Thursday, 29 July 2021

002 ‏FARIN JEKADA ANNABI MUHAMMAD ‎ﷺ

FARIN JEKADA, ANNABI MUHAMMAD ﷺ

Fitowa ta biyu 002

Manzon Allah ﷺ yana da wasu haƙƙoƙi masu tarin yawa da ba za'a iya ƙirge su ba, waɗanda suka zama wajibi mu kula dasu kwarai da gaske.
Ga kaɗan daga cikin su:

1. IMANI DA MANZON ALLAH ﷺ

Ma'anar imani da Manzon Allah ﷺ kamar yadda wasu daga cikin Malamai suka faɗa shine: 
a) Gasgata shi a cikin duk abinda ya faɗa ko ya bada labari
b) Yi Mashi biyayya a cikin dukkan komai
c) Bin Shari'ar Manzon Allah ﷺ
Don haka ne ma wasu daga cikin Malamai suka ce gasgata Manzon Allah ﷺ yana ɗaukar abubuwa guda biyu:
NA FARKO: Tabbatar da AnnabtarSa ﷺ da gasgata Shi akan duk abinda ya isar daga Ubangijin Shi SWT, da kuma yadda cewa Wannan ya keɓanci Manzon Allah ﷺ ne kawai (Ma'ana: babu wani Annabi da zai zo da irin wannan a bayan Shi ﷺ

NA BIYU: Gasgata Shi ﷺ a cikin abinda yazo dashi, ka yarda cewa yazo dashi ne daga wurin Allah SWT, sannan kuma wajibi ne a bishi.

Wajibi ne a Gasgata Manzon Allah ﷺ a cikin dukkan abinda ya bada labari daga Allah SWT, Na abubuwan da suke na Gaibu ne, Labarin Wuta da Aljanna, Labarin tanadin Sakamako mai kyau ga wanda ya kyautata aiki, da mummunan sakamako Ga wanda ya ɓata aikinsa, Labarin Azabar ƙabari da kuma Ni'imomin dake cikin shi, da dukkanin wani abu da Manzon Allah ﷺ ya bada labari dole ne a Gasgata Shi ﷺ.
Allah Maɗaukakin sarki yana cewa:
وَمَا يَنطِقُ عَنِ الۡهَوَىٰ، إِنۡ هُوَ إِلاَّ وَحۡيُُ يُوحَىٰ
Ma'ana:
Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa.
(MaganarSa ﷺ) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.

Zamu dakata a nan Saboda kada Rubutun yayi Tsayi, a fitowa ta gaba zamuyi Magana akan: ABUBUWAN DAKE WARWARE IMANI DA MANZON ALLAH ﷺ Allah ya ɗora mu akan Tafarki na gaskiya har ƙarshen Rayuwar mu, Allah ya kare Addinmu na Musulunci daga Makircin yahudu da Nasara🤲 yaa Allah ka rugurguza duk masu taɓa ƙima da mutuncin Manzon Allah ﷺ a duk inda suke, yaa Allah da wanda akayi yaji daɗi, da wanda yayi, da wanda yana da ikon magana amma yayi shiru Saboda kada arna suce mashi mai tsats-tsauran ra'ayin addini, yaa Ubangiji duk ka tozarta su a nan duniya da gobe ƙiyama🤲 yaa Ubangiji ka ƙara mana Son Annabi Muhammad ﷺ🤲 kasa mu mutu muna masu bin shiriyar Annabi Muhammad ﷺ


✍️ Hashim Sirajo Uba Ats-tsamawy Tsafe
atstsamawy@gmail.com
18/12/1442AH
28/07/2021

No comments: