Monday, 30 December 2019

WAJIBI NE MUSULMI SU BI SUNNAH CIKIN ADDININSU

WAJIBI NE MUSULMI SU BI SUNNAH CIKIN ADDININSU:

Dr. Ibrahim jalo jalingo

1. Wajibi ne al'ummar Musulmi su kasance masu bin sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah iya iyawarsu cikin Aqidah, da Ibadah, da kuma Mu'amalah.

2. Lalle hadithin Annabi mai tsira da amincin Allah shi ne sama da mazhabar ko wane malami, fiqhunsa  kuma shi ne sama da fiqhun ko wane faqihi.

3. Bin mazhabar wani malami daga cikin Malaman Musulunci ba laifi ba ne matukar dai hakan bai kai mutum ga barin yin aiki da wani ingantaccen hadithin manzon Allah mai tsira da amincin Allah ba, in kuma ya kai shi ga barin yin aiki da wani ingantaccen nassin hadithin Annabi to lalle hakan ya haramta a bisa ittifakin dukkan Magabata na kwarai; saboda Annabi Muhammadu ne kawai Allah Ya aiko wa wannan Al'umma, duk kuma wani wanda ba shi ba to mabiyi yake a gare shi, kuma maganarsa shi Annabi tana sama da maganarsa.

4. To amma idan aka sami wata mas'ala da babu nassin Annabi mai tsira da amincin Allah a kanta to a nan dukkan wani malami mai ikon yin ijtihadi sai ya yi ijtihadinsa  domin neman kaiwa ga hukuncin Shari'ah a cikinta, duk kuma hukuncin da ya samu kaiwa gare shi cikin ijtihadin nasa to da shi ne zai bauta wa Allah Ubangijinsa.

5. Shi kuma aammiy mara ikon yin ijtihadi irin na Ilmi sai ya yi koyi da wanda zuciyarsa ta fi kwanciya da shi cikin mujtahidan da suka yi ijtihadin Ilmi a cikin wannan mas'ala wacce babu ingantaccen nassin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah a cikinta. Wannan shi ne abin da Shari'ar Musuluncin ta tabbatar.

6. Da wannan ne za a san cewa:  wajibi ne a kan ko wane musulmi ya gina addininsa a kan sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah; saboda duk wanda ya bar yin aiki da ingantaccen hadithin Annabi mai tsira da amincin Allah cikin wata mas'ala daga cikin mas'aloli kuma cikin zabinsa da jin dadinsa a bisa hujjar cewa: mazhabarsa ta saba wa hadithin, ko wata darika tasa ta saba wa hadithin, ko wani tsari na kungiyarsa ya saba wa hadithin, ko wani tsari na duniyarsa ya saba wa hadithin to lalle wannan ya bace ya bar hanyar Muminai, ya bar fikhun Sahabbai da Tabi'ai da Tabi'ut Tabi'in, Wannan shi ne abin da nassoshin Alkur'ani mai girma da Sunnah mai daraja ke tabbatarwa.
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah ya ce cikin Majmuu'ul Fataawaa 24/202:-
‎((واما من تبينت له السنة فظن ان غيرها خير منها فهو ضال مبتدع بل كافر)).
Ma'ana: ((Amma wannan da Sunnah ta bayyana gare shi, sannan ya yi zaton cewa waninta ya fi ta alheri, to shi dan'bidi'ah ne, kai kafiri ne ma)).
Ya kuma ce cikin littafin 27/125:-
‎((ومن ترك النقل المصدق عن القائل المعصوم واتبع نقلا غير مصدق عن قائل غير معصوم فقد ضل ضلالا بعيدا)).
Ma'ana: ((Wanda ya bar nakalin da aka gaskata daga mai fada wanda yake ma'asuu'mi, sannan ya bi nakalin da ba a gaskata ba daga mai fadan da ba ma'asuu'mi ba, hakika ya bace bata mai nisa)).
Allah Ka tausaya wa al'ummarmu Ka cusa musu ganin girman Annabi da son bin sunnarsa cikin zukatansu. Ameen.

001 ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI*
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

Wallafar: *Ash-Sheikh Muhammad Sani Liman Tsafe(ABU HURAIRAH)*

_001_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

✅ *MECE CE ZUMUNTA?*

*_IBN ATHEER_* yana cewa: Zumunta tana nufin taimakawa yan uwa na bangaren dangantaka da sarakuta da kula da halayen su koda kuwa suna zaune a wurare masu nisa koda kuma suna munana maka (a daya bangaren kuma yanke zumunta yana nufin kishiyar abubuwan da aka ambata a baya).

✅ *DA WANE ABU AKE SADAR  DA ZUMUNTA?*
   Ana sadar da zumunta da al’amura masu yawa kamar ziyartarsu,                                                 bibiyar halayansu, tambaya game dasu, aika masu da kyaututtuka da kuma saukar da kowannensu a matsayin da ya dace dashi, da bada sadaka ga fakirai daga cikinsu, da tausasa ma mawadatansu(Binsu a hankali) da girmama manyansu, da kuma tausaya ma kananansu, da masu rauninsu, da yawan tambayar halin da suke ciki, da kuma ziyartarsu da kanka ko ka aika wasika ko kayi amfani da wayar salula.
Mafi girman abin da ake sadar da zumunta da shi shine yin wa'azi garesu, kamar yadda Allah madaukakin sarki yake fada wa manzonshi cewa: *_"(KAYI GARGADI GA DANGINKA MAKUSANTA)"_* [shu'araa 214]
   Haka kuma Manzon Allah (salallahu alaihi wasallam) ya rinka kiran danginsa domin ganin sun shigo addinin musulunci.
Saboda haka mutum yayi kwadayin kiran yan uwansa zuwa ga shiriya ya umurce su da aiki mai kyau, ya kuma hane su da aikata miyagun ayyuka.
Zumunta tana bambanta gwargwadon  kusanci da matsayi na wadanda ake sadar da zumunta zuwa garesu,  zumunci da yake tsakanin uba da dan-dansa yana da bambanci da dan-dan dan uwa na nesa. Bugu da kari, zumunta tana bambanta gwargwadon halayen wadanda za’a sadarmawa suke ciki, kamar sadar da zumunta ga marar lafiya da mabukaci ta bambanta da sadarwa ga waninsu. Haka ma sadarwa ga babba ta bambanta da ta karami. Haka sadar da zumunta yana bambanta ta fuskar bigire, wanda yake zaune a cikin gari ya bambanta da wanda yake zaune a wani gari wajen ziyartar shi, tambayar halin da yake ciki, da yi masa sallama ko aika mashi da sakonni.

ZAMU DAKATA A NAN, INSHA ALLAHU A GABA ZA KUJI *FALALAR SADA ZUMUNTA*

DOMIN CIGABA DA SAMUN WANNAN RUBUTU KUNA IYA AIKEWA DA SAQON WHATSAPP ZUWA GA: +2349030201868

#ABBAN_SINAN
https://fb.me/abbansinan