TSARKI DA YADDA AKE
YINSA
Shinfida: Mu sani ya 'yan-uwa masu albarka,
wannan addini na musulunci addinine da yake
cikakken addini ta kowanne bangare, bai takaitu
ga alwala da sallaba kadai, ya shafi kowanne
bangare na rayuwa, kamar tsafta kiwon lafiya
zamantakewa, kasuwanci taimakon juna, tsare-
tsaren gudanarwa dadai sauransu.
A yanzu zamu kawo bayanaine da suka shafi
tsarki, dame-dame ake yiwa tsarki? Me rashin
tsarkin yake jawowa? Ya ladubban yin tsarkin
suke? Ya ake shiga makewayi? Dadai sauran
wadansu batutuwa da suke da alaka da wannan
maudu'i, da fatan Allah ya yi mana jagora ya
kuma fahimtar da mu.
Abubuwan Da Akewa Tsarki: ana yin tsarki ne
daga dukkan abinda ya fito ta daya daga
mafitar guda biyu ko ma ta duka inbanda hutu
(tusa). Kenan ana yiwa fitsari, bayangida
maniyyi maziyyi jinin al'ada….tsarki, kawai dai
idan mutum yana da alwala sai ya yi tusa to
alwalar kawai zai sake ba sai ya dauki butu ya
yi tsarki ba.
Hukuncin Tsarki: Tsarki wajibine, saboda haka
dukkan wanda dayan wadancan abubuwa da
makamantansu suka same shi to dole ya
tabbata ya gabatar da ya yi tsarki.
Abinda Ake Tsarki Da Shi : Abinda ake tsarki da
ashar'ance shine ruwa mai tsarki mai
tsarkakewa, wannan shi ake kira Istinja'u .
Saidai idan mutum bai sami ruwanba sai ya yi
da duwatsu a kalla guda uku, idan ya ga na
ukun ya fito a bushe ba wata laima shikenen,
idan kuma akwai laima to sai ya kara su kai
biyar wuturi ake bukata (3,5,7,9…) wannan kuma
ana yinshi a fitsari ko bayan gida, sannan idan
ka sami ruwa ba sai ka sake ba, wannan
hukunci shi ake kira Istijmari , ka samu ka hada
duka a lokaci guda, misali idan ka yi bayan gida
sai kasa tsinke ko takarda mara rubutu sai ka
share sannan sai ka biyo shi da ruwa. Kenan
ba'a tsarki da yawu (miyau).
Kada asha'afa, idan aka yi la'akari da abinda
ya fita da kuma abinda ya fantsamo maka, za'a
raba tsarki zuwa gida biyu:
(1) Tsarkin Hadasi: Shine tsarkin abinda ya fita
daga dayan mafita guda biyu, kamar fitsari,
maziyyi…'.
(2) Tsarkin Kabasi: Shine tsarkake abinda ya
taba jiki ko tufafi ko kuma wuri, kuma ko
wannensu baya yiwuwa said a ruwa mai tsarki
mai tsarkakewa.
Amma idan aka yi la'akari da girma ko rashin
girma za'a kasa tsarki zuwa gida biyu shima:
(1) Babba wanda ake kira Hadasul Akbar:
Ankira shi babbane domin ba'a tsarkaka daga
gareshi sai an yi wanka, kamar fitar maniyyi, ko
saduwa, ko daukewar jinin al'ada ko na biki.
(2) Karami wanda ake kira Hadasul Asghar:
wanda yake tsarki ko alwala ta wadatar, kamar
fitsari ko maziyyi.
Yadda ake yi: Da farko mutum ya wanke
hannunsa na hagu kafin ya sa a wurin da zai
wanke, domin hannun sa ya koshi da ruwa,
sannan sai ya wanke wurin fitsari. Daga nan
kuma sai ya fara wanke wurin bayan gida
musamman idan ya kaatse, ana bukatar mutum
ya wanke al'aurar sa baki dayanta musamman
idan maziyyi ne ya fita.
Ladubban Zagawa (Fitsari Ko Bayangida):
Akwai tsari na ladubba da musulunci yake da su
a lokacin da mutum ya ke niyyar kewayawa,
wannan zai nuna maka cewa musulunci ya
karade komai:
(1) Anbaton Allah : Ana bukatar kafin ka shiga
ka ambaci Allah domin ba'a anbaton Allah a
makewayi, kuma ka nemi Allah ya tsareka da
sharrin aljanu, domin irin wadannan wurare
matattarace ta su, yace:
ﺑِﺴْﻢِ ﺍَﻟﻠﻪِ، ﺍَﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺇِﻧِّﻲ ﺃَﻋُﻮﺫُ ﺑِﻚَ ﻣِﻦَ ﺍَﻟْﺨُﺒُﺚِ
ﻭَﺍﻟْﺨَﺒَﺎﺋِﺚِ
Ma'ana: Da sunan Allah, Ya Allah lalle ni ina
neman tsarinka (Ka tsareni) daga aljanu maza da
kuma aljanu mata.
Idan kuma zaka fito sai kace:
ﻏُﻔْﺮَﺍﻧَﻚَ، ﺍَﻟْﺤَﻤْﺪُ ﻟﻠﻪِ ﺍَﻟَّﺬِﻱ ﺃَﺫْﻫَﺐَ ﻋَﻨِّﻲ ﺍَﻷَﺫَﻯ
ﻭَﻋَﺎﻓَﺎﻧِﻲ
Ma'ana: (Ina neman) gafarar Ka , Dukkan godiya
ta tabbata ga Allah wanda ya rabani da wannan
kazantar kuma ya bani lafiya.
Ka sani ba'a shiga bayi da dukkan wani da
yake dauke da sunan Allah, kamar zobe, ko
carbi…'. Hakanan kuma ba'a katse bayangida da
dukkan wani abu da yake da sunan Allah.
(2) Fara Gabatar Da Kafar Hagu Lokacin Shiga,
kafar dama kuma lokacin fita.
(3) Ayi A Tsugunne: kada mutum ya yi fitsari
ko bayan gida a tsaye, sai dai idan wurin
kangone ko yana tsoron fitarin ya fallatso masa,
sannan ba wanda zai ganshi ya samu ya yi a
tsaye.
(4) Tabbatuwa A Cikin Sutura: ana bukatar
kada mutum ya yaye al'aurar sa tun yana tsaye,
sai ya tsugunna ya yi dab da kasa sai ya daga
suturarsa, domin ba'a yarda wani ya ga al'aurar
wani ba in ba miji da mataba, amma halin ko
unkula da wasu suke nunawa na bayyanar da
al'aurarsu ga kowa muddin jinsi gudane wannan
baidaceba, sai ka ji wana yace 'Ai duka
mazane, abinda kake da shi ina dashi', wannan
ba koyarwar musulunci bace, haka namma
mata, wannan zai kaika ka ga maza sun tube
suna wanka lokaci guda a dakin wanka guda,
haka namma mata, wai sun dauka abinda yake
haram shine namiji ya ga al'aurar mace ko
mace ta ga al'aurar namiji, kai wani lokaci kana
tafiya a cikin mota sai kai arba da wani
gabjejen kato yana wanka a rafi, wani kuma a
gefan titi ya kafe mashin ko ya je kayan
tallansa, duk wadannan bakewawan halaye
bane, mutum musulmi ya nisance su.
(5) Yafi Bada Karfi A Kafarsa Ta Hagu: Kenan
abinda akafi so shine mutum ya fi bayar da
karfinsa a kan kafarsa ta hagu.
(6) Ya Bude Tsakanin Cinyoyinsa: kenan kada
ya matse, ballantana ya sa matsattsiyar tufa
wacce idan yana fitsari na gaban ne kawai zai
fita, sannan idan ya mayar cikin wando sauran
ya gangaro, Allah ya sawwake.
(7) Ya Nisanci Inda Ruwa Yake: musulunci bai
yadda mutun ya yi fitsari ko bayan gida a inda
ruwa yakeba ko kusa dashi, dan wannan zai
haifar da cututtuka.
(8) Ya Rufe Kansa: Ana son wanda yake
bayangida ya rufe kansa a daidai lokacin da
yake yi, domin koda wani ya yi kuskuren
ganinsa to shi bai ganshiba, abin zai zo da
sauki, amma ba zaka ji dadiba kana bayan gida
ka hada ido da wani, wanda zai iya zama
dalibinka ne ko suruki ko da..,'.
(8) Kada Ayi Magana: anhana mutum yana
bayan gida yana Magana, sai dai idan akwai
dalili mai kwari, kamar ka ga makaho ya nufi
rijiya ko karamin yaro…'.
(9) Kada A Tari Iska: an hana idan mutum zai
yi bayan gida a dawa (daji) an hana ya tari iska,
domin zai bsowa jama'a warin bayan gidansa,
kenan sai ya yi nesa, ya kuma duba ina iska
take kadawa.
(10) Kaucewa Rami: Ba'a yarda idan za ka yi
fitsari ko bayangida ka yi aramiba saidai idan
kai ka haka, domin bakasan mekecikin ramin ba,
takan yiwu akwai mugun abu.
(11) Kaucewa Wuraran Tsinuwa: Wadannan
wurare sune wuraran da mutane suke yawan
tsinema dukkan wanda ya yi musu bayangida a
wurin, wadannan wurare sune:
(a) Inda mutane suke zama su huta, jikin
bangone ko karkashin bishi komadai inane.
(b) Kan hanya: Akwai rashin mutunci mutum ya
zo kan hanya ya gicciya bayangida, wannan
dabi'a musulunci bai yarda da ita ba.
( c ) Mashayarruwa: Hakanan baya cikin
karantarwar musulunci mutum ya zo inda
al'umma suke diban ruwa rafine ko wani gulbi
ko gindin fanfo komadai inane ya aikata wannan
ta'asa. Wadannan wurare uku musulunci ya
hana a aikata wannan danyan aiki a wurin,
domin mutum yana jawa kansa tsinuwa, Allah
ya tsaremu.
(12) Nesa Da Jama'a : ana bukatar dukkan
wanda zai yi bayan gida ya yi nesa da jama'a ta
yadda ba za su ganshiba kuma ba za su ji
nishin shiba, ba zai yi kyauba ace kana bayan
gida mutane suna ganinka ko suna jin nshinka,
ko da a bayan bishiya ko ganyan kargo sai ka
boye, amma sau da yawa mutane suna tafiya a
mota da motar ta tsaya sai ka ga kowa ya
tsaya dab da motar, sannan ba za'a tafi a
barshiba.
(13) Kada Ya Fuskanci Alkibla: wato inda
mutum yake kallo lokacin sallah, kuma kada ya
juya mata baya, wannan idan a dajine, amma
idan a gidane to da sauki.
Abubuwan Da Rashin Tsarki Yake Hanawa:
kamar yadda bayani ya gabata cewar tsarki
wajibine, to mu sani idan mutum bashi da tsarki
bai halatta a gareshi wadannan abubuwanba:
(1) Sallah: Bai halatta ga wanda bashi da tsarki
ba ya yi sallah nafila ko farillah.
(2) Dawafi: Kewayan Ka'aba kenan a birnin
makkah, saboda haka idan mutum yana dawafi
sai ya yi tusa to dawafisa ya warware sai ya
sake alwala domin ita tusa ba'a yi mata tsarki.
(3) Sujjadar Tilawa: Wato sujjadar da mutum
zai yi ida yana karatun Alkur'ani mai girma sai
ya kai wadansu gurare, domin ba shi da tsarki,
dudda malamai sun kawa juna sani akai.
(4) Kabli Ko Ba'adi : Bai halatta ga wanda bashi
da tsarki ba ya yi kabli ko ba'adiba har sai ya yi
tsarki, idan akce kabli ana nufin sujjadar da
mutum zai yi kafin ya yi sallama, amma idan
ake ba'adi to wacce zai yi bayan sallama. Idan
jiya ba'adi ta kamaka sai kuma ka manta baka
yi to ya halatta ka yi ta a yanzu idan kana da
tsarki.
(5) Daukar Alkur'ani Mai Tsarki: idan mutum
bashi da tsarki to sai yi tsarki kafin ya taba
wannan littafi mai tsarki.
Kammalawa: ina fatan wadannan takaitattun
bayanai sun warkar da abinda ake bukata, kuma
sun nuna lallai addinin musulunci gamamman
addinine da ya shafi komai ya kuma yi bayani
akan komai, domin idan yakai bayan gida sai an
nunawa mutum yadda ya kamata ya yi to ashe
wannan ba karamin gata musulunci ya yi mana,
muna godiya ga Allah.