Saturday, 23 November 2019

020 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MU KYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa na Ashirin 020_

Gabatarwa: *Farida bintu salis*

*FASALI NA BIYU*

*CIKI NA ZAMANIN HAILA DA GWARGODONSA.*

Zance acikin wannan fasalin yana da matsayi guda 2.

*MATSAYI NA FARKO:*  A cikin shekarun da haila take zuwa acikin su.

*MATSAYI NA BIYU:*  A cikin lokacin Haila.

Amma shekarun da haila tafi rinjaye acikinsu MATSAYI NA FARKO shine: tsakanin
shekara 12 Zuwa shekara 50, amma ana samu sau da yawa mace tana yin haila a kafin
haka ko bayan haka gwargodon halinta da tasowarta da kuma tsufanta. Lallai malamai
sunyi sa6ani akan shin shekarun da haila take zuwa aciki suna da iyaka da aka ayyana ta
yadda mace ba zatayi haila gabanninsu ba ko bayansu. Kuma shin jinin da yake zuwa ga
mace a gabanninsu ko bayansu jinin haila ne ko na cuta? Malamai sunyi sa6ani acikin
wannan.
Darimiy yace: Bayan ya kawo sabanin: dukkan wadannan kuskure ne awajena domai a
baki dayan wannan yana komawa ne izuwa samuwar jinin, duk jinin da ya samu a kowani
hali da shekaru, ya wajaba a sanya shi a matsayin haila. Wallahu a'alamu. (Al-majmu'u
sharhil Muhazzab 1/336)
Wannan abunda Darimiy ya fada shine daidai, kuma shine za6in Sheikhul Islam Ibn
Taimiyyah. Wato duk sanda mace taga haila to ita mai haila ce koda bata cika shekara 9
ba ko kuma ta wuce shekara 50. Wannan kuwa saboda ALLAH da Manzonsa (SAW) sun
rataya hukuncin haila ne bisa suwarsa. Kuma ALLAH da Manzonsa (SAW) basu iyakance
wasu ayyanannun shekaru ba game da wannan ya wajaba komawa zuwa sumuwar jinin
wanda aka rataya hukunce hukunce a kansa. Iyakance shi da ayyanannun shekaru yana
buqatar dalili daga Qur'an ko sunnah. Gashi kuwa babu dalili akan haka.
Amma MATSAYI NA BIYU: Shine gwargodon Haila wato gwargodon zamaninta, haqiqa
malamai sunyi sa6ani mai yawa a kusan zantuka guda 6 koma 7.
Ibnul Munzir Yace: "wata jama'a tace: babu wata iyaka ta kwanaki ga mafi qarancin Haila
ko mafi yawanta"sai nace: wannan magana kamar maganar Darimiy ce wacce ta gabata,
haka kuma shine za6in Sheikhul Islam Ibn Taimiyyah kuma shine dai dai domin qur'ani
da sunnah da kuma abunda ake gani yau da gobe, sun nuna hakan.

ZAMU CIGABA INSHA ALLAHU

https://fb.me/abbansinan

Thursday, 21 November 2019

019 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na sha Tara  19_

LITTAFI: *JININ DABI'A GA MATA.*

WALLAFAR: *SHEIKH MUHAMMAD SALIH AL'UTHAYMEEN.*

FASSARAR: *UTHMAN MUSA GABARI*

GABATARWA: *FARIDAH BINTU SALIS(Bintus~sunnah)*

*MA'ANAR JININ HAILA DA HIKIMARSA!!!*

HAILA AYAREN LARABCI: shine kwararar abu da kuma gudanarsa.

A SHARI'A: shine jini da yake faruwa ga mace na dabi'a ba tare da wani sababi ba acikin
wasu sanannun lokuta.
Shine jini na dabi'a ( mai zubowa) ba tare da wani sababi na rashin lafiya ba ko rauni ko zubewar ciki ko haihuwa ba.
Saboda cewa shi jinine na dabi'a don haka yana sabawa gwargodon halin mace da yanayin tasowarta da tsufanta, saboda haka mata suna sassa6awa a cikinsa, sassabawa
mabanbanta na zahiri.

*HIKIMA A CIKINSA:*  yayin da dan tayi(yaro) ya kasance acikin mahaifiyarsa bazai yuwu ya
ringa yin kalaci da irin abunda mutum na wajen ciki yake yin kalaci dashi ba. Kuma bazai
yuwu ga wanda yafi kowa tausayinsa ba ya iya sadar da kalaci gare shi (ta kowace hanya
ba) saboda haka sai ALLAH (SWT) ya sanya jijiyoyin jini acikin mace wanda ta hanyar sune dan tayin(yaron) da yake cikin mahaifiyarsa zai dinga yin kalaci acikin mahaifiyarsa ta hanyar cibiya, jinin zai dinga shiga ta jijiyoyin d'an cikin yayi kalaci dashi. Tsarki ya tabbata ga ALLAH mafi kyawun masu halitta.
Wannan shine hikimar wannan saboda haka idan mace ta dauki ciki sai haila ta yanke mata sai 'yan kadan ne ke yin Haila idan suna da ciki, haka kuma masu shayarwa kadan ne ake samun wacce take yin Haila a cikinsu, musamman a farkon lokacin
shayarwa.

A NAN ZAMU DAKATA SAI A LOKACI NA GABA INSHA ALLAHU.


DOMIN SHIGA GROUPS DIN: *MU KYAUTATA NIYYA* NA MAZA KO NA MATA SAI A AYI MAGANA TA WHATSAPP NUMBER:
+2348064734911

https://fb.me/abbansinan

Saturday, 2 November 2019

06 BIDI'AR BIKIN MAULIDIN ANNABI MUHAMMAD

🖋 *BIKIN MAULIDIN ANNABI MUHAMMAD S.A.W*

● BABBAN MALAMI AT-TUWAIJARY (RH) YANA CEWA:

*《 Bikin maulidin Annabi Muhammad S.A.W a cikin shi akwai kamanceceniya da maulidin Annabi Isah A.S, yan bidi'ah suna yin maulidi ne da manufar cewa Annabi Muhammad S.A.W shi yafi chancanta da a girmama sama da Annabi Isah A.S, a wurin maulidi ana rera wakoki da Qasidodi na wuce gona da iri a wurin yabon Manzon Allah S.A.W, bayan Manzon Allah S.A.W yayi hani da yin hakan inda yake cewa: "Kada ku wuce gona da iri a wurin yabo na, kamar yadda kiristoci suka wuce gona da iri akan Annabi Isah A.S, ni bawan Allah ne, kuce bawan Allah Kuma Manzon shi... 》.*

📓📔 |[ الرد القوي على الرفاعي والمجهول وابن علوي للشيخ حمود التويجري (ص ٨٧) ]|

https://fb.me/abbansinan

#ABBAN_SINAN
+2349030201868

05 BIDI'AR BIKIN MAULIDIN ANNABI

● *BIDI'AR BIKIN MAULIDIN ANNABI MUHAMMAD S.A.W*

BABBAN MALAMI BASHEER AL-IBRAHIMY(RH) YANA CEWA:

*《 Manzon Allah S.A.W Yana kwadaitar daku akan riko da addini, ba riko da maulidi ba》.*

📓📔 |[ الآثار (١٤٤/٤) ]|

https://fb.me/abbansinan

#ABBAN_SINAN
+2349030201868

SHIN MAULIDI YANA DA WANI DALILI NE?

🖋 *SHIN WAI MAULIDI YANA DA WANI DALILI NE?*

● IMAM ASH-SHAUKANY(RH) YAKE CEWA:

*《 Har yanzu bamu samu dalili dake nuna tabbatuwar maulidi ba a cikin qur'ani ko hadisi ko ijima'in malamai, ko Qiyasi, ko wasu hujjoji, barima musulmai sunyi ittifaqi cewa ba'asan maulidi ba a zamanin Manzon Allah S.A.W da Sahabbai, haka a Qarnukan Nan guda uku masu daraja》.*

📓📔 |[ الفتح الرباني (١٠٨٧/٢) ]|

https://fb.me/abbansinan

#ABBAN_SINAN
+2349030201868

04 BIDI'AR BIKIN MAULIDIN ANNABI MUHAMMAD

🖋 *BIDI'AR BIKIN MAULIDIN ANNABI MUHAMMAD S.A.W*

● MALAMAN LAJNATUD DA'IMAH(Allah ya gafarta musu) SUKA CE:

*《Bukukuwan da akeyi saboda munasaba ta ranar da aka haifi Annabi bidi'ah ce haramtacciya, saboda babu dalili a cikin qur'ani ko hadisi da yake nuna halascin yin hakan, Kuma ba'a samu wani daya daga cikin khalifofin Annabi ba Wanda ya aikata, haka a cikin Qarnukan Nan masu falala ba'a samu wani Wanda ya aikata ba》.*

📓📔|[ فتاوى اللجنة الدائمة (٢٤٤/٢) ]|

https://fb.me/abbansinan

#ABBAN_SINAN
+2349030201868

03. BIDI'AR BIKIN MAULIDIN ANNABI MUHAMMAD

*🖋 BIDI'AR MAULIDIN ANNABI.A.W*

● ALLAMA AT-TUWAIJARY(RH) YANA CEWA:

*《Wadannan da suka riki maulidi ya zama idi, basu daga cikin wadanda ake yima fatar Allah ya basu lada akan wannan bidi'ar, abunda ma muke jiye musu tsoro shine azabar Allah, saboda saba umurnin abunda Manzon Allah S.A.W da Sahabbai suke akanshi.*
📓📔 |[ الرد القوي على الرفاعي والمجهول ابن علوي (ص ٢٢٣) ]|

https://fb.me/abbansinan

WANENE MAI GIRMAN KAI?

*WANENE MAI GIRMAN KAI GA ALLAH*❓

🍂IBN BA'D'DA AL-UKBARY(RH) YANA CEWA:

*Duk Wanda yaji gaskiya yayi inkarinta bayan yasan gaskiya ce, wannan Yana daga cikin masu girman Kai ga Allah, duk Wanda ya taimaka wurin yin sabo/zunubi/laifi Yana daga cikin tawagar shaidan.*

*📚 الإبانة في شرح أصول الديانة (٦٨٨)*

https://fb.me/abbansinan

02 BIDI'AR BIKIN MAULIDIN ANNABI MUHAMMAD

*🖋 BIDI'AR BIKIN MAULIDIN ANNABI S.A.W*

● AL-ALLAMA NASIRUDDEEN AL-ALBANY(RH) YANA CEWA:

*Mu AHLISSUNNAH dasu(yan bidi'ah) mun hadu akan cewa wannan bikin na maulidi abune kirkirarre, bai kasance ba a zamanin Manzon Allah S.A.W, Kai ba zamanin Manzon Allah S.A.W kadai ba, har karni uku(300+ years) suka wuce ba'a San dashi ba, Manzon Allah S.A.W bai taba yin biki ba saboda murnar haihuwar wani mutum a rayuwarsa, bikin maulidi hanyace ta kiristoci nasraniyya, masihiyya, musulunci bai San da maulidi ba Sam a wadancan karni masu daraja da muka ambata.*

📓📔 |[ من شريط بدعة المولد ]|

https://fb.me/abbansinan

01 BIDI'AR BIKIN MAULIDIN ANNABI

*🖋 BIDI'AR BIKIN MAULIDIN ANNABI S.A.W*

AL-ALLAMA ABDULLAHI BN HUMAID(RH) YANA CEWA:

*《Masu tsayuwa akan wadancan bukukuwan(maulidi) idan suna nufin sunyi hakan ne saboda girmama Manzon Allah S.A.W, toh su sani su masu sabawa shiriyarshi ne, masu kuskure ne akan hakan, baya daga cikin girmama Manzon Allah S.A.W kirkiro bidi'ah a cikin addinin daya zo dashi, ta hanyar ragi ko Kari, ko chanjawa ko karkatarwa, kyakyawar niyya da manufa Mai kyau basu halasta kirkiro bidi'ah a cikin addini 》.*

📓📔 |[ الرسائل الحسان في نصائح الإخوان للشيخ ابن حميد (ص ٣٩) ]|

https://fb.me/abbansinan

KIRKIRAR BIDI'AH

*KIRKIRAR BIDI'AH A CIKIN ADDINI IZGILI NE DA ALLAH; DOMIN KANA KUSANTAR MASHI ABUNDA BAI SHAR'ANTA BA.*

القول المفيد على كتاب التوحيد لابن عثيمين (١/٦٧)

https://fb.me/abbansinan

KO YANA HALASTA YIN BIKIN MAULIDIN ANNABI KO WANI DAGA CIKIN MAGABATA

🎤🎤🎤🎤🎤🎤🎤
*_KO YANA HALASTA YIN BIKIN MAULIDIN ANNABI KO WANI DAGA CIKIN MAGABATA...!!!???_*
🔊🔈🔊🔈🔉🔉🔊

_Fitowa ta daya 001_

_Rubutawa:_ *Hashim Surajo Uba Tsamiya*  *(ABU SINÃN)*

    *_Godiya ta tabbata ga Allah, Tsira da Amincin Allah SU tabbata ga Manzon Allah s.a.w da mutanen gidansa da  Sahabbansa da wadanda suka bi tafarkinsa._*

_Bayan haka;_

```Naga da cewar nayi wannan rubutun ne saboda yadda naga watan da yan bidi'ah ke sheke ayarsu ya kama, sannan kuma a wannan watane suke rudar jahillai suna batar dasu.
Amsar taken wannan rubutu itace; Bai halasta ayi bikin Maulidin Annabi ko maulidin waninsa daga cikin magabata, saboda yin haka yana daga cikin bidi'o'in da aka kirkiro a cikin addini, domin kuwa Manzon Allah s.a.w bai yiba, haka ma khalifofinshi guda Hudu shiryayyu da sauran sahabbai da wadanda suka bisu da kyautatawa duk basu yi maulidi ba, tare da cewa sunfi kowa sanin Sunnah da kuma aiki da ita, sunfi kowa So da kyaunar Annabi Muhammad s.a.w da kuma biyayya ga shari"'arsa, bisa wadanda suka zo bayansu.
Hadisi ya tabbata daga Annabi Muhammad s.a.w cewa;```
(من أحدث في أمرنا هذا ما ليس منه فهو رد).

_Ma'ana;_ *_Wanda ya kirkiro wani Abu a cikin wannan Al'amari namu(Addininmu) Wanda baya cikinsa, toh wannan Abu an mayar masa dashi.(Baza'a karba ba)_*

_Manzon Allah s.a.w a wani hadisin kuma sai yace;_
عليكم بسنتي وسنة الخلفاء الراشدين المهديين من بعدي، تمسكوا بها وعضوا عليها بالنواجد وإياكم ومحدثات الأمور، فإن كل محدثة بدعة وكل بدعة ضلالة.

_Ma'ana;_ *_Kuyi Riko da sunnah ta da sunnar khalifofi shiryayyu masu shiryarwa a bayana, kuyi riko da ita, kuma Ku cije a kanta da ha'koranku na can ciki, kuma Ku kiyayi kirkirarrun al'amurra, domin dukkan 'kir'kirarren Abu (a cikin Addini) bidi'ah ne, kuma dukkan bidi'ah bata CE._*

  ```A cikin wadannan hadisai biyu, akwai kashedi mai tsanani a kan kirkirar bidi'ah da kuma aiki da ita!
Allah madaukakin sarki ya fada a cikin littafinsa mai tsarki cewa;```
((وما ءاتكم الرسول فخذوه وما نهاكم عنه فانتهوا)).

_Ma'ana;_ *_Abin da Manzon Allah yazo muku dashi to Ku rikeshi, abin da kuma ya haneku ga barinsa, toh Ku hanu. [Al-hashr, aya ta 7]_*
A nan Allah yayi mana umurni da bin manzon Allah ba da yin maulidi ba

A wani wurin kuma sai Allah yace;
((فليحذر الذين يخالفون عن أمره أن تصيبهم فتنة أو يصيبكم عذاب أليم))
_Ma'ana;_ *_Wadanda suke saba wa umurninsa, baza suyi tunanin wata fitina ta samesu ba, ko wata azaba mai radadi ta samesu[An-Nur, aya ta 63]_*
A Wata ayar sai Allah yace;
اليوم أكملت لكم دينكم وأتممت عليكم نعمتي ورضيت لكم الإسلام دينا.

_Ma'ana;_ *_A yau na kammala maku addininku, kuma na cika ni'imata a kanku, kuma na yarda da musulunci ya zama Addini a gareku._*
          [Al-ma'ida aya ya 3]
 
Da kuwa ace maulidi addinine da yazo kafin saukar wannan ayar.

```Ayoyi da suke da irin wannan ma'ana suna da yawa, kuma kirkiro irin wadannan tarurruka na Maulidi yana nuna cewa Allah s.w.t bai cika Addini ba! Kuma Manzon Allah s.a.w bai Isarwa Al'umma da abunda ya kamata suyi aiki dashi ba! (Wanda duk ya fadi haka kuwa to tabbas ya zama ARNE)
Domin kuwa manzon Allah s.a.w a cikin hadisi ingantace yake cewa;
((ما بعث الله من نبي إلا كان حقا عليه أن يدل أمته على خير ما يعلمه لهم، وينذرهم شر ما يعلمه لهم)).

Ma'ana; Allah bai aiko wani Annabi ba, face ya kasance hakki ne akan wannan Annabin ya nuna wa Al'ummarsa Alherin da ya sani garesu, kuma yayi musu gargadi daga sharrin da ya sani garesu. [Muslim]

Wadannan ayoyi da hadissai kawai sun isa su tabbatar mana da cewa Maulidi ba Addinin Annabi Muhammadu bane, ba ya daga cikin hanyoyin shiriya na Addini, Hasali ma BIDI'AH CE abar kyama.

Sai mun hadu a fitowa na gaba.

*ABU SINÃN*
📞08064734911

Https://fb.me/abbansinan