAMA DA KUMA KASALAR ZUWA ZIYARA; Akwai daga cikin mutane wadanda idan gidan su ko garin su yana nesa sai a dinga jin kasalar zuwa ziyartarsu, wanda wannan sai ya nisantasu da yan'uwansu.
Nisan wuri bai kamata ba ya zama dalili na yanke zumunta, musamman wannan zamanin da ake da hanyoyin sadarwa daban daban, Allah ya bamu ikon kulawa da zumunta.
12. MAKWABTAKA A TSAKANIN YAN UWA
Da yawa Makwabtaka tana gadar da yankewar zumunta a tsakanin yan'uwa. Umar Dan khaddab yace ku umurci yan'uwanku su dinga ziyartar yan'uwansu amma kada suyi makwabtaka da juna a gidajensu, sannan sau dayawa kusanci a tsakanin gidajen yan'uwa yana haifar da sashen wasu matsaloli wadanda suke haifar da fada a tsakanin 'ya'yansu wanda wannan yakan zarce har zuwa ga iyayensu sai wannan ya haifar da gaba da yanke zumunci a tsakaninsu.
13. KARANCIN KAUDA KAI DA HAKURI A KANSU:
Sashen wasu mutane suna da karancin kauda kai da kuma hakuri akan abin da yan'uwansu suka yi masu. Wasu yan'uwan da an samu sabani tsakaninsu ko wani kuskure da ya afku sai su yanke zumunta, su kaurace ma yan'uwansu.
14. HASSADA:
     Akwai daga cikin yan’uwa wanda Allah yake azirtawa da ilimi ko wani babban matsayi ko dukiya mai yawa sai ka same shi yana yima yan'uwansa hidima yana kyautata ma su, sannan ka samu sashen yan'uwansa suna nuna masa hassada da kiyayya da haifar da rikici tsakanin shi da su, suna cewa duk abin da yake yi masu ba domin Allah yake yi ba.
15. YAWAN WASA:
    Lallai yawan wasa (da sunan wai abokin wasa) yana haifar da mummunan abu a tsakanin yan'uwa domin wani yana iya fadar kalma mai muni ga dan'uwansa ba tare da ya kula da hadarinta ba agare shi, wannan sai ya gadar da kiyayya da gaba a tsakaninsu a sanadiyyar wannan Kalmar.
16. ANNAMIMANCI DA KARBAR GULMA:
    Akwai da yawa daga cikin yan'uwa wadanda dabi'arsu shine yawo da annamimanci a tsakanin yan'uwa domin su kawo rabuwar kai da gurbata tsakanin yan’uwa wanda wannan yana gadar da yanke zumunta, sai dai abu mafi muni shine karbar gulma da yadda da ita shi ke haifar da yankewar zumunta.
17. SHAGALTUWA DA DUNIYA: Shagaltuwa da duniya da son yawan tara abin duniya yana hana mutun sadar da zumunta, da kuma samun lokacin ziyartar yan'uwansa da nuna soyayyar shi zuwa gare su.
18 MIYAGUN HALAYE NA MATAR SHI: wasu daga cikin mutane ana jarabtarsu da muguwar mata mai mummunan dabi’a mai yawan sukar yan'uwansa, bata son yayi mu’amala da yan'uwansa ko wasu, tana dogewa wajan ganin ta raba shi da yan'uwansa tana hana shi ziyartarsu, da sadar da zumunta zuwa garesu, idan yan uwan sa suka ziyarceshi sai tayi ta fushi tana murtike fuska. Bugu da kari akwai mazajen da suke mika ragamar zumuncinsu ga matarsu sai wanda ta yarda dashi yake sadarmawa, wanda bata yarda da shi ba sai ya yanke ma sa.
19. MANTAWA DA WASU YAN'UWA A LOKACIN WALIMA KO WATA HIDIMA:               Hakika wani daga cikin yan'uwa yakan shirya walima ko wata hidima ya gayyaci yan'uwansa sai ya manta da wani ko wasu, sai su da ba’a gayyata ba su munana masa zato, su nuna kamar an wulakantasu an zabi wasu wadanda suka fisu, wannan  nasa ya kaurace masu da yanke zumunta a tsakaninsu.
      Wadannan sune  kadan daga cikin abubuwan dake janyo kauracewa juna da kuma yanke zumunta. Ya kamata a basu kulawa ta musamman da hattara da fadawa cikinsu.
6. ABUBUWAN DA SUKE TAIMAKAWA WAJAN SADAR DA ZUMUNTA
   Akwai abubuwa da yawa da suke taimakawa mutum wajan sadar da zumunta. Ga kadan daga cikinsu kamar haka:
Yin tunanin manya-manyan darajoji da suka tabbata ga mai sadar da zumunta: Lallai sanin kyakykyawan sakamakon aiki da kuma hango kyakykyawan karshe dake samun mai sadar da zumunta yana taimaka maka wajen sadar da zumunta.
Nazari akan mummunan karshe ga mai yanke zumunta: kula da abin da yanke zumunci yake janyowa na bakin ciki da damuwa da hasara, da nadama da sauransu, yana taimakawa mutun ya nisanci yanke zumunta ya kuma sadar da ita.
Neman taimakon Allah: Wannan yana tabbata ne ta hanyar rokon Allah ya datar da kai ya kuma taimake ka bisa sadar da zumunta ga yan uwanka.
Maida mummuna da kyakykyawa: Yana daga cikin abin da yake wanzar da soyayya da kuma kiyaye zumuncin dake tsakin yan'uwa shine musanya mummuna da kyakykyawa. Karbar uzurunsu idan sun yi kuskure da kuma basu uzuri. Yana daga mafi kyawan abin da zan fada acikin wannan shine abin da ya gudana tsakanin Annabi Yusuf da yan'uwansa, hakika sun aikata abin da suka aikata amma yayin da suka bada uzuri ya karbi uzurinsu ya musu rangwame mai kyau, bama wannan kadai ba, har addu’a yayi musu kuma ya roki Allah ya gafarta musu.
Yi musu rangwame da kauda kai daga aibobansu koda basu baka uzuri ba: Wannan yana daga cikin abin da yake nuna karamcin mutum da kuma girman himmarsa, mai hankali tatacce yana yin rangwame da kau da kai daga ambaton aiboban yan'uwansa, baya ambaton laifukan su ko da kuwa basu bada uziri ba.
Kan-kan dakai da saukin ma’amala: Wannan yana daya daga cikin abubuwan da suke sanya soyayyar yan uwa ga dan uwansu kuma su kusance shi.
Nisantar husuma da yawan jayayya da jidali ko fada da yan uwa.
Barin yi masu gori da neman sai sun ran kamaka: ya zama dole mutun ya bar yima yan'uwansa gori idan ya basu wani abu ko ya ziyarcesu, ko ya basu wata kyauta da dai sauransu.
Juriya da daukar duk wani aibantawa daga yan'uwa: Lallai wannan yana daga cikin abubuwa mafi kyau, shine mutun ya kauda kai yayi hakuri da duk wata suka ko tsegumi da yan’uwansa suke mashi, saboda shedan na shige da fice don ganin ya haifar da matsala a tsakanin yan'wa.
Gaugawar aikawa da kyauta idan aka samu sabani a tsakanin yan’uwa: Kyauta tana janyo Soyayya da kaunar juna, sannan kuma tana hana mummunan zato. Saboda Annabi (SAW) yace; ''KUYI KYAUTA KU SO JUNA''
Kwadayin kawo gyara da sulhu a tsakanin yan'uwa idan an samu sabani: Yana daga cikin abin da ya kamata ga duk masu hankali da natsuwa shine su yi sauri su kawo gyara da sulhu idan wata matsala ta taso a tsakanin yan'uwa, domin idan ba’ayi haka ba sharrin yana iya game kowa.
Gaggauta rabon gado: Yakamata idan aka samu rasa rai a gida na uba ko na uwa a gaggauta raba gado domin kowa ya amshi rabonshi, wannan yana kawar da rigima da yawan neman sai anraba kuma wannan yana kara dankon zumunci a tsakain yan’uwa.
Shirya taro na wata-wata ko shekara-shekara: Lallai ire-iren wadannan tarukka suna dauke da alherai masu yawa domin a nan ne za’a san juna asadar da zumunta ga juna, ayima juna wassiya da dai sauransu.
Kaddamar da gidauniya ko kafa asusu: Yana daga cikin abin da ke karfafa zumunta, shine samar da gidauniya ko wani asusu da za'a rika tara kudi duk wata ko shekara domin tallafawa yan'uwa. Da wannan gudunmawa da aka bada za'a iya tallafawa yan'uwa idan wasu matsaloli sun tunkaresu.
Kwamitin masu bada shawara: Yana da kyau a samar da kwamitota wadanda zasu rika bada shawara a karkashin kwamitin zumunta, kamar kwamitin ilimi, Kwamitin sulhu, da sauransu. Ta haka ne kowa zai san hakkinsa da kuma hakkin yan'uwansa a kansa.
Kula da halayansu da ba kowa matsayinsa: Akwai daga cikin yan'uwa wanda yake yarda da kadan daga sadarwar da akayi masa, koda a shekara za’a ziyarceshi sau daya, koda ta wayar salulane, wani ma ko da sakin fuskane da kuma Magana. Akwai wanda bai yarda da komai sai ziyara ako da yaushe. Duka wadannan a kula dasu saboda zumunta ta tabbata.
Sadar da zumunta don Allah: Zumunta Ibada ce mai girma don haka ana sadar da ita ne don Allah shi kadai bashi da abokin tarayya, kamar yadda Allah (SWT) yake fada: ''KUJI TSORON ALLAH DA KUKE ROQON JUNA DASHI, KUMA KU KIYAYE ZUMUNTA. [Nisa'i aya ta 1]
Hakikanin mai sadar da zumunta don Allah shine mai sadar da zumuntar sa ga yan uwanshi ko sun sadar mashi ko basu sadar mashi ba, kamar yadda Bukhari ya ruwaito cikin sahihin littafinsa, manzon Allah (SAW) yana cewa: ''BAI ZAMA MAI SADAR DA ZUMUNTA BA, WANDA SAI AN SADAR MASHI SANNAN YA SADAR, HAKIKANIN MAI SADAR DA ZUMUNTA SHINE WANDA IDAN AN YANKE MASHI SAI YAYI KOKARIN SADARWA''.  [Bukhari 5991]
7. FALALAR SADAR DA ZUMUNTA GA ABOKAN MAHAIFI DA MAHAIFIYA DA YAN'UWAN MATA KO MIJI
An karbo daga Abdullahi dan Umar yace Manzon Allah (SAW) yace: “Lallai mafi kyakykyawan biyayya shine mutun ya sadar da zumunta ga abokan mahaifinsa” (muslim-2552)
An karbo Daga Aisha (R) tace: ''Ban taba kishi da matan Manzon Allah (SAW) ba irin yadda nike kishi da khadija (R), ban taba Ganinta ba, sai dai Annabi yana yawan ambatonta. Sau da yawa yakan yanka akuya ya raba ya aikawa abokanta, da yawa nikan ce masa kamar babu wata mace a duniya sai khadija! Sai yace “lallai Khadija ta kasance kaza-kaza (ya lissafa abubuwan kirki na ta da yawa) sannan diyana gaba daya duka ita ta haifesu”. (Buhari 3818-muslim 2435).
8. YAYA ZA’A MAGANCE MATSALAR YANKE ZUMUNCI
     Bayanai sun gabata a baya dangane da matsayin yanke zumunta da cutarwarsa ga mutun da irin sabubban da ke janyo yanke zumunta idan abin ya kasance haka lallai ya zama wajibi ga mai hankali ya tsoraci hadarin yanke zumunta, kuma ya nisanci dukkan sabubban da zasu ja shi zuwa ga yanke zumunta.
Abin da ya cancanta a gare shi shine ya sadar da ita dukkan sadarwa, ya kuma san girman sha'anin zumunta yayi kirdadon sabubban da zasu sa shi sadar da ita, ya kiyaye dukkan ladubban da ya kamata ya kiyaye, tare da yan'uwansa.
YANKE ZUMUNTA YANA DAGA CIKIN ALAMOMIN TASHIN ALKIYAMA.
An karbo daga Abdullahi ibn Amru bn As, Yace Manzon Allah (SAW) yace: ''kiyama ba zata tsaya ba har sai alfasha, da neman aikata Alfashar ya bayyana da yanke zumunta da mummunar makwabtaka”. (Ahmad ya ruwaito)
Hakika labarin da Annabi ya bada ya tabbata, domin Alfasha ta watsu a tsakanin mafi yawa daga cikin mutane, ba tare da sun damu da tattauna abubuwan da suke aikatawa na laifukka ba, basu kuma damu da mummunan sakamakon da zasu hadu dashi ba a dalilin yanke zumunta.
Zaka ga dan'uwa ba ya sadarwa ga dan'uwansa sai yankewa da juya baya. Watanni da shekaru suna shudewa alhali suna zaune cikin gari guda basu ziyartar juna, basu sadarma juna, lallai babu shakka wannan yana nuna raunin imanin mutane.
KAMMALAWA
Muna godiya ga Allah (subhanahu wata`ala) wanda daga cikin ni`imominsa ne ya bamu damar kammala wannan littafi mai albarka, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad(salallahu alaihi wasallam) wanda yayi addu`ah da cewa wanda ya sadar da zumunta Allah ya sadar dashi da rahamarsa, wanda kuma ya yanke zumunta ka yankeshi daga samun rahama. ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU

07059593000