Tuesday, 14 July 2020

MAKABARTA GIDAN KOWA DA KOWA

*MAKABARTA GIDAN KOWA DA KOWA*

*LADUBBAN ZIYARAR MAKABARTA*


Godiya ta tabbata ga Allah shi kadai Wanda ya halitta rayuwa kamar yanda yaso Kuma yake karbarta a lokacin da yaso, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad S.A.W Wanda aka baiwa zabin zaman duniya ko Kuma komawa zuwa ga Allah, ya zabi ya koma zuwa ga mahaliccinsa.

Bayan haka:

Dalilin wannan rubutun shine, kasantuwar Koda yaushe Allah yana karbar rayukan mutane, wadanda ke raye kuma suna ziyarar makabartu domin binne wadanda Allah ya karbi rayukansu, toh amma Sai naga yanzu al'ummar da muke rayuwa a cikinta mun gafala daga kabari da Kuma Azabar dake tattare dashi, wannan ne yasa naga dacewar in tunatar da yan uwana musulmi akan kabari da Kuma ziyarar shi.

*HAKURI IDAN ANYI MAKA MUTUWA*

Manzon Allah S.A.W ya wuce wasu kaburbura a wata Rana, Sai ya ga wata mata tana kuka😢 a kusa da Wani kabari, Sai Annabi S.A.W yace mata: kiji tsoron Allah, kiyi hakuri, ita wannan matar Bata San cewa Annabi S.A.W bane yake mata magana, Sai tace mashi: tafi ka kyale ni, saboda Kai musibar da ta sameni bata same ka bane don haka.
Sai Manzon Allah S.A.W ya wuce ya kyaleta, Sai ake fada mata cewa: Shifa Wanda yake maki magana Annabi ne! Sai ta tafi da sauri ta sameshi, tace: Ni bansan kai Annabi bane. Sai Annabi S.A.W yace mata:
Hakuri a lokacin mutuwa shi yafi.[Bukhari da Muslim]
Ita musiba tana bukatar hakuri, dole ne musulmi yayi hakuri idan Wani Abu na damuwa ya sameshi, Manzon Allah S.A.W ya ziyarci kabarin mahaifiyarshi, Sai yace: na nemi izinin ubangiji akan a bani dama in nema mata gafara, Amma ba'a bani izini ba, Sai na nemi izini akan ziyartar kabarinta, Sai akayi mani izini. Sai Annabi S.A.W yace: ku ziyarci kaburbura, domin suna tuna mutuwa.
 [مسلم وأبو داود]
Daya daga cikin magabata yake cewa: Idan al'amurra suka tsananta gareka, toh ka ziyarci kaburbura, domin ziyarar kabari tana tausasa zukata, tana tuna maka da lahira.
Uthman bn Affan(R.A) ya kasance idan aka ambaci Aljanna da Wuta a gabanshi baya kuka, Amma da zarar an ambaci kabari Sai ya fashe da kuka. Sai aka tambayeshi akan hakan, Sai yace: Naji Manzon Allah S.A.W yaana cewa:
Kabari shine farkon masaukin lahira, idan ka tsira daga gareshi, abunda zai biyo bayanshi yafi sauki, idan baka tsira daga gareshi ba, abunda zai biyo bayanshi yafi tsanani
  [أحمد]

Ziyarar kaburbura Yana da wasu ladubba da ya kamata musulmi ya ladabtu dasu, daga cikinsu akwai:

1. HALARTO DA NIYYA: Dole ne musulmi ya kudurce zai ziyarci makabarta ne don Allah, sannan Kuma domin ya gyara bannar da zuciyar shi ke aikatawa.

2. YIMA MAMATA ADDU'AH: Ana bukatar Mai ziyarar makabarta yayima mamatan dake kwance a cikin kaburbura addu'ah, kamar yadda Annabi Muhammad S.A.W ya koyar da sahabbanshi, addu'ar itace kamar haka:
السلام عليكم أهل الديار من المؤمنين والمسلمين، ويرحم الله المستقدمين منا والمستأخرين، وإنا إن شاء الله بكم لاحقون.
 [مسلم].

Fassarar addu'ar itace kamar haka: 
Amincin Allah ya tabbata ga ma'abota wadannan gidaje, muminai da musulmai, Allah yayi rahama ga wadannan suka Dade da mutuwa daga cikinmu da Kuma yan baya, Kuma in Allah ya yarda mu ma zamuyi tarayya daku a wannan gida

3. BA'A ZAUNAWA, KO TAFIYA AKAN KABURBURA:
Dole ne musulmi yayi kokarin ganin daina zama ko kishingid'a, ko zirga zirga a saman kaburbura, saboda fadar Annabi Muhammad S.A.W cewa: Mutum ya zauna akan garwashin Wuta, ya Kona tufafinsa, ya taba fatar jikinsa, shi yafi alkhairi gareshi akan ya zauna/ya du'ka akan/a gaban kabari
 [مسلم]

4. KARANTA ALQUR'ANI DA KUMA TAWASSALI AKAN ALLAH YA KAI LADAR GA MAMATA:
Babu laifi mutum ya karanta Wani Abu daga cikin abunda ya sawwaka gareshi na Qur'ani Mai girma, sannan ya roki Allah ya karba mashi abunda ya karanta, sannan ladar Allah ya Kai ga mamacin.

5. BAYA HALASTA TABARRUKI DA KABURBURA:
Baya halasta a nemi tabarruki da kaburbura, kamar yadda baya halasta a sumbaci kabari kamar yadda jahilai daga cikin gama-garin mutane suke aikatawa, dogaro da Hadisin da Annabi Muhammad S.A.W yake cewa: Idan zakayi roko ka roki Allah, idan zaka nemi tsari, ka nemi tsarin Allah
[الترمذي].

6. BA'A DARIYA KO WASA A MAKABARTA:
Dariya da wasa a cikin makabarta dalilai ne na kekashewar zuciya, makabarta wuri ne dake sa musulmi ya nisanci wasan tsalle tsalle da guje guje a cikinta, saboda kaburbura suna tunatar da Mai dauke duk Wani jin dadi(MUTUWA), a cikinta akwai tunani Amma ga Masu hankali daga cikin mutane.

7. YABO GA WADANDA SUKA MUTU, DA AMBATON KYAWAWAN AYYUKANSU:
Baya halasta zagin mamata, ko ambaton kurakuran su, matukar sun mutu akan musulunci,
Annabi Muhammad S.A.W Yana cewa: kada ku zagi mamata, domin su sun Rika sun riski abunda suka gabatar
 [البخاري]

A Wani Hadisin Manzon Allah S.A.W Yana cewa: kada ku ambaci matattunku Sai da alkhairi
 [النسائي]

8. BA'A SALLAH A MAKABARTA:
Annabin Rahama S.A.W yayi hani akan yin sallah a a makabarta, ko fuskantar makabarta a lokacin da mutum yake sallah, an riwaito daga Abdullahi Dan Umar (R.A) yace: Manzon Allah S.A.W yayi hani akan yin sallah a wurare guda bakwai, 1. A cikin bola(juji), 2. Kwata(Mayanka), 3. Makabarta, 4. Magamar hanya, 5. Makewayi(Toilet), 6. Wurin da ake daure rakuma, 7. Da kuma saman dakin ka'aba
[ابن ماجه]

Musulmi Yana da kyau ya Rika ziyarar makabarta, zuciyarshi zata cika da tausayi da imani, Sai kaga kana aikata ayyukan kwarai, Sai kaga Allah ya datar dakai kana yi mashi biyayya, kana lizimtar abubuwan da Allah yace ayi, kana nisantar abubuwan da Allah ya hana. Haka nan Kuma ziyarar musulmi zuwa makabarta tana sanya musulmi ya Rika tsoron wannan rayuwar ta duniya, musamman idan ya tsaya a gaban kabari tsayuwa ta dubo da tunani, kana tunanin halin da wadanda ke cikin kaburburan suke a lokacin da suna duniya, suna Kai da kawo, suna ayyuka mabanbanta, Amma fa yanzu gashi basu iya aikata komai daga cikin abubuwan da suke aikatawa a duniya, abunda zai tseratar dasu kadai ayyukansu na Alkhairi da suka aikata a duniya, sannan Sai Kai kayi tunani a karan kanka, kaima Wani lokaci zaka kasance a cikin irin wannan halin. Wannan Sai ya taimakeka wurin yin aiki na kwarai a nan duniya, domin tseratar da kanka daga azaba a ranar hisabi.


Allah muke roko daya gafartawa mamatanmu, mu Kuma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da imani🤲🤲🤲



Dan uwanku a musulunci
✍ *ABU SINAN*
+2349030201868
atstsamawy@gmail.com

No comments: