Tuesday, 30 March 2021

05 HUKUNCE HUKUNCEN TA'AZIYYA

HUKUNCE-HUKUNCEN TA'AZIYYA A MUSULUNCI.

DARASI NA BIYAR (005) DA NA SHIDDA (006)

📒ABU NA BIYAR: SUNNAH NE DANGIN MAMACI DA MAKWABTAN SA SUYI ABINCIN DA KOSAR DA IYALAN MAMACI SU AIKA MASU📒

📌1.Yana daga cikin karantarwar Annabi Muhammad SALLAL LAHU ALAIHI WASALLAM domin tausaya ga iyalan mamaci, dangin sa da makwabtan sa su aika masu abincin da zai Kosar da su. Saboda Hadithin Abdullahi bin Ja'afar da yake cewa: lokacin da labarin mutuwar mahaifin mu (Ja'afar) ya zo, sai Annabi SALLAL LAHU ALAIHI WASALLAM yace: "KUYI ABINCI DON IYALAN GIDAN JA'AFAR (ku aika masu) HAKIKA ABIN DAKE SHAGALTAR DA SU YA ZO MASU". [Abu Dawud da Tirmiziy da bin Majah suka ruwaito sa kuma Hadithi ne ingantacce].

🖋️Haka kuma Imam As-Shafi'iy a cikin littafin sa AL-UMM yana cewa: "INA SO GA DANGI DA MAKWABTAN MAMACI SUYIWA IYALAN MAMACI ABINCI DA ZAI KOSAR DASU A YINI DA DAREN DA YA RASSU, DOMIN SUNNAH NE KUMA YANA DAGA CIKIN AYUKKAN MUTANEN KIRKI A GABANIN MU (Sahabbai da Tabi'ai) DA MA NA BAYAN MU (sauran mabiyan Sunnar Annabi). A karshe sai ya kawo Hadithin Abdullahi bin ja'afar da ya gabata.

📒ABU NA SHIDDA:MUSTAHABBANCIN SHAFA KAN MARAYA DA TAUSAYA MASA📒

📌1. Mustahabbi ne shafa kan maraya da girmama sa, saboda Hadithin Abdullahi bin Ja'afar da yake cewa:.....Manzon Allah ya wuce mu yana kan dabba ni da Qathm da Ubaidullah bin Abbas, sai yace ku miko man shi (wannan yaro) sai aka mika ni ya dora ni a gabansa, sai yacewa Qathm ku miko man shi, sai aka mika masa shi, sai ya dora sa a bayan sa...... a duk lokacin da ya shafi kaina sai yace: "YA ALLAH KA MAYEWA JA'AFAR A CIKIN IYALAN SA". [Ahmad da Baihaqiy suka ruwaito sa kuma Hadithi ne ingantacce].

Wannan shine abinda Sunnar Annabi Muhammad SALLAL LAHU ALAIHI WASALLAM ta tabbatar dangane da ta'aziyya.

Wallahu a'alamu bissawab.

✍️ Nasiru Bala Bungudu
(Chief Imam Salih bin Abdil Aziz Juma'at Mosque Bungudu)

04 HUKUNCE HUKUNCEN TA'AZIYYA

HUKUNCE-HUKUNCEN TA'AZIYYA A MUSULUNCI.

DARASI NA HUDU (004)

📒ABU NA HUDU: ABUBUWA UKU DA YA KAMATA A NISANTA A LOKACIN MUTUWA📒

Ya kamata a nisanci al'amurra uku da matane ke yawan yi lokacin da aka yi mutuwa.

📌1. Tururuwar mutane wurin shiga gidan da akayi mutuwa, bai dace ba mutane su dinga shiga gidajen da aka yi mutuwa alhali basu da hurumin shiga gidan da sunan yiwa mata ta'aziyya.

📌2. Taruwa a wani kebantaccen wuri domin karbar gaisuwa (ta'aziyya), kamar Masallaci ko gida ko Makabarta. Musamman yanzu wuraren karbar gaisuwa ya dauki wani sabon salo, wani lokaci kaga kamar buki ake yi an kawo rumfuna da kujeri sai abinci ake kawowa kala-kala, wani lokaci kuma ya zama wurin sharholiya da shaci fadi da giba da aibanta shugabanni da Yan siyasa da masu kudi harma da malaman addini. Kai abin bai tsaya nan ba wasu sun mayar da wurin karbar gaisuwa wani dandalin siyasa da rabawa matasa zauna gari banza kudade.

📌3. Abinci da iyalan mamaci ke tanada domin tarbon masu zuwa ta'aziyya, dalili akan haka shine: Hadithin Abdullahi Albajaliy yace: mu (Sahabbai) "MUN DAUKI TARUWA DON KARBAR GAISUWA (ta'aziyya) DA TANADIN ABINCI DON MASU TA'AZIYYA A MATSAYIN NIYAHAH (wato kururuwa ko kukan mutuwa). [Ahmad da bin Majah suka ruwaito sa, Imam An-Nawawiy ya inganta shi]

🖋️Haka kuma Imam An-Nawawiy a cikin littafin sa AL-MAJMU' sharhin MUHAZZAB na Shayhin Malami Shayraziy cewa yayi: " AMMA ZAMA DOMIN TA'AZIYYA IMAM AS-SAFI'IY DA SHAYRAZIY SUN NASSANTA KARHANCIN SA(kyamar sa)" abinda yake nufi sun karhanta taruwar iyalan mamaci a gida domin mai son yayi masu ta'aziyya ya same su yayi masu ta'aziyya, dai dai abin da ya kamata su tafi wajen bukatun su (na yau da kullum), duk wanda ya ya hadu dasu yayi masu ta'aziyya. Kuma babu bambanci wajen karhanta wannan zama tsakanin maza da mata.

🖋️Abinda Imam An-Nawawiy ya fada yana cikin littafin Imam As-shafi'iy: AL-UMM 1/248, ga kuma abinda yake cewa a cikin littafin: "INA KYAMAR TARON KARBAR TA'AZIYYA KODA BABU KUKA DOMIN YANA SABANTA BAKIN CIKI DA KALLAFA WAHALHALU NA KASHIN DUKIYA".

🖋️Shi kuma bin Humam ya nassanta karhancin a cikin littafin sa SHARHUL HIDAYAH 1/473, kuma yace: BIDI'AH CE MAI MUNI" kuma wannan shine mazhabar Hanabila kamar yadda yake cikin AL-INSWAF 2/565.

Kuma abinda kowa ya sani ne kamar yadda bayani ya gabata wurin karbar gaisuwa ya zama wurin fira, giba, kallon mata, labarin Yan siyasa, Yan kwallo, shugabanni, masu kudi da dai sauran su. Wanda hankali lafiyayye ba zai yarda da wannan ba balantana Shari'ah.

Wallahu a'alamu bissawab

Mu hadu a darasi na biyar (005)insha'allah

✍️ Nasiru Bala Bungudu
(Chief Imam Salih bin Abdil Aziz Juma'at Mosque Bungudu)

03 HUKUNCE HUKUNCEN TA'AZIYYA

HUKUNCE-HUKUNCEN TA'AZIYYA A MUSULUNCI.

DARASI NA UKU (003)

📒ABU NA UKU: BA'A IYAKANCE TA'AZIYYA DA KWANA UKU BA KAMAR YADDA WASU SUKE RIYAWA 📒

Ita Ta'aziyya ba'a iyakance lokacin yin ta da kwana uku ba, a'a, ana yin ta duk lokacin da aka ga fa'idar yin ta ko kuma lokacin da aka samu haduwa da wanda aka yiwa rassuwa, saboda Hadithin Abdullahi bin ja'afar da ya gabata a darasi na biyu kamar yadda yake cewa: bayan shi ja'afar yayi shahada sai Annabi SALLAL LAHU ALAIHI WASALLAM yayi jinkiri na kwana uku bai je gidan Ja'afar ba, sannan yazo yace: "KADA KU SAKE KUKA GA DAN UWANA DAGA YAU".
Abdullahi yace: sai Annabi yasa aka zo damu, sai muka zama kamar 'ya'yan tsuntsaye (saboda maraici) kuma yasa aka aske muna kawunan mu sannan ya mike hannu na a sama yace: YA ALLAH KA MAYEWA JA'AFAR A CIKIN IYALAN SA, KA SANYA ALBARKA GA ABDULLAHI (dansa) KUMA KA SANYA ALBARKA GA KASUWANCIN SA". ya fadi haka har dau uku. Daga nan dai mahaifiyar mu ta zo tana ambata masa maraicin mu kuma tana cike da damuwa, sai Annabi ya ce mata: "KINA JI MASU TSORON TALAUCI NE? ALHALI NINE MAJIBINCIN SU DUNIYA DA LAHIRA?".

Wallahu a'alamu bissawab.

Mu hadu a darasi na hudu(004) insha'allah.

✍️ Nasiru Bala Bungudu
(Chief Imam Salih bin Abdil Aziz juma'at Mosque, Bungudu)