Wednesday, 7 December 2016

IBN TAIMIYYA BAI YARDA DA MAULIDI BA, HASALI YAYI FADA DA ITA...

🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴
*_IBN TAIMIYYA BAI YARDA DA BIDI'AR MAULIDI BA, HASALI MA YAYI FA'DA DA ITA_*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

_001 Fitowa Na daya_

_Rubutawa:_ *_Hashim Surajo Uba Tsamiya(ABU SINÃN)_*

بسم الله الر حمن الر حيم

```Godiya ta tabbata ga Allah shi kadai, Tsira da amincin Allah su tabbata ga Wanda babu wani Annabi bayansa, tare da iyalan gidansa da sahabbansa baki daya.

Bayan haka;
Nayi nufin yin wannan rubutu ne saboda Wata 'karya dake yawo a kafofin sadarwa na zamani(social medias) akan cewa ibn taimiyya yace Maulidi halas ne, har ma yace akwai lada ga Wanda yayi. Maganar wacce suke sama mata gindin zama a cikin littafin shehin Malamin mai suna((I'KTIDA'UL SIRA'DUL MUSTAQEEM)).
Kafin bada amsa ga maganar ya kamata masu karatu kusan cewa Malamai ba ma'asumai bane! Suna dai dai suna kuskure.
Amma ga wata magana ta ibn Taimiyya akan maulidi;```
قال ابن تيمية-رحمه الله- ((فإن هذا [يعنى الإحتفال بالمولد] لم يفعله السلف مع قيام المقتضى له وعدم المانع منه، ولو كان هذا خير محضا أو راجحا لكان السلف رضي الله عنهم أحق به منا، فإنهم كانوا أشد محبة لرسول الله صلى الله عليه وسلم وتعظيما له منا، وهم على الخير أحرص، وإنما كمال محبته ةتعظيمه في متابعته، وطاعته واتباع أمره، وإحياء سنته باطنا وظاهرا، ونشر ما بعث به، والجهاد على ذلك بالقلب واليد واللسان، فإن هذه هي طريقة السابقين الأولين من المهاجرين والأنصار والذين اتبعوهم بإحسان...))    {اقتضاء صراط المستقيم ص ٣٥٠ دار ابن الهثيم}

_Ma'ana;_ *_"Ibn Taimiyya -Allah yayi masa Rahama- a cikin littafinsa [Iktida'ul siradul mustakim] yana cewa; Lallai wannan (Bukin maulidi) magabata basu aikatashi ba tare da suna da damar yin hakan kuma babu abunda zai hanasu, da wani aikin Alkhairi ne babba ko kuma mafi rinjaye da magabata-Allah ya yarda dasu- su sukafi cancanta  su aikatashi fiye damu, domin sun fimu son Annabi Muhammad Tsira da Aminci SU tabbata a gareshi da girmamashi kuma sun fi mu kwadayi ga Alkhairi, to amma abin da ke cikakken so da girmamawa ga Annabi shine bin sunnarsa, da yi masa biyayya da bin umurninsa da rayar da sunnarsa a boye da bayyane da kuma watsa abin da aka aikoshi dashi da kuma yin kokarin yadashi da Alkalami da hannu da kuma halshe, kuma wannan shine tafarkin wadanda suka gabacemu daga cikin muhajiruna da Ansar da wadanda suka bisu da kyautatawa._* [Iktida'u siradul mustakim shafi na 350]

   ```wannan shine abin da sheikhul Islam Allah yayi masa rahama ya fada game da bukin maulidi, kuma wannan karara yake cewa bidi'ah ne daga cikin bidi'o'i, Wanda yasa dole muyi yaki dashi.
   Sai dai yan bidi'ah saboda son rai da son zuciya sun bar wannan magana dake nuna cewa maulidi bidi'ah ne, sunyi riko da Abinda yayi dai dai da son rayuwarsu, kamar yadda dama wannan shine Al'adarsu Qur'an ma yayi bayani a cikin suratul [Ali imran aya ta 7]  daman su mutane ne masu son shubuha.
Su kuwa Ahlis Sunnah ba haka suke ba. Imamul wa'ki'i ibn jarrah yake cewa;```
((أهل السنة يكتبون مالهم وما عليهم، وأهل الأهواء يكتبون مالهم)).
[ذم الكلام للهروي ٣٣٨]

_Ma'ana;_ *_"Ahlus sunnah suna rubuta abinda yake hujja a garesu da Wanda yake hujja akansu, amma masu bin son zuciya (YAN BIDI'AH) suna rubuta abinda yake hujja garesu kawai._* [Zammul kalam 338]

```wannan rubutu zai zamo shimfida na warware wannan shubuha, fitowa ta gaba zanyi bayani akan maganar da ibn taimiyya ya fada wanda yan bidi'ah suke ganin cewa hujja ne garesu.
Allah ya karemu daga bin son zuciya da watsi da sunnar Manzon Allah, Allah ya tabbatar da dugaduganmu akan bin sunnah da aiki da sunnah.```


Copyright©
*_Hashim Surajo Uba Tsamiya(ABU SINÃN)_*
Https://mobile.facebook.com/hashimusurajo.tsamiya
📞08064734911
Http://hashimtsamiya.blogspot.com
atstsamawy@gmail.com

KO YANA HALASTA YIN BIKIN MAULIDIN ANNABI MUHAMMAD S.A.W KO WANI DAGA CIKIN MAGABATA...!!!???

🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KO YANA HALASTA YIN BIKIN MAULIDIN ANNABI MUHAMMAD S.A.W KO WANI DAGA CIKIN MAGABATA...!!!???*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

  _Fitowa ta biyu (002)_

     _Rubutawa;_ *_Hashim Surajo Uba Tsamiya(ABU SINÃN)_*

*Godiya ta tabbata ga Allah Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah s.a.w da mutanen gidansa da sahabbansa da duk Wanda yabi tafarkinsa da kyautatawa har tashin kiyama.*

_Bayan haka;_

_Nayi rubutu mai irin wannan take Wanda nace fitowa na gaba yana nan zuwa, to kuma insha Allahu zan cigaba da bada hujja akan haramcin Maulidi da kuma zamanshi bidi'ah abar kyama.  Manzon Allah s.a.w ya kasance idan zaiyi huduba bayan ya godewa Allah, ya nemi taimakonshi da gafararshi daga karshe sai yace;_
(( أما بعد، فإن خير الحديث كتاب الله وخير الهدي هدي محمد صلى الله عليه وسلم وشر الأمور محدثاتها وكل بدعة ضلالة)).

_Ma'ana;_ *_"Bayan haka; Lallai fiyayyen zance shine littafin Allah, kuma fiyayyar shiriya ita ce shiriyar Muhammad s.a.w, kuma mafi sharrin al'amurra sune wadanda aka kirkiro, kuma dukkan bidi'ah bata ce"_* [Muslim ya ruwaito]

```Bayan wannan; yana daga cikin abunda yasa Malamai suka kyamaci bidi'ar Maulidi; bayan zamanshi bidi'ah, akwai haduwa mata da maza da wake wake da amfani da kayan kid'a (Badujala, piano,...) Da shaye shayen abubuwan dake sa maye, da wasu sharrance sharrance, wani lokaci Abunda yafi wadancan yana faruwa, wato shirka da Allah, ta hanyar wuce gona da iri wajen yabon Manzon Allah s.a.w ko waninsa kamar; Tijjani, Inyassi, jelani, Mahadi, Hussain,  yaa Ali, ko waliyi na wheelbarrow. Za kaga ana Addu'ah ana Neman agajinsu da taimakonsu ko fadar cewa Annabi Muhammad s.a.w yasan gaibi ko wani daga cikin waliyyai, wadannan abubuwa duk zaka samu suna faruwa a wajen Maulidi. Shi kuwa Annabin Rahama s.a.w cewa yayi;```
((إياكم والغلو في الدين، فإنما أهلك من كان قبلكم الغلو في الدين)).

_Ma'ana;_ *_"Ku kiyayi yin shishshigi a cikin Addini, saboda babu wani Abu Wanda ya hallaka wadanda suka gabace ku face shishshigi a cikin addini._*

A wani Hadisin Manzon Allah s.a.w cewa yayi;
((لاتطروني كما أطرت النصاري ابن مريم إنما أنا عبد فقولوا: عبدالله ورسوله))

_Ma'ana;_ *_"Kada Ku zurfafa wajen yabo gareni kamar yadda kiristoci suka zurfafa wajen yabo ga Dan Maryam(Annabi isah) ni bawa ne kawai, saboda haka kuce; bawan Allah kuma manzon Allah._* [Bukhari ya ruwaito]

```Abin mamaki shine zaka samu da yawa daga cikin mutane suna kokari wajen halartar wadannan tarurrukan na bidi'ah, kuma suna kare masu yinsu, amma kuma sai kaga basa halartar wuraren Neman ilimi, Inda za'a nuna maka yadda zakabi Allah da Manzonsa ba inda za'a nuna maka falalar karya ta waliyyan karya ba. Babu shakka wannan yana daga cikin raunin imani da kuma karancin basira, kuma yana nuna cewa tsatsa ta rufe zukatansu ta nau'o'in zunubai da sabon Allah.

    Allah ya karemu daga fadawa cikin shirka da bidi'ah da bata.

     SUNNAH SAK

             BIDI'AH SAM

   MAULIDI SAM SAM SAN SAM SAM

Wa'ka:

DA MAULIDI NE ALAMAR SON MANZO

     DAN FODIO DA BA ZAYA CE MAR BIDI'AH BA.```

Copyright©
*_Hashim Surajo Uba Tsamiya(ABU SINÃN)_*
📞08064734911📞
Https://mobile.facebook.com/hashimusurajo.tsamiya

Http://hashimtsamiya.blogspot.com

atstsamawy@gmail.com