🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KO YANA HALASTA YIN BIKIN MAULIDIN ANNABI MUHAMMAD S.A.W KO WANI DAGA CIKIN MAGABATA...!!!???*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
_Fitowa ta biyu (002)_
_Rubutawa;_ *_Hashim Surajo Uba Tsamiya(ABU SINÃN)_*
*Godiya ta tabbata ga Allah Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah s.a.w da mutanen gidansa da sahabbansa da duk Wanda yabi tafarkinsa da kyautatawa har tashin kiyama.*
_Bayan haka;_
_Nayi rubutu mai irin wannan take Wanda nace fitowa na gaba yana nan zuwa, to kuma insha Allahu zan cigaba da bada hujja akan haramcin Maulidi da kuma zamanshi bidi'ah abar kyama. Manzon Allah s.a.w ya kasance idan zaiyi huduba bayan ya godewa Allah, ya nemi taimakonshi da gafararshi daga karshe sai yace;_
(( أما بعد، فإن خير الحديث كتاب الله وخير الهدي هدي محمد صلى الله عليه وسلم وشر الأمور محدثاتها وكل بدعة ضلالة)).
_Ma'ana;_ *_"Bayan haka; Lallai fiyayyen zance shine littafin Allah, kuma fiyayyar shiriya ita ce shiriyar Muhammad s.a.w, kuma mafi sharrin al'amurra sune wadanda aka kirkiro, kuma dukkan bidi'ah bata ce"_* [Muslim ya ruwaito]
```Bayan wannan; yana daga cikin abunda yasa Malamai suka kyamaci bidi'ar Maulidi; bayan zamanshi bidi'ah, akwai haduwa mata da maza da wake wake da amfani da kayan kid'a (Badujala, piano,...) Da shaye shayen abubuwan dake sa maye, da wasu sharrance sharrance, wani lokaci Abunda yafi wadancan yana faruwa, wato shirka da Allah, ta hanyar wuce gona da iri wajen yabon Manzon Allah s.a.w ko waninsa kamar; Tijjani, Inyassi, jelani, Mahadi, Hussain, yaa Ali, ko waliyi na wheelbarrow. Za kaga ana Addu'ah ana Neman agajinsu da taimakonsu ko fadar cewa Annabi Muhammad s.a.w yasan gaibi ko wani daga cikin waliyyai, wadannan abubuwa duk zaka samu suna faruwa a wajen Maulidi. Shi kuwa Annabin Rahama s.a.w cewa yayi;```
((إياكم والغلو في الدين، فإنما أهلك من كان قبلكم الغلو في الدين)).
_Ma'ana;_ *_"Ku kiyayi yin shishshigi a cikin Addini, saboda babu wani Abu Wanda ya hallaka wadanda suka gabace ku face shishshigi a cikin addini._*
A wani Hadisin Manzon Allah s.a.w cewa yayi;
((لاتطروني كما أطرت النصاري ابن مريم إنما أنا عبد فقولوا: عبدالله ورسوله))
_Ma'ana;_ *_"Kada Ku zurfafa wajen yabo gareni kamar yadda kiristoci suka zurfafa wajen yabo ga Dan Maryam(Annabi isah) ni bawa ne kawai, saboda haka kuce; bawan Allah kuma manzon Allah._* [Bukhari ya ruwaito]
```Abin mamaki shine zaka samu da yawa daga cikin mutane suna kokari wajen halartar wadannan tarurrukan na bidi'ah, kuma suna kare masu yinsu, amma kuma sai kaga basa halartar wuraren Neman ilimi, Inda za'a nuna maka yadda zakabi Allah da Manzonsa ba inda za'a nuna maka falalar karya ta waliyyan karya ba. Babu shakka wannan yana daga cikin raunin imani da kuma karancin basira, kuma yana nuna cewa tsatsa ta rufe zukatansu ta nau'o'in zunubai da sabon Allah.
Allah ya karemu daga fadawa cikin shirka da bidi'ah da bata.
SUNNAH SAK
BIDI'AH SAM
MAULIDI SAM SAM SAN SAM SAM
Wa'ka:
DA MAULIDI NE ALAMAR SON MANZO
DAN FODIO DA BA ZAYA CE MAR BIDI'AH BA.```
Copyright©
*_Hashim Surajo Uba Tsamiya(ABU SINÃN)_*
📞08064734911📞
Https://mobile.facebook.com/hashimusurajo.tsamiya
Http://hashimtsamiya.blogspot.com
atstsamawy@gmail.com
No comments:
Post a Comment