*NASIHAR BARKA DA SAFIYA 002*
*_(Nine Yusuf wannan kuma ɗan uwana ne)_*
Wannan maganar Annabin Allah Yusuf (Alaihissalam) ce, a lokacin da yayi maganar shine shugaban ƙasar Misira kuma taskar arzikin ƙasar na akan ikonsa...
Tare da haka, bai juya baya ya kalli matsayinsa ko muƙamin da yake akai ba, sai ya ambaci sunansa tsurar shi ba tare da wani laƙabi ba, domin wanda yake da zuciya mai girma, da ɗabi'u maɗaukaka baya juyawa ya kalli wani matsayi na mulki ko kuɗi ko yayi alfahari ya riƙa ɗagãwa da hakan a cikin mutane.
Dr. Hussein Al~feefy
_____________________________
Ni(Abu Sinan) nace, naji a cikin wani karatu da Fadhilatush-Sheikh Dr. Swalih bn Abdillah bn Hamd Al-Osaimi (H) aka tambaye shi cewa: meyasa kake ambatar sunan su Ibn Taimiyya da Ibnul Qayyim gãya ba tare da laƙabin Sheikh, ko Al-allama ko Ustaz da sauransu ba?
Sai ya da amsa da cewa: Wanda Allah ya ɗaukaka baya buƙatar wata ɗaukakar mutane, yace Abubakar Siddiq, ko Aliyu ko Abu Huraira (Radiyallahu Anhum) ka taɓa jin za'a kira su an ce Al-allama Abu Huraira? Ko Fadhilatush-Sheikh Aliyu Bn Abi Ɗalib? Yace sun wuce wannan matsayin, don haka ne ma aka samu wasu daga cikin magabata suna kyamatar wannan laƙubban.
___________________________
Amma yau Ɗalibin da bai gama zama a harkar ilimi ba idan zaka kira sunan shi kai tsaye sai yaga ka ƙasƙanta shi saboda rashin ikhlasi a cikin ayyuka.
Allah ya ganar damu ya bamu ikon yin ibada domin shi
© *AbbanSinan Tsamiya*
01 Rabi'u Thani, 1444AH
27 October, 2022