Tuesday, 22 October 2019

BAKIN RIJIYA BA WURIN WASAN MAKAHO BANE...

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAKIN RIJIYA BA WURIN WASAN MAKAHO BANE....*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki Wanda ya hada yi mashi biyayya da yima malamai biyayya a aya daya a cikin Qur'ani, tsira da aminci su kara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad s.a.w Wanda yace: MALAMAI MAGADA ANNABAWA NE...

Bayan haka:

*NAMAN MALAMAI GUBA NE...*

  Abu ne sananne cewa malamai magada annabawa ne, kuma sune sukafi kowa falala bayan manzanni, sune fitilar dake haskawa jahilan dake cikin duhu domin su gane gaskiya, sune ke riko da hannun mutane zuwa ga hanyar shiriya, kuma sune sukafi kowa tsoron Allah, Allah s.w.t yana cewa: "ABUN SANI KADAI SHINE WADANDA SUKAFI KOWA TSORON ALLAH DAGA CIKIN BAYINSHI SUNE MALAMAI[Fadir:28], A wani wurin kuma Allah s.w.t yace: " SHIN KO MASU ILIMI ZASUYI DAI DAI DA JAHILAI? [Zumar:9]
Sai dai duk da wannan daraja tasu sai kaga an samu wasu daga cikin mutane wadanda aka jarabta da raunin imani, da rashin yiwa harshe linzami, da rashin sanin mutuncin na gaba dasu, sai ka gansu suna wulaqanta malaman wannan al'umma, wadanda sune suka takura rayukansu domin hidimtawa addini, da nuna wa musulmai hanyar shiriya. Amma a tare da hakan sai kaga an samu wasu masu gurbataccen tunani suna zagi da cin mutuncinsu.

*MAGANGANUN MANYAN MALAMAN MUSULUNCI AKAN MASU ZAGIN MALAMAI.*

_Saboda mu kubutar da yan uwanmu dalibban ilimi da irin wannan rudani ya kwasa..._

🔷Imamud-dahawy(RH) a cikin littafinshi(Dahawiyya) [2/740] yana cewa: "Malaman salaf wadanda suka gabata da kuma wadanda suka biyo bayansu sune ma'abota alkhairi da Sanin hadisi, sune ma'abota fiqhu da bincike, kada ka ambacesu sai da magana mai kyau, duk Wanda ya ambacesu da mummuna to baya kan shiriya(batacce ne).

🔶Haka imamu Ahmad(RH) yana cewa: " Naman malamai guba ne, duk Wanda ya taba zaiyi rashin lafiya, wanda yaci zai mutu murus.[Almu'eed fy adabul mufeed wal mustafeed, shafi na 71]

🔹Haka malik bn dinaar(RH) yana cewa: "Ya ishi mutum sharri, ka kasance kai ba mutumin kwarai bane amma kuma sai ka koma zagin mutanen kwarai." [Sha'abul iman, na imamul baihaqy;5/316]

🔸Haka ibnul Mubarak (RH) yana cewa; "Duk Wanda ke wulaqanta malamai, toh ya sani cewa lahirarshi ce yake wulaqantawa...[siyaru A'alamun nubala' 4/408]

🔹Alhafiz ibn Asakir ya fadi kwatankwacin wannan magana, haka ABU SINAN AL-ASDY(R) a cikin [Tarteebul madarik, 2/14]

*KARSHEN/SAKAMAKON MAI ZAGI DA CIN MUTUNCIN MALAMAI*

1. *Ya chanchanci a kirashi da sunan fasiqi bayan da yana da imani:*
  Kamar yadda aya ta [11] a cikin suratu hujraat ta tabbatar da hakan

2. *Ya sunnanta wata sunnah mummuna:*
       Duk Wanda ya sunnanta mugun aiki yana da zunubin aikin da zunubin duk Wanda yayi koyi dashi.

3. *Yana daga cikin mafi sharrin halitta:*
        Imamu Ahmad ya fitar da hadisi daga Abdurrahman bn ganam(R.A) daga manzon Allah s.a.w yace: " Mafi alkhairin mutane sune wadanda idan ka gansu za kaga suna ambaton Allah, mafi sharrin mutane sune masu yada Annamimanci, masu rabawa tsakanin masoya...

4. *Ya daura damarar yaki da Allah:*
         A hadisin bukhari(Hadisin qudusy) Allah s.w.t yana cewa: "Duk Wanda yayi adawa ko fada da masoyina, toh yazo ina shelanta mashi fada dani.

5. *Zai hadu da addu'ar malamin da ya zalunta/ya daga:*
        Addu'ar Wanda aka zalunta ba tada shamaki tsakaninta da Allah, toh ina ga addu'ar waliyyin Allah? Wanda Allah ke fada dangane dasu yana cewa: " idan suka rokeni zan Karba musu, idan suka nemi tsarina zan tsaresu...[Bukhary]

6. *Allah zai hukuntashi da abunda yayi:*
         Rama cuta ga macuci ibada inji malam bahaushe, kai dake zagin malamai ka tsoraci ramuwar da Allah s.w.t zaiyi musu a kanka!

7. *Za'a jarabceshi da mutuwar zuciya:*
         Babban malami IBN ASAKIR(R) yana cewa: "Duk Wanda ya saki harshenshi akan zagin malamai, Allah zai jarabceshi da mutuwar zuciya tun kafin ya bar duniya.

8. *Duk mai zagin malamai yana cikin hadari babba:*
           Wanda ke zagin malamai saboda addininsu, da maganganunsu akan hukunce-hukuncen shari'ah, ko don sun fadi wata magana ta gaskiya wacce ba yayi maka dadi ba, lallai kana cikin hadari babba, karanta aya ta [65-66] dake cikin suratu tauba.

9. *Allah zai jarabceshi da mummunar cikawa(iyyazan Billah):*
            Wannan itace sunnar Allah ga duk wani dan banzan da ya cutar da annabawan Allah tun daga fir'auna har zuwa wannan lokacin da muke cikin.

ALLAH YA NUNA MANA GASKIYA YA BAMU IKON BINTA, YA NUNA MANA QARYA YA BAMU IKON KAUCE MATA, ALLAH YA KARE HARSUNAN MU DAGA ZAGIN MALAMAI, MASU YI KUMA ALLAH YA SHIRYESU IDAN MASU SHIRYUWA NE, IDAN BA MASU SHIRYUWA BANE KAYI MANA MAGANINSU.

✍ *ABBAN_SINAN*
+2348064734911🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

+2348064734911