*MINENE GASKIYAR MAGANA AKAN HADE SALLOLIN AZHR DA LA'ASAR KO MAGRIB DA ISHA'I A LOKACIN SANYI MAI TSANANI???*
Rubutawa: *ABU_SINAN ATS~TSAMAWY*
Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad S.A.W da iyalan gidansa da sahabbansa baki daya.
Bayan Haka:
Yan uwa Yana da kyau mu fahimci cewa ita fa shari'ah tazo mana da sauki a lokacin da aka shiga cikin tsanani, haka tazo mana da saukakawa a cikin ibada a kowane al'amari Wanda a cikinsa akwai wahala da takura wacce take a bayyane. Kamar yadda Allah madaukakin sarki yake cewa:
*يريد الله بكم اليسر ولا يريد بكم العسر...*
Da Kuma inda Allah madaukakin sarki yake cewa:
*وما جعل عليكم في الدين من حرج...*
Duka Wadannan suna nuna Mana cewa addinin Allah sauki ne dashi.
Yazo a cikin sahihul bukhari, Hadisin da Abi Hurairah ya ruwaito, Manzon Allah S.A.W yace: *_"Lallai shi addini sauki ne, babu Wanda zai dauki addini da tsanani face sai addinin ya rinjayeshi...."_*
Allah madaukakin sarki Yana son mu karbi sauki daga gareshi a lokacin da ya saukaka Mana, ko a cikin abubuwan da ya saukaka Mana.
Ya tabbata a Sunnah, saukakawa a cikin ibada a lokacin da ake zaune gida da lokacin tafiya a wani yanayi kebantacce. Daga cikin abin da ya tabbata na saukakawa akwai *sanyi Mai tsanani ga mutane.*
Dalilin hakan shine saboda gudun kada mutum ya kamu da rashin lafiya a rayuwarsa.
Amma sanyi Wanda baya cutarwa baya halasta, hukuncinsa kamar hukuncin sauran sanyi ne na jin dadi da more rayuwa.
*AN RANGWANTA YIN SALLAH A GIDA KAMAR YADDA AKA RANGWANTA HADE SALLOLI A LOKACIN SANYI MAI TSANANI*
An rangwanta ma Wanda sanyi Mai tsanani ya shafa da yayi Sallah a gidansa, ya bar jama'ah a masallaci. Dalilin hakan shine abin da Nafi' ya ruwaito cewa: *_"ibn Umar ya kira Sallah a wani dare Mai sanyi a wani gari ko wuri da ake Kira DHAJNAN, Sannan yace: kuyi Sallah a cikin gidajenku, sai ya bamu labari cewa: Manzon Allah S.A.W Yana umurtar ladan ya kira Sallah Sannan ya sashi ya fadi cewa: KUYI SALLAR KU A DAKUNAN KU. A dare Mai sanyi, ko lokacin da sukayi doguwar tafiya."_*[Bukhari da Muslim]
Haka Abu Daud yayi babi a cikin littafin shi, sunan babin: *_BABIN DAKE MAGANA AKAN RABUWA DA JAMA'AH A DARE MAI SANYI._*
Haka Babban Malami *Ibn Qudama* a cikin littafin shi Mai suna: المغني yace: *_Anyi uzuri ga barin jama'ah saboda tsananin iska a dare Mai duhu Kuma Mai sanyi._*
Haka Muslim ya fitar a cikin littafin shi, daga Ibn Abbas (R.A) yace: *_"Manzon Allah S.A.W yayi sallar azhr da la'asar a lokaci guda, magrib da isha'i a lokaci guda ba tare da akwai tsoro ba, ba tare da yayi tafiya ba, ba Kuma ruwan sama akayi ba. An tambayi Ibn Abbas: me yasa yayi hakan toh? Sai yace: Yana nufin kada ya tsananta ma al'ummarshi ne."_*
Saboda haka abin da yake ingantacce shine, ana hade sallolin azhr da la'asar ko magrib da isha'i a lokacin da sanyi ya tsananta.
Haka imamu Ahmad ya ruwaito cewa: *_"Abdullahi Dan Umar ya kasance yana hada salloli a daren da ake tsananin sanyi."_*
Abin da yake na dai dai ga musulmi shine ya saukaka ma kanshi da saukakawar mahaliccinshi, kada ya tsananta ma kanshi ko al'ummarshi.
Akwai maganganun malaman mazhabobin Malikiyya da Shafi'iyya da Ahmad da Abu hanifa akan wannan matsalar. Mazhabin Abu Hanifa kadai ne ya sabawa sauran mazhabobin, shi Abu Hanifa ma yana ganin cewa baya halasta a hade wata Sallah idan ba a arfa ba(Azhr da la'asar) ko muzdhalifa(Magrib da isha'i)
Amma sauran mazhabobin guda uku duk sun yarda a hade salloli saboda tsananin sanyi, inda suka danyi sabani shine wasu na ganin cewa ba za'a hade azhr da la'asar ba wasu Kuma sunce har su za'a hade matukar sanyin da ake ya tsananta.
ALLAH MADAUKAKIN SARKI SHINE MASANI.
#ABU_SINAN
+2349030201868
https://fb.me/abbansinan
No comments:
Post a Comment