Friday, 15 February 2019

01 MATSALOLIN SHAYE SHAYE

💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊
*MATSALOLIN SHAYE-SHAYE A CIKIN AL’UMMA.*
🚬🚬🚬🚬🚬🚬🚬🚬🚬🚬

Rubutawa: *SHEIKH NASIR BALA BUNGUDU*


*ABUBUWAN DAKE CIKI*

✅ GABATARWA

✅ MA’ANAR MAGANI

✅ MA’ANAR SHAYE-SHAYE

✅ DALILAN DA SUKE JAWO SHAYE-SHAYE A CIKIN AL’UMMA

✅ WASU DAGA CIKIN MIYAGUN MAGUNGUNNA /DA KAYAN MAYE DA AKE TU’AMMALI DASU

✅ MATAKAN SOMA SHAYE-SHAYE

✅ ALAMOMIN DA AKE GANE MAI SHAYE-SHAYE DASU

✅ SLANGS DA AKE AMFANI DASU DOMIN BADDA SAWU

✅ ILLOLIN SHAYE-SHAYE

✅ MAFITA

     Shaye-shaye dadadden abu ne a cikin al’ummomi daban-daban
Shaye-shaye ya zama ruwan dare ba birni ba kauye ba rugga ba zango ba manya ba kanana ba maza ba mata. Kuma musulunci yabi matakai daban-daban don magance matsalar shaye-shaye da kawar dashi kasancewar larabawa suna cikin wadanda ke tu’ammali da shaye-shaye kamar yadda Hassanu bin Thabit yake cewa: )WA NASRABUHA FA TATRUKUNA MULUKAN WALA YANAHNIHUNA AL-LIQA’ U)

MA’ANAR MAGANI: Shi dai magani ko kwaya shine duk wani abu da in ya shiga jikin dan adam yake kawo wani canji ga kwakwalwa ko jikin sa, ta ko wane fanni misali, ko ta hanyar sha, ko shafawa, Ko shakawa ko yin allura, ko kurkura.

MA’ANAR SHAYE-SHAYE:

Sha ko amfani da maganin da doka ta hana amfani dashi
Sha ko amfani da magani barkatai ba tare da izinin likita ba. Sha ko amfani da abubuwan da addinin musulunci ya hana Wuce umurnin likita wajen shan magani

*DALILAN DA SUKE JAWO SHAYE-SHAYE A CIKIN AL’UMMA*

Jahilci Matsalolin rayuwa kamar (rashin aikin yi, mutuwar aure, damuwa ko bacin rai) Miyagun abokai
Koyo daga masu yi,
Al’adu, gado Hada-hadar siyasa, Sakacin iyaye game da tarbiyya da rashin tsawatawa,
Yanayin wurin zama (Environment),Sakar ma yara dukiya,
'Bata garin masu sayar da magani,
Shan magani da nufin biya ma juna bukatar aure, Samun magungunnan cikin sauki,
Sakacin hukuma,
Bata garin jamián tsaro, Cin hanci da rashawa, Sha don samar da kuzari ko karfin jiki.

Wadannan kadan ne daga ciki.

Zamu cigaba insha Allahu

✍ *Hashim Siraj Uba atstsamawy ( _ABU-SINAN_ )*
+2348064734911

WAZAN ZABA? 2015/2019

🔶🔶🔶🔶🔶🔶🔶🔶🔶🔶
*وليتذكرأولولألباب !!!*
*Domin masu hankali suyi tunani!!!*
🔷🔷🔷🔷🔷🔷🔷🔷🔷🔷

_Rubutawa;_ *MURYAR SHABABU AHLIS-SUNNAH WALJAMA'AH TSAFE*

_Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu._

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki wanda ya fifita Addinin Musulunci akan duk sauran addinai a bayan kasa, Ya kuma fifita Musulmai akan wanda ba Musulmi ba, ya kuma bayyana shine addinin da zai karba a ranar alkiyama.
Tsira da aminci Allah su tabbata ga shugaban mu da yafi duk wani shugaba a doron kasa, wanda yafi kowa cikin halittun Allah (S.W.T) baki daya; Annabi Muhammad (S.A.W) da iyalansa da sahabbansa da wadanda suka taimaki addinin  Allah da dukiyarsu da kawunansu, da wadanda suka bisu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

1⃣ *SHIN KO SIYASA ADDINI CE???*
          Siyasa na iya zama  addini ta lura da fadar Allah (S.W.T) *“Kace lallai sallah ta da yanka na da rayuwata da mutuwa ta na Allah ne Ubangijin halittu, babu abokin tarayya a gareshi, Kuma da wannan ne aka umarce ni kuma nine farkon masu mika wuya”*
{Al-An’am; 162-163}.

Tunda an umarci Manzon Allah (S.A.W) da cewa dukkan rayuwarshi yayi ta ga Allah (S.W.T), haka ma kai/ke aka umurce ku da dukkan rayuwar ka/ki yita ga Allah (S.W.T). Duk wanda zai jagorance ku zai jibinci Al’amurranku ne da addinin ku, to wajibine ya zama musulmi na kwarai.
Hakanan malamai sunce za’a saka addini a cikin siyasa ta lura da wasu abubuwa masu zuwa, ga kadan daga cikinsu:

✅ *_Ya kasance ga musulmi ga kafiri:_*
wajibine a zabi Musulmi.

✅ *_Ya kasance ga musulmi na kwarai ga kuma na banza (Fasiki):_*
Wajibine a zabi Musulmi na kwarai.

✅ *_Ya kasance ga Musulmai duka na kwarai amma daya yafi daya Imani, tausayi, taimako da son addini:_*
wajibi ne a zabi mai imani da tausayi da taimakon al’umma da son addini.

Duk wannan wajibi ne a saka addini a cikin siyasa domin duba ga abunda zai kawo ci gaba ga addini da al’umma, sannan wace amsa za ka/ki ba ma Allah (S.W.T) a ranar alkiyama idan ya tambayeka/ki dalilinka/ki na zabar kafiri ko fasiki alhali ga Musulmi ko mumini.

2. *Shin ko ya halatta in zabi kafiri alhali ga Musulmi?*

A’a baya halasta a zabi kafiri alhali ga musulmi, dalili kuwa Allah (S.W.T) yana cewa: *_“Ya ku wadanda sukayi imani kada ku riki kafirai a matsayin masoya koma bayan muminai shin kuna nufin sanya ma Allah dalili bayyananne ne a kanku”._*
{Al-Nisa’; 144}.

Allah ya kara cewa: *_“Ya ku wadanda sukayi imani kada ku riki abokan sirri daga waninku (wadanda ba Musulmai ba), basu takaita maku barna kuma suna gurin abunda zai cutar da ku, hakika kiyayya ta bayyana daga bakunansu amma abunda zukatansu ke boyewa ne mafi girma, kuma lallai mun bayyana ayoyi ne a gareku domin ku hankalta. Ku dinnan kune kuke sonsu (alhali) su basu son ku…”_*
{Ali-Imran; 118-119}.

Allah ya kara cewa: *_“Ya ku wadanda sukayi imani kada ku riki makiyana da makiyanku (a matsayin) masoya kuna jefa soyayya zuwa garesu alhali kuwa sun kafirta da abunda yazo maku na gaskiya…”_*
{Al-mumtahina; 1}.

3. *Wa ya kamata in zaba a matsayin shugaba (wanda zai jibinci al-amurrana)?*

Zabar shugaba nuni ne ga so da kauna da kuma yarda da cewa wanda ka zaba ka yarda ya jibinci al-amurran rayuwar ka da addininka, to dole ne ka zabi wanda yasan kima da mutuncin rayuwar taka da addininka.
Allah (S.W.T) yana cewa *_“Abun sani majibincin al-amurranku (shine) Allah da ManzonSa da wadanda suke tsayar da sallah suke bada zakkah...._*

Duk wanda ya jibinci Allah da ManzonSa, kace rundunar Allah itace mai rinjaye” {Al-Ma’idah; 55-56}.

Muna rokon Allah yasa ayi wannan zabe lafiya, ya zaba muna shuwagabanni na kwarai masu kaunar addininmu na musulunci ba masu fada dashi ba.

*SANARWA!!!*

Mun rubuta wannan takarda ba don goyon bayan wata jam’iyya ko wani mutum ba, a’a munyi ta ne domin isar da sakon Allah (S.W.T) zuwa ga bayinsa da nufin kawo gyara ga al’ummarmu da rayuwarmu.

Wassalamu Alaikum.

*SHABABU AHLIS SUNNAH WAL JAMA’AH TSAFE ZAMFARA STATE*
08064607294, 08139348898

shababuahlissunnahwjtsf@gmail.com

02 MATSALOLIN SHAYE SHAYE

💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊
*MATSALOLIN SHAYE-SHAYE A CIKIN AL'UMMA.*
🚬🚬🚬🚬🚬🚬🚬🚬🚬🚬

_Fitowa Na biyu 002_

Rubutawa: *SHEIKH NASIR BALA BUNGUDU*


*WASU DAGA CIKIN MIYAGUN KWAYOYIN DA AKE TU’AMMALI DASU.*

Giya (burkutu), golder, power stout, googgoro, Star, lion dragen), Tabar wiwi, (indian Hemp) Cociene (Hodar ibilis), Heroine
D5, (Valium, Diazepam, Exol5),
Tramol(Tramadol),
Sholisho(sholi),
Snuff tobacco (Shisha), Maganin mura da ake sha ba bisa ka’ida ba kamar: (Emzolyn, tutolyn/codein, benalyn/codein)
Afarci kasa (pemolin tablet)
R C D, Kashin kadangare,Baabaa jijji, Buke, Zamalo,
Bula, Kwata, Tururin masai, Kan ashana,
Lohi, Alabukun, Shake,Kurkura.

*MATAKAN SOMA SHAYE-SHAYE*

✅ *GWAJI*: wannan shine mataki na farko wanda mutun zai soma ko fara kusantar mu’amala da shaye-shaye har fara tabawa kadan .

✅ *MASU SHAYE-SHAYEN GANIN DAMA:* Wannan matakin yana shane lokacin da yaga dama baya sa kudin sa sai ya samu na banza. Kamar irin wuraren taruwar jama’a wuraren biki,da ayukkan gayya da suran su.

✅ *MASU SHAYE-SHAYE AKAI AKAI:*
Wannan shine matakin fara shaye shaye gadan-gadan ko yana da kudi ko baya dasu sai ya sha.

✅ *WADANDA SUKA DOGARA AKAN SHAYE-SHAYE:*
  wadannan sune suka kai matakin ba zasu iya komi ba sai sun sha idan basu sha ba ba zasu zauna lafiya ba wanda yakai wannan matakinkullum zaka same shi cikin maye.

✅ *ALAMOMIN DA AKE GANE MAI SHAYE-SHAYE DASU:*
Rashin natsuwa
Halin lalaci Yawan abokai barkatai
Yawan fushi da rashin hakuri
Rashin ladabi da rashin kunya Amfani da bakin gilashi (Ba bisa kai’ida ba) Tinted Glass Yawan arangama da jami’an tsaro
Samun mutum da miyagun kwayoyi
Yawan yawo da ruwa ko lemon kwalba Rashin biyayya ga maganar magabata da rena su.
Yawan bacci
Ladabin kura
Jan lebo ko bakin baki
Dafewar tafukkan hannu da kafa
Amfani da kayan kamshi don kawar da wari eg comfo,tiger etc

*SLANGS DA AKE AMFANI DASU DOMIN BADDA SAWU:*

Masu tu’ammali da kayan maye suna amfani da wasu yarurrukka ko sunaye domin badda sawu ga sauran jama’a, ga misalign wasu daga ciki:
COCAINE: Blow,bump,c,candy,coke,crack,flake,rock,snow,snuff,sneeze.da dai sauransu.

DAGA: Blunt,green,dope,ganja,grass,smoke,chacks,herb,marry jane, pot,reefer, tree. Hashish,ganye, weed,cannabis, Magani, kaya.

✅ *ILLOLIN SHAYE-SHAYE A ADDINANCE:*
raunin Imani, hana ibada, gusar da kunya, bude kofofin alfasha da kaba’irori, zubar da mutunci, gusar da ni’ima, aikin shedan ne.

✅ *ZAMANTAKEWA:* lalata zumunci da wargaza dangantaka, kora daga wurin aiki ko makaranta

✅ *TATTALIN ARZIKI:*
yawan kashin kudade don ceto masu shaye-shaye ko biyan barnar da suka yi, sace-sace da barnata dukiyoyi, talauci.

✅ *KIWON LAFIYA:*
yawan kawo hatsari yayin tuki, ciwon huhu, ciwon hauka, yawan tunani mai tsanani mai muni, daukar mummunan mataki, kasha mazakuta, yawan lalaci, cancer ko wace iri ta mahaifa,na nono da sauran su.

✅ *TSARO:*
yawan tashe-tashen hankulla da zaman dar-dar da rashin tabbas, yawan kashe-kashe, zubar jinin wanda baiji bai gani ba bugling.

✅ *MAFITA*
Ya zama wajibi iyeye da tarbiyar da Allah ya wajabata masu ta yayan su musamman matasa da budurwai masu shekaru 15-20 (Teenagers) golden age of a teenagers galibi suke shiga wasu dabi’u na banza. Don haka dole ne a dinga kula da harkokin su na yau da kullum da kuma abokan da yaran su ke hulda dasu.
Dole ne magidanta su kula da irin mutanen dake shige da fice a gidajen su kuma su kula da irin mutanen da matan su da yayan su suke mua’amala dasu (maza da mata) kasancewar yanzu matan aure sun shiga cikin shaye-shaye dumu-dumu.
Wajibi ne sarakuna da malaman addini su tashi tsaye haikan wajen tsawatarwa da fadakarwa akan illolin shaye-shaye a mahangar addini da rayuwa.
Wajibi ne al’umma su bayar da cikakken goyon baya da hadin kai ga jami’an tsaro da jami’an hukumar yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi a lokacin da suke gudanar da ayukkan su.
Wajibi ne ga makarantu kungiyoyin addini,da kungiyoyin sa kai da ban a gwamnati ba wurin taimakawa kokarin gwamnati wurin wayar da kai game da illolin shaye-shaye tare da fallasawa gami da bankado masu ruwa da tsaki wurin wannan mummunar dabi’a.
Daga karshe wajibi ne ga dai-daikun al’umma da su tashi tsaye wajen bada gudummuwa ga yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi domin kaucewa fadawar al’umma cikin halaka.
Yazama wajibi ga gwamnati da masu rike da mukaman siyasa da kungiyoyi kai harma da dai-daiku masu hannu da shuni su samar da cibiyoyin koyar da sana’ o’in hannu (skills acquisition centres) domin horar da dimbin matasa da basu da aikin yi.
A karshe muna yabawa gwamnatin tarayya wato Federal Government akan haramta shigowa tare da sarrafa sinadarin codein, kuma muna kira ga sauran matakan gwamnati da su marawa wannan mataki na gwamnati wajen samar da dokoki da daukar matakai da zasu rage ko kawar da shaye-shaye daga cikin al’ umma.

✍ *Nasiru Bala Bungudu (Abu-Khadijah)*
08067234355

6- Ramadan 1439 AH / 22- May 2018