Monday, 6 January 2020

JILSATIL ISTIRAHAH DA HUKUNCIN TA A CIKIN SALLAH

🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*JILSATIL ISTIRAHA  DA HUKUNCIN TA A CIKIN SALLAH*
💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐

Rubutawa: *ABBAN SINAN ATS~TSAMAWY*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, muna gode masa, muna neman taimakonsa, muna neman gafararsa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu, duk Wanda Allah ya shiryar babu Mai batar dashi, Wanda Kuma ya batar babu Mai shiryar dashi. Kuma na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Kuma na shaida cewa Annabi Muhammad S.A.W bawan Allah ne Kuma Manzonsa ne.

Bayan haka:

Yaa Kai Dan uwana Kuma masoyina:

Wannan matsalar tana daga cikin mats'aloli Wadanda keda ala'ka da Sallah, wato(jilsatil istirahah), malamai sunyi sabani(Allah yayi masu rahama 👏) akan hukuncinta, da hukuncin wasu mas'aloli dake da ala'ka da ita.
Kowanne daga cikin malaman yana da dalilai akan abin da ya tafi akan shi.

Saboda haka a Matsayin ka na musulmi kayi addini da addinin Allah madaukakin sarki akan abin da yake na dai dai, kada ka dauki Ta'assubanci da ta'kalidanci don kawai kana son kayi sabani da yan uwanka musulmi akan abin da ijtihadinsu ya lurar dasu Kuma zuciyarsu ta natsu dashi.

*MI AKE CEWA JILSATIL ISTIRAHAH?*

*Jilsatil istirahah:* Wani zama ne gajere da Mai Sallah keyi bayan ya dago daga sujada ta biyu a Raka'ar farko kafin yayi yunkurin tashi zuwa ga Raka'a ta biyu da kuma bayan dagowa daga sujada ta biyu a Raka'a ta uku kafin yunkurin tashi zuwa Raka'a ta hudu, babu wani zikiri kebantacce da ake yi a lokacin zaman.

Abin da ake nufi shine; idan Mai Sallah ya kare Raka'a ta farko, yayi nufin tashi domin kawo Raka'a ta biyu, kafin ya tashi zai zauna zama dan kadan Sannan ya tashi, haka idan ya kare Raka'a ta uku yayi nufin tashi domin kawo Raka'a ta hudu, sai ya zauna zama dan kadan Sannan ya tashi.

Ana Kiran wannan zaman: *جلسة الأوتار* wato zaman wutiri, saboda Yana kasancewa bayan Raka'o'in wutiri(Ta farko da ta uku) a cikin Sallah.

*HUKUNCIN JILSATIL ISTIRAHAH*

Malamai sunyi ittifaqi akan cewa jilsatil istirahah ba ta daga cikin abubuwan da suke wajibi a cikin Sallah.
Sai dai sunyi sabani akan hukuncinta, shin Sunnah ce ko kuwa? Wannan har ya kaisu ga maganganu guda uku.

*NA FARKO:*
Sun tafi akan cewa Sunnah ce mustahabbiya, wannan shine mazhabin shafi'iyyah akan zance Wanda yafi shahara.
Imamun nawawy(R) yake cewa: Da wannan ne Malik bnul huwairith da Abu Humaid da Abu Qatada, da wasu jama'ah daga cikin sahabbai(ALLAH YA YARDA DASU) suka tafi akanshi, haka Abu Qilabah da waninshi a cikin tabi'ai duk suna akan wannan fahimta.
المجموع، شرح المهذب(3/443)

*DALILIN SU AKAN HAKA*

1. Hadisin Malik bnul huwairith (R.A) cewa: ya ga Annabi Muhammad (S.A.W) Yana Sallah, idan ya kasance a wutiri a cikin sallar shi baya yunkurin tashi har sai ya dai daita a zaune
[Bukhari 823]

Da yace a (wutiri a cikin sallar shi) Yana nufin Raka'a ta farko kafin yaje ta biyu, da Raka'a ta uku kafin yaje ta hudu

Akwai wata riwayar daban da bukhari ya riwaito a hadisi Mai lamba ta 824, daga Abi Qilabah yace: Malik ibnul huwairith ya zo mana, sai yayi Sallah a tare damu a masallacin mu wannan, sai yace: Ni wallahi zanyi Sallah a tare daku Amma ba ina nufin zanyi Sallah bane, sai dai ina nufin in ganar daku yadda Naga Annabi Muhammad (S.A.W) Yana Sallah? Sai Ayyub yace: sai muka ce da Abi Qilabah: To ta ya ya sallar shi take? Sai yace: irin sallar wannan dattijon namu Yana nufin (Amru bn salamah) sai Ayyub yace: wannan dattijon ya kasance "Yana cika kabbara, idan ya dago kanshi daga sujada ta biyu sai ya zauna, ya dai daita akan kasa Sannan sai ya tashi.

Abu Daud ma ya riwaito a hadisi Mai lamba ta 842, Kuma Albany ya inganta a sahihu Abi Daud, hadisi Mai lamba ta 748 cewa Amru bn salamah (Limamin su) ya kasance idan ya dago kanshi daga sujada ta karshe a Raka'a ta farko sai ya zauna, Sannan ya tashi.

Akwai wata riwayar a wurin Ahmad, a hadisi Mai lamba ta 20558 daga Abi Qilabah yace: (Abu Sulaiman, Malik bnul huwairith yazo a masallacin mu, sai yace: Wallahi ni zanyi Sallah, ba ina nufin Sallah bane, sai dai ina nufin in ganar daku yadda Naga  Annabi Muhammad (S.A.W) Yana Sallah? Sai yace: sai ya zauna a Raka'a ta farko bayan ya dago kanshi daga sujada ta karshe, Sannan ya tashi.
Akwai wata riwayar daban wacce ita ma Imamu Ahmad ya riwaito a hadisi Mai lamba ta 20539

Malaman da suke ganin Sunnah ce mustahabbiya suka ce: daga cikin abin da zai kara karfafa mustahabbancin yin ta shine, shi Malik ibnul huwairith shine Wanda ya riwaito hadisin dake cikin bukhari Mai lamba ta 631cewa Manzon Allah (S.A.W) yace:
صلوا كما رأيتموني أصلي
Babban Malami, Alhafiz ibn hajar(R) a cikin fatahul bary, sharhin Sahihul bukhari (2/302) a inda yake sharhin hadisin Malik bnul huwairith sai yace: a cikin shi akwai shar'ancin yin jilsatil istirahah, Kuma imamush shafi'i yana akan hakan, da wani yanki na manyan Malaman hadisi, haka a Musnad Ahmad akwai riwayoyi guda biyu....

2. Hadisin Abi Humaid Assa'idy, a inda yake siffanta sallar Annabi Muhammad (S.A.W), yace: *_"Sannan yayi sujada, Sannan yace: ALLAHU AKBAR, Sannan ya kafa 'kafar shi, ya zauna, ya dai daita har sai da kowane 'kashi ya koma mazaunin shi, Sannan ya Mike.
[ Tirmidhi ya riwaito a hadisi Mai lamba ta 304, da ibn khuzaimah a hadisi Mai lamba ta 685, da Ahmad a hadisi Mai lamba ta 23647, Kuma Albany ya inganta shi a cikin
إرواء الغليل في تخريج أحاديث منار السبيل(2/14)
Kuma babban malami Mai fatawa, Sheikh bin baaz ya rinjayar da wannan zancen. A inda yake cewa: jilsatil istirahah Sunnah ce, ba wajiba ba, wannan shi yafi inganci, wasu daga cikin malamai suna cewa Sunnah ce ga masu rauni da gajiyayyu,  kamar mara lafiya da tsoho, da sauran masu rauni, abin da yafi rinjaye shine Sunnah ce kawai ga kowa, idan mutum bai yiba a wasu lokutta babu laifi.
فتاوى نور على الدرب (2/327)

*NA BIYU*
Sun tafi akan cewa ba Sunnah bace, wannan shine mazhabin malikiyyah, da hanafiyyah, sufyan Athauri da Abu yazeed da ishaq ibn rahwiyyah, duk sun tafi akan cewa ba Sunnah bace.

*DALILIN SU AKAN HAKA*
1. Hadisin Nan na مسيء صلاة suka ce: Manzon Allah (S.A.W) bai ambaci wannan zaman ba a lokacin da yake karantar da wannan Wanda baiyi Sallah dai dai ba, da ace an shar'anta ta da ya ambata mashi ita.

*ABIN DA ZAMU CE AKAN WANNAN*
Manzon Allah (S.A.W) Yana karantar dashi wajibi ne kawai👌 ba tare da sunnoni ba(idan ka koma cikin hadisin za kaga hakan).

2. Hadisin Abi Humaid Assa'idy: inda yake cewa: sai yayi kabbara, yayi sujada, Sannan yayi kabbara, sai ya Mike bai zauna ba. [Abu Daud ya riwaito a hadisi Mai lamba ta 733 da imamul Baihaqy a hadisi Mai lamba ta 2749 da Ibn hibban a hadisi Mai lamba ta 1866.

*ABIN DA ZAMU CE AKAN WANNAN*

Shi wannan hadisin Dha'ifi ne, Albany a cikinضعيف أبي داود 171 yace: hadisin Dha'ifi ne da wannan siyaqin da suka kawo, saboda a cikin isnadin akwai wani Wanda ake Kira Isah bn Abdullah, Ibnul madeeny yace: Majhul ne(ba'a sanshi ba)

3. Hadisin Nu'uman bn Abi Ayyash, yace: na riski ba mutum guda kadai ba daga cikin sahabban Annabi Muhammad (S.A.W) sun kasance idan suka dago kansu daga sujadar karshe ta Raka'a ta farko da Raka'a ta uku suna mikewa basu zaunawa. [Ibn Abi Shaibah ya riwaito a hadisi Mai lamba ta 3989]

*ABIN DA ZAMU CE AKAN WANNAN*

Rashin yin jilsatil istirahah ga wasu daga cikin sahabbai ba zai sa ta zamo ba Sunnah ba, saboda barin abin da ba wajibi ba ya halasta.

Daga karshe, ni a Matsayi na na dalibi, dogarona da hadisan da suka a cikin bukhari da Abu Dauda ingantattu, ina akan fatawar malamai na farko akan cewa Sunnah ce mustahabbiya, Wanda yayi zai samu ladar koyi, Wanda baiyi ba sallar shi ta cika shi ma.

ALLAH YA QARA HADA KAWUNANMU AKAN KARANTARWAR ANNABI MUHAMMAD S.A.W, YAYI MANA JAGORA A CIKIN AL'AMURRAN MU NA YAU DA KULLUM.

✍ *Hashim Siraj Uba ats~tsamawy _(ABU SINAN)_*
+2349030201868

Https://fb.me/abbansinan