🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI*
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Wallafar: *Ash-Sheikh Muhammad Sani Liman Tsafe(ABU HURAIRAH)*
_001_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
✅ *MECE CE ZUMUNTA?*
*_IBN ATHEER_* yana cewa: Zumunta tana nufin taimakawa yan uwa na bangaren dangantaka da sarakuta da kula da halayen su koda kuwa suna zaune a wurare masu nisa koda kuma suna munana maka (a daya bangaren kuma yanke zumunta yana nufin kishiyar abubuwan da aka ambata a baya).
✅ *DA WANE ABU AKE SADAR DA ZUMUNTA?*
Ana sadar da zumunta da al’amura masu yawa kamar ziyartarsu, bibiyar halayansu, tambaya game dasu, aika masu da kyaututtuka da kuma saukar da kowannensu a matsayin da ya dace dashi, da bada sadaka ga fakirai daga cikinsu, da tausasa ma mawadatansu(Binsu a hankali) da girmama manyansu, da kuma tausaya ma kananansu, da masu rauninsu, da yawan tambayar halin da suke ciki, da kuma ziyartarsu da kanka ko ka aika wasika ko kayi amfani da wayar salula.
Mafi girman abin da ake sadar da zumunta da shi shine yin wa'azi garesu, kamar yadda Allah madaukakin sarki yake fada wa manzonshi cewa: *_"(KAYI GARGADI GA DANGINKA MAKUSANTA)"_* [shu'araa 214]
Haka kuma Manzon Allah (salallahu alaihi wasallam) ya rinka kiran danginsa domin ganin sun shigo addinin musulunci.
Saboda haka mutum yayi kwadayin kiran yan uwansa zuwa ga shiriya ya umurce su da aiki mai kyau, ya kuma hane su da aikata miyagun ayyuka.
Zumunta tana bambanta gwargwadon kusanci da matsayi na wadanda ake sadar da zumunta zuwa garesu, zumunci da yake tsakanin uba da dan-dansa yana da bambanci da dan-dan dan uwa na nesa. Bugu da kari, zumunta tana bambanta gwargwadon halayen wadanda za’a sadarmawa suke ciki, kamar sadar da zumunta ga marar lafiya da mabukaci ta bambanta da sadarwa ga waninsu. Haka ma sadarwa ga babba ta bambanta da ta karami. Haka sadar da zumunta yana bambanta ta fuskar bigire, wanda yake zaune a cikin gari ya bambanta da wanda yake zaune a wani gari wajen ziyartar shi, tambayar halin da yake ciki, da yi masa sallama ko aika mashi da sakonni.
ZAMU DAKATA A NAN, INSHA ALLAHU A GABA ZA KUJI *FALALAR SADA ZUMUNTA*
DOMIN CIGABA DA SAMUN WANNAN RUBUTU KUNA IYA AIKEWA DA SAQON WHATSAPP ZUWA GA: +2349030201868
#ABBAN_SINAN
https://fb.me/abbansinan
No comments:
Post a Comment