🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI*
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Wallafar: *Ash-Sheikh Muhammad Sani Liman Tsafe (ABU HURAIRAH)*
_002_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
✅ *FALALAR SADA ZUMUNTA*
Sadar da zumunta yana da tarin falala mai yawa kadan daga ciki sun hada da:
Sadar da zumunta alama ce dake nuna cewar bawa yayi imani da Allah da kuma ranar lahira. kamar yadda hadithin da Abu Huraira ya riwaito daga manzon Allah (SAW) yace: ''Duk wanda yayi imani da Allah da kuma Ranar Lahira to ya Karrama Bakonsa, haka nan wanda yayi imani da Allah da ranar lahira to ya sadar da zumuntarsa (Buhari ya riwaito shi 6138”).
Lallai sadar da zumunta sababine na yalwar arziki da kuma tsawon rayuwar dan adam da kuma samun albarka a cikin su.
An karbo hadithi daga Anas (R) yace manzon Allah, yace:''Duk wanda yake so a shimfida arzikinsa a kuma jinkirta masa rayuwarsa to ya sadar da zumuntarsa" *(Buhari 5986- Muslim 2557).*
Abdullahi dan Umar (R) yace ''Duk wanda ya kiyaye ubangijinsa, ya sadar da zumuntar sa to za’a jinkirata masa ajalinsa, kuma dukiyarsa zata yalwata, sannan iyalansa zasu so shi.”
*(Tirmizi-1979- Buhari adabul mufrad-58).*
3. Sadar da zumunta yana janyo sadarwar Allah ga wanda ya sadar da ita.
Abu Huraira ya ruwaito hadithi daga manzon Allah (S.A.W) yace ''Lallai Allah ya hallicci dukkan halitta bayan ya kammala sai zumunta ta tashi sai tace nan ne matsayin da zan nemi tsari daga wanda ya yanke ni? Sai Allah (S.W.T) yace eh; shin ko kin yarda in sadar ma wanda ya sadar dake in kuma yanke ma wanda ya yanke ki? Sai tace eh, sai Allah yace haka zai kasance gareki''.
*(Bukhari -5987- muslim 2554).*
4. Sadar da zumunta yana daya daga cikin manyan sabubban da ke shigar da mutun Aljanna. Abu Ayubal Ansari yace ''Lallai wani mutum; yace ya manzon Allah ka ba ni labarin aikin da zai shigar dani aljanna kuma ya nisanta ni daga shiga wuta, sai manzon Allah yace ''ka bauta ma Allah kada ka hadashi da komai a wajan bauta, ka tsaida sallah, ka bada zakka, ka sadar da zumunta.
*(Bukhari 1396-muslim 13)*
5. sadar da zumunta yin da'a ne ga Allah da Manzonsa, Allah (S.W.T) ya fada a cikin Alqur’ani yana mai yabon masu sadarda zumunta “sune wadanda suke sadar da abin da Allah yace a sadar dashi (Zumunci) suna jin tsoron ubanginsu kuma suna tsoron mummunan hisabi"
*(Suratul Ra’ad 21)*
An karbo hadisi daga Abu sufyan a cikin hadisinsa mai tsawo a cikin kissar *Hirkala* yace ma Abu sufyan mine ne Manzon Allah yake umurtar ku dashi sai Abu sufyan yace: yana cewa ku bauta ma Allah shi kadai kada ku hadashi da komai a wajen bauta, kubar ababen da iyayenku ke fada,kuma yana umartarmu da yin Sallah da riko da gaskiya da kamewa, da kuma sadar da zumunta
*(Muslim 1883)*
6. Sadar da zumunta yana daya daga cikin kyawawan ayyuka a cikin addinin musulunci, Allah (SWT) yana cewa: ''kuba ma’aboci kusanci hakkinsa (ana nufin dan'uwa) *(Isra’i 26)*
Haka nan a wani wurin yace, kuji tsoron Allah wanda kuke rokon juna dashi kuma ku sadar da zumunta *(Suratul Nisa’i 1).* Ya kuma kara cewa ku bauta ma Allah kada ku hadashi da komai a wajen bauta, ku kyautata ma iyayenku da makusantanku (yan'uwanku na zumunta) da marayu da miskinai da makwabci na kusa.
A NAN ZAMUYI BURKI SAI A LOKACI NA GABA INDA ZAKUJI *HADARIN DA KE CIKIN YANKE ZUMUNTA*
DOMIN CIGABA DA SAMUN WANNAN RUBUTU KUNA IYA AIKEWA DA SAQON WHATSAPP ZUWA GA: +2349030201868 DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA*
#ABBAN_SINAN
https://fb.me/abbansinan