.
*MACE BA'A TABA YI MATA KISHIYA*
*TA KIRKI*
1● In ka auro *USTAZIYA,* tace:
Munafukan gari, Allah a baki,
sharri a zuci, in ko ka auro 'yar
gayu tace ta fitsare kafa, ba tada
kamun kai.
2● In ka auro *MAI KYAU* tace
kyalkyal banza, ka auro mara
kyau tace an cuce ka.
3● In ka auro *FARA* tace Sadaka
Yalla ko Hasken Ambi, in baka ce
tace Bayan Tukunya.
4● Ka auro daga *DANGINTA* tace
kana son bata zumunta, in kaje
wani gun tace Tsintattar Mage.
5● Ka auro *yar makota,* tace
wadda ta gama sanin sirrimmu?,
in kaje nesa tace baa san asalinta
ba.
6● In ka auro *Babba,* tace an
kwaso kwashi kwaraf, in ko
karama tace girma ya fadi.
7● In ka auro *KAWARTA* tace duk
matan duniya?, don cin fuska da
cin amana?, in ko ka auri 'yar
aikin gidan, tace Tir !, wai iyakar
wulakanci ke nan, kuma baka da
taste.
8● Ka auro *YAR MANYA* tace: Kuda
wajen kwadayi akan mutu, in
'yar talakawa ka auro tace: Allazi
Wahidin, Allah baku mu samu.
9● In ka auri *YAR AMININ KA* tace:
Tsohon Banza, yau Baba ya koma
Bobo, in ko abokiyar aikinka a
ofis ka auro, sai tace: Abin boye
ya fito fili.
10● In ka auro mai *ABIN HANNUNTA*, ( wato Business woman) tace: Kano Jiddah
ko 'yar Dubai, in ko ba mai sana'a
bace, tace an kwaso cima zaune.
11● In ka auro *YAR MALAMAI* tace
asirce ka aka yi ba yinka bane, in
ko 'yar bata da karatu, sai tace
gidansu ko sallah baa iya ba.
12● In ka auro daga *DANGINKA*
tace ana son a hade kai a ware
ta, in kuwa bazawara ka auro, sai
tace: In kaga godiya da sirdi, to
wani ta kayar kuma wani mai
gigi zata sake kayarwa..........
_
Yaushe kenan zaa auro kishiya ta
kirki?
_
WAI ME YA SA mata basa SON
KISHIYA NE?
No comments:
Post a Comment