Thursday, 29 July 2021

002 ‏FARIN JEKADA ANNABI MUHAMMAD ‎ﷺ

FARIN JEKADA, ANNABI MUHAMMAD ﷺ

Fitowa ta biyu 002

Manzon Allah ﷺ yana da wasu haƙƙoƙi masu tarin yawa da ba za'a iya ƙirge su ba, waɗanda suka zama wajibi mu kula dasu kwarai da gaske.
Ga kaɗan daga cikin su:

1. IMANI DA MANZON ALLAH ﷺ

Ma'anar imani da Manzon Allah ﷺ kamar yadda wasu daga cikin Malamai suka faɗa shine: 
a) Gasgata shi a cikin duk abinda ya faɗa ko ya bada labari
b) Yi Mashi biyayya a cikin dukkan komai
c) Bin Shari'ar Manzon Allah ﷺ
Don haka ne ma wasu daga cikin Malamai suka ce gasgata Manzon Allah ﷺ yana ɗaukar abubuwa guda biyu:
NA FARKO: Tabbatar da AnnabtarSa ﷺ da gasgata Shi akan duk abinda ya isar daga Ubangijin Shi SWT, da kuma yadda cewa Wannan ya keɓanci Manzon Allah ﷺ ne kawai (Ma'ana: babu wani Annabi da zai zo da irin wannan a bayan Shi ﷺ

NA BIYU: Gasgata Shi ﷺ a cikin abinda yazo dashi, ka yarda cewa yazo dashi ne daga wurin Allah SWT, sannan kuma wajibi ne a bishi.

Wajibi ne a Gasgata Manzon Allah ﷺ a cikin dukkan abinda ya bada labari daga Allah SWT, Na abubuwan da suke na Gaibu ne, Labarin Wuta da Aljanna, Labarin tanadin Sakamako mai kyau ga wanda ya kyautata aiki, da mummunan sakamako Ga wanda ya ɓata aikinsa, Labarin Azabar ƙabari da kuma Ni'imomin dake cikin shi, da dukkanin wani abu da Manzon Allah ﷺ ya bada labari dole ne a Gasgata Shi ﷺ.
Allah Maɗaukakin sarki yana cewa:
وَمَا يَنطِقُ عَنِ الۡهَوَىٰ، إِنۡ هُوَ إِلاَّ وَحۡيُُ يُوحَىٰ
Ma'ana:
Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa.
(MaganarSa ﷺ) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.

Zamu dakata a nan Saboda kada Rubutun yayi Tsayi, a fitowa ta gaba zamuyi Magana akan: ABUBUWAN DAKE WARWARE IMANI DA MANZON ALLAH ﷺ Allah ya ɗora mu akan Tafarki na gaskiya har ƙarshen Rayuwar mu, Allah ya kare Addinmu na Musulunci daga Makircin yahudu da Nasara🤲 yaa Allah ka rugurguza duk masu taɓa ƙima da mutuncin Manzon Allah ﷺ a duk inda suke, yaa Allah da wanda akayi yaji daɗi, da wanda yayi, da wanda yana da ikon magana amma yayi shiru Saboda kada arna suce mashi mai tsats-tsauran ra'ayin addini, yaa Ubangiji duk ka tozarta su a nan duniya da gobe ƙiyama🤲 yaa Ubangiji ka ƙara mana Son Annabi Muhammad ﷺ🤲 kasa mu mutu muna masu bin shiriyar Annabi Muhammad ﷺ


✍️ Hashim Sirajo Uba Ats-tsamawy Tsafe
atstsamawy@gmail.com
18/12/1442AH
28/07/2021

01 ‏FARIN JEKADA ANNABI MUHAMMAD ‎ﷺ

FARIN JEKADA, ANNABI MUHAMMAD ﷺ 

Fitowa ta Farko 001

KO KASAN MA’NAR MUHAMMADUR RASULULLAHI ﷺ ?

Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) wanda ya haɗa Sunan shi da sunan Manzon sa a wajen kalmar Shahada.

Tsira da Aminci su tabbata ga Manzonsa wanda ya fayyace mana ma’anar kalmar shahada ga ayyukansa.

Ma’anar ka shaida MUHAMMADU Manzon Allah ne, shine yin furuci a ɓoye da bayanne, cewa lallai Annabi Muhammad ﷺ bawan Allah ne kuma Manzon Allah ne zuwa ga mutane baki daya, da kuma aiki da abun da wannan kalmar ke ɗauke da shi.

Ya kamata kai Ɗan uwa Musulmi kasani cewa kalmar MUHAMMADURRASULULLAH ﷺ 
tana da ma’ana da rukunnai da sharuɗɗa, da kuma abun da ta hukunta. Ga yadda ma’anar take:

Yiwa Manzon Allah ﷺ ɗa’a a cikin abinda yayi umurni, gasgata shi a cikin abinda ya bada labari, nisantar abinda ya hana ko ya tsoratar, ba’a bautar Allah, bautar kuma ta samu karɓuwa face yadda Manzon Allah ﷺ 
ya tsara (ya shar’anta).
Dole ne mai faɗar Muhammadur Rasululahi ﷺ 
 yayi aiki da waɗannan bayanai, domin faɗar hakan da harshe kawai ba zai wadatar ba.

RUKUNAN MUHAMMADUR RASULULLAHI ﷺ 
 GUDA BIYU (2) NE:

RUKUNI NA FARKO: 
SHINE ZAMAN SHI BAWAN ALLAH:
 Zaman shi bawan Allah yana kore zurfafawa gareshi. Kamar yadda hadisin da Bukhari ya ruwaito yana cewa "Kada ku ɗagani kamar yadda nasara suka ɗaga ISA DAN MARYAM (A.S) Ni bawan Allah ne kuma Manzonsa ne.”
Ma’anar bawan Allah shine: mutum ne wanda aka halitta daga cikin halittar Allah yana gudana a gareshi abin da yake gudana ga mutane kamar yadda Allah SWT ke faɗa cewa: - “Kace masu lallai ni mutum ne irinku (Suratul Kahfi 109). Cewa da wasu keyi Manzon Allah ﷺ  ba mutum bane wannan zurfafawa ne, da kuma nakkasa shi. Masu faɗar wannan sun can-can-ci a hukunta su.

RUKUNI NA BIYU: SHINE MANZON ALLAH (S.A.W): - Ma’anar Manzon Allah ﷺ 
shine wanda aka aiko ga wasu ko kuma ga mutane baki ɗaya don kira ga Allah. Shi Mai bushara ne mai gargadi.

SHARUDDAN MUHAMMAD RASULULLAH ﷺ 
 GUDA SHIDA (6) NE:

1. Furuci da ManzancinSa da kudiri a cikin zuciya.

2. Bin Manzon Allah ﷺ da aiki da abunda yazo da shi na gaskiya, da barin abun daya hana na ɓarna.
3. Gasgata abin da ya bada labari na gaibu daya wuce da kuma mai zuwa.

4. Son Manzon Allah ﷺ fiye da kanka da dukiyarka da uwayenka da sauran mutane baki daya.

5. Gabatar da zancen shi akan zancen ko wane mutum da kuma aiki da sunnar Shi ﷺ 

6. Bashi kariya daga kowace nakasa da kuma kare sunnar shi iya karfinka.

ABINDA KALMAR TAKE HUKUNTAWA SHINE:

Yi mashi Ɗa’a, gasgatashi, barin abin da ba sunnar Shi bane, (kamar bidi’o’i da ƙage-ƙage)ﷺ 

FADAKARWA

A karshe muna kira ga ‘yan uwa Musulmi su sani cewa Allah bai karɓar duk wani aiki face sai ya cika sharuɗɗa guda biyu (2).

IKHLASI: - Shine yin aiki don Allah

MUTABA’A: - Bin Manzon Allah ﷺ 
sau da kafa a cikin duk abinda zaka gabatar, kamar yadda bayanai suka gabata.

Daga karshe muna roƙon Allah (S.W.T) ya aza mu kan bin Sunnar Manzon Allah ﷺ  kuma ya kashemu a kanta Amin.

Rubutawa
Abu Sinan, Hashim Sirajo Uba Ats-tsamawy Tsafe
17/12/1442AH
27/07/2021