Monday, 23 December 2019

JAKAR MAGORIN ADDININ MUSULUNCI

GABATARWA
Da sunan Allah Mai Rahama mai sadar da rahamarsa ga bayi, Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Rahama Annabi Muhammad (S.A.W.) wanda yake shine yazo mana da bayanin duk abinda rayuwar Dan Adam ta kunsa tun daga halittarsa har zuwa komawa ga Ubangijinsa.
Dalilan da suka sa muka hada wannan littafi shine:-
A masallacin mu na Abu Huraira duk lokacin da mukayi karatu, a cikin karance  karancen  da muke yi tsakanin Magriba da IshaI, muna kokarin fitar da mukaloli domin amfanin alummar musulmi, har ya kai mun fitar da mukala fiye da hamsin (50)
Wannan shine asalin littafin.
Jamaa sun dade suna bamu Shawarwari cewa ya kamata mu hada wadannan mukalat don su koma littafi guda domin amfanin alummar musulmi baki daya, wannan na daga cikin abinda ya jawo hankalinmu wajan hada wannan littafi.
Mun sama wannan littafi suna (Jakar Magorin Musulunci) saboda irin abunda ya kunsa daban-daban na bangarorin addinin musulunci.
Mun hada wannan littafi ne don shiga cikin wadanda Allah yace "Ku zama alumma wadda zata kira mutane zuwa ga alheri kuma tayi umurni da maarufi kuma tayi hani da munkari, masu yin haka sune masu babban rabo" (AlImrana 110).
Muna rokon Allah madaukakin sarki da sunayen sa kyawawa da suffofinsa madaukaka ya sanya wannan aiki mun yi shine don neman fuskarsa maigirma, lalle shi majibincin haka ne kuma mai iko ne akai.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammadu da Alayensa da Sahabbansa Baki daya.

GODIYA
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah (S.W.T) wanda ya aiko da manzanninsa domin kira da karantarwa ga bayinsa kuma ya saukar da littafai domin su zama abubuwan karantarwa da tunatarwa ga bayinsa kuma ya sanya ilimi ya zama tabbacin harsashin bauta masa.
Tsira da aminincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) wanda yake shine cikamakin Annabawa kuma shugaban manzanni. Sannan muna mika matukar godiya  ga wadanda suka taimaka wajen ganin wannan littafi ya kamala. Daga cikin su akwai:-
Sarkin Yakin Tsafe  Alh. Sanda Adamu wanda shine jigon tafiya wajen hada wannan littafi, kuma shine farkon wanda ya fara bada shawarar  yin Mukalat, kuma yayi amfani da dukiyar sa, da lokacin sa, wajen ganin suna fitowa a duk lokacin da mukayi karatu har zuwa hada wannan littafi. Muna fata Allah ya sakamasa da mafificin alherinsa duniya da lahira amin.
Wadanda suka taimaka da dukiyar su tun lokacin shigar dashi computer na farko har zuwa kammala bugashi. Suma muna masu fatar Allah ya saka masu da alheri amin.
Wadanda suka bayar da gudunmawarsu wajen gyara tsarin rubutun Hausa, da kuma dukkanin wadanda suka bayar da gudummawa ta kowane fanni, muna rokon Allah yayi masu sakayya da mafificin sakamakonsa, amin.




TAALIKI
Sai dai a kula cewa dukkan abubuwan da aka rubata matukar takaitawa ce akai ba wai anrarrabe muduin filla filla ba ne,don haka fitila ce aka haska akan lamarin.Duk inda akayi  muwafaka da dacewa da daidai acikin wannan  littafi taimakone daga Allah.Dukkan kurakurai dake cikin wannan litafi kasawa ce tamu amatsayin mu na Almajira.Da fatar Allah {SWT} ya gafarta muna baki daya.
Akarshe muna farin ciki da duk wani gyara day a dace ayi.Idan ansamu kuskure ne a tuntube mu a cibiyar  Abu Hurairah da ke a garin Tsafe Jahar Zamfara Nigeria.
                                                          
                                                                                                                       Amir Sani Liman
                                                                                                                               Limamin masallacin
                                                                                                            AbuHuraih
                                                                                                                   Yar yara Tsafe
                                                                                                                      Zamafara State.
                                                                                                                   07036200007,
                                                                                                                   07081995555,
                                                                                                                  07059593000

1                            KO KASAN MAANAR KALMAR  SHAHADA?
Godiya ta tabbata ga Allah ((S.W.T)) wanda yasa kalmar shahada itace farkon kalmar shiga musulunci. Tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah (S.A.W.) wanda ya  fayyace mana maanar Kalmar Shahada. Maana da rukunnai, da sharudda, da kuma abun da take hukuntarwa. Wanda fadarta kawai da harshe bazai isa ba, face sai ka san wadannan abubuwa.
MAANAR  LAILAHA ILLA ALLAH, GUDA BIYU NE: - 
Ba wanda ya chan-chanci a bauta masa, bauta ta gaskiya sai Allah. (Maana shine, kudiri da furuci lallai ba wanda ya chan-chanci bauta ta gaskiya sai Allah.)   
RUKUNAN LAILAHA GUDA BIYU NE: -
Korewa! Shine ka kore duk wani abun bauta wanda ba Allah ba.
Tabbatarwa! shine  bauta  ga Allah shi kadai. Kamar yadda  ya fada a hikaya  ga Annabi Ibrahim yace lallai ni na barranta da duk abun da kuke bauta mawa, sai dai Allah wanda ya kagani (ya halliceni) (Suratul Zukhruf aya 26).
SHARUDDAN LAILAHA ILLALLAH
Babu makawa ga duk mai fadar Lailaha illallah, yasan sharudanta guda bakwai (7) In har bai sansu ba fadar kalmar bata da amfani gareshi.  
Sanin maanar ta: da zaka fadi kalmar amma bakasan maanarta ba fadar  ba tada anfani  gareka. Saboda hadisin da Imamu Musulum ya ruwaito: Hadisi na 26, Manzon Allah (S.A.W) yace duk wanda ya mutu yana sane  da maanar lailahaillah zai shiga Aljanna.
Yakini (sakankacewa): - Maana shine  ka sakankace da maanar ta a cikin  zuciyraka. Imam Musulum  ya ruwaito cewa manzon (S.A.W) yace ma wani sahabinsa. Duk wanda ka hadu dashi bayan lambun nan yana  mai shedawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah sannan kuma zuciyarsa ta tabbatar da kalmar to kayi mashi bushara da Aljannah. Lambar {Hadisi na 31}.    
Karba: Maanar  karba shine abun da kalmar ta hukunta na kudiri ga zuci da fada da harshe da kuma aiki da gabobi, da rashin sabawa abun da kalmar take dauke da shi. Allah (S.W.T) yace lallai su sun kasance idan ance masu lailaha illallahu sai suna girman kai (Suurah saf 25).
Kamar halin da muke ciki a yau ga masu bautama kaburbura. Aga suna fadar Lailaha illallah amma kuma suna bautar kaburbura.
Mika  Wuya: Maana shine mika wuya ga abun da kalmar take nunawa. Kamar yadda Allah (S.W.T.) ke fada Wanda ya mika fuskarsa zuwa ga Allah, alhali yana mai kyautatawa, hakika yayi riko da igiya amintatta (Surah Lukuman 22).
Gasgatawa: - maana shine gasgata kalmar da zuci da fadarta da halshe, in ba haka ba to mutum ya zama munafiki. Kamar yanda manzon Allah yake fada cewa. "Babu wani mutum da ya sheda babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ya sheda ni manzonsa ne kuma bawansa ne  yana mai gasgata haka a cikin zuciyasa face Allah ya haramta mashi shiga wuta ( Bukhari 128).
So: - Maanar shine kaso mai son wadannan kalmomi (2) na kalmar shahada, kaki maikinsu, kuma kaso Allah da manzonsa (S.A.W) Allah (S.W.T) na cewa  Lallai masoyinka shine Allah da Manzonsa da kuma wadanda sukayi imani. (Surah Maida 55)
IKHLASI:- Maanarsa shime ka tsabtace aikin ka daga dattin shirka, kada ka fadi kalmar shahada don kwadayin duniya ko don riya ko don jiyarwa.
Kamar yadda yazo a cikin hadisin Itban, Manzon Allah (S.A.W) yace Lallai Allah ya haramta shiga wuta ga wanda ya fadi kalmar shahada yana mai neman fuskar Allah da fadarta (Bukahri ya ruwaito 99)
Kada ka manta ya kai dan uwa mai karatu munce kalmar shahada tana da Maana, Rukunnai, Sharudda, da kuma abun da take hukuntarwa.
To abun da kalmar take hukuntarwa shine yin tawaye (baraa) ga duk abun bauta wanda ba Allah ba.
Domin akwai da yawa masu fadar kalmar shahada suna zuwa wajen Boka da Malaman Tsibbu, Malaman Duba, da bautama Kaburbura.
FADAKARWA
Akwai fassarori da dama da ake yima kalamar shahada wadanda basu dace da kalmar ba, shine yasa muka ga yadace mu fadakar da Alumma akansu, don kar su fada a cikin hadari.
Suna cewa wai maanarta babu abun bauta sai Allah. Alhali akwai abubuwan bauta da yawa.
Suna cewa babu mahalicci sai Allah, shima wannan kuskure ne.
Suna cewa babu sarki sai Allah, shima wannan kuskure ne tunda ga sarakunan ku nan.
Suna cewa babu abun bauta samamme sai Allah. Kenan a wajen su duk wanda ake bauta mawa ya zama Allah kenan.
Suna cewa babu hukuma sai ta Allah, shima wannan kuskure ne. maanar kalmar shahada ta gaskiya:- shine babu wanda ya can-canci a bauta masa, bauta ta gaskiya sai Allah, kenan duk wanda ake bautamawa wanda ba Allah ba to bauta ce amma ta karya. Kamar in da Allah (S.W.T) yake fada cewa  Haka shaanin yake lallai bautama Allah shine gaskiya, lallai bautama wani bayansa shine barna, lallai Allah shine mai girma (surah Hajj 62)
KO KASAN MANAR MUHAMMADUR RASULULLAHI (S.A.W)
Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) wanda ya hada sunansa da sunan Manzon sa a wajen kalmar shahada.
Tsira da aminci su tabbata ga manzonsa wanda ya fayyace muna manar kalmar shahada ga ayyukansa.
A bayanin mu da ya  gabata munji maanar LAILAHA ILLALLAH. A yanzu kuma zamuyi bayanin MUHAMMADURRASULULLAHI (S.A.W)
Maanar ka shaida MUHAMMADU manzon Allah ne, shine yin furuci boye da fili, cewa lallai shi bawan Allah ne kuma Manzon Allah ne zuwa ga mutane baki daya, da kuma aiki da abun da wannan kalmar ke dauke da shi.
Ya kamata kai Dan Uwa musulmi kasani cewa kalmar MUHAMMADU RASULULLAH (S.A.W) tana da maana da rukunnai da sharudda, da kuma abun da ta hukunta. To kuma ga yadda maanar take:-
Yima manzon Allah daa a cikin abunda yayi umurni
Gasganta shi a cikin abunda ya bada labari
Nisantar abunda ya hana ko ya tsoratar.
Baa bautar Allah, bautar kuma ta samu karbuwa face yadda manzon Allah ya tsara (ya sharanta).
Dole ne mai fadar Muhammadur Rasululahi (S.A.W) yayi aiki da wadannan bayanai, domin fadan hakan da harshe kadai bai isa.
RUKUNAN MUHAMMADUR RASULULLAHI (S.A.W) GUDA BIYU (2) NE:-
Rukuni na farko shine zaman shi bawan ALLAH:- Zaman shi bawan Allah yana kore zurfafawa gareshi. Kamar yadda hadisin da Bukhari ya ruwaito yana cewa "Kada ku dagani kamar yadda nasara suka daga ISA DAN MARYAM (A.S) Ni bawan Allah ne kuma Manzonsa ne.
Maanar bawan Allah shi mutu ne wanda aka halitta daga cikin halittar Allah yana gudana a gareshi abun da yake gudana ga mutane kamar yadda Allah ke fada cewa:- Kace masu lallaini mutum ne irinku (Suratul Kahfi 109). Cewa da wasu keyi manzon Allah ba mutum bane wannan zurfafawa ne, da kuma nakkasa shi. Masu fadar wannan sun can-can-ci a hukunta su.
RUKUNI NA BIYU SHINE MANZON ALLAH (S.A.W) :- Maanar Manzon Allah shine wanda aka aiko ga wasu ko kuma ga mutane baki daya don kira ga Allah. Shi Mai bushara ne mai gargadi.
SHARUDDAN MUHAMMAD RASULULLAH (S.A.W) GUDA SHIDA (6) NE:-
Furuci da manzoncinsa da kudiri a cikin zuciya.
Bin manzon Allah da aiki da abunda yazo da shi na gaskiya, da barin abun daya hana na barna.
Gasganta abun da ya bada labari na gaibu daya wuce da kuma mai zuwa.
Son Manzon Allah fiye da kanka da dukiyarka da uwayenka da sauran mutane baki daya.
Gabatar da zancen shi akan zancen ko wane mutum da kuma aiki da sunnar shi.
Bashi kariya daga kowace nakasa da kuma kare sunnar shi iya karfinka.
ABUNDA KALMAR TAKE HUKUNTAWA SHINE:-
Yi mashi Daa, gasgatashi, barin abun daba sunna bane, kamar bidioI da kage-kage .
FADAKARWA
A karshen muna kira ga yan uwa Musulmi su sani cewa Allah bai karbar duk wani aiki face sai ya cika sharudda guda biyu (2).
1. IKHLASI:- Shine yin aiki don Allah.
2. MUTABAA:- Bin manzon Allah sau da kafa a cikin duk abinda zaka gabatar, kamar yadda bayanai suka gabata. Daga karshe muna rokon Allah (S.W.T) ya aza mu kan bin sunnar manzon Allah (S.W.A) kuma ya kashemu a kanta Amin.
SIFFOFIN MANZON ALLAH (SALALLAHU ALAIHI WA SALLAM)
An karbo daga Yazid al Farisi, kuma shi marubuchi ne, yace Naga Manzon Allah (S.A.W) a cikin mafarki a lokacin Abdullahi Dan Abbas R.A, sai nacewa Abdullahi, lalle ni naga manzon Allah a cikin mafarki sai Ibn Abbas yace Manzon Allah yace lalle shaidan bai samun damar  yayi kama dani. Don haka wanda ya ganni a cikin mafarki to hakika nine ya gani. Sai Abdullahi ya tambayeni  ko kana iya kwatanta mani namijin da ka gani a cikin mafarkinka?. Sai nace E, zan kwatanta maka mutum a tsakanin mutane biyu. Jikinshi da namanshi sunfi karkata zuwa wajen fari, kuma mai bakin idanu ne, kuma mai kyakkyawar dariya ne, mai kyakkyawar fuska ne, kuma hakika yana da cikakken gemu da saje a kowane kuncinsa da habarsa. Sai Abdullahi yace  Da ka ganshi a falke to ba zaka kwatantashi fiye da yadda ka kwatantashi yanzu ba"
Wani mutum ya tambayi Al-Barau Ibn Azib  Shin fuskar Manzon Allah misalin takobi ce? Sai yace Aa, misalin dai wata ne. Manzon Allah ya kasance idan yana farin ciki, fuskarsa tana haske, sai kace wani yanki ne na wata. Mun kasance muna gane haka daga Manzon Allah (S.A.W).
Daga Abu Is'hak yace  Naji Barau yana cewa Manzon Allah yafi kowa kyawun fuska, kuma yafi kowa kyan siffa. Shi ba dogo bane shi ba gajere bane, S.A.W.
An karbo daga Jabir Ibn Abdullahi RA. Yace Manzon Allah bai taba kange ni ba daga wajenshi tun lokacin da na musulunta, kuma duk lokacin daya gannni sai yayai murmushi S.A.W
An karbo daga Jabir Ibn Sumra yana cewa Manzon Allah S.A.W ya kasance mai wadataccen baki, sannan kuma mai girman idanu ne, sannan kuma mai madaidaicin dudduge ne S.A.W.
An karbo daga Aliyu Ibn Abi Talib RA, yace  Manzon Allah S.A.W. ba mai tsawo bane kuma ba gajere bane, mai kaurin tafuna ne da yatsu, mai cikakken  kai ne, gashinsa mai laushi, wanda yake farawa daga kirjinsa zuwa cibiya. Kuma idan yana tafiya yana tafiya ne da jikinsa baki daya, kamar wanda yake gangarowa daga tudu, (ba kasala ko karkace  karkace).
An karbo daga Anas Ibn Malik RA, yace Manzon Allah ba dogo bane ainun, kuma shi ba gajere bane, sannan kuma shi ba fari bane fes, kuma shi ba ja bane jawur, sannan kuma gashinsa ba takurarre bane kuma ba watse yake ba. Ya kasance baya dariya face ya fara da murmushi, kuma bai waiwaye sai baki daya, kuma idan yana tafiya, yana tafiya ne baki daya, babu kasala. Idan yana tafiya tareda sahabbai, sai ya sasu gaba, yace ku bar bayana domin malaiku masu tsaro.
8. Hatimun Nubuwwa.
An tambayi Aba Said Al-khudriy akan Hatimin Manzon Allah (S.A.W.) Sai yace Hatimin, wata tsoka ce bayyananniya a bayan Manzon Allah (S.A.W.) .
9. Furfura
An karbo daga Anas Ibn Malik RA yace Na kirga yawan furfurar dake kan Manzon Allah da gemunshi, kuma abinda na samu furfura goma sha hudu. gashinshi ya kasance yana sauka ga kafadunsa.
Kwalli:- An karbo daga Abdullahi Ibn Abbas RA yace: Manzon Allah S.A.W yace Fiyayyen kwallinku, yaku Musulmi, shine Al-ithmit, domin wannan kwalli yana kara karfin gani kuma yana tsirar da gashi.
Zobe:-  An karbo daga Abdullahi Ibn Umar RA yace: lalle Manzon Allah (S.A.W) ya riki zobe na azurfa, kuma ya sanya mashi tozo mai bin tafin hannu, sanan a cikinsa ya zana (Muhamadur Rasulullah), sannan ya hana wani ya zana sunan shi ga zobe.
Rawani:- An karbo daga Amru Ibn Harith RA yace: lalle Manzon Allah (S.A.W) yayiwa mutane huduba yana sanye da rawani baki a kanshi.
An karbo daga Abdullahi Ibn Umar RA yace: Manzon Allah (S.A.W.) ya kasance idan ya nada rawani, yana sauko dashi tsakanin kafadunsa.
13. Wando:- An karbo daga Ubaid Ibn Khalid Al  Muharibiy RA, yace wata rana ina tafiya cikin Madina sai ga wani mutum a bayana yana ce mani Daga wandonka, yin haka shine nuna tsoron Allah (ko da na waiwaya) sai naga ashe Manzon Allah ne [SAW]. sai nace Ya Manzon Allah, ai wanan wandon mai launin baki  baki ne da fari  fari. Sai manzon Allah[SAW] yace amma ai dani zakayi koyi. Sai Ubaid ya dubi wandon Manzon Allah[SAW] sai ya ganshi a tsakiyar kwabri.

                    8.          MATSAYIN TARON MAULIDI A MUSULUNCI
Ba shakka Allah S.W.T. ya sharantawa musulmi ranakun Idi guda biyu wadanda suke haduwa a cikinsu domin zikiri da yin sallah. Sune Idin karshen Azumi da Idin Layya domin su maye gurbin idodin jahiliyya. Haka kuma ya sa mana ranar Jumaa da ranar Arafah da kuma kwana ukku bayan Arafah domin taruwa da zikiri. Allah S.W.T bai shar’anta mana wani taro ba domin haihuwar wani, Annabi ne ko ba Annabi ba. Kuma tabbas dalilai sun tusgo daga Kurani da Hadisi wadanda suke tabbatar da kasancewar taron Maulidi bidia ne a cikin Addini, kuma yin koyi ne da makiya Allah da Manzonsa, wato Yahudu da Nasara da waninsu. Don haka ya zama wajibi ga musulmi da su barshi su tsoratar game da shi, suyi jayayya da duk wanda ya aikata shi. Haka kuma wajibine ne kaucewa yin duk wani abu da zai nuna halacci ko kuma kyawon taron maulidi ako ina, musaman a Radiyo ko Talbijin da sauran kafafen watsa labarai, saboda yazo a cikin Hadisi ingantacce cewa Manzon Allah S.A.W yace Duk wanda ya kirkiro wani abu a cikin wannan addini, wanda addini bai zo da shi ba, to an mayar masa Haka kuma yazo a cikin Sahihil Muslim daga Jabir RA cewa Manzon Allah S.A.W ya kasance yana fadi a cikin hudubar Jumaa...  Bayan haka, fiyyaen zance shi ne Alkurani, kuma ingatacciyar shiriya shine shiriyar Muhammad (S.A.W.) , kuma mafi sharrin alamari shine wanda aka kirkiro (wato bidia), sannan kowace bidia batace. Haka kuma yazo a Musnad na Imam Ahamad da isnadi mai kyau daga ibn Umar RA daga Manzon Allah (S.A.W.) , wanda yace wanda yayi kama da mutane, to yana cikinsu. A cikin maanar wannan Hadisi ya bayyana cewa wajibi ne ayi hattara da bin makiya Allah a wajen I’dodinsu da wanin I’dodin. Mafi daukakar halitta, Manzon Allah (S.A.W.)  baiyi taron bukin haihuwarsa ba, kuma sahabbai RA da Tabiai da Tabiutt Tabiuna basuyi ba. Da ace maulidin Annabi wani abu ne mai kyau, to da wadannan sun riga mu, kuma da Annabi (S.A.W.)  ya kwadaitar da alummarshi suyi haka.
Farkon wadanda suka fara maulidi sune yan Shia fadimiyya a cikin karni na Hudu (shekara 400) bayan hijirar Manzon Allah (S.A.W.) .
Hakika sun kirkiro maulidi shidda a wannan lokaci. Na farko shine Maulidin Annabi, na biyu shine Maulidin Aliyu, na uku shine Maulidin Fadimatuz Zahra, na hudu shine Maulidin Hassan, na biyar shine Maulidin Hussaini, na shida shine Maulidin shugabansu na wannan lokacin.
Shi maulidi yana tattare da manyan bidioI na haramchi da karhanci da ma abinda ya zarce wannan  wato shirka.
Zikirin da akeyi cikn taro ana dukan kirji ana ambaton sunan Allah a wulakance  ALLAH, ALLAH
Mata suna caba ado su fito su garwaya da mazan daba nasu ba.
Suna rokon Manzon Allah (S.A.W.)  a wajen Maulidi. Suna cewa Ya Muhammadu ka agaza mana, ka yaye mana talauci, ka bamu arziki. da dai sauransu. Da Manzon Allah zaiji wannan, da yayi masu hukunchi da shirka babba. Domin Allah ya umurci Manzonsa cewa ya fadawa jamaa cewa.. Ni ban mallaki wata shiriya ko cuta gareku ba.
Suna ambatawa a wajen Maulidi cewa Allah ya halicci Manzon Allah daga hasken Shi, sannan ya halicci sauran jamaa daga hasken Manzon Allah. To Allah ya karyatasu a cikin Alkurani domin yana cewa Kace masu, lalle ni mutum ne kamarku, banbanci na daku anayi mani wahayi. Lallai abin bautarku abin bauta ne guda (wato Allah)
Suna ambatawa a wajen Maulidi cewa Allah ya halicci duniya domin Manzon Allah kawai. Alkurani ya karyata su inda Allah (S.W.T) yake cewa Ban halicci Aljani da Mutum ba sai dai kawai domin su bauta mani.
Wadansu suna riya cewa ai ranar Maulidi ba wani abu sukeyi ba illa karanta tarihin Manzon Allah da liyafa. To ai mai son Manzon Allah kullum yake karanta tarihinsa, ta yin abubuwan daya kwadaitar ayi ba daga shekara sai shekara ba. Kuma ma an haifi Annabi a cikin watan Rabiul Auwal kuma a cikin sa ya rasu (S.A.W.) To shin murnar haihuwar akeyi ko kuma murnar mutuwarsa?
A karshen taron Maulidi, kowa da yake wurin, yakan mike tsaye kyam, wai a wannan lokaci Annabi zai bayyana a gabansu. To wannan karya ce, domin fadar Allah cewa Gaba garesu (su matattu) akwai wani makangi, har zuwa tashin kiyama.
Mafi yawan masu taron Maulidi basu samun barci, wanda hakan yakan haifarda su rasa Sallar Asuba a cikin JamI, wasu ma su rasa ta gaba daya, alhali rasa Sallar Asuba ko kuma rashin yinta a JamI alama ce ta munafunci kamar yadda Annabi (S.A.W.)  ya ambata.
Wasu suna ruduwa da yawan mutanen dake bukin Maulidi a duniya. To kada wannan ya burge ka domin kuwa Allah yace ..Idan kabi taron mafi yawan wadanda ke bayan kasa, zasu batar da kai daga barin hanyar Allah. Baa gane gaskiya da yawan mutane, gaskiya tana nan ga bin abin da Allah yace da abinda Manzon Allah yazo dashi. Hassanul Basri yace Lalle mabiya sunna sune mafi karancin mutane a lokacin da ya wuce, kuma zasu ci gaba da zama mafi karanci anan gaba.
ALLAH YA SHIRYARDAMU AMIN.
5. RUBABBUN HUJJOJIN DA YAN MAULIDI KE DOGARA AKANSU DA RADDI
GODIYA TA TABBATA GA Allah ((S.W.T)) wanda yafada a cikin littafinsa. Shine wanda ya saukar da littafi a kanka cikinsa akwai ayoyi dake dauke da hukunce hukunce wadanda sune asalin littafi sannan akwai wasu masu rikici. Amma wadanda akwai karkata a cikin zukatansu sai suna bin abunda ya rikita a gareshi. (Ali Imaran aya (7) ). Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzonsa (S.A.W) wanda yace duk wanda ya kaga wani abu a cikin wannan addini wanda bamu mukace ba to zaa mayar masa. Bayan haka kamar yadda bayani ya gabata Maulidi bidia ne ba yada asali a cikin Musulunci. Shia Fadimiyya ne suka kirkiro shi a cikin karni na hudu (4) domin su kawo rabuwa a cikin addainin Musulunci. Wanda har ya kai ayanzu wasu jahilai suna dauka addini ne saboda wasu rubabbun hujjoji. Wannan ne yasa mukaga ya dace muyiwa Alummar musulmi bayani akan rubabbun hujjojinda suke dogara akansu da kuma raddi akansu.

SHUBUHA (1)
Suna cewa wai Maulidi yana da asali a cikin Al-qurani inda Allah yace  kace da falalar Allah da rahamarsa sai su kace shine wai haihuwar Manzon Allah (S.A.W).
AMSA: Sahabbai da tabiai dama tabiut tabiina sun fassara cewa abinda ake nufi da falalar Allah da rahamarsa shine Al-kitabu was sunnah. Don haka muna son akawo mana wani magabaci da yayi fassara inrin taku.
SHUBHUHA (2)
Suna bada wata rubabbar hujja a cikin wani hadisi da Imamu Albaihaki ya ruwaito cewa wai Manzon Allah ya maimata bukin ranar haihuwarsa ya yanka dabba bayan aikoshi. Sai suka ce kenan ana taron Maulidi.
AMSA: Wannan hadisin bai nuna haliccin maulidi tunda ba duk shekara yayi hakan ba.
SHUBUHA: (3)
Suna dogaro da wani hadisi cewa lokacin da aka haifi Manzon Allah (S.A.W.) wata baiwa ta kawowa Abi Lahab busharar samun Manzon Allah (S.A.W.) sai yace ya yanta ta. Saboda haka duk ranar litinin anayi mashi saukin azaba. Sai suna cewa mu yafi cancanta da muyi haka.
AMSA: Wannan hadisi mai rauni ne. Sannan kuma ya sabawa zahirin aya Inda Allah kecewa zamu sanya aikin kafiri ya zama kura abin watsarwa (Sura Alfurqan aya ta 23). Sannan yin koyi da Abi  Lahab koyi ne da kafiri. Idan kuma ance haka kenan duk wanda yayi maulidi zai shiga wuta kenan sai ranar shabiyu ga Rabiul Auwal zai samu sauki. Mu dai muna rokon Allah kariya daga shiga wuta ko na minti daya ne.
SHUBUHA (4)
Suna cewa taron maulidi wai taro ne na zikiri da sadakoki da yabon Allah da manzonsa da karatun Alkurani. To menene abun kyama a ciki?.
AMSA: Sun manta Allah yayi umurni a cikin Alqurani cewa arinka yin zikiri safe da maraice, kuma Manzon Allah ya koyar da mu zikirora  da suka dace akowane lokaci kamar zikirin shiga gida, bayi, kwantawa barci, shiga mota, cin abinci, shan abin sha, da sauransu. Hakama sadaka da karatun Alqurani kowane lokaci Manzon Allah ya kwadaitar da mu yinsu ba sai shekara ba.
SHUBUHA (5)
Suna cewa duk wanda baya maulidi baya son Manzon Allah (S.A.W.) wai masu yin maulidi sune masoya  Manzon Allah (S.A.W.) na gaskiya.
AMSA: Alhali Allah (S.W.T) yayi mana bayanin yadda ake son Manzon Allah a cikin ayoyi da dama a cikin Alqurani Mai girma Kadan daga ciki Allah yace Ka fadamasu idan dai har kun kasance kuna son Allah to ku bini  ni (Manzon Allah) sai Allah ya soku. (Ali Imrana). Kuma ya fada a wata aya Kyakkyawan koyi ya tabbata gareku daga Manzon Allah, amma ga mai kaunar Allah da ranar lahira. Wadannan ayoyi suna nuna cewa ashe son Manzon Allah shine yi masa daa ga abinda yazo dashi da kuma gazgatashi ga abunda yabada labari da nisantar abunda ya hana da kuma bautawa Allah da abunda ya sharanta. Ba taron kide  kide ba da jan riga akasa da kuma aske gemu.
SHUBUHA (6)
Suna cewa wai Maulidi ya halatta, saboda an tanbayi Manzon Allah game da Azumin Ranar Litinin sai yace rana ce da aka haifeni kuma itace aka saukar mani da Alqurani. Wai sai sukace ashe kenan ana bukin Maulidi, tunda Manzon Allah ya girmama ranar haihuwarsa.
AMSA: Indai da gaske su ma Masoya Manzon Allah ne to duk ranar litinin suyi azumi. Kamar yadda Manzon Allah yake yin azumi duk ranar litinin. Anan zamu iya gane cewa tunawa da Manzon Allah na hakika shine yin azumin duk ranar litinin ba kamar yadda suke bukukuwa duk shekara ba. To mun gane cewa ashe masoya shaidan ne ba masoya Manzon Allah bane tunda suka bar hanyar da Manzon Allah yabi.
SHUBUHA (7)
Suna cewa in maulidi bidiane to ita Mota, Radio, Lasifika, Agogo, Mashin da sauransu su minene?
AMSA: Sun jahilci hadisin Manzon Allah dake cewa Wanda ya kaga wani abu a cikin al-amarinmu wannan maanar shine a cikin (Addini)  wato duk wanda yazo da wani aiki wanda Annabi baiyi ba da manufar ya samu lada to an mayar mashi da aikinsa. To wanda yayi Mota, Radio, da sauransu don ya samu lada yayi su ne? ko don ya samu kudi?
SHUBUHA (8)
Suna cewa in ance Maulidi bidiane to Musabaka da kuma Jan baki da akeyi in ana tafsiri,shin  Annabi yayi haka ne?
AMSA: To kenan dai sun jahilci abunda ake cewa sunna. In hakane to ga bayanin sunnah. Abunda ake cema sunna shine aikin Manzon Allah ko umrninsa ko abunda yaga anayi ya tabbatar, Karatun Alkurani Allah da kansa yayi umarni a ayishi hakama Manzon Allah yayi umarni da karatun Al-qurani kamar yadda Imam Muslim ya ruwaito wani hadisi, Manzon Allah [SAW] ya cema Abu Musa Al-Ashari yace jiya na wuce kana kiraa hakika anbaka murya irinta mutanen gidan Annabi Dawud [AS], sai yace danasan kana saurarena da nayi wata kiraa wadda tafi wannan dadi don in kayatar dakai. Kuma Manzon Allah yace bai tareda wanda bai rera karatun Qurani. Kuma sun manta karatun da sukeyi na littaffan fiqhu , tunda ga cikin Mukhtasar, Askari da Risalah duk sunyi fasali kan Musabaka ku duba ku gani.
SHUBUHA (9)
Suna dogara da hadisin da Annabi ke cewa duk wanda ya sunnanta wata sunna yana da ladarta, shiyasa suke ikirairi cewa sun kawo wata sunnah shine Maulidi.
AMSA: Sun jahilci wannan hadisi shima, don haka su koma cikin Muslim su gano dalilin fadin hadisin, abun nufi anan shine duk wani aiki da Allah ko Manzonsa suka ce ayi, sai kayishi inda baasan aikin ba to kanada ladar wanda yayi koyi dakai hakama kuma aikin sabo (Bidia) shima kanada zunubin wanda yayi koyi dakai.
SHUBUHA (10)
Da suna yin Maulidi duk sha biyu ga watan Rabiul Auwal to amma yanzu kowane lokaci yi suke shin wannan wani wahayi ne suka samu daga shedan koko?
AMSA: Wannan na nuna mana cewa Maulidi ba ibada bace ta Allah sai dai ta shedan. Don kuwa inda ibada ce to da ansamu lokacin farawa da kuma karewa. A karshe bincike na ilimi yana nuna cewa Manzon Allah (S.A.W.) An haifeshi 9 ga Rabiul Auwal ya kuma rasu 12 ga Rabiul Auwal. Ga tambaya. Shin murnar haihuwar sane ya kamata ayi koko bakin cikin rasuwarshi?
Muna fatar Allah ya ganar damu gaskiya ya bamu ikon binta ya kuma nuna mana karya ya bamu ikon gujemata amin.
6. MUHIMMANCIN KIRAN SALLAH DA SHARUDANTA
Manzon Allah (S.A.W) yace mafi tsawon wuya a ranar tashin kiyama shine wanda yake kiran Salla (wato Ladan). Haka kuma yace duk wanda ya shekara goma Sha biyu yana Kiran sallah to babu shakka Aljanna ta wajaba a gareshi, sannan kuma ana rubuta lada sittin (60) ga duk wanda ya kira Sallah idan Zaa yi sallah (Ibn Majah ya ruwaito wannan hadisin).
Bayan haka, Ibn Mulaika yace Malamai sunyi bayani game da wasu abubuwa guda ukku wadanda sune dalilai guda ukku dake sa ana yin kiran Sallah. Abubuwan kuwa sune:-
Ana yin kiran Sallah domin tabbatar da kalamar Tauhidi.
Ana yin kiran Sallah domin shedawa mutane lokacin Sallah yayi
Ana yin kiran sallah domin a gane cewar wannan garin na mususlmai ne
KURA - KUREN DA KE IYA FITAR DA MUTUM MUSULUNCHI A CIKIN KIRAN SALLAH
Tsawaita madda (wato tsawaita sauti) a wurin ASH HADU.
Tsayawa a wurin ILAHA, sannan mutum ya tashi a wurin ILLALLAH.
Yin madda (wato tsawaita sauti) a wurin AKBAR.
Kin shigar da DALUN a cikin RAUN a wajen MUHAMMADURRASULULLAH.
Kin fitar da HAUN a karshen HAIYA ALASSAH.
Tsayawa a karshen kalma tare da kuma fitar da harafin karshe misali, kamar cewa HAYYAALALSALATI. Da dai sauransu.
KARIN BAYANI
Malamai sun yi bayani cewar ana son duk mai kiran sallah ya kasance mai babbar murya, kuma a duk lokaci da zai kira Sallah ana so ya kasance yana mai wal-wala da jin dadai, domin baa son mutum ya kasance kamar bai da lafiya.
Haka kuma, dole ne mutum ya koyi yadda ake kiran Sallah kafin ya fara kiran sallah. Domin idan mutum bai koyi kiran Sallah ba, to hakika zai jefa kansa a cikin halaka. Allah ya tsaremu Amin.
7. ADDU’OIN DA AKEYI NA IBADA BAYAN SALLAME SALLAH

اسغفر الله         اسغفر الله              اسغفر الله
   اللهم أنت السلام ومنك السلام تباركت يا ذا الجلال والإكرام
اللهم أعنى على ذكرك وشكرك وحسن عبادتك
لاإله إلا الله وحده لا شريك له له الملك وله ا لحمد وهو على كل شئ قدير
اللهم لا مانع لما أعطيت ولا معطى لما منعت ولا ينفع ذا الجد منك الجد
  اللهم إنى أعوذ بك من الجبن وأعوذ بك من العجز والكسل وأعوذ بك من ان أرد الى أرذال العمر وأعوذ بك من فتنة الدنيا ومن عذاب القبر
ثم تقرا آية الكرسي
قل هو الله أحد* ...........Sannan Sai falaqi Da Nasi
تسبح الله ثلاث ثلاثين، وتحميد الله ثلاث وثلاثين، وتكبير الله ثلاث وثلاثين
Subhanallah sau 33, Alhamdulillah sau 33, Allahu Akbar sau 33
الدعاء الإستعاذة
8. ADDU’OIN NEMAN TSARI
ما يعوذ به الأولاد، من العين .1
Addu’ar neman tsari  daga kandun baka
اللهم إنى أعوذ بك بكلمات الله التامة من كل شيطان وهامة وكل عين لامة

02 دعا ء الفزع فى النوم ومن بلى بالوحشة
Wanda aka jarraba da demuwa ko firgita a cikin barci yarika karanta wannan addu’a
أعوذ بكلمات الله التامات من غضبة وعقابة وشر عبادة ومن همزات

الشياطين وأن يحضرون

وتتعوذبها من كل شيئ ءتخافه وعندما تحل بموضع او تجلس بمكان  .3

Adduar neman tsari daga dukkan abinda kake tsoro a cikin tafiya ko sauka wani sabon wuri da neman tsari daga sharrin mutum da dabba.

أعوذ بكلمات الله التا ما ت من شر ما خلق

يقول لردكيد مردة الشياطين الإنس والجن .4
Addua’r warware cutar sharrin mutum ko aljani

أعوذ بكلمات  الله التاما ت  التى لا يجاوزهن بر ولا فاجر من شرما خلق وبرأ وذرأ ومن شرما ينزل من السماء،

ومن شر ما ذرأ فى الأرض ومن شر ما يخرج منها ومن شر فتن الليل والنهار ومن كل طارق الا طارقا يطرق بخير

يارحمن

05اذا رأي أحدكم رأيا يكرها فلينفل عن يساره ثلاث مرات ثم ليقل
Idan kayi mugun mafarki, bayan ka farka sai kayi tofi sau ukku hagu sannan sai ka karanta wannan addu’a
اللهم انى أعوذ بك من عمل الشيطان وسيئات الأحلام
مايقول له عند الجماع اذ ا قضي بينهما ولد لم يضره .6
Addu’ar da akeyi wurin jima’I don kariya ga abinda za’a haifa
بسم الله اللهم جنبنا الشيطان وجنب الشيطان ما رزقتنا

9. MENENE MATSAYIN AZUMIN TSOFAFFI A SHARI’A?
Allah ((S.W.T)) yana fada a cikin littafinsa mai tsarki cewa Lalle adadin yawan watannai a wajen Allah goma sha biyu (12) ne a cikin littafin Allah ranar da aka halicci sammai da kasai. Daga ciki akwai 4 masu alfarma. Wannan shine addini madaidaici. Kada ku zalunci kawunanaku a cikinsu. (Suratul Tauba, aya 25).
Hadisi ya nuna mana cewa wadanan watanni  sune Zulqiida, Zulhijja, Muharram da Rajab. Alfarmar su kuwa itace a girmama su da daraja su sama da sauran watannin. Sannan kuma cewar Allah (S.W.T) kada ku zalunchi kawunan ku a cikinsu, yana nufin kada ku sabi Allah kuma ku kiyaye kawunanaku matukar kiyayewa a cikinsu.
A karkashin wannan ne ya wajaba mu jawo hankalin yan uwa akan bidioI da akeyi a cikin watan Rajab, wato watan azumin tsofaffi. Daga ciki akwai shi azumin da akeyi, inda zaka ga tsofaffi suna azumtar watan gaba daya, ko suyi rabi ko abinda yafi haka ko ya kasa haka. Wasu ma sun fara azumi kenan har zuwa ranar da aka ga watan Sallah. To a zahiri zaa ga kamar haka wani abin kirki ne. Sai dai mu tuna da hadisin Manzon Allah (S.A.W) inda yake bamu umurni mu kaucewa dukkan ayyukan ibada wadanda shi Annabi baiyi  ba kuma bai bada umarni ayi ba, Sahabbai ba suyi ba, Tabiai da Tabiut Tabiina duk basu yi ba.
Ibn Kayyim ya ruwaito cewa Manzon Allah (S.A.W.) bai taba azumin wata 3 (Rajab, Shaaban da Ramadan) a jere ba, kuma bai taba azumin watan Rajab ba,  kuma baiso ayi shi ba. Ibn Majah ya ruwaito cewa Manzon Allah (S.A.W.) ya hana yin azumin watan Rajab. Ya tabbata cewa  Sayyidina Abubakar (R.A.) ya kyamaci iyalinsa suyi azumin tsofaffi. Haka shima Sayyidina Umar (R.A) ya tsananta ga masu yin azumin tsofaffi, inda har yakai yana bulala ga duk wanda yayi irn wannan azumi, har yana cewa watan Rajab wata ne wanda Jahilai ne ke azumi a cikinsa. Anan muna jawo hankalin jamaa akan wasu hadisai da ake kafa hujja dasu na yin azumin watan Rajab. To bincike ya tabbatar cewa wadannan hadisai kodai masu rauni ne ko kuma na karya ne wadanda baa aiki dasu. Ibn Hajar ya fada a cikin littafinsa mai suna Tabayyuni Ajabi bima warada fi fadalil Rajab cewa  babu wani ingantaccen hadisi wanda yake nuna falalar watan Rajab, ko yin azumi a cikinsa, ko yin nafilolin dare ko rana a cikin watan Rajab. Don haka duk hadisin da yazo da falalar wannan wata kodai ya zama mai rauni ko kuma karya ce kawai. Annabi (S.A.W.) yace  Wanda ya bada wani labari yace daga gareni ne, alhali yasan cewa ba daga wajena bane, to ya tabbata cikin manyan makaryata a duniya.
To daga wannan zaa gane sharrin da shedan yake kullawa tsofaffi na bata lokacinsu da karfinsu wajen yin azumin watan Rajab, amma sai yace masu su huta a cikin watan Shaaban, wanda shine Annabi (S.A.W.) yayi umrni a yawaita azumi a cikinsa. Don Karin bayani a saurari wasikarmu ta gaba wadda zatayi magana kan falalar watan Shaaban insha Allahu Taala.
Domin Karin bayani a duba wadannan littafai.
Tuhfatu al ahwazi  sharhin Tirmizi, juzI na 3, shafi 160-163.
As Sunnanu wal mubtadiati, shafi 144  148
Tabayyinul Ajabi bima warada fi fadali Rajab  na Ibn Hajar Al  Askalani

MATSAYIN AZUMI DA SALLOLIN DA AKEYI A CIKIN WATAN SHAABAN

Godya ta tabbata ga Allah (S.W.T) wanda ya farlanta azumin Ramadan. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzonsa Muhammad (S.A.W.) da ya  sunnanta azumin Nafila. Hakika yin azumin nafila a cikin watan Shaaban sunna ne, domin ya tabbata a cikin hadisai masu dama cewa Manzon Allah (S.A.W.) yafi yawaita azumin nafila a cikin watan Shaaban. Imam Muslim ya ruwaito daga Aisha (R.A.) cewa bata taba ganin Manzon Allah yana cika wata guda cur yana azumi ba face azumin watan Ramadan. Haka kuma bata taba ganin watan da Manzon Allah yafi yawan azumin nafila a cikinsa ba, irin watan Shaaban. A cikin wani hadisi dai, an tambayi Aisha RA yadda Manzon Allah yake azumin nafila. Sai tace Annabi ya kasance yana azumin nafila har kace ba zai bari ba, wani lokaci kuma ya huta hark ace  bazai yi azumin ba, kuma bata taba ganin Annabi yana yawaita azumin nafila ba inba cikin watan Shaaban ba. Yana azumin watan  Shaaban duka sai kadan yake ragewa. Imam Muslim ya ruwaito wannan hadisi.
Wadannan hadisai suna nuna mana karara cewa azumin watan Shaaban shine sunnar Manzon Allah (S.A.W.) sabanin abinda jahilai sukeyi na azumin watan Rajab, wato azumin watan tsofaffi.
FALALAR RABIN WATAN SHAABAN

Albarkoki da falalar watan Shaaban basu tsaya ga yin azumin nafila kawai ba. Allah (S.A.T.) yana zubo falalarsa yayinda watan ya raba, kamar yadda hadisi ya tabbatar. An karbo daga Abu Musa Al-Ashari daga Manzon Allah (S.A.W.) wanda yace Lalle Allah (S.W.T) yana tsinkaya a cikin daren rabin Shaaban, sai ya gafartawa dukkan halittarsa, in banda mushirikai da mai gaba da Dan Uwansa. Ibn Majah ya ruwaito wannan hadisi kuma Muhammad Nasiruddeen Albani ya ingantashi. Wannan hadisi yana nuna mana irin alherin da Allah (S.W.T.) yake saukarwa bayinsa a daren rabin watan Shaaban. Wanda a ciki baa nuna an kebe wani aiki da akeyi a daren ba, sabanin yadda aka gina wata bidia ta yin sallah rakaa 100, kowace rakaa zaa karanta kulhuwallahu 10 .. da dai sauransu. To wannan hadisi bai nuna ayi haka ba. Duk hadisin da yazo da irin wannan Sallah ko dai mai rauni ne ko kuma karya ce aka yiwa Manzon Allah (S.A.W.).
Bugu da kari manyan Tabiai irinsu Adau da Ibn Abi Mulaika da manyan malaman fikihun Madina da almajiran Imamu Malik duk sun tafi akan cewa wannan sallar da akeyi a daren rabin watan Shaaban bidiace, bata tabbata ba a lokacin Manzon Allah (S.A.W.). Shima Imamun Nawawi yace salloli da akeyi a cikin watan Rajab da rabin Shaaban bidioI ne wadanda ake musu, kuma masu muni. Allah ya nuna mana gaskiya gaskiya ce, ya bamu ikon binta, ya nuna mana karya karya ce ya bamu ikon guje mata
Domin Karin bayani a duba Wadannan littafai kamar haka:-
1. As Sunnanu Wal mubtadiati, shafi na 149
2. Tuhfatu al ahwazi Sharhin Tirmizi, juzI na 3, shafi 160  163.
3. Al  Madkhal na Ibn Hajji, juzI na 3, shafi na 50.

11. YAYA ZAMU FUSKANCI AZUMIN RAMADAN
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya sanya azumi ya zama daya daga cikin rukunana Musulunchi. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (S.A.W.) fiyayyen wanda yayi sallah kuma yayi azumi Sallallahu Alaihi wa sallam.
Bayan haka hadisai inganttu masu yawa sunzo da kwadaitarwa da bada romon azumin wattan Ramadan, wadanda suke nuna falalar ibada da daukaka da matsayi da mai Azumi yake samu, sannan kuma ga gafara ga zunubbai koda kuwa sunkai yawan kumfar teku.
An karbo daga Abu Huraira RA cewa Manzon Allah (S.A.W.) yace Duk wanda yayi azumin watan Ramadan yana mai imani da Allah, yana mai neman  lada daga Allah, to an gafarta mashi dukkan abinda ya gabatar na zunubai. Imam Bukhari ya ruwaito wannan hadisi na 1901. Imam Muslim ma ya ruwaito shi a hadisi na 759
Haka nan kuma an karbo daga Abu Huraira R.A. cewa wata rana Manzon Allah (S.A.W.)  yahau Mumbari. Yana hawa sai yace Amin, Amin, Amin ( sau uku (3) ). Sai sahabbai suka tambayeshi dalilin cewa Amin, Amin, Amin. Sai Annabi yace Lalle Malaika Jibril yazo mani yace  Lalle duk wanda ya riski watan Ramadan amma baa gafarta masa ba a cikin watan, har ya shiga wuta, to Allah ya nisanta shi daga rahama. Sai Jibril yace mani ce Amin. Ahmad bn Hambal ya ruwaito wannan hadisi. Hadisi na 246, da kuma Baihaki a juzI na 4, shafi na 204 da Ibn Huzaimah, hadisi na 192.
Har wayau dai daga Abu Huraira RA yace, Manzon Allah (S.A.W.)  yace Salloli guda biyar (5), Jumaa zuwa wata Jumaa, Ramadan zuwa wani Ramadan suna kankare abinda mutum ya gabatar na laifuffuka tsakaninsu, idan dai mutum ya nisanci manyan zunubbai. Imam Muslim ya ruwaito a hadisi na 233.
To shin zamu fuskanci azumin watan Ramadan ne da barci da rana da rashin barci da dare wajen kallace  kallace da hirar banza, kokuwa zamu fusakance shi ne domin kawai tanadin abinci da abinsha mai dadi, ko kuwa zamu fuskanceshi ne da zuciya mai kunci da fuska mai duhu  wai zaa shiga watan kuntata.
Amsa:- To duk wadannan basu kamata da wannan wata  mai alafarma ba. Shi Musulmi na gaskiya yana fuskantar watan Azumi ne da tuba ta gaskiya da ayyuka na kwarai da karatun alkurani da ambaton Allah da yawaita nafilfili da yawaita halartar wuraran Tafsirai da bada dukiyoyi wajen ciyar da masu azumi musamman yan uwa na jini. Lokaci dai ne na takara wajen gabatar da ayyukan alheri.
Kuma ku sani cewa idan bawa bai tsabtace gabobinsa ba daga Zunubi na boye, kamar su Keta da Algusshu, da Munaficci da Yaudara da Giba da Annamimanci, to baida komi na azumi sai dai yunwa da kishirwa. Yazo a cikin Sahihul Bukhari cewa Manzon Allah (S.A.W.)  yace Wanda bai bar karya da aiki da karya ba, to Allah bai bukatar barin cin abincinshi da abin shanshi. Hadisi na 903.
Haka kuma hadisai inganatattu sun nuna cewa Allah ((S.W.T)) ya kebance watan Ramadan da wasu abubuwa masu yawa wanda babu su a sauran watannin shekara. Daga cikin wadannan abubuwa akawai daren Lailatul Kadari. A cikin watan Ramadan ne ake bude kofofin Aljanna.  a  kulle kofofin wuta, kuma a cikin sane ake daure shaidanu musamman shaidanun aljanu.  Kuma cikinsa ne Malaiku kema masu azumi istigfari lokacin bude baki. Kuma a cikin sane  wani mai kira zaiyi kira Ya kai mai neman alheri, ka gabato, Ya kai mai aikata sharri, ka takaita" kuma lalle a cikinsa ne Allah (S.W.T) yake ‘yanta mutane masu yawa daga shiga wuta.

                                               12.  ADDU’O’I CIKIN WATAN AZUMI
بسم الله الرحمن الرحيم
Addu’ar buda baki
ذهب الظمأ وابتلت العروق وثبت الأجر إن شاء الله .1
Addu’ar da idan wani ya baka abinci zakayi masa.

أكل طعامكم الأبرار  وصلت عليكم الملا ئكة وأفطر عندكم الصائمون .2
اللهم أطعم من أطعمنى واسق من سقانى .3
اللهم اغفر لهم وارحمهم وبارك فيما رزقتهم .4
YAYA ANNABI (S.A.W.)  YAYI SALLAR TARAWIHI?
Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) wanda ya farlanta azumin wata Ramadan. Tsira da amincin Allah su tabbata ga manzonsa Muhammad (S.A.W.)  wanda ya sunnanta mana Sallar Tarawihi.
Bayan haka, ya danuwa musulmi barkarmu da shiga wannan wata mai albarka, wato watan Ramadan. Watan haske, Watan Rahama, Watan Ibada. Bayan shi kanshi azumi, wata babbar ibadar da ake kwadaitar da ita a cikin wannan wata itace tarawihi. To yadda Annabi yayi sallar Tarawihi, ya kuma bada umurni ayi ta shine zamu bayyana anan insha Allah.
ManzonAllah (S.A.W) yana rakaa 13 a sallar Tarawihi. Amma ga yadda suka zama goma sha ukun. Aisha RA tace Manzon Allah (S.A.W.)  wani lokaci yana rakaa goma, wato yana sallama bayan kowace rakaa 2, sai ya cika da wutiri rakaa daya daga nan sai bayan alfijir ya keto sai ya tashi ya kawo Rakaatanil Fijri rakaa 2. idan aka hada wadancan rakaoI goma sha daya na farko sun bada jimlar 13 kenan.
Manzon Allah (S.A.W.)  wani lokaci yana rakaoi 13 kamar dai yadda Aisha RA ta kasa su yana raka;a 2 bayan sallar ishaI inda yake karantawa kowace rakaa fatiha kawai kamar yadda ya saba yi koda ba cikin watan Ramadan ba sannan sai ya kawo rakaa 6, yana sallama bayan kowace rakaa 2. Sannan sai ya kawo rakaa 5 a jere ba tareda ya zauna ba sai a karshen rakaa ta biyar din. Wannan shi ya bada jimlar rakaa 13. To anan ya kamata a fahimci yadda wadannan salloli suka zama rakaa 13, sabanin yadda wasu suke yinsu a yanzu.
Manzon Allah (S.A.W.)  yana rakaa goma sha daya. Bayan kowace rakaa 2 yayi sallama. Sannan sai ya cika witirin rakaa guda. Anan ne Aisha RA take cewa Annabi bai taba wuce rakaa goma sha daya ba, a cikin Ramadan ne ko kuma ba Ramadan ba.
Manzon Allah (S.A.W.)  yana rakaa goma sha daya. Da farko zaiyi rakaa 4 jere, ba tareda rabawa tsakaninsu ba. Sai karshen ta hudin ya sallame. Sannan sai ya kawo wasu rakaoI 4 kamar na farko daga nan sai ya sallame. Bayan wannan sai ya kawo rakaa 3 a jere na wutiri sannan ya sallame.
Manzon Allah (S.A.W.)  yana rakao’i 8 a jere, sai karshen ta takawas din ya zauna. Yayi tahiya, yayi salati. Ba zai sallame ba, sai ya mike ya kawo wutirin rakaa daya, sai ya zauna yayi tahiya, yayai sallama. Bayan wannan sai yayai rakaa 2 a zaune.
Manzon Allah (S.A.W.)  yana rakaa 6 jere, sai karshen ta shida ya zauna, yayi tahiya, yayi salati. Ba zai sallame ba, sai ya mike ya kawo witirin rakaa guda, sai ya zauna yayi tahiya yayi sallama. Bayan wannan sai yai rakaa 2 a  zaune.
Ya danuwana, wannan shine tsarin yadda Manzon Allah yayi sallar tarawihi, kuma ya bada umarni ayi,kamar yadda Bukhari ya ruwaito hadisin da Manzon Allah (S.A.W.)  yake cewa  Kuyi salllah kamar yadda kuka ga ina sallah. Hadisi na 631. Haka kuma Khalifa na 2 Umar Dan Khaddabi RA ya raya wannan sunna kuma yayai umarni da ita. Haka nan kuma Imamu Malik ya fada a cikin littafin Al Masabihu fi Salatit Trawihi, da kuma sharhin Tirmizi Tuhfatul Akhwaz  cewa duk wani hadisin da yazo da cewa ana sallar tarawih rakaa 27 ko 30 ko 40, to wannna hadisi bashi da asali kuma karya ne. Abinda yake alheri mu tsaya ga inda Annabi (S.A.W.)  ya tsaya, wato rakaa goma sha daya.
Daga karshe muna jawo hankalin yan uwa da mu kula da yin kunuti a cikin witiri, wato bayan an karanta fatiha da sura, kafin rukui. Haka Manzon Allah (S.A.W.)  yayi kamar yadda aka ruwaito daga Hassan Dan Aliyu Ibn Abi Talib RA.
Don Karin bayani a duba wadannan littafai.
Muwadda Malik, Bulugul Marami, Tuhfatul Akhwaz (shrhin tirmizi), Al Masabihu fi salatil Tarawih na Imam Suyidi, sifatu saumin Nabiyyi fi Ramadan, Kiyamu Ramadan na Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albani, Salatul Tarawih, shima na Albani.

                14      KWANA GOMA (10) NA KARSHEN RAMADAN
                         (Falalarsu da Ayyukan da ake so ayi a cikinsu)
Yabo da godiya sun ta tabbata ga Allah (S.W.T) wanda yake sa albarka ga ayyukan ibada. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzonsa Muhammad (S.A.W.)  wanda ya bayyana mana yadda ake ibadoji.
Bayan haka, ya danuwa, kamar yadda ka sani, watan Ramadan mai Albarka yana dauke da haske da falala mai tarin yawa, wanda ake bukatar Musulmi ya dage ga yin ayyukan ibada fiye da a cikin sauran watanni. To kuma a cikin kwanaki goma na karshen watan, yafi cancanata mu rubanya irin wanan dagewa ta neman rahamar Allah (S.W.T) ta hanayr nafiloli da zikirai da sauransu.
An karbo daga Aisha RA cewa a cikin kwanaki goma na karshen Ramadan, Manzon Allah (S.A.W.)  yana kara zage damtse wajen yin ibdada ta hanyar raya wadannann dararen da kuma umurtarsu suma suyi haka. Imam Bukhari ya ruwaito wannan hadisi a cikin Sahih nashi, hadisi 2024.
Daga cikin ayyukan ibada da ake so a yawaita a cikin wadannan darare akwai Itikafi da Sallar Tahajjud, kamar yadda hadisi ya tabbata Manzon Allah (S.A.W.)  yayai Iitikafi a cikin goma na karshen Ramandan har lokacin da Allah ya karbi rayuwarsa. Hakanan kuma matansa sunci gaba da yin Iitikafi bayan rasuwarsa (S.A.W.) . Hadisi na 2029 a cikin Sahihul Bukhari . Haka kuma a hadsisi na 2027 na Bukharin dai, Manzon Alah (S.A.W.)  yace Wanda yake son yayi Iitikafi tare damu to yayi a cikin kwana goma na karshen Ramadan, domin hakika an nuna mani darean lailatul kadri a cikin wadannan kwanaki.
Wadannan hadisai suna nuna mana mahimmancin Iitikafi, inda bawan Allah yakan bar duk wata walwala ta duniya, ya shiga kuncin kadaita da bauta domin kawai neman yardan Allah (S.W.T). Sai dai ya kamata a kula, wanda yake son yayi Iitikafi irin wanda Manzon Allah (S.A.W.)  yayi, to sai ya shiga bayan sallar Asuba, ba kamar yadda wasu sukeyi ba na shiga bayan sallar laasar ba, saboda hadisin da Imam Bukhari ya fitar,hadisi na 2023, inda Aisha RA take cewa Manzon Allah ya kasance yana shiga Iitikafi a cikin darare goma na karshen Ramadan, inda ni nike kafa mashi hema (tanti) a cikin masallaci, sai yayi sallar Asuba sannan ya shiga. Iitikafi.
Wata babbar falala da ake samu a cikin goma na karshen Ramadan itace samun Lailatul Kadri. Allah (S.W.T) ya saukar da sura sukkutum a cikin littafinsa mai tsarki inda yake mana bayanin girman daren da falalar dake tattare a cikinsa. Allah mai girma da daukaka yace Lalle mun saukar da wannan Alkurani a cikin daren daraja. Me ya sanar dakai abun da ake cewa Daren Daraja. Daren darajja yafi daga wata dubu. Malaiku na sassauka a cikin daren tareda Malaika Jibrilu da izinin Ubangijinsu daga dukkan umarni (wanda Allah (S.W.T) ya basu). Aminci ya tabbata ga wannan daren har zuwa fitowar Alfijir.  A cikin wannan sura zamu fahimci cewa idan mutum ya dace da daren Lailatul kadri, kuma aka same shi yana ibada a cikinsa, to zaa bashi ladar ibadar kwatankwacin shera 83. Abu Huraira RA yace Manzon Allah (S.A.W.) yace Wanda ya tsayu a daren Lalatul Kadri yana mai imani, kuma yana mai neman lada, an gafarta masa dukkan abinda ya gabatar na zunubansa. Imamu Bukhari ya fitar da wannan hadisi mai lamba 2014. Ya kamata Musulmi su kula da lokkutan daya kamata a nemi daren Lailatul kadari, kamar yadda hadisi yazo a cikin Sahihul Bukhari, hadisi na 2023, inda Ubada Ibn Samit yake cewa Manzon Allah [SAW]yace:- Na fito domin in baku labarin lokacin daren lailatul kadri, sai na taras da wane da wane suna jayayya. Sanadin wannan jayayya  sai aka dauke mani sanin wannan daren. Kila wannan yafi zama alheri gareku. Don haka ku nemeshi daren 29 da daren 27 da daren 25. Haka kuma an karbo daga Aisha RA cewa Manzon Allah (S.A.W.)  yace Ku nemi daren lailatul kadri a cikin witri (mara) na goma na karshen Ramadan. Sahihul Bukhari hadisi na 2017.
Alamomin da ake gane Lailatul Kadri zata zo sune:
Da safe rana zata fito babu haske sosai, sannan cikin daren babu zafi babu sanyi, kamar yadda Ubayyu Ibn Kaab yace. Manzon Allah (S.A.W.)  yace Safiyar Lailatul kadri zata fito babu haske a gareta sosai, kai kace an rufeta ne. sai ta dago sosai sannan zata bayyana. Muslim ya ruwaito wannan hadisi mai lamba 762. Abdullahi Dan Abbas RA ya ruwaito cewa Manzon Allah yace Daren Lailatul kadri dare ne mai sauki, wanda babu hayaniya a cikinsa, babu zafi babu sanyi a ciki. Imam Dayalisi da Ibn Huzaima da Bazzar suka fitar da wannan hadisi. Anso ga wanda ya ga wadannan alamomi a cikin daran ya yawaita wannan Adduar kamar yadda Aisha ta ambata a ciki hadisin da ta tambayi Manazon Allah (S.A.W.)  cewa  Idan na dace da daran lailatul kadri, me zance a cikinsa? Sai Manzon Allah[SAW] yace Kice, ya Allah kaine mai rangwame, kuma kana son rangwame, kayi mani rangwame
ALLAH YA BAMU DACEWA DA BIN SUNNAR MANZON ALLAH (S.A.W.) .
Domin Karin bayani a duba Sahihul Bukhari da Muslim da Bulugul Maram.
                                14    MENE HUKUNCIN AZUMIN TASUA DA ASHURA
Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) wanda ya farlanta azumin watan Ramadan. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzonsa Muhammad (S.A.W.) wanda ya sunnan ta azumin Tasua da Ashura.
Bayan haka, ya dan uwana, lalle ne ka sani azumin tasua da ashura sunna ne na Annabi (S.A.W.). An karbo daga Abdullahi dan Abbas (RA) yace lokacinda Manzon Allah yazo Madina ya taras da yahudawa suna azumin ashura, sai ya tambayesu Wane irin azumi ne wannan? sai sukace, Muna azumin wannan rana ne domin ita rana ce mai daraja wadda a cikinta ne Allah ya tserar da Annabi Musa (AS) da Bani Israila daga Makiyinsu (Firauna), don haka Musa (AS) yake azumin wannan yini. Sai Manzon Allah (S.A.W.)  yace Ni na fiku cacanta da inyi koyi da Musa[AS]. Bukhari da Muslim suka ruwaito wanan hadisi.
Harwayau dai an karbo daga Abbas (RA), yace lokacin da Annabi (S.A.W.)  yake Azumin Ashura sai Sahabbai sukace Ya Manzon Allah wannan fa, Yahudawa da Nasara sun girmama shi, Daga nan sai Manzon Allah (S.A.W.)  yace in Allah yaso idan shekara ta dawo zamu azumci Tasua tareda Ashura. To sai dai kuma Annabi (S.A.W.)  ya rasu kafin dawowar shekara. Musulim da Abu Dawuda suka ruwaito. Wanna shi yafi karfafa cewa azumin Tasua da Ashura sunna ne.
Syed Sabik ya fada a cikinFikhus Sunna cewa Malamai sun kasa azumin Ashura cikin darajoji uku. Daraja ta farko itace mutum ya azumci ranar tara da goma da sha daya ga watan, wato Tasua da Ashura da yini mai bima Ashura. Wannan yayi daidai da umurnin Annabi (S.A.W.)  da ya bayar cewa Musulmi yayi azumin nafila ukku kowa ne wata. Idan mutum yayi azumin wadannan ranaku, ya samu ladar sunna biyu ko kuma fiye da haka. Daraja ta biyu itace mutum yayi azumin Tasua da na Ashura. Ta ukku itace mutum yayi azumin Ashura shi kadai. Sai dai alura akwai wasu abubuwa da akeyi ranar Ashura wadanda ake ganin kamar addini ne, alhali ba addini bane. Daga cikinsu akwai:-
Taron nuna bakin cikin mutuwar Sayyidina Hussaini Dan Aliyu Bn Abi Talib wanda yan Shia sukeyi kowace ranar Ashura. Wannan taron Bidia ne bai da asali a addinin musulunci.
Daukar daren Ashura ya zama daren cika-ciki, shima bidia ne.
Akwai hadisin da mutane suke aiki dashi suna wahal da kansu wajen kara cefane wai domin yalwatawa iyalinsu a ranar Ashura. To wanan hadisi mai rauni ne baa aiki da shi.
Wasu suna cewa wai a ranar Ashura idan aka sa rariya aka dubi ranna wai zaa iya ganin yan matan Aljanna. Duk wannan tatsuniya ce ta shaidan. Allah ya tsare mu amin.
FADAKARWA
Yawancin hadisan da ake kawowa gameda falalar Asura indai ba wadanda muka ambata a sama ba, to hadisai ne masu rauni wadanda bai kamata ayi aiki dasu ba. Don haka danuwa kada ka rudu da yawan malaman da suke irin wannan waazi a kafafen watsa labaru da sauran wuraren waazi. Allah yasa muyi muwafaka da sunnar Manzon Allah (S.A.W.)  Amin.
MUHIMANCIN KWANA GOMA NA FARKON WATAN ZHULHIJJAH
Dalilai da yawa na sharia suna nuna falalar dake kunshe a cikin wadannan kwanaki goma na farkon watan zulhijja, wato watan sallar layya.
Allah (S.W.T) yana cewa a cikin suratul Fajr, aya ta daya da ta biyu ina rantsuwa da Alfijr da kuma Darare Goma. Magabata da yawa sun fassara dararen da cewa darare goma ne na farko watan Zhul-hijjah.
An ruwaito ingantattun hadisai da yawa inda Manzon Allah (S.A.W.)  yayi Magana akan falalar dake kunshe a cikin kwanaki goma na farkon watan zhul-hijja. Daga cikinsu akwai:-
Hadisin Abdullahi Ibn Abbas (RA) wanda Imam Bukhari da Imam Tirmizi suka ruwaito Manzon Allah (S.A.W.)  yake cewa Babu wasu kwanaki da aiki nagari yafi soyuwa ga Allah a cikinsu kamar wadannan kwanaki goma sai sahabbai suka ce Harda jihadi fi sabilillah ya Manzon Allah?. Sai Annabi yace naam, sai dai mutumin daya fita yaki da jikinsa da dukiyarsa, amma kuma daga shi har dukiyar bai dawo da ko guda ba.
An karbo daga Abdullahi Ibn Umar (RA) cewa Manzon Allah (S.A.W.)  yace Babu wasu ayyuka da suka fi girma a wajen Allah kuma suka fi soyuwa a gareshi kamar wadanda akayi a cikin kwanaki goma na farkon watan Zulhijjah. Don haka ku yawaita Tahlili da Tahmidi da Takbiri a cikinsu. Imamu Ahmad ya fitar da Hadisin.
A cikin wadannan kwanaki ne ake samun ranar Arafat da ranar Sallar Layya wadanda kowace daga cikin wadannan ranaku tana da falala mai dimbin yawa kamar yadda aka samo daga ingantattun hadisan Manzon Allah (S.A.W.). Shehin Islam Ibn Taimiyya ya fada a cikin littafinsa Majmuul Fatawa cewa wadannan hadisai suke nuni ga cewa darare goma na farkon Zul-Hijjah sunfi darare goma na karshen watan Ramadan.
WADANNE AYYUKA NE AKE BUKATAR AYI A CIKIN WADANNAN KWANAKI GOMA

Tuba ta gaskiya daga barin laifuffuka.
Yin aikin Hajji da Umra
Kiyaye ayyukan Farilla a cikin lokutansu.
Yawaita Nafiloli
Yawaita ambaton Allah, kamar yadda Allah ya fada a cikin aya ta 28 a Suratul Hajji
Maana:- ku yawaita ambaton Allah a cikin kwanaki sanannu (wato kwana goma na farkon watan Zul-Hijjah)
Bayyanar da kabbarori a cikin Masallatai da Gidaje da hanyoyi da sauransu, kamar yadda Abdullahi Ibn Umar da Abu Huraira suka yi. Ga yadda ake kabbarorin.
Allahu Akbar, Allahu Akbar Kabirah
Allahu Akbar, Allahu Akbar, La ilaha illallahu wallahu Akbar, wa lillahil hamd.
Wadannan kabbarori mutane da yawa sun watsar dasu, wasu da yawa ma basu san anayinsu ba, don haka muna kira ga yan uwa Musulmi damu raya wadannan kabbarori.
7. AZUMI:- Anso Musulmi ya Azumci wadannan ranaku goma. An karbo daga Uwar Mummunai Hafsat RA tace Manzon Allah (S.A.W.)  bai kasance yana barin abubuwa hudu ba. Azumin Ashura da Azumin kwana goma na farkon zulhijja da azumin kwana ukku kowane wata da kuma Rakaatanil Fajari Imam Ahmad da Abu Dawud da NisaI suka ruwaito, kuma hadisi ne ingantacce. Sai dai a kula baa yin azumi Ranar Sallah.
8. LAYYA:- Layya sunnar Annabi[SAW] ce mai karfi ga wanda ya samu hali, wasu Malamai ma suna cewa wajibi ce saboda maganar Allah da yace Kayi sallah domin Ubangijinka kuma kayi suka (layya).
9. A yawaita ayyukan tallafi da jinkai ga masu rauni kamarsu zawarori da marayau da miskinai ta hanayar taimaka masu da ragunan layya da dunkin sallah da duk abinda zaisa suyi idi cikin farin ciki kamar kowa.
10. Ita kanta SALLAR IDI da RANAR SALLAR suna da dimbin falala da albarkoki.
FADAKARWA: Idan watan Zul-Hijja ya tsaya baya halatta ga duk wanda yake nufin yin layya yayi aski ko ya cire wani gashi a jikinsa ko ya cire akaifa ko wata fata a cikin kwanakin nan goma na farko har sai ya yanka layyarsa.

MENENE ALAKAR TSAYUWAR ARFAT DA IDINMU NA LAYYA?
Godiya ta tabbata ga Allah (SWT) wanda ya farlanta mana aikin hajji. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzonsa Annabi Muhammad (S.A.W.) wanda ya wajabta Idin layya tare da layya.
Yakai danuwa muslmi, a bana mun samu banbancin kwanukan wata tsakanin mu da Saudiya. To menene mafita? Amsa:- Mafita shine bin Allah da manzonsa Annabi Muhammad (S.A.W.). Allah (S.W.T) ya tsara muna lokuttan ibadar mu na sallah, Azumi, Layya da aikin Hajji. Manzonsa Annabi Muhammad (S.A.W.) ya fayyace muna yadda ayyukan suke a cikin sunnah.
Imam Malik yace babu abun da zai inganta wannan alumma tamu saida abunda ya inganta alummar farko, akwai wasu hukunce-hukunce da zasu iya walwale muna wannan matsalar kamar guda biyar (5).
An karbo daga Anas (RA) yace Manzon Allah (S.A.W.) yazo Madina ya iskesu da wasu ranaku (2) da suka kebesu domin yin wasa, sai ya tambaye su cewa wadannan ranaku fa? Sai sukace mun kasance muna wasa a cikinsu tun lokacin jahiliyya. Sai Manzon Allah (S.A.W.) yace to yanzu Allah ya musanya maku da ranar Idil Layya da Idil Fitr. Abu Dawuda (1134). Sayeed Sabiq ya fada a cikin Fiqhu Sunnah cewa Sallar Idi (2) an sharantasu a shekarar farko ta hijra. Sheikh Salih Uthaimin a sharhinsa na Riyadul Saliheen yace shi aikin hajji an farlantashi a shekara ta tara bayan hijira. Anan zamu gano sai bayan an shekara (9) anayin ibadar layya sannan akak sharanta aikin hajji. Don haka ashe ba a bin mamaki bane don an samu sabanin kwanuka.
An karbo daga Aisha (RA) tace Manzon Allah (S.A.W.) yace Idil fitr, itace ranar da mutane suka dauka ranar Idil Fitir ga lissafinsu. Ita kuma Idin Layya itace ranar da mutane suka dauka itace Idin Layya ga lissafinsu Imam Turmithi (802). Sheikh Ali Bassam ya fada a cikin Sharhin da yayi na Bulugul Marami, yace idan mutane su kayi arfa (8) ko (10) ga wata ko sukayi Idil layya (10) ga wata sai akayi arfa kuma (10) ga wata. Yace layyarsu tayi hakama tayi tun da dai sun bi lissafinsu ne.
A lokacin sahabbai, anga wata a kasa Sham daren Jumaa, Maawuya yana Gwamna sannan kuma aka ganshi daren Asabar a Madina lokacin  Abdullahi Dan Abbas. Da suka hadu a Madina sai Abdullahi Dan Abbas yace kowa yayi amfani da ganinsa domin haka Manzon Allah[SAW] ya umurce mu. Imama tirmizi (1300). Imam Sanani ya fada a cikin Subul-salam sharhin Bulugul Marami cewa wajibi ne ga mutane subi yankin da suke a wajen ganin wata. Hakama a wajen aikin hajji saboda Anabi Muhammad (S.A.W.)  yace Arfarku ranar da kuka dauka itace Arfa.
An tambayi Manzon Allah[SAW] game da azumin ranar Arfa sai yace Azumin yinin Arfa yana kankare zunnuban shekaru (2) Anan ne zamu iya gano cewa ashe ba Arfa akeyi ma azumi ba, a cikin yinin ne akeyin azumin. Da wannan ne muka fahimci cewa inkai azumin yinin ko an hau arfa ko ba'a hau ba kayi azumin yinin arfa to yayi domin azumin shi ya gabaci Arfa. Shi kuma yinin yana kamawa (9) ga wata. Anan ne muka gano cewa babu hujja cewa sai kabi Saudiyya domin lokkutan mu sunsha bamban. In kun lura lokacin da muke Sallah Asubah a Nigeria a Saudia rana tayi. Haka ma tsayuwar Arfa anayin shi da rana ne, to a wata kasa tsakiyar dare ne adaidai lokacin, ya zasuyi kenan.
Wajibi ne yin daa ga shugabanninmu na musulunchi indai ba wajen saba ma Allah ba.
Allah (S.W.T) yana cewa yaku wadanda sukayi imani kubi Manzo da majibinta (shuwagabanni) alamuranku. Imam Bukhari ya ruwaito hadisi: cewa Manzon Allah (S.A.W) yace wanda yabi shugabanni hakika ya bini wanda kuma ya saba masu hakika ya saba mani.
Don haka idan Sarkin Musulmi ya bada sanarwa anga wata wani kuma yaki bi, to ya kamata a yakeshi don yazama dan tawaye mai tsallake iyakar Allah da manzonsa (S.A.W).
FADAKARWA:- Yaku yan uwa musulmi yana da kayu duk lokacin da wata matsala ta taso, ba dai-dai ba ne kayi amfani da raayi ko ina ganin ya dace, ya zama wajibi ka binciki malamai. Kuma su malaman ka kula da irin hujjojinsa da suke bayarwa domin suma ana masu daa ne idan sun bi Allah da Mansonsa.
Daga karshe muna rokon Allah (S.W.T) ya aza mu kan bin sunnar Manzon Allah (S.A.W) kuma ya kashemu a kanta Amin.
(6) Haka nan an tambayi Ibn Taimiyya a cikin Fatawal Kubura juzi na biyu shafi na 353, idan mutane suka ga watan zulhijja (misali Najeriya) hukumar Saudiya, basu ganshi ba ko za suyi azumin Arfa?.
AMSA:- Zasu yi azumin tara ga wata kamar yanda yake a wajansu dudda a Saudiya ba rannan bane Arfa.
Saboda Hadisin Abi Huraira inda yace Manzon Allah yace “Azumin ku ranar da ake azumi a wajenku, ajewar ku ranar da kuka aje, layyarku ranar da ku ka dauka ranar layya a wajenku. Abu Dauda da Tirmizi da Ibn Majah su ka ruwaito. Sheikh Usaimin shima haka ya fada a cikin fatawa tashi juzI na 26 shafi na 92

18. LAYYA DA HUKUNCE - HUKUNCENTA
1. Me ake nufi da layya?
Layya wata ibada ce akeyi ranar Babbar Sallah ta hanyar yanka dabbobin niima (Rakumma, Shanu, Tumaki da Awaki) domin neman kusanta ga Allah S.W.T.

2. MENENE HUKUNCIN LAYYA A SHARIA?
Layya wajibi ce ga kowane Muslmi baligi wanda yake da halin sayen dabbar. Allah (S.W.T) yana fada a cikin Suratul Khauthar aya ta 2  kayi sallah domin ubangijinka kuma ka soke layyarka.
Sannan kuma Ibn Majah ya fitar da hadisi da Abu Huraira ya ruwaito cewa Manzon Allah[SAW] yace wanda yake da halin yin layya, amma yaki yi, kar ya kuskura ya kusanci masallacinmu.
3. KO AKWAI WATA FALALA DA KE TATTARE DA LAYYA?
Falala mai yawa tana nan cikin yin layya. Manzon Allah (S.A.W.)  yace Yini mafi falala daga cikin ranaku shine yinin Babbar Sallah  wato yinin da ake layya a cikinsa, daga nan sai sauran kwanakin zama Mina bayan sallah.
Sheikhul Isalam Ibn Taimiyyah yace mafi girma daga ibada ta jiki itace Sallah, sannan mafi girman ibada ta kudi itace layya.
4. WADANNE HIKIMOMI KE KUNSHE A CIKIN LAYYA
Hikimomi dake cikin layya suna da yawa. Daga ciki:-
Ta hanyar layya musulmi yana kara kusantar Allah.
Ta hanyar layya Musulmi na wadatar da talakawa da mabukata.
Tana kara soyayya tsakanin abokai da yanuwa wadanda aka aikawa da naman layya.
Tana bada dama a wadata iyali da nama, kamar yadda yazo a hadisi Manzon Allah (S.A.W.)  yace kwanakin layya kwanaki ne na ci da sha da kuma ambaton Allah.
Ranar sallah da yankan layya suna bayyanar da alamomin addinin Musulunchi.
Yin layya yana tunatar muna da shiryayyun shugabannin farko Annabi Ibrahim (A.S) da Annabi Ismail (A.S) da mabiyansu wajen bin umurnin Allah da kuma hankuri wajen zartar da umurni.
Yin layya yana kamanta wanda yake gida da mahajjaci wajen sunnar nan ta kabbarori a cikin wadannan kwanaki 3 da kuma hana aski da yanke akaifa ga duk wanda yayi nufin yin layya kamar yadda aka hana mahajjaci yin wadannan abubuwa.
    5. DA WADANNE IRIN DABBOBI AKE YIN LAYYA?
Ana yin layya kodai da rakuma koda shanu ko da tumaki ko da awaki.
    6. KO INA IYA YANKA DABBA DA NUFIN DUK WANDA YAKE GIDANA YA SHIGA CIKIN LAYYAR.
Wannnan ya halarta karkashin hadisi da Imamu Malik ya fitar Abu Ayyubul Ansari yake cewa muna yanke akuya guda domin mai gida da mutanen gidan.
     7. KO YA HALATTA GA MAIGIDA DA YA YANSA SUYI KAMFANI SU SAYI RAGO KO AKUYA SUYI LAYYA.
Ya halatta, da sharadin suna zaune gida guda. Idan suna gidaje daban daban to bai halitta ba. Ahmad da Abu Dauda sun fidda hadisi da Manzon Allah,(S.A.W.) yace  yaku mutane lallai ne a kowane gida ayi layya kowa ce shekara.
8. Ko daidai ne mutanen unguwa su hada kudi su sayi sa ko rakumi su yanka.?
Eh ya halatta mutane bakwai suna iya hada kudi su sayi Sa, su yanka. Mutum goma kuma suna iya hada kudi su sayi rakumi su yanka.
9. WANE LOKACI NE AKE YANKAN LAYYA.?
Ana yankan layya ranar Babbar sallah bayan liman ya yanke Ragonsa da kuma kwanaki biyu bayan ranar sallah.
FADAKARWA:- A lura cewa layya a matsayinta na ibada ta shafi kowa da kowa. Maana matar aure da matashi wanda baiyi aure ba ko kuma Yan mata wadanda Allah ya hore masu abin yin layya, to wajibi ne suyi. Kar a dogara da cewa wadda maigida yayi ta wadatar. ALLAH YAYI MUNA JAGORA, AMIN.
19. KO KASAN BIDIOIN DAKE FARUWA CIKIN AIKIN HAJJI?
Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) wanda ya farlanata aikin hajji. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah (S.A.W.)  wanda ya tsara yadda zaayi aikin hajji, a cikin hadisi inda yake cewa ku riki aikin hajji daga wajena.
Yazo daga Manzon Allah (S.A.W.)  cewa duk aikin da babu umurninmu a ciki to zaa maida ma mai aikin da aikinsa sa Aikin Hajii yana da bidioI da yawa, akwai kusan bidia dari da sabain da shidda (176) a cikin aikin hajji, amma zamu tantance daga wadanda suka shafemu.
Imamu Malik ya tsaya wajen Rijiyar Zam-zam yana cewa yaku mutane wanda ya sannni ya sanni wanda bai sannin ba to nine Malik bin Anas, ina gargadi ga duk wanda yazo aikin haji yana bisa wata bidia kada ya wahalar da kansa bisa barna. (wato kenan ba aikin hajjinsa).
Bidiane yin sallah rakaa biyu lokacin da mahajjaci zai bar gidansa
Bidia ne kulla yan uwantaka da mace wadda ba muharrama ba koda abokin mijinta ne.
Bidia ne fitar da kafadar dama  lokacin da Alhaji yayi harama alhali anayin wannan ne lokacin da Alhaji zaiyi dawafin ummarah kawai Bayan nan ba inda ya halarta yayi hakanan.
Bidia ne yin lafazi wajen yin niyya: domin muhallin niyya shine kuduri a zuciya
Bidia ne wani nayin talbiya wasu na amsawa: domin ana son kowa yayi da kansa
Bidia ne matsetseniya da tunkudar juna a wajen sumbantar Hajarul Aswad
Bidia ne wani nayin addua wasu na amsawa
Bidia ne shafar kaaba da shafar mukamar Annabi Ibrahim[AS]
Bidia ne yin Addua a wajen indararon kaaba
Bidiane yin wanka da ruwan zam-zam, da manufar samun kudi
Bidia ne yin hailala kafa dari da karanta kulhuwallahu kafa dari wajen tsayuwar Arfa
Bidia ne hawan dutsen rahama wajen tsayuwar Arfa
Bidia ne wanke duwatsun jifa da ruwa kafin ayi jifa
Bidia ne cewa ka jefi shaidan domin ba shaidan ne ake jifaba ibada ce. Annabi Ibrahim shine ya jefi shedan.
Bidia ne yin jifa da takalma ko wani babban  dutse
Bidia ne yankan dabbar Hadaya kafin ranar Arfa
Bidia ne fara aske bangaren kai na  hagu kafin na dama
Bidia ne wucewa gaban mai sallah a kaaba
Bidia ne cewa mutum Alhaji idan ya dawo aikin hajji musamman idan mutum keson a ce mashi ko shi ke rubutawa a takarda.
Bidia ne  sa hakori ga namiji ko mace da manufar a cema mutum Alhaji ko Hajiya.
Bidia ne niyyar ziyarar kabarin Manzon Allah(S.A.W.)  kawai sai dai a yi niyyar ziyarar Masallacin Manzon Allah daga nan sai a wuce a ziyarci kabarin.
Bidia ne gabatar da ziyarar kabarin Manzon Allah [SAW] kafin yin nafila.
Bidia ne fuskantar kabarin Manzon Allah (S.A.W.)  lokacin da ake yin Addua.
Bidia ne tawassuli da alfarma ko darajar Manzon Allah (S.A.W.)  wajen Addua.
Bidia ne rokon Manzon Allah (S.A.W.)  ceto ko waninsa wajen addua.
Bidia ne kudurin yin sati guda Madina domin samun jamin sallah Arbain dan kubuta daga wuta da munafunci.
Bidia ne sunbantar Kabarin Manzon Allah (S.A.W.)  ko tabashi da hannu.
Bidia ne ziyarar kabarin Manzon Allah (S.A.W.)  kowace sallah.
Bidia ne ziyarar wasu Masallatai kamar Masjid Ijaba, Kiblataini da Sittatu Masajid sai idan kaje ne yawon bude idanu kawai.
Bidia ne Mahajjaci ya kallafa ma kansa sallah a Masallacin Fatima ko na Aisha da sauran Masallatai in banda na Annabi (S.A.W.).
Bidia ne ziyarar makabartar Bakia kullum; maimakon sau daya a sati kamar yadda Annabi (S.A.W.)  yayi.
Bidia ne fitowa masallacin Manzon Allah (S.A.W.)  da baya-baya ko na Kaaba
Bidia ne cewa Arfa ranar Jumaa tana dai-dai da Arfa sabain da wadda ba ranar Jumaa ba.
Da fatar yanuwa musulmi zasu kiyaye. Domin Manzon Allah[SAW] yace dukkan Bidia batace, dukkkan bata tana wuta (wato maabocin Bidia yana wuta) sannan wani hadisi wanda Manzon Allah (S.A.W.)  yake cewa duk maabocin Bidia Allah baya karbar tubarshi sai ya bar bidia.
IDAN ANA SON KARIN BAYANI A DUBA WADANNAN LITTAFAN
Almadhal na ibn Hajj
Ihayaus sunna wa Ikhmadul Bidia na Sehu Usman Bin Fodiyo
Attahziru minal Bidia na Abdul-Azeez Bin Baz
Munassikul Hajj wal-umrah na Albani

20. ADDUOIN DA AKE KARANTAWA DON RASHIN LAFIYA
* كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يعوذ بعض أهله يمسح بيده ويقول 1

Manzon Allah (S.A.W.) ya kasance yana neman tsari ga sashen iyalinsa, sai ya yi shafa da hannunsa na dama sai yace…

* اللهم رب الناس اذهب الباس اشفى انت الشافى لا شفاء إلا شفائك شفاء لا يغادر سقاما.

* إذا وجد الإنسان وجعا يجده فى جسده فيضع يده على الذى يألم من جسده ويقول: 2
Idan mutum ya samu wata rashin lafiya a jikinsa, sai ya aza hannunsa inda yake jin radadi sai yace (بسم الله)sau ukku  sannan yakaranta wannan addu’ar sau bakwai
أعوذ بعزة الله وقدرته من شر ما أجد وأحاذر.
*كان النبي صلى الله عليه وسلم: يأخذ من ريق نفسه على إصبعه السبابة ثم يضعه على التراب 3

Manzon Allah[SAW] ya kasance yana tofa miyau a manuninsa, sannan ya aza shi kan turbaya, sai ya dago ya aza yatsan inda yake jin ciwo sai yace…

بسم الله تربة أرضنا بريقة بعضنا يشفى سقيمنا بإذن ربنا.
*أن جبريل أتى النبي (ص) فقال يا محمد اشتكيت؟ قال نعم" قال 4

Lalle Mala’ika Jibril (A.S) Ya zowa Manzon Allah (S.A.W.)  yace Ya Muhammad bakada lafiya? Sai Annabi (S.A.W.))yace E Lalle bani da Lafiya, Sai Jibril (A.S) ya karanta mashi wannan addu’a ya tofa mashi a jikinshi.

بسم الله أرقيك من كل شئ يؤذيك من شر كل نفس أو عين حاسد, الله يشفيك بسم الله أرقيك
قال لنبي (ص) من عادمر يضا لم يحضر أ جله فقال عنده سبع مرات ألا عافاه الله من ذلك المريض. * 5
Manzon Allah[SAW] yace duk wanda ya je gaida maras lafiya  ya karanta masa wannan addu’a sau bakwai indai ba ajalinsa ya zo ba, to zai warke……
أسأل الله العظيم رب العظيم أن يشفيك
دعاء المريض الذى يأس من حياته * 6
Wanda ya kwanta rashin lafiya kuma yana ganin bazai tashi ba, to Manzon Allah[SAW] ya umurce shi ya yawaita karanta wannan addu’a.

اللهم اغفرلى وارحمنى وألحقن بالرفيق الأعلى
*من لدغه العقرب أوالجية يقر أبأم القرأن  يجمع بزق ويتفل: الحمد لله رب العالمين الرحمن الرحيم- إلى اخر ها 7
Wanda Kunama ko Maciji suka ciza, ya karanta fatiha ya tara miyau ya tofa a wurin da aka ciza. In Allah Yaso zata fadi
                                                                                                                                                        *كان النبي (ص) يفتل على نفسه في المريض الذى مات فيه بالمعوذات ثم يسح وجهه و يقل0  قل أعوذ برب الفلق إلى اخرها. قل أعوذ برب الناس إلى اخرها
Idan rashin lafiya ya tsananta, sai maras lafiya ya karanta kul’ auzu bi Rabbil Falak da bi Rabbin Nasi, ya tofa a tafukansa sai ya shafa a fuskarsa
ABUBUWA SHA BIYU DA SUKA WAJABA GA MARAR LAFIYA YA AIKATA
1. Ya yarda da abinda Allah ya hukunta masa, yayi hakuri da abinda ALLAH ya kaddara masa, ya kyautata zato ga ubangijinsa.
2. Ya kasance yana tsoro ga azabar ALLAH kuma yana kauna ga rahamarsa in ya mutu.
3. Kada yayi burin mutuwa don rashin lafiya ya tsananta gareshi.
Annabi (S.A.W.)  yace sai dai kace ALLAH ka rayani matukar rayuwar tafi zama alheri a gareni; ko ka kasheni matukar kashewar tafi zama alheri gareni"
4.Ya maida hakkoki ga masu su in ya samu dama, in bai samu dama ba yayi wasiyya.
Ba makawa gareshi ya gaggauta yin wasiyya (musamman ma inda hakkokin wasu wajenshi).
Yayi wasiyya ga yan uwansa (wadanda basu gadonsa) da makwabtansa da masu yi masa hidima (maana yayi masu alheri da wani abu daga dukiyarsa)
Ya kamata ne yayi wasiyya da kashi daya bisa ukku (1/3) na dukiyarsa; kada yafi haka; anfi son ma ya kasa hakan.
Wajibi ne ya kafa shedu biyu adilai kuma Musulmi (akan wasiyyarsa).
Baya halatta ya sanya uwayensa ko yayansa ko yan uwansa masu gadon a cikin wasiyyar.
Ya haramta a gareshi yayi wasiyyar kada abaiwa wani daga cikin yayansa gado; ko yace afi-fita wani akan wani wajen rabon, domin cutarwa ne.
Annabi (S.A.W.)  yace Babu cuta, Babu cutarwa
Duk wasiyyar data sabawa sharia, to wannan wasiyyar zaa watsar da ita.
Yayi wasiyyar akan gaggauta rufe shi in ya mutu (kada ayi jinkiri). Yayi wasiyyar kar ayi masa kuka idan ya mutu.
Annabi (S.A.W.) yace: kuka ga mamaci na kara azaba a kabari ya kuma yi wasiyyar akan kar ayi shelar mutuwarsa a Rediyo, ko Lasifika da dai sauransu. Annabi (S.A.W) yayi hani ga shelar mutuwa.
ALAMOMIN WANDA YAYI MUTUWAR SHAHADA

Manzon Allah (S.A.W.)  yace akwai alamomi goma sha Tara (19) wadanda ke nuna mutum yayi mutuwar shahada sune: -
Wanda ya kasance maganarsa ta karshe kafin ya mutu itace La’ilaha illa Lahu.
Wanda ya mutu goshinsa na jibi.
Wanda ya mutum daren jumaa (wato bayan yammar Alhamis) ko kuma a cikin yinin jumaar.
Wanda aka kashe a fagen yakin jihadi.
Wanda ya mutu a cikin wani aiki na daukaka addinin musulunci.
Wanda ya mutu a cikin annoba (misali lokacin kolera ko amai da zawo da dai makamantansu).
Wanda  ya mutu a sanadin ciwon ciki
Wanda ruwa yaci
Wanda gini ya fada mashi ya mutu
Matar da ta mutu wajen haihuwa.
Wanda ya mutu sanadin konewa a cikin gobara
Wanda ciwon bulala ya zama sanadin mutuwarsa.
Wanda ciwon tarin huka (T.B.) ya zama sanadin mutuwarsa.
Wanda ya mutu wajen kariyar dukiyarsa (Misali wanda yayi fada da yan fashi amma suka kasheshi).
Wanda ya mutu wajen kare martabar addinin musulunci.
Wanda ya mutu wajen kariyar ransa da na iyalinsa
Wanda ya mutu wajen gadin jamaar musulmi (Misali Yan Banga da ire-irensu).
Wanda ya mutu yayin da yake yin aikin alheri (Misali yayinda yake yin azumi ko sadaka da sauransu).
Wanda azzalumin shugaba ya kashe don kawai fadin gaskiya.
Manzon Allah S.A.W. yace wanda ya mutu a daya daga cikin wadannan halulluka 19, to yana da busharar cewa shi dan Aljannane.
ALLAH YA SAMU DAGA CIKINSU AMIN.
23. ABUBUWAN DAYA KAMATA A KIYAYE WAJEN WANKA GAWA

Yima mamaci wanka wajibi ne a Sharia kamar yadda yazo a cikin Hadisi. Manzon Allah (SAW) ya bada umurnin ayiwa wani mahajjaci wanka bayan ya fado daga kan taguwarsa, ta taka shi ya mutu. A wajen yin wannan wankan akwai ladubban da ya zama wajibi a kiyaye.
Wajibi ne wanda zaiyiwa mamaci wanka ya zamo mai ilimin yadda ake wankan gawa ne kamar yadda sunna tazo dashi.
Anso wanda zaiyiwa mamaci wanka bayan kasancewarsa mai ilimi ya zama danuwa ne na kusa.
Ana wankan mamaci karanci sau ukku ko fiyeda haka.
Yawan wankan ya zama wutiri (wato mara) misali ko sau ukku ko sau biyar ko sau bakwai.
Ayi amfani da ganyen magarya ko sabulu wajen yi mashi wankan.
A zuba turaren Kafur ko makamancinsa a cikin rowan da zaayi mashi wanka na karshe.
Idan mace ce wajibi ne a kwance kitsonta a wanke gashin da kyau.
Anyi umurnin a shace gashin da kyau, na namiji ne ko na mace.
Bayan an wanke gashin mace sai ayi mashi kulli ukku.
Bayan an wanke kai sai ayiwa mamaci alwalla.
Wajen wanka ana bukatar a fara  bangaren dama sannan  na hagu.
Kamata yayi maza suyiwa maza wanka, mata suyiwa mata.
Bayan an  cire kayan dake jikin mamaci sai a rufe alaurarshi da wani zane, daga nan sai a shiga wanka ta amfani da wani kyalle ko soso.
Dudda  ance maza suyiwa maza wanka, mata suyiwa mata, anso miji  ya wanke matarsa ita kuma ta wanke mijinta. Annabi (SAW) yace wa Aisha Da zaki mutu kafinni, da ni zanyi maki wanka, in sa maki likkafani, inyi maki Sallah, sannan in rufe ki. Haka kuma yayinda Manzon Allah[SAW] ya rasu Aisha (RA) tace In banda hankulanmu sun dauku a wannan lokaci, to babu wanda  yafi  cancanta yayi masa wanka inba  mu-matansa ba.
Mustahabbi ne ga wanda yayiwa mamaci wanka shima daga baya yayi wanka, wanda kuma ya dauki gawar mamacin shi kuma yayi alwalla.
Wanda yayiwa mamaci wanka yana da lada mai girma amma da sharadin bai bayyana wani aibi da ya gani a jikin mamacin ba. kuma yayi wankan don Allah kawai. Manzon Allah (SAW) yace Wanda yayiwa mamaci wanka ya boye wani aibin daya gani a jikinsa, Allah zai gafarta mashi sau 40, wanda kuma ya gina mashi kabari ya sanya shi ciki, ladarshi zata rika gudana kamar wanda ya gina gida ya sa wasu bayin Allah ciki ba tareda biyan ko kwabo ba. Wanda kuma yayi mashi likkafani Allah zai tufatar dashi da tufafi masu tsada a cikin Aljanna.
ALLAH YASA MU DACE AMIN.
                           24. YADDA AKE SALLAR  GAWA (JANAZA)

Ya Dan uwa ka sani cewa Sallar Gawa farilla ce, wadda wasu kan iya daukewa wasu. Amma kuma sanin hukucinta wajibi ne ga kowane Musulmi. Sallar Gawa ana yi mata karanci kabbara 4 haka kuma ana yin kabbara 5 ko 6 har zuwa 9.
Amma dai kabbara 4 tafi shahara.
A kabbara ta farko ana karanta fatiha da sura, a kabbara ta biyu ana karanta salatin Ibrahimiyya, wani lokaci ya kara da addua a cikin kabbara ta biyun. Kabbara ta 3 da ta hudu ana adduo’i. Ga irin Addu'o'in da yakeyi (S.A.W.)
اللهم اغفر له وارحمه، وعافه واعف عنه، وأكرم نزله، ووسع مدخله، واغسله بالماء والثلج والبرد، ونقه من الخطايا

كما ينقى الثوب الأبيض من الدنس، وأبدله دارا خير ا من داره وأهلا خيرا من أهله وزوجا خيرا من زوجته وأدخله

الجنة وأعذه من عذاب القبر ومن عذاب النار.

اللهم اغفر لحينا وميتنا وصغيرنا و كبيرنا  وذكرنا وأنثانا، وشاهدنا وغائبنا. اللهم من أحييته منا فأحيه على الإسلام،

ومن توفيته منا فتو فه على الإيمان. اللهم لا تحر منا أجره ولا تضلنا بعده اللهم اجعله لنا سلفا وفرطا وذخرا.

اللهم إنه عبدك وابن عبدك و ا بن أمتك ، كان يشهد أن لا إله إلا أنت وأن محمد عبدك  ورسولك، وأنت أعلم به، اللهم

إن كان محسنا فزد فى حسناته، وإن كان مسيئا فتجاوز عن سييئاته، اللهم لا تحرمنا أ جره، ولا تفتنا بعده
.

اللهم إن فلان  بن فلان فى ذمتك وحبل جوارك. فقه من فتنه القبر وعذاب النار وأنت أهل الوفاء الحق، اللهم فاغفر له وارحمه فإنك أنت الغفور الرحيم.
KO KASAN ABIN DA MANZON ALLAH (S.A.W. ) YACE AKAN
GINA KABARI
Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) wanda ya aza mutuwa ga kowace rai inda yake cewa “Kowace Rai Mai dandana Mutuwa ce.”
Tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad (S.A.W.) da kuma Alayansa, wanda ya sunnanta tona kabari ko LAHADI ko SHAQQU.
Bayan haka kamar yadda aka sani Musulunci bai bar komai ba face  ya tsara yadda zaayi shi, hatta zuwa makabarta da yadda zaa tona kabarin  mamaci.
Amma a halin yanzu an wayi gari mutane suna gina kabari batare da koyi da sunnar Manzon Allah (SWA) ba. A cikin Hadisin da JABIR  ya ruwaito (R.A.), yace Manzon Allah[SAW] yayi hani  ashafa ma kabari siminti ko a debo wata (TURBAYA KO YASHI) a zuba a kan kabari, ko kuma ayi rubutu a kansa (SUNAN MAMACI, SHEKARA, KO AYAR AL-QURANI). Imam Muslim ne ya ruwaito Hadisi na 970. Abu Dauda ma ya ruwaito shi Hadisi na 3225. Imam Tirmizi  ya ruwaito Hadisi na 1052. Imam NisaI ya ruwaito Hadisi na 2025. Ibn  Majah ya ruwaito Hadisi  na 1563.
Imam ShafiI yace wannan Hadisi shine hujja da ke nuna haram cin yin gini akan kabari. Hakama yayi bayani cewa idan a makabarta ne akayi ginin to haramcin  yafi muni. Amma in a cikin gida ne to anyi MAKARUHI.
Amma kuma  Mutane su sani bai halatta ba arufe mutun  gida  ko da yayi wasiya da haka. Sabo da wani mutun ya tambayi Imam Hanbali cewa idan mutun yayi wasiya a rufe shi a gida ko yana halatta a rufe shi? Imam  Hanbali yace aa a kaishi makabarta.
Haka ma Abdullahi Ibn Umar (R.A) yace  rufe mutun a makabarta yafi alheri fiye da a rufe shi cikin gida. Sabo da abubuwa  biyu (2).
Annabi  yayi umurni cewa dukkan sahabbai da Diyansa (R.A.) wadanda suka rigashi rasuwa da a rufe su a Makabarta.
Zaka samu dinbin ADDUO'I ga masu kai ziyara da masu kai mamata a wurin. Sabanin  wanda aka rufe a gida.
To me yasa aka rufe MANZON ALLAH (S.A.W.) a gida?
Amsa:- 
Saboda Hadsin da Abubakar (R.A.) ya ruwaito a cikin Muwadda Malik yace yaji MANZON ALLAH (S.A.W.) yana cewa baa rufe wani Annabi ba face sai wurin da ya mutu. Wannan shine dalilin rufe MANZON ALLAH (S.A.W.) a cikin dakin AISHA (R.A).
Yazo a cikin SAHIHUL BUKHARI, an tambayi AISHA (R.A.) me yasa aka rufe MANZON ALLAH (S.A.W.) da abokansa (Abubakar da Umar R.A.) a cikin dakinta. Sai tace anyi haka ne domin kada mutane su dauki Kabarinsa Masallaci su rika yimasa (Sujjada ko Rokonsa).

BAYAN HANI SAI UMURNIN ROSAWA
Saboda Manzon ALLAH (S.A.W.) yasan akwai kangararu daga cikin bayi dake tsallake iyakar ALLAH da MANZONSA, shi yasa bayan yayi hani sai kuma yayi umurni na rosa duk ginin da akayi akan kabari.
An anso Hadisi daga Abu Wail yace lallai Sayyadina Aliyu (R.A.) yace ma Abi Hayyaj Al-asad, zan aike ka ga abun da MANZON ALLAH (S.A.W.)  ya aike ni akansa yace kar kabar wani Kabari mai tudu ko gini face ka dai dai ta shi (face ka ruguzashi) ko MUTUM-MUTUMI face ka kaudashi. Muslim ya ruwaito Hadisi na 969, Imam Turmuzi Hadisi na 1049, Abu Dauda Hadisi na 3218, Imam Nisai Hadisi na 2026.
Hakama dukkan Malaman Mazahabobi sunyi ALLAH wadai da mai wannan aiki.
Imam Malik ya karhanta yin ginin kabari da laka ko Suminti, Imam Shafii yace ni na kyamaci yin ginin Kabari ko debo wata kasa daban azuba sama domin ni banga kabarin wani sahabi da akaima haka ba.
Imamu Ibn Hambali yace bai cikin sunnar Manzon ALLAH (S.A.W.) yima Kabari gini ko yi mashi kawa ko kuma yin kubbobi a cikinsa ko sa fitila a makabarta.
Abinda yazo ga Sunnah shine aza dutse don alama, kamar yadda Anas ya ruwaito Manzon ALLAH (S.A.W.) ya aza dutse a Kabarin USUMAN BIN MAZUM don alama, Iban Majah hadisi na 1561.
Hakama yazo a cikin MUKHATASAR Shafi na 115 cewa makaruhi ne mikewa tsaye idan anga gawa, da kuma DAYYACE KABARI dayi ma kabari fenti da gini a kansa ko zagayeshi da waya, in don alfahari ne to haramun ne. Hakama yazo a RISALA wato SAMARUDDANI shafi na 320 yace makaruhi ne yin gini ga kabari da yi masa siminti.
A cikin sharhin Askari wato FATAHUL JAWAD shafi 110 makaruhi ne yin gini ga kabari ko shafa siminti.
SHEIKH USUMAN IBN FODIYO yace yin gini akan kabari bidia ce makaruhi ya idan ba akan alfahari ba, in kuwa akwai alfahari to haramune. Aduba IHYAU SUNNAH WA IKAMADUL BIDIA shafi 112.
Domin karin bayani kaduba wadannan litafai:-
Sahihu Muslim
Sahihu Turmathi
Risala
Fatahu Jawad
Fiqihu Sunnan
Daga karshe muna rokon ALLAH (S.W.T) ya ganar damu gaskiya ya bamu ikon binta ya kuma nuna mana karya ya bamu ikon guje mata.
26. YAYA ANNABI (S.A.W.) YAYI WA MAMACI ADDUA BAYAN RUFESHI
Godiya da yabo sun tabbata ga Allah (S.W.T) wanda ya wajabta mutuwa ga kowace rai, inda yake cewa (S.W.T) Kowace rai mai dandana mutuwa ce.
Tsira da aminci su tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammad (S.A.W.) wanda yace Ku nemarwa dan uwanku gafara kuma ku rokar mashi tabbatuwa domin yanzu zaa tambayeshi.
Bayan haka, kamar dai yadda muke tunatarwa a kowane lokaci, baya halatta ga Musulumi yayi amfani da son rai wajen gabatar da aikin ibada. Wajibi ne duk abinda zamuyi mu tabbatar ya dace da umurnin Manzon Allah (S.A.W.). Akan haka ne wannan lokaci muke son mu yiwa yan uwa nasiha akan yadda Annabi (S.A.W.)  yayi addua kuma ya bada umurni ayi ga mamaci bayan an rufeshi.
Manzon Allah (S.A.W.)  ya kasance idan ya raka gawa zuwa makabarta, yakan cire takalminshi kuma ya umurci Sahabbai suma su cire takalminsu. Idan zai shiga sai yayi addua yace Amincin Allah ya tabbata gareku ku maabota wannan gida na muminai da musulumai. In Allah yaso mu masu tarar daku ne. Muna rokon Allah ya yafe mana damu daku Sannan idan zai sanya mamaci a cikin kabari yana cewa Da sunah Allah muke sa wannan mumini, a bisa addinin Annabi Muhammad (S.A.W.).  Bayan an gama rufeshi sai Annabi yayi  masa addua  kuma ya umurci sahabbai dake wajen suma  suyi mashi addua.
Saboda Hadisin da Uthman Bin Affan ya ruwaito inda yake cewa Idan an gama  binne mamaci, Manzon Allah (S.A.W.)  yakan tsaya akan shi mamacin yayi mashi addua kuma ya umurcemu cewa Ku nemarwa dan uwanku gafara da kuma tabbatuwa wajen bada amsa, domin yanzu zaa tambayeshi.  Wannan Hadisi Abu Dauda ya ruwaito shi Hadisi na 3221.
Wannan Hadisin yana nuna mana karara cewa Manzon Allah (S.A.W.)  shi kadai yake adduar, haka suma  Sahabbai guda-gudansu suke adduar, sabanin yadda wasu sukeyi yanzu inda ake addua cikin jamI, hakanan kuma Malamai da dama sun tabbatar da cewa yin addua  a makabarta, wani naja wasu na bi, ya sabawa koyarwa Manzon Allah (S.A.W.)  da Sahabbansa. Yazo a cikin Fikhu Sunnah juzui na I, shafi 401, Sayyadina Aliyu [RA] idan ya gama rufe mamaci yakan daga hannu yayi addua shi kadai, sai yace wannan bawanka ne, ya sauka gareka, kuma kai ne mai fiyayyen masauki gareshi, ka gafarta mashi kuma ka yalwanta makwancinshi. Wannan ma wata hujja ce dake nuna cewa addua cikin makabarta guda-guda akeyinta. Haka nan kuma yazo a cikin littafin Fatawowi a Jana’iza a Musulunci na Sheikh Muhd Salihu Uthaimin, shafi na hamsin 50, inda aka tambaye shi mi nene matsayin yin addua ga mamaci, wani na bayarwa wasu na karbawa, ko kuma ace A karanto kaza-da-kaza. Sai Sheikh yace wannan bidia ce wadda ta sabawa aikin Manzon Allah (S.A.W.)  da Sahabbansa[RA]. Abinda ya dace da Sunnah shine kowa yayi addua da kansa. Anyi fatawa ga majalisar fatawowi ta manyan Malaman Musuluncin duniya cewa wasu Malamai sunyi hukuncin cewa baa adduar jam’i ga mamaci bayan an rufeshi, wasu Malaman sukace babu laifi ayi. Shin minene matsayin sharia akan wannan matsala, sai ita wannan majalisa tace ita dai addua ibada ce, ita kuma ibada  taukifi ce wato wani zartas da hukunci ne daga Allah da Manzonsa wanda babu wanda ya isa yayi wata kwaskwarima. Don haka bai halatta wani ya bautawa Allah da abinda shi Allah bai sharanta mashi ba, kuma bai tabbata ba daga Manzon Allah (S.A.W.).  Don haka ita wannan majalisa ta zartas cewa mafi daidai a cikin wannan matsala shine yin adduar jam'i a makabarta bidia ne. A duba. Lajanatin fataawa. Juzi na 9, shafi na 16. Bugu da kari ya nuna babu inda yazo a cikin tsarin ibada ta addua inda Manzon Allah[SAW] ko Sahabbansa suka taru sukayi addua a jam’i cewa A karanto Ayatulkursiyau, ko A karanto Kaza-da-kaza dadai sauransu. Abin da ya tabbata shine duk lokacin da Manzon Allah zaiyi addua sai dai kawai ya daga hannayansa ya fara adduar Sahabbai suna cewa Amin, Amin, Amin. Shi yasa Shehu Uthma Dan Fodiyo a cikin littafinsa Ihyaus Sunnah, shafi na 102 yake cewa baya hallata bayan liman  ya sallame sallah ya juyo yacewa mamu a karanta kaza-da-kaza ayi addua, domin wannan bidia ne. To ashe ko wannan ya isa ya nuna muna cewa idan  har zaa hana bidiar adduar jam’i idan an gama sallar farila, to wannan ya isa ya kore adduar jam’i bayan an rufe mamaci. Kai karshe ma Shehu Uthman yace dukkan abinda Annabi baiyi ba, to ba shakka barin wannan aikin wajibi ne kuma yinsa bidia ne.
Hakanan kuma  yin addua a cikin Jam’i idan anzo gaisuwar taaziyya cewa A karanta-kaza-da-kaza shima wannan bidia ne domin babu inda aka nuna cewa Manzon Allah (S.A.W.)  yayi haka. Abinda ya tabbata shine idan Manzon Allah (S.A.W.)  yazo gaisuwar ta’aziyya ga abunda yake cewa Lalle naga  Allah abinda ya karba, kuma  na gareshi abinda ya bayar. Kowane abu yana da ajali a wajen Allah, wanda shi Allah ya sanya mashi, don haka sai kuyi hakuri kuma ku nemi lada. A lokacin Manzon Allah (S.A.W.)  ya kaiwa Abdullahi ibn Jafar, gaisuwar mutuwar mahaifansa cewa yayi Ya Allah ka gadar da kyakkyawan  gado ga jaafar kuma kaiwa dansa Abdullahi albarka. A wata ruwayar, lokacinda Annabi (S.A.W.)  yakai gaisuwa ga Ummu Salma  lokacin da mijinta Abu salma  ya rasu cewa yayi ya Allah ka gafartawa Abu Salma ka daga darajarsa a cikin shiryayyu, ka sa mashi makwafi a cikin zuriarsa ka gafarta muna damu dashi, ya Ubangijin halitta. Ka yalwata kabarinsa, kuma kasa haske a ciki. Dukkan wadannan hadisai ingantattu ne wadanda Imam Bukhari da Muslim da Ahmad da Hakeem suka ruwaito.
To yakai Dan Uwa da kake zuwa wajen ta’aziyya  kace a kawo tahiya bakin saliheen, a kawo kulhuwalahu, da dai sauransu, don Allah ina ka samo wannan? Mudai ga yadda muka karanta Manzon Allah yayi. Hakama Adduar da akeyi a makabarta ya kamata ta tsaya inda Manzon Allah (S.A.W.)  ya tsaida ta, kamar yadda sahabai sukayi inda suke cewa ya Allah ka gafarta mashi, ya Allah ka tabbatar da shi wajen bada amsa Babban sahabin nan Amar bin Yaseer yace ya na da kyau a dauki lokaci mai tsawo ana  addua bayan an binne mammci Wannan hadisi malamai sunyi kiyasin  wannan lokaci zaikai tsakanin minti 30 zuwa 40.
Daga karshe muna kira ga yan uwanmu kashi biyu da suji tsoron Allah. Kashi na farko sune  wadanda ke kokarin cewa sai anyi jam’in addua bayan rufe mamaci kunga dai tabbaci cewa Manzon Allah (S.A.W.)  da sahabbansa [RA] da sauran magabata na gari basuyi haka ba, don haka ka bin ka ka-da-ka kanni, wanan ba hujja bace. Wajen Annabi ake karbo hukuci ba wajen-ka kanni ba, kashi na biyu kuma sune wadanda su sam basu yin adduar ta daidaikun. To kuma kun sabawa umurnin Manzon Allah (S.A.W.), don haka ku tuba kuma ku gyara daga yau.
Muna rokon Allah ya yafe muna kura-kuranmu, kuma ya bamu ikon bin sunnar manzonsa (S.A.W.)
Domin Karin bayani a duba 1. Fatul Bari 2. Fikhu Sunnanh 3. Zaadl Maad 4. Ahkamul Janzaiz 5. Fataawal JanaizA ta Uthaimin 6. Ahamkul taaziyya ta Abi Suhaif.

    27. MINENE MATSAYIN KACIYAR MATA A MUSULUNCI?
Godiya ta tabbata ga Allah (SWT) wanda ya halitta mutum kuma ya tsara mashi yadda zai gudanar da rayuwarsa. Tsira da aminci su tabbata ga Manzon sa (S.A.W.) wanda ya sunnanta yin kaciya ga maza da mata. Bayan haka ya danuwa musulmi yana da kyau duk aikin da zakayi ka bincika don jin ya sharia tace ayi wannan aiki, domin ka da kashiga cikin hadarin da yana iya fitar dakai musulunci batare da kasani ba.
Ya kai danuwa abunda ya jawo hankalinmu game da yin bayanin kaciyar mata, shine domin jin irin maganganu da ke fitowa daga kafafen watsa labarai na kasashen  waje da na  gida. Wadannan gidajen Redio  suna suka game da kaciyar mata batare da sanin me sharia tace game da hakan ba, illa tsabar raayin su da son rai.
Don haka ne muka ga yadace muyima jamaar musulmi bayani abun da shari’a tace game da kaciyar mata.
Bayanin mu zai kasance a cikin jimloli guda shidda: -
Hujjoji sun zo daga  Manzon Allah (S.A.W.) da suka nuna mahimmancin kaciyar mata: - A cikin Hadisin da Bukhari da Musulim suka ruwaito daga Abu Huraira (R.A.) Manzon Allah (S.A.W.) yace abu biyar suna cikin addini (i). Yin Kaciya (ii). Aske gashin mara (iii). Cire gashin hamata (iv). Yanke akaifa (v). Rage gashin baki. Wannan hadisin yana nuna halarcin yin kaciyar maza da mata. Haka ma an karbo daga Aisha (R.A.) tace Manzon Allah (S.A.W.) yace idan mutum ya zauna tsakanin kafafuwa hudu, kaciya ta shafi kaciya wanka ya wajaba gareshi. Musulmi (349). A cikin wata ruwaya ta Imam Ahmad, Manzon Allah (S.A.W.) yace idan kaciya ta hadu da kaciya to wanka ya wajaba. Ibn Hajar yace wandannan Hadisan karara suna nuna halaccin yin kaciyar mata, batare da wani kwane kwane ba. Imam Bukhari a cikin littafin shi ADABUL MUFRAD yayi babi da ke karantar da kaciyar mata, ya fitar a cikin hadisi na (1247) daga UMMUL ALKAMA tace wasu yara mata diyan yan uwan Aisha (RA) anyi masu kaciyar sai akace ma Aisha baza a kira wani wanda zai daukar masu lokaci da wasa ba? Aisha (RA) tace ana iya kira. Wannan hadisi shima ya nuna halaccin kaciyar mata. Kuma hadisin Albani ya ingantashi.
Hanyar da Musulunci yabi ta ilimin likitanci wajen yi ma Mata kaciya: - Kaciyar mata abu ce da ta riga ta watsu kafin aiko Manzon Allah (S.A.W.). Da Manzon Allah (S.A.W.) yazo da Musulunci sai ya tabbatar da kaciyar mata.Ya kuma bayyana hanyar da zaayita batare da an cutar da mata ba. Domin Manzon Allah ((S.A.W.) ) shine shugaban likitocin duniya. An karbo daga Anas Ibn Malik (R.A.) lalle Manzon Allah (S.A.W.) yace ma Ummu Adiyya (R.A.) ita mace ce da ke ma mata kaciya a cikin garin Madina. Yace mata ki yanki saman labban farji. Kada ki yankeshi duka. Sai yace yin kaciyar mace yana kara kyau kuma yana gamsar da miji. Imam Dabrani ya ruwaito shi da isnadi mai kyau. Sheikh Albani ya sahhaha hadisin a cikin Sahiha hadisi na (722). Da kuma Sahihul Jamii’ (498). A cikin wannan hadisin Manzon Allah (S.A.W.) yana nuni da cewa bai halatta a wuce wuri wajen yin kaciyar har a cutar da su. To wannan ne ma yasa  ya koyar da Ummu Adiyya yadda yakamata tayi kaciyar mata. Da wannan ne muke kira ga duk masu shaawar kaciyar mata suyi ta yadda Manzon Allah (S.A..W) ya  koyar da ita ba dadi ba kari.
MINENE HUKUNCIN MUSULUNCI GAME DA KACIYAR  MATA: - Malamai sun kasu kashi biyu, kashi na farko sunce kaciyar mata wajibi ce. Kashi na biyu sun ce Sunnah ce. Mazhabar Shafiiyya sun tafi akan cewa wajibi ce. Sauran mazhabobi  sun tafi akan Sunnah ce. SHEIKH SHANQIDI ya fada a cikin littafin sa IKHTIYARU JALLIYA cewa kaciyar maza da mata wajibi ce. Shima SHEIKH ALI BASSAM ya fada a cikin littafin IKHTIYARU JALLIYA   cewa kaciyar wajibi ce.
HIKIMAR KACIYAR MATA A MUSULUNCI: - kadan daga cikin hikimomin musunlunci Akan kaciyar mata sun hada da: - (i). Tabbatar da shariar Allah da Sunnar Manzon Allah (S.A.W.). (ii). Tsarki da tsafta Wanda ke bayuwa wajen yin fitsari da kyau. (iii). Kyautata halitta har ta kasance bisa kan Addini madaidaici (iv). Daidaita shaawa (v). Sanar da alamar ibada ba alada ba (vi). Kara kyawon fuska da gamsar da miji.
MAGANGANUN MAGABATA AKAN KACIYAR MATA:- Imam Abu Hanifa (RA) yace  lalle yin kaciya ga maza da mata sunna ne. Imam Malik (RA) yace lalle  yana daga cikin addini yin kaciyar maza da mata. Imam Shafii (RA) yace lalle waijibi ne ga maza da mata suyi kaciya. Imam Ahmad Ibn Hanbali (RA) shima yace wajibi ne ga maza da mata su yi kaciya.
WANE LOKACI NE YAKAMATA AYI KACIYA: - Malamai sun ce ana yin kaciya tun ran da yaro ya kwana bakwai da haihuwa. Wasu Malamai suka ce daga shekara bakwai (7) zuwa goma (10) ake ma mata kaciya.
Daga karshe muna kira ga musulmi da suyi hattara da makiya musulunci dake
kokarin nuna cewa kaciyar mata bata cikin musulunci.
Domin Karin bayani sai ka duba wadannan liatatafai: -
AL ADABUL MUFRAD na Imam Bukhari.
TAASILU HITANULINAS na Malaman Sudan.
ALKHITANU RAAYUL DINI WAL ILIMI FI HITANU AULADI WAL B ANATI na Abubakar Abdulrazaq.
TUKHFATU MAUDUDU FI AHKAMU MAULUD na Ibn Kayyyim Aljauzee.
AHKAMU JARAHATU DIBBIYA na Imam Shanqidi.
ASBABU MUKHARABATU KHIFAD FI SUUDAN na Sheikh Abdulsalam.
ASARARUL KHITAN na sheikh Hassan Shamsu Basha.
28. YAYA SUTURAR MUSULMI NAMIJI YA KAMATA TA ZAMA?
Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) wanda ya umurci Dan Adam daya kyautata sa sutura, inda yake cewa Yaku Yan Adam Ku riki kawarku a lokacin kowace Sallah. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzonsa Muhammad (S.A.W.) wanda yace Allah yana son idan yayiwa bawa niima to yaga niimar a jikin bawan.
Bayan haka ya dan uwa, kasani cewa Musulunci bai bar komi ba face ya tsara yadda zaayi shi. Hatta yadda Musulmi zai rika sa sutura,kamar yadda  Manzon Allah (S.A.W.)  ya bayyana, kuma wajibi ne mubi yadda yayi bayanin. Anan zamu yi bayani a takaice ladubban da suka wajaba a kiyaye wajen sa tufafi.
Ladabi na farko wajibi ne wandon Musulmi da rigarsa su tsaya rabin kwabri, ko kuma zuwa idon sawu -amma kada ya wuce idon sawun. Imam muslim ya ruwaito hadisi a cikin sahih nashi, hadisi na 2850, inda Manzon Allah (S.A.W.)  yake cewa Wanda ya ja tufanshi a kasa da nufin takama, Allah bai kallonshi a ranar kiyama. Sai sayyadina Abubakar yace ya Manzon Allah ni gyabto na yana sauka kasa, sai na janyeshi sai Manzon Allah (S.A.W.)  yace  Ai kai ba kana yi ne don takama ba Hakanan Imam  Muslim ya sake ruwaito wani hadisi na 106 inda Manzon Allah (S.A.W.)  yake cewa A ranar tashin kiyama, Allah ba zai yi Magana da wasu mutane 3 ba, ba zai kallesu ba, kallon rahama, ba zai tsarkakesu ba, kuma suna da azaba mai radadi. Sai Abu Zarri yace sun tabe, sunyi hasara. Su wanene wadannan mutum uku ya Manzon Allah [SAW]? Sai Annabi (S.A.W) yace wanda yake sakin suturarsa kasa, da mai gori idan yayi wani abun alheri da mai rantsuwar karya wajan saida kaya domin saurin saida nasa. Imam Bukhari ya fitar da hadisi na 5787 inda Manzon Allah (S.A.W.) yake cewa suturar Mumini ta tsaya rabin kwabri. Ba laifi takai kusa da idon  sawu, amma idan ta wuce idon sawu, to tana cikin wuta. Wato mai suturar zai shiga wuta kenan. Malaman hadisi sun hada wadannan hadisai 2 suka fitar da hukuncin cewa wanda yake sakin suturarsa domin alfahari, to shi yake da tarin wadancan nauoin ukuba guda 4 wanda kuma yake sakin sutura don kawai alada ko kuma rashin kula, to shine zaayiwa azabar wuta ta tsaya a idon sawunshi, kamar yadda Sheikh Muhammad Salih Usaimin yayi tsokaci a cikin sharhin da yayiwa Riyadus Saliheen.
Baya halatta kayi sutura da alhariri, wato wani dangin leshi na ainihi wanda akeyi da wasu halittu, bada auduga ba, wanda kuma yake da sulbi sosai tamkar siliki. Haka nan kuma ka sani haramun ne kayi amfani da zobe ko agogo ko makamantansu na zinari tsantsa, saboda hadisin da Imam Tirmizi ya fitar, hadisi na 1720, Annabi (S.A.W.)  Yace An halatta alhariri ga matan alummata amma anyi haninsa ga mazansu.
Baa yarda kasa sutura shahararriya ba. Imam Shaukani ya bayyana sutura Shahararriya da cewa sutura ce wadda tayi fice wajen yadinta ko kuma wajen dinki, wanda kuma babu mai irinta sai kai (one in town), ko kuma kaskantanciya domin nuna gudun duniya da kuma riya. Abu Dawuda ya fitar da hadisi na 4030, shi kuma Ibn Majah a hadisi na 3607 inda Manzon Allah (S.A.W.)  Yake cewa wanda yasa sutura shahararriya anan duniya, Allah zai tufatar dashi sutura kaskantacciya a lahira, sannan ya hura wuta a cikin rigar.
Baya halatta sayen sutura mai tsadar da ta wuce hankali, wanda yana iya kaiwa ga almubazzaranci. Misali sai kaga mutum ya sayi shadda N40,000 wadda kuma bata wuce ta N5000 da komi ba. Wannan almubazzaranci ne kuma Allah (S.W.T) yace mai almubazzaranci danuwan shedan ne. suratul israI, aya ta 27. Imam Tirmizi ya fitar da hadisi na 2017 inda Manzon Allah (S.A.W.)  yake cewa Dukkan mutumin daya kaucewa sa sutura mai tsada, alhali yana da halin sayenta don kawai tawaliu ga Allah zai kirashi a ranar kiyama a gaban shugabannin halitta, a bashi zabi, yasa duk suturar da yake so.
kada kasa sutura ja-jawur, domin Manzon Allah (S.A.W.) , yayi hani a sanya tufafin kissiyu, (wato Alhariri), da sutura ja-jawur Muslim ya fitar da hadisi mai lamba 2780. Amma a kula cewa wannan hanin ya shafi asin da-asin ne, wato riga da jamfa da wando duk jajaye.
Kada kasa tufafi wanda mata ne ke sasu, saboda hadisin Ibn Majah na 588 inda Manzon Allah yake laantar namiji mai shigar mata da mace mai shigar maza.
An hana kasa tufafi irin na kafirai kamarsu Kwat da Shat da wando mai matse jiki yana fitar da siffar alaura ko kuma rashin sa hula. Annabi (S.A.W.)  Yace wanda yayi kama da mutane to yana cikinsu.
Kada kasa sutura mai dauke da hoton mutum ko wata dabba domin yin hoto haramune kamar yadda Manzon Allah (S.A.W.)  yake cewa dukkan wanda yayi hoto anan duniya zaa tilasta mashi ya hura masa rai a lahira alhali bashi iyawa.
Anso mafi yawan suturar Musulmi ta zama farace. Imam Tirmizi ya ruwaito a hadisi na (994) cewa Manzon Allah ((S.A.W.) ) Yace Ku sanya fararen kaya domin itace fiyayyar sutura, kuma kuyiwa matattunku likkafani da ita. Sheikh Muhammad Salihu Uthaimin yace yana daga cikin cikar mutum ya yawaita sanya fararen kaya.
Sunnace Idan zaka sanya tufafi ka karanta wannan Addua. Godiya ta  tabbata ga Allah wanda ya tufatar dani wannan tufa, kuma ya azurtani ita, ba tare da dabara ko wani karfi daga gareni ba.
Muna fatan yan uwa zasu yi aiki da abinda ke kunshe a cikin wannan nasiha domin neman dacewa da aiki da sunnar Manzon Allah (S.A.W).
Don Karin bayani adubi
Fathul Bari (sharhin Bukhari) JuzI na 10, shafi 433
Sharhin Tirmizi JuzI na 5,shafi na 115
Riyadussaliheen  Kitabul-Libas
Bulugul-Marami  Babin Libass
YAYA SHARIA TA TSARA SUTURAR MACE?
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah (S.W.T) wanda yace a cikin littafinsa mai girma Ya kai wannan Annabi, ka cewa matanka da matan mummunai su saukarda suturarsu har zuwa kasa. Wannan yafi sauki wajen ganesu ba tare da an cutar dasu ba. (Suratul Ahzab, aya ta 59). Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzonsa Muhammad (S.A.W.) wanda yace a karshen zamani mata zasu sa sutura amma kuma suna tsirara, saboda rashin sa suturar da sharia ta tsara. Bayan haka kamar yadda muka sani, musulunci bai bar komi ba face ya shata yadda zaa yi shi a samu rahamar ubangiji (S.W.T). Don haka a wanan wasika zamu gabatar da yadda sharia ta wajabta yadda mace zata yi sutura idan zata fita waje.
Ladabi na farko. Wajibi ne mace ta rufe dukkan jikinta in banda fuska da tafuna, kamar yadda aya mai girma ta sama ta ambata. Hakanan kuma Manzon Allah (S.A.W.)  yace a cikin hadisin Ibn Majah da Tirmizi  zai kasance a karshen alumma ta zaa samu wasu mata sun sa tufafi amma kuma ga su tsirara, kawunanan su kamar tozon rakumi, ku laance su domin su laantattu ne.
Sunna ce mai karfi tasa nikaf (wato kyallen rufe fuska), saboda hadisin da aka samo daga Safiyya bint Shuaib tace Naga Aisha RA tana dawafin Kaaba sanye da nikaf. Abdurrazak ya ruwaito wannan hadisi a littafinsa Musnid, juzi na 5, shafis na 24.
Har wayau dai an karbo daga Aisha RA cewa Mun kasance muna tafiya, lokacin da duk mahaya dawaki suka riske mu zamu saki nikabinmu, idan sun wuce sai mu bude Ahamad ya fitar da wannan hadisi, JuzI na 6 shafi na 30. Ibn Jarud shima ya kawo shi a hadisi na 418, sannan an samoshi a cikin (Irwaul Ghalil) hadisi na 1023.
Baa son hijabin ya zama mai kawa ne da yawa, yadda zai iya jawo hankalin a kura mata ido. Wannan ya tabbata a cikin aya ta 31, Suratul Nur inda Ubangiji Taala yake cewa Kada ku bayyanar da kawarku .. haka nan cikin Suratul Ahzab aya ta 33, Allah Taala yana cewa kada ku rinka yin kawa, irin kawar jahilan farko..
Hijabin ya kasance mai kauri ne ba mai shara-shara ba. Manzon Allah (S.A.W.)  yace Karshen alummata wasu mata zasu sa tufafi, amma kuma suna tsirara . Ibn Abdul Barr yace abinda wannan hadisi ke nufi shine sa tufafi marasa kauri. Dabarani ya fitar da hadisin a cikin Muujamu Sagir hadisi na 232. Shima Sheikh Albani ya kawo shi a cikin Silsilatus Sahiha hadisi na 1326
Wajibi ne hijabi ya kasance mai fadi sosai ba mai kunci ba wanda yake matse jikin mace har ana ganin siffar jikinta. Usama Ibn Zaid RA yace Manzon Allah (S.A.W.)  Ya tufatar dani wata sutura mai kauri wadda Dahiyatul Kalbi yai mashi hadayarta sai naba matata wannan riga sai Manzon Allah[SAW] yace me yasa ban sa rigar daya bani ba, sai nace masa ai na ba matata wannan riga sai Manzon Allah (S.A.W.)  yace ka umurceta da ta sa wani hijabi mai kauri a samanta, domin ina jin tsoron rigar ta kwatanta girman jikinta. Ahamad da Baihaki da Hakim suka ruwaito hadisin. Diyaul Makadasi ya kawo wannan hadisi a cikin littafinsa Ahadithu Mukhtar Juzi na daya, shafi na 441.
Kada mace ta kuskura ta shafa turare a jikinta lokacinda zata fita. Saboda hadisai da dama da suka hana mata sa turare idan zasu fita. Daga Abu Musa Al-ashari ya bada labarin cewa Manzon Allah (S.A.W.)  Yace Duk matar da tasa turare ta wuce wasu suka ji kanshin turaren to ita mazinaciyace. A cikin wani hadisin kuma Zainab Ath- Thakafiyya tace Manzon Allah (S.A.W.)  yace. Idan dayarku zata fita zuwa Masallaci, kada ta kuskura tasa turare. Ahmad da Muslim da As’habus Sunan suka ruwaito wannan hadisi.
Kada mace tasa tufafin da sukayi kama da na maza, saboda hadisai da dama da suka zo, inda Manzon Allah (S.A.W.)  Ya laanci mace mai kama da maza. Hakanan kuma Manzon Allah (S.A.W.)  ya laanci mace mai sa kayan maza. Kuma ya laanci namiji mai sa kayan mata. Haka nan a hadisin Abdullahi Ibn Amr, wanda yace yaji Manzon Allah (S.A.W.)  yana cewa Bai tare damu, namijin da yayi kama da mata, haka kuma bata tare damu matar da tayi kama da maza. Ahmad da Hakim da Ibn Hibban da Ashabus Sunan suka ruwaito wannan hadisi.
Kada mace tasa kayan da sukayi kama da kayan kafirai mata, domin Allah ya hana mu kamance-ce-niya da Yahudu da Nasara ta kowace hanya, saboda fadar Allah [SWT] acikin suratul Hadid kada ku kasance kamar wadanda aka ba littafi kafinku, sai guri ya tsawaita akansu, zukatansu suka bushe, mafi yawansu kuma fasikai ne. A cikin wani hadisi kuma Shaddad Ibn Aus ya ruwaito cewa Manzon Allah (S.A.W.) Yace KU sabawa Yahudawa, domin su basu yin Sallah da takalmi. Abu Dawud ya ruwaito wannan hadisi 652.
Baa yarda kisa sutura Shahararriya ba. Shaukani ya bayyana sutura shahararriya da cewa sutura ce wadda tayi fice kuma ta zarce tsara, wadda babu mai irinta sai dai ke, ko kuma kisa kaskantacciya domin wai nuna gudun duniya da wani abu mai kama da wannan. Abu Dauda ya fitar da hadisi na 4030, shi kuma Ibn Majah na 3607, in da Manzon Allah (S.A.W.)  yake cewa Duk wanda yasa sutura shahararriya anan duniya, Allah zai tufatar dashi sutura kaskantacciya a lahira, sannan ya  hura mashi wuta a rigar.
Kada kisa sutura mai dauke da hotuna, misalai atamfa dake dauke da hoton yan siyasa da makamantansu. Kamar yadda Manzon Allah (S.A.W.) yake cewa Duk wanda yayi hoton wani abu anan duniya, zaa tilasta mashi hura mashi rai ranar kiyama, alhali bashi iyawa.
Baya halatta sayen sutura mai tsadar da ta wuce hankali. Wanda yana iya kaiwa ga almubazzaranci. Misali don nuna isa, sai kaga mace ta sayi leshi na 50,000, alhali baifi na dubu biyar ba da kome. Wannan almubazzaranci ne kuma Allah (S.W.T) yana cewa Mai Almubazzaranci dan uwan shedan ne Suratul IsaraI, aya ta 27. Imam Tirmizi ya fitar da hadisi na 2017 inda Manzon Allah [SAW]yake cewa dukkan mutumin da ya kaucewa sa sutura mai tsada, alhali yana da halin sayenta don kawai  tawaliu, to Allah zai kirashi ranar kiyama a gaban shugabannin halitta, a bashi zabi yasa dukkan suturar da yake so.
Sunna ce idan mace zata sa tufa ta karanta wannar addua Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya tufatar dani wannan tufa, kuma ya azzurtani ita ba tare da dubara ko wani karfi ba.
Muna rokon Allah (S.W.T) ya azurta mu da fahimtar sunnar Manzon Allah (S.A.W) ya bamu ikon binta.
Don Karin bayani a duba wadannan littafai
Riyadussaliheeen (Kitabul-Libas)
Jalbababul Maratul Muslima fil kitabi was sunna na Albani.
Hirasatul Fadila na Bukar Ibn Abi Zaid.
     30            ME MUSULUNCHI YA TANADA IDAN RANA KO WATA SUKAYI KUSUFI
Yan uwa sunji a kafafen watsa labarai cewa akwai alamar rana ko wata zasuyi kusufi daga lokaci kaza zuwa lokaci kaza:- kilama harda bada ranakun da wannan alamari zai faru.
To da farko dai ya kamata a sani cewa sanin zaayi wannan kusufin kafin zuwansa wani Ilimi ne da Allah[SWT] ya yarda dan adam ya sani.
Me ake nufi da kusufi?
Kusufi shine gushewar hasken rana dukkansa ko wani sashensa ko kuma gushewar hasken wata dukkansa ko kuma sashensa.
Mi yake kawo kusufi?
Malaman Falaki (astronomers) irinsu Sheikhul Islam Ibn Taimiyya sunyi bayani cewa rana da wata kowanne ya na tafiya a magudanarshi. To idan rana zatayi kusufi wata zai shiga tsakaninta da duniyarmu, idan kuma rana ta shiga tsakanin duniyarmu da wata sai a samu kusufin wata. Wannan aladace ta Allah [SWT]cewa rana bata kusufi sai karshen wata (wato kowane daga cikin watannin Musulunci), kamar yadda watan baya kusufi sai a tsakiyar kwanaki watan.
An karbo daga Uwar Muminai Aisha RA tace Manzon Allah (S.A.W.)  yace Lalle rana da wata basu shafewa domin mutuwar wani mutum ko rayuwarsa, sai dai su, wasu alamomi ne daga cikin alamomin Allah (S.W.T) da Allah yake baiwa bayinsa tsoro dasu. Kamar yadda Allah yake cewa a cikin suratul IsraI, aya ta 59, Bamu kasance muna aiko da wasu ayoyi ba, sai dai domin tsoratarwa,
Wadanne abubuwa ne sharia ta shimfida lokacin da rana tayi kusufi?
Babban abinda ake so a gabatar yayinda rana tayi kusufi itace sallah. Sallar nan kuma akwai yadda Manzon Allah (S.A.W.)  yayi umurni ayi ta. Itace kamar haka.
Na farko dai zaayi kiran sallah. Shi kuma wannan kiran sallah ya banbanta da kiran sallah wanda aka saba da shi, kiran sallar kusufi ladan zai rika cewa As salatu Jamiatu ko sau 3 ko sau 5 ko sau 7 gwargwadon abinda ya saukaka na wutiri (mara.)
Da jin wannan kiran sallah to sai jamaa maza da mata su taru a Masallatai, musamman Masallatan jumaa.
Bayan an taru sai liman ya jagoranci sallah. Idan an sallame sai yayiwa jamaa huduba, wadda a cikinta zai jawo hankali akan dalilan da suke sa ayi kusufi da kuma tsoratarwa gameda sabon Allah[SWT].
To banda sallah akwai wadansu abubuwan kuma da ake gabatarwa a yayin kusufi?
An so a yawaita sadaka da kabbarori da adduar neman tsari daga azabar kabari, kamar yadda Imamul Bukhari ya ruwaito inda Aisha RA take cewa Rana ta shafe a lokacin Manzon Allah (S.A.W.) , sai Manzon Allah yayi sallah tare da mutane, wanda a cikinta ya tsawaita karatu sannan yayi rukui kuma ya tsawaita rukuin, sannan ya taso daga rukuin ya tsawaita tsayuwar, koma-bayan wadda yayi da farko sannan yayi rukui na biyu, ya tsawaita rukuin amma bai kai tsawon na farko ba. sannan yayi sujada sannan ya aikata ga rakaa ta biyu (2) kamar yadda ya aikata ga rakaa ta farko. Sai ya juyo alhali ranar ta yaye sai yayi huduba inda a ciki yayi godiya ga Allah[SWT] kuma yayi yabo gareshi, sannan yace lalle rana da wata ayoyi ne daga cikin ayoyin Allah, basu shafewa saboda mutuwar wani ko rayuwarsa. Don haka idan kunga haka ya faru, to ku roki Allah, kuyi kabbara, kuyi sallah, kuyi sadaka, sannan kuma ya umurcemu damu roki tsarin Allah daga azabar kabari.. A kula da wasu aladu da akeyi idan rana ko wata sunyi kusufi sun sabawa shariar musulunci.
Daga ciki akwai.
Mutane su rika bi rariya  rariya suna waka cewa Rana saki bawanki.. da sauransu.
Mutane su rika kewaye gari suna zikirori, shima wannan bidia ne.
Haka kuma bida ce mutane suyi zamansu a gidajensu ba tare da zuwa masallatai domin salloli ba.
               LADUBBAN AMFANI DA WAYA (Handset)
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya hore wa Annabi Suleiman iska yana kaishi inda yaso, kuma ya dauko mashi maganganu daga ko ina ya bukata, wanda wani bangare na wannan niima ta riskemu a halin yanzu ta hanyoyin sadarwa na zamani.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzonsa Muhammad (S.A.W.)  wanda shine ya isarda sakon Allah garemu.
Bayan haka yan uwa mu tuna cewa addinin mu  ya tsara yadda zamuyi amfani da dukkan niimomin da Allah (S.W.T) ya saukar mana. Idan munbi tsarin addinin zamu amfana duniya da lahira. Idan kuma muka bi son zuciyarmu to munyi hasara. Daga cikin niimomin wannan zamani akwai wayar sadarwa .. walau ta girke a gida da kuma ta hannu. To zamu kawo wasu daga cikin ladubban da sharia ta tsara wajen yin amfani da waya.
Da farko dai kafin kasayi waya wajibi ne kayi tunanin cewa shin kana bukatar waya- ba wai kawai kaima ka shiga yayi ba. Idan ka tabbata kana da bukatarta to kai hattara da sayen mai tsada domin kar ka fada ramin almubazzaranci. Hakim ya ruwaito hadisin mai lamba 7188 inda Manzo Allah (S.A.W.)  yake cewa kuci ku sha, kuyi sadaka ba tareda barna ko kankanba ta wuce wuri ba, lalle Allah yana son yaga niimar da yayiwa bawansa.
Kafin kayi Magana idan ka buga ko an bugo maka ka tuna zancen Allah inda yake cewa. Ba zakayi wani lafazi ba face a gabanka akwai mai tsaro wanda yake halarace wato dai kada ka yarda ka sharara karya misali kana Tsafe sai kace ai kana Abuja-da dai sauran karairayi.
Ka tabbata ka kashe wayarka a cikin masallaci ko makabarta da dai sauran wuraren zama masu bukatar a kiyaye ladubban zama ta hanyar zance ko aiki. Idan har ka manta baka kashe wayar ba, aka bugo maka alhali kana daya daga cikin wadannan wurare to kayi maza ka daukota ka kashe domin sautinta yana cutar da sauran jamaar dake wurin musamman idan har kayi kuskuren sanya sauti da bai dace ba, kamarsu kida da wani abu mai kama da haka.
Kayi hattara da sanya sauti wanda ya sabawa musulunci, kamarsu kade-kade da wake-wake wanda wannan haramun ne. Haka nan  kuma sharia bata yarda kasa karatun Kurani ko wani zikiri ba, wanda in an kira ka zaka iya yanke wata aya ko zikiri.
Ya danuwa kada kayi amfani da waya idan kana jan Mota ko Babur ko keke, don kada kasa kanka ko wadanda ka dauko cikin hatsari. Idan ya zama dole ka amsa wayar, to ka tsaya ka amsa, sannan ka cigaba da tafiya.
Kada ka bari mutane daban  daban suna amafani da wayar ka. Misali yayanka da barorinka da sauransu, domin tana yiwuwa su rika kira inda bai dace ace ana kira da wayarka ba. Haka kuma kada ka saiwa na kasa da kai, misali yayanka da barori wadanda basu mallaki hankalin su ba waya. Domin duka wata barna da zasuyi da ita kana da kamisho.
Kayi amfani da wayarka wajen daukaka kalmar Allah. Misali kayi kira ko ka aika sako na abinda ya shafi nasiha akan aikin alheri ko tunatarwa akan halartar muhadara ko daurin aure ko sada zumunta ko gaida maras lafiya da dai abubuwa masu kama da haka.
Kafin ka buga wata lamba ka tabbatar da ingancin lambar, kuma ka kara tantancewa sannan ka buga domin kada  ka shagaltar da wani da wasa kana tsammani wani ne wanda kake wasa da shi.
Ka kula da lokacin da zaka buga waya. Ka tuna akawai lokacin Sallah, akwai lokacin barci, akawai lokacin cin abinci.
Ka takaita yawan buga waya. Idan ka buga sau daya, sau biyu, sau ukku baa dauka ba, to kayi hakuri sai wani lokaci can gaba. Saboda aiki da hadisin Imam Bukhari na 6245 dana Imam Malik 2153 inda Manzon Allah (S.A.W.)  yake cewa idan dayanku ya nemi izini sau 3 bai samu ba to ya juya.
Idan zakayi Magana a waya to ka tsaida kanka akan maganar da ka kira kayi. Maana kada ka maida waya wani dandalin hira ko kuma maganganun da basu da amfani. Ka tuna ko banza ma kudinka ne kake konewa.
A kula da cewa wanda ya buga waya, to shi keda nauyin yin sallama da zaran ta shiga, sannan wanda aka buga mawa ya maida sallamar. Mai bugawar kuma shine zaiyi sallamar bankwana. Mu sani cewa Hello ba gaisuwar musulunchi bace, sai dai idan wanda ka kira ko ya kira ka ba musulmi bane to kana iya ce mashi Hello.  Wanda ya bugo waya baiyi sallama ba to baa karba mashi, saboda hadisin  da aka ruwaito inda Manzon Allah (S.A.W) yake cewa Wanda ya fara Magana baiyi sallama ba, kada a karba mashi.
Ka sassauta maganarka idan kana Magana a waya. Kada kayi ta kuwwa ko daga murya ko kai kawo. Wannan koyi ne da wasiyyar da Lukman yayiwa dansa a cikin Akurani cewa idan yana Magana ya sassauta muryarshi. Domin lalle mafi munin sauti shine sautin jaki. Amma kuma kada maganar taka ta zama kamar kana rada, yadda wanda kake maganar da shi bai jinka sosai.
Ka kiyaye tsarin Magana da wanda kake Magana da shi. Wato ka sanya natsuwa da ladabi yayinda kake Magana da wanda ya girme ka ko shugabanka ko wani dan uwa na saman ka ballantana Malami mai aiki da iliminsa. Manzon Allah (S.A.W.) yace: Baya tareda mu wanda bai girmama manyanmu ba, baiji tausayin na kasa ba, kuma bai san hakkin Malamammu ba. Abu Dawud, Hadisi na 4134 da Tirmizi, 1566.
Wajen yin fatawa ga Malami ta waya, bayan ka buga wayar, kayi sallama, to sai kayiwa Malamin addua ta alheri. Bayan yagama amsa fatawarka, sai kayi adduar Allah ya saka da alheri, kuma ka rufe da sallama.
Kada ka rika Magana a tsakar gidanka yadda zaa rika jin sautin matanka da yayanka. Na gare ka ka tsare alaurar gidanka.
Kada ka kuskura kayi waya ko Text ta hanyar facebook, 2go, Twitter dadai sauransu wanda zai tsoratar da musulmi, ko yaci mutuncinsa ko tozartar dashi, ko ya keta alfarmarshi domin dukan wadannan haramun ne. Imam Muslim ya ruwaito hadisin da Manzon Allah[SAW] ke cewa Musulmi dan uwan Musulmi ne, kada ya zalunce shi, kada ya wulakantashi, kada ya tabar dashi. Dukkan musulmi haram ne a zubar da jininsa, haram ne a ci mutuncinsa, haram ne aci dukiyarsa.
Ka guji yin magana da mtum da harshen da bai iya ba. Wanda Hausa kawai ya iya, baya jin larabci, to kayi Magana dashi da Hausar. Amma in yana jin Larabci to sai kuyi Magana da larabci, ko da kuwa dukkanku Hausawa ne, domin Larabci yafi Hausa daraja, domin shine harshen Alkurani.
Ka kaucewa yin amfani da wayar hukuma ga kiraye  kirayen da basu shafi aikin hukuma ba. Idan kuma har an kiraka akan wayar hukuma, to kataikata wajen amsa wannan kiran idan bai shafi aikin hukumar ba.
Bai halatta ga mace tayi Magana da wanda ba mijinta ba, kuma ba muharraminta ba, saida izinin mijinta ko mahaifinta idan bata da miji, domin haka yana afkar da munanan ayyuka, kamarsu kashe aure da neman mata ta waya da sauran irinsu
Idan lalura takama mace tayi magana da wanda ba muharraminta ba, to kada ta tausasa murya. Aiki da umurnin Allah (S.W.T) cewa kada matan Manzon Allah (S.A.W.)  su tausasa muryarsu ga wani wanda yake da cuta a zuciyarsa don yaji dadin zancensu  har yakai ga barna. Haka kuma idan an buga waya kada mace tayi saurin karbawa idan dai akwai wani namiji ko yaro a kusa.
Allah ya bamu ikon kiyayewa amin.

32   YA ZAMU FUSKANCI SABUWAR SHEKARAR MUSULUNCI A SHARI’AH?
Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) wanda ya sanya watanni (12) su zama shekara guda tun lokacin daya halicci sammai da kassai kamar yadda yake cewa a cikin Alkurani, Lallai ne kidayayyun watanni a wurin Allah wata shabiyu (12) ne a cikin littafin Allah tun ranar daya halicci sammai da kassai daga cinkinsu akwai hudu masu alfarma .Daga cikin masu Alfarma akwai watan Almuharran. Tsira da Aminci Allah (S.W.T) su tabbata ga Manzonsa Annabi Muhammad (S.A.W) wanda lissafin watanni ya fara daga lokacin Hijiransa daga Makka zuwa Madina. Bayan haka, wajibi ne ga musulmi ya kula da wasu muhimman masaloli dasuka shafi zuwan sabuwar shekarar musulinci;
Wajibi ne ga musulmi yakula da lissafin watannin musulunci a dukkan harakokinsa na yau da kullun sabanin abin da yake faruwa yanzu inda mukafi sanin watannin kafirai fiye da na muslunci.
Wajibi ne ga kowane musulmi yayiwa kansa hisabin abubuwan daya gabatar a cikin shekarar data gabata. Idan yayi aikin alheri to ya godewa Allah[SWT], idan kuma yayi kuskure, ya roki Allah ya yafe masa,  Umar bin Khadab (R.A) yace kuyima kanku hisabi tun gabanin ayi maku hisabi. Ibn Kayyum Al-Jauzi (R.A) yace yana daga cikin halakar rayuwa gobe kiyama idan ta koma ma ubangijinta batare da tana wa kan ta hisabi ba a kowane lokaci.
Yazama wajibi ga dukan musulmi ya kara aiyukan alheri da na ibada zuwa ga ubangijinsa idan sabuwa shekara ta kama, sannan ya tuba daga miyagun ayyukan da yakeyi domin ajalinsa ne yake kara kusantowa, kamar yanda hadisi yazo a cikin (Buhari 4970) Manzon Allah (S.A.W.) yayin da aka sanar dashi ajalinsa ya kusa sai aka umurce shi da ya yawaita yin tasbihi  da istigafari da godiya zuwa ga ubangijinsa wannan hadisin shi ke kara samu yawaita aikin alheri kafin ajali yazo
Wajibi ne musulmi ya tuna cewa wannan shekara mai wucewa amfa cire shekara guda daga cikin shekarun da Allah ya debar masa a duniya kuma shekarar nan baza ta sake dawowa ba har abada. Ashe wannan na kara nuna mana mu kara tashi tsaye domin neman guzuri ba murna ba.
                   BIDIOIN DA AKE SHIGARWA IDAN SHEKARAR MUSULUNCI TA FARA
Bidia ne tara mutane domin murnar sabuwar shekarar Musulunci kamar yin waazi farkon shekarar Musulunci da Faretin yara da ake yi a dukkan farkon shekara.
Bidia ne aikawa da gaisuwa zuwa ga mutane ta hanyoyi kamar ta kati, sakon waya (Text) ko fada da baki don murnar sigowar sabuwar shekara.
Bidia ne bada hutu da akeyi na Gwamnati wanda ya kunshi maaikata, da yan makaranta don murnar sabuwar shekara ta fara. Domin koyi ne da kiristoci da yahudawa.
Bidia ne yin bukukuwa ranar Ashura domin murnar zuwan ranar, kamar dafa abinci da yin dinke  dinke kamar ranar sallah. Sabanin abunda Manzon Allah (S.A.W.) ya umrci ayi nayin azumi a wannan ranar.
Bidia ne daukar ranar Ashura ta zama ranar bakin ciki kamar irin yadda yan shia keyi na tsaga jikinsu da wuka da bugun jikinsu da yage suturar su da kuma sa bakaken kaya, sabanin abinda Manzon Allah (S.A.W.) yace baya tare da mu wanda ya mari kansa koya kece rigarsa ko yayi mummunar addua don ya rasa wani. Buhari 1294.
Bidia ne kiran walima domin cin abinci ko shan lemu da kayan tande  tande don murnar zuwan sabuwar shekarar musulunci.
Wajibi ne Musulmi ya auna duk abinda zai yi da maaunin sharia kafin ya aikata. Wannan ya hada da abubuwa da suka shafi shigowar sabuwar shekarar Musulunci. Ba dai  dai bane muyi koyi da Yahudawa da Nasara wajen bukukuwan shigowar sabuwar shekara ta hanyar tarurruka, laccoci ko wasu abubuwa masu kama da haka. Wannan ya sabama karantarwar Manzon Allah (S.A.W.) da sauran magabata na gari. Ya Allah ka sanya muna wannan sabuwar shekara ta zama mai albarka da arziki da wal  wala da zaman lafiya da cigaban Mususlunci da Musulmai a ko ina a duniya, ka kuma cika muna shekarar da kyawawan ayyuka Amin. Ga sunayen watannin musulunci da ya kamata kowane Muslumi Namiji ko Mace ya sansu.;-
1. Al- Muharram 2. Safar 3. Rabiul Auwal 4. Rabiu Thani
5. Jimada Awwal 6. Jimada Akhir 7. Rajab 8. Shaaban  
9. Ramadan 10. Shawwal 11. Zulkiida 12. Zul hajjah.
33. KO KASAN MEMENE BIDIA?
Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) wanda ya wajabta mana bin Manzonsa Annabi Muhammad (S.A.W.)  Tsira da amiincin Allah su tabbata ga Manzon Allah (S.A.W.)  wanda yace dukkan  bidia batace dukkan bata tana cikin wuta.
Minene Bidia? Bidia itace ka kaga ko kirkiro wani abu a cikin addini bayan kammaluwar addinin. Yazo cikin Sahihu Muslim, cewa duk wanda ya kaga wani abu a cikin wannan addini wanda babu umurninmu a cikinsa an mayar masa .
Ko Bidia tana da kashe  kashe? Bidia ta kasu kashi biyu.
Bidia ta diniyya watau ta addini:- Itace wadda kayi da manufar kusanci zuwa ga Allah [SWT]. Wannan tayi dai-dai da Hadisi wanda Manzon Allah (S.A.W.) yace, duk wanda ya kaga wani abu a cikin wannan addini babu umurninmu to an mayar masa.
Bidia Adiyya ko danawuyya:- Abinda ake cema Bidia adiyya ko danawuyya shine abunda mutane suka kirkiro don amfanin kansu kamar Keke, Mota, Lasifika, Jirgi, da sauransu. Wadanda sun yi sune  ba don addini ba ko neman kusanci zuwa ga Allah. Sunyi sune domin daular duniya. Bidia mai laifi itace bidiar da aka kirkiro don addini  ko neman kusanci zuwa ga Allah. Don haka ayi hattara da miyagun malamai da suka cuda bidia ta addini da ta duniya don cimma manufar kansu ta duniya.
Tambaya: Minene hukuncin addini game da bidia? Babu shakka lallai Bidia cikin addini batace mai kai mutum zuwa ga wuta kamar yadda Manzon Allah (S.A.W.)  yace, Kashedinku da kage-kagen al-amurah: lallai dukkan abun da aka kaga bidia ne kuma kowace bidia batace ABU DAUWADA (1407).
Minene Sakamakon Dan Bidia?
Baa ansar tubar dan bidia sai lokacin daya bar Bidiar. Saboda Manzon Allah (S.A.W.) yace Allah ya kange amsar tubar duk dan bidia sai ya bar bidiar. IBN MUNZUR ya ruwaitoshi, Albani ya iganta hadisin a cikin SAHIHUL JAMII (1699).
Aikin dan Bidia shirme ne saboda Manzon Allah (S.A.W.) yace duk wanda ya kaga wani abu cikin addini zaa mayar masa da abunsa.
Duk dan bidia baya shan ruwan tabkin Manzon Allah; Saboda Manzon Allah yace zaazo da mutane ranar kiyama da hasken fuska dana kafafu sai inyi masu maraba gindin tabkina, sai Malaiku su kangesu daga gareni, sai ince lafiya? Sai suce sunyi bidia bayan baka nan sai ince ayi nesa-nesa dasu. BUKHARI (7306).
Dan bidia yana da kamishon  laifin duk wanda yayi aiki da bidiar da yazo da ita har zuwa ranar kiyama saboda Manzon Allah (S.A.W.) yace duk wanda yayi kira zuwa ga bata, laifin na gareshi na duk wanda yabi wannan batar. Muslim (2674).
Dan bidia laantaaccen Allah ne duk inda ka ganshi saboda Manzon Allah ya laancceshi, malaiku sun laanceshi, mutane ma sun laanceshi BUKHARI (7306).
Dan bidia yana rarraba kan alummah domin dayin bidia ne Alummah take rarrabuwa, kamar yadda Manzon Allah yace; Duk wanda ya rayu cikinku zaiga sabani mai yawa don haka ku rike Sunnah ta. ABU DAUWUDU (4707).
Dan bidia yana boye gaskiya bayason a ganta don bidiarshi taci gaba kamar yadda Allah yace ‘lalle wadannan dake boye gaskiya bayan an bayyanar da ita to Allah ya laacensu kuma masu laanta sun laancesu’.
Dan bidia yana cin gyaran shariar musulunci kuma ya dauki kansa mai tsara addini alhali kuwa Allah yana cewa a yau na cika addininku kuma na cika niimata a kanku. MAIDA AYA. (3)
Dan bidia maibin son ransa ne mai tsaurin kai ga sharia, kuma mai sabama Allah da Manzonsa ne. Allah (S.W.T) yana cewa kuyi ma Allah daa kuma ku yima Manzonsa daa.
Dan bidia yana mummunar cikawa domin shedan yana biyoma dan Adam ta ko wace Hanya idan ya sameka a tarkon bidia sai yace wannan mun gama da shi a kyale shi.
Muna rokon Allah (S.W.T) yakare mu daga fadawa cikin tarkon bidia.

                 BANBANCI TSAKANIN BIDIA DA SA‘BO
Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) wanda ya sanya ma dan Adam hankali domin ya gane gaskiya da bata. Tsira da aminci su tabbata ga Manzonsa wanda yayi bayanin da mai hankali ke iya dauka. Bayan haka ku sani yaku yanuwa Musulmi Manzon Allah (SAW) yayi bayani cikakeke akan hadarin bin bidia da kuma makomar Dan Bidia. Wannan bayani ya gabata a wasikarmu ta baya. Yanzu kuma zamuyi bayani akan banbanci tsakanin dan bidia da mai sabo dama sauran bayanai.
Banbance  banbancen dake tsakanin bidia da sabo suna da yawa Kadan daga cikinsu: -
Shi mai sabo yana shiga cikin sabo, yasan sabon ne yakeyi. Kamar mai shangiya, zina, shan taba, chacha, da sauransu duk mai yin wannan yasan sa‘bo ne. Amma Dan Bidia yayin da yakeyin bidiarsa yana dauka addini ne yakeyi, to wannan ba karamin hadari bane.
Lalle shi mai sabo yana sabama Al-qurani da Hadisi ne yayin da yakeyin sabo. Shi ko dan bidia yana bata Qurani da Hadisi ne yayin da yake yin bidiarshi. Don kuwa yana cin gyaran Qurani da Hadisine.
Shi mai sabo aibin sabonsa yana tsayawa gareshi ne baya shafar kowa. Shi ko Dan Bidia bidiarshi tana shafar Alumma ne don sai su dauka addini ne yakeyi musaman ga jahilai.
Ita bidia tana faruwa akan jahilci da mummunar fahimtar hukunce- hukunce na Sharia. Sabo yana faruwa ne akan fahimta da kuma sani, wannan yana sa mai sa‘bo saurin nadama, fiye da dan bidia.
Dalilian dakesa Bidia ta yadu tsakanin alumma sune kamar haka: -
Jahilci: - kowa yasani cewa jahilci shine babban aibi a cikin musulunci. Saboda Allah yana cewa Kada ka tsaya akan abun da baka da ilimi gareshi. (IsraI 36).
Bin son rai: - idan mutum nabin son ranshi, to yanzun ne zai fada a cikin bidia. Allah yana cewa babu wanda yafi kowa bacewa irin wanda ke bin son ranshi batare da shiriya ba daga Allah. (Qasas 50).
Dogara da hankali ko watsar da nassoshi na aukar da mutum cikin bidia. Takalidanci da malamai da Taasubanci: - Takalidance shine biyyaya ga malamai ta makanta. Taasubancin shi kuma bin abun da ka tashi kaga anayi ko da ya sabama sharia.
Shirun malamai da kuma boye ilimi da sukeyi. Wannan shima yana kawo yaduwar bidia.
Dogara da hadisai masu rauni ko na karya. Shima wannan na kawo yaduwar bidia.
Rashin bin tafarkin magabata watau Sahabbai, Tabiai da Tabiit Tabiina Rashin kula da sunnonin Manzon Allah (S.A.W.) da aiki da su. Shima wannan yana kawo yaduwar bidioi.
Yawan malamai yan bidia shima yana sa bidia ta yadu. Saboda watsata da tallarta da suke yi.
Bin Ayoyin Alqurani masu rikici da kuma bin hadisan Manzon Allah (S.A.W.) masu rikici sai ayi watsi da wadanda ke dauke da hukunce  hukunce. Shi ma yana kawo yaduwar bidia. Maana anan tawili ga ayoyin Alqurani da hadisai wadanda ke dauke da suffofin Allah da sunayensa.
Ga wasu kadan daga cikin bidioin daya wajaba aguje mawa: -
Taron Maulidi: - wannan kowa yasan bidia ne
Neman tubarriki da yin Sallah ga kabarin wani Salihi ko Waliyyi shima bidiane.
Taron zanen suna da akeyi na maza shima bidiane
Taron adduar mamaci ta ukku, ko bakwai, ko arbain shima bidia ne.
Adduar da liman ke jagoranta bayan an gama sallar farilla shima bidiane abinda ya dace da sunnah kowa yayi da kansa.
Zaman amsar gaisuwa da akeyi bayan anyi rasuwa har tsawon kwana ukku na maza da mata shima bidiane.
Jagorantar mutane wajen addua a makabarta cewa Salati ashirin, Hailala sha daya, Tahiya bakin salihina da sauran ire-irensu a wajen gaisuwa shima bidiane. Abunda ya dace da sunnah kowa yayi tashi da kansa.
Gina kabari ko zagayeshi da bulo shima bidiane abunda ya dace da sunnah shine aza dutse wajen kansa domin alama.
Jan Chasbaha (carbi) bayan an gama sallah ko ratayashi ga wuya ko yawo dashi cikin kasuwa da ofis  ofis ga hannu kana ja shima bidiane, abunda ya dace da sunnah idan zakayi tasbihi ko zikiri kayi lissafi da yatsu ko gabobinsu.
Yin kari ga wanke gabobin alwalla fiye da uku shima bididane.
Daga karshe muna fatar yanuwa musulmi zasu tashi  tsaye ga binciken gaskiya da aiki da ita domin malamai na cewa ana amsar gaskiya ko da daga wurin shedan ne. Muna rokon Allah ya bamu ikon binciken gaskiya da kuma aiki da ita.
Domin Karin bayani a duba wadannan littafai:
Ihayaussunnna na Sheikh Danfodiyo
Bayanin BidiI na Sheikh Danfodiyo
Nurul Al-bab na Sheikh Danfodiyo
Nurul Sunnah Wazulmatul Bidia na Sheikh Said Al-khahdani
Akhadhauna Fil Ibadati na Dr. Musdafa Murad
Wa kullu Bidiatul Dalala na Sheikh Abdur-rahman Alsanuri.
35       MENE BANBANCI TSAKANIN MALAMI DA BOKA
Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) wanda yake shiryadda wanda yaso akan tafarki madaidaici. Tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah (S.A.W.)  wanda ya bayyana mana hanyoyin kusanta zuwa ga Allah (S.W.T).
Bayan haka, wajibi ne a jawo hankalin yanuwa domin su gane bambamci tsakanin malami na gaskiya da wanda a zahiri yake sa rigar malanta, amma a boye shi boka ne.
Akwai alamomi da yawa da suke nuna cewa mutum boka ne koda kuwa a zahiri yana nuna shi malami ne. Daga cikin wadannan alamomi akwai:-
Wanda idan akaje wajensa neman taimako sai ya tambayi sunan wanda yazo da sunan mahaifiyarsa da mahaifi.
Wanda yake cewa mai neman taimako ya kawo wani abu nashi a hada ayi aiki. Misali takalmi ko riga ko gashi ko akaifa da sauransu.
Wanda a wasu lokutta da ka shiga wajensa zai fadi sunanka da inda ka fito da sauransu, alhali kai baka taba saninsa ba.
Wanda yake cewa a kawo wasu abubuwa da babu su ko kuma masu wuyar samu, kamar bera maraya, ko beraye goma sha daya wanda aka kama suna barci ko biri makaho da dai sauransu. Idan baka iya kawosu sai yace ka bada kudi a samu mai kawosu.
Wanda yake karance  karancen shirme da kiran wanin Allah kamar Aljannu da shedanu da waliyyai da sauransu.
Wanda zaice a kawo wasu nauoin dabbobi kamarsu bakar akuya wadanda zaayi aiki da su, ko a umurci maras lafiya yaje ya binne irin wadannan dabbobi gindin wani itace ko dutse.
Wanda yake wulakanta kurani ta hanyar rubuta shi da najasa kamar jinin biki ko na haila.
Wanda yake bugun kasa domin ya gayawa mutum abinda zai samu ko ya same shi anan gaba.
Wanda yake ba mai bukata ko maras lafiya wani abu kamar kaho ko kambu ko laya, koma dai duk wani abu wanda a cikinsa adduoi ne na shirme da shirka, a umrceshi ya rataya ko ya aje karkashin matashi.
Wanda yake zana siffofin aljannu (dalamusai) a takarda ya jika takardar a ruwa kuma ya umurci maras lafiya yayi wanka da ruwan a wani wurin da baa ganinsa kamar makabarta ko wani kangon gini.
Wanda yake umurtar mai bukata yasa rigar layu ko Falmara wadda aka zana mata dalamusai ko wasu lambobi
Wanda yake bada wani abu da manufar zai iya sa mace taso miji ko kuma mallakeshi da dai wani abu mai kama da wannan.
Wanda yake umurnin direba ya daura kan kura ko hakorinta ko wani kyalle ga motar da manufar wai wannan zai kareshi daga hadari.
Wanda yake umurnin masu mota su lika charbi ko hoton wani Shehi a gilas din motar da manufar wannan charbi ko Shehi zai kare wannan mota daga hadari.
Wanda yake umurtar a lika hoton Shehi ko layu a gida ko ofis ko shago da manufar wadannan abubuwan zasu iya jawo wani alheri ko kare wani sharri.
Wanda yake amfani da kwai wanda aka zana dalamusai ko kuma kwado na rufe kofa da riyawar cewa wannan yana iya rufe bakin wani.
Wanda zai bada wasu abubuwa yace aje a rufe wasu kebantattun wurare, kamarsu gulbi ko makabarta ko suri ko magamar hanyoyi da sauransu.
Wanda yake bada wani irin zobe, yawanci na azurfa wanda aka zanawa dalamusai da manufar wannan zobe zai iya jawo mashi wani alheri ko ya kauda mashi wani sharri.
Wanda yake amfani da allon karfe ko tafasashshiyar dalma domin wai kona wani da ake son a halaka.
Wanda ke bada labari ga maras lafiya cewa wani ne ya jefe shi ko kuma yayi masa wani kafi a gidansa.
Wanda wasu alamonin fasikanci suka bayyana gareshi. Misali wanda ke aske gemu, ko ya bar gashin baki  bazo-bazo, ko sakin wando ko riga suna jan kasa ko kuma rashin halartar sallar jami.
Wanda yake duba na charbi. Wato yana amfani da charbi ta yin zane dashi ko kuma ba mabukaci charbin yana ja da riya cewa idan yakai wuri kaza na charbin to akwai alheri, amma in ya tsaya wuri kaza na charbin to wannan sharri ne.

FADAKARWA
Wadannan alamomi da aka ambata kadan ne daga cikin hanyoyin da ake bi wajen zare imanin mutum da halakar dashi da sunan malanta. Don haka wajibi ne mutum yayi hankali da Yan-duba da bokaye da malamam tsibbu. Manzon Allah (S.A.W.)  yace Wanda yaje wajen boka ko malamin duba, kuma ya gasagata abinda suka fada to ya kafircewa abinda aka saukarwa Annabi (S.A.W.) . A wata ruwayar Manzon Allah (S.A.W.)  yace :Wanda yaje wajen Boka ko Dan Duba amma bai gasgata abinda suka ce ba, baida sallar kwana 40. Malamai 4 suka ruwaito wannan Hadisi.
ALLAH YA TSARE MANA IMANINMU AMIN.

36   ABUBUWAN DA SUKA WAJABA GA LIKITA KO MAI MAGANIN GARGAJIYA SU KIYAYE
Godiya ta tabbata ga Allah wanda yake jarrabar bawansa da rashin lafiya, wanda kuma yasa waraka ga kowane irin ciwo.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzonsa Muhammad (S.A.W.)  wanda shine shugaban likitocin duniya baki daya, kuma wanda yace Lalle Allah bai saukarda wata cuta ba face ya saukarda warakarta. Wanda ya sani ya sani, wanda kuma bai sani ba, to bai sanin ba. Ibn Majah ya ruwaito, kuma Albani ya inganta hadisin a cikin Sahih Jami,i Hadisi na 223.
Bayan haka, a dalilin karuwar cututtuka a wanna lokaci da kuma yawaitar masu bada magungunan gargajiya da na bature ya zama wajibi a binciko abubbuwan da shariar musulunci ta shimfida game da bada magani. Da farko dai tukun, wajibi ne ga wanda yake son shiga sanaar maganin gargajiya ko na bature ya samu isashshen ilimin wanna harka, saboda fadin Manzon Allah (S.A.W.) cewa Wanda yayi magani, alhali baida ilimin wannan maganin kafin ya bada shi, to shi mai biyan diyya ne idan an samu salwantar rayuwa ko wata gaba sakamakon bada wannan magani. Abu Dauda ne ya ruwaito wannan hadisi, hadisi na 4586. Wanna hadisi yana nuna kenan idan ka bada magani ba tare da ilimi ba, kuma ka samu matsala, to ko baka biya anan duniya ba, zaka biya gobe kiyama. Don haka ga wasu masaloli wadanda wajibi ne ga masanin maganin gargajiya dana bature su kiyaye.
Wajibi ne yayi nazari akan irin rashin lafiyar da aka zo da ita.
Yayi kokari ya gane sababin dake iya kawo wannan rashin lafiya. Misali idan zazzabi ne, shin sauro ne ya kawo shi ko wani abu.
Yayi dubi ga karfin jikin maras lafiya dangane da karfin cutar. Shin karfin jikinsa yana iya jurewa karfin maganin ko aa
Ya gane abubuwan da jikin maras lafiya ya saba dasu na dabia kamarsu abinci ko abinsha, da abinda bai saba dashi ba.
Yayi laakari da shekarun maras lafiya da aikinsa da garinsu da yanayin turbayar garin da bugawar iska a wannan lokaci.
Haka kuma yayi laakari da lokacin shekara da ake ciki. Damina ce ko lokacin zafi ko hunturu da sauransu.
Yayi nazarin maganin da yafi dacewa da yin gogayya da cutar, haka kuma ya gane karfi da darajar maganin.
Ya tabbata cewa bayan an kauda cutar, to wata cutar, wadda watakila tafi waccan ta farko bata maye gurbinta ba?.
Wajen bada maganin ya fara da mai sauki. Misali idan cin wani abinci ko rashin cinsa ko wani motsa jiki zaifi alfanu to kada a tilasta masa sayen magani don neman kudi.
A kaucewa bada wani magani tun kafin wanda aka fara bayarwa bai gama aiki a jikin maras lafiya ba. Maana a daina chakuda magunguna iri-iri wajen warkar da ciwo guda. Annabi (S.A.W.)  yace Kowace cuta, idan ta hadu da maganinta, ana warkewa da izinin Allah Muslim ne ya ruwaito wannan Hadisi na 2204. Wato kenan warkewa ba a cikin chakuda magunguna take ba.
Banda sanin ilimin magunguna, wajibi ne kwararren mai bada magani ya kasance yana da ilimin halayyar zuciya da jikin Dan Adam, da kuma maganin warkar da cutar zuciya. Wannan bai bukatar wata kwaya ko sassake. Watakila abinda yake bukata shine zikiri da hailala da istigfari da sauransu.
Wajibi ne mai magani yayi ta licin maras lafiya yana ta lelenshi kamar yadda ake lici da lelen karamin yaro.
Ya kasance yana iya wakarda maras lafiya bata hanyar magunguna da aka saba dasu ba kawai, harma da hanyoyin samun waraka ta adduoi kamar yadda suka zo a Kurani da Hadisi. Haka kuma ya kasance yana iya warkar da maras lafiya ko da da zance ne na hikima.
kwararren mai bada magani shine wanda sanaarsa ta kewaye wadannan abubuwa guda 4:-
Kiyaye lafiyar da kenan
Kokarin ganin lafiyar da aka rasa ta dawo gwargwadon hali.
Gusadda illar dake kawo rashin lafiyar ko kuma karanta ta gwargwadon hali
Gabatar da wata karamar cuta domin hana aukuwar wata babbar cuta. Misali a yanke dan yatsa domin gudun yaduwar cutar tetanus wadda ke iya kaiwa ga mutuwa.
Babban alamari shine mai magani yaji tsoron Allah. Ya gane shin yana iya maganin cutar nan, ko kuwa karfin hali zaiyi don kawai ya samu kudi.
Dukkan mai magani wanda bai cika wadannan sharudda ba, to bai cancanci wannan sanaa ba.
FADAKARWA
Muna kira ga yanuwa Musulmi cewa suyi hattara da neman magani wajen wadanda basu san kwarewarsu ga ilimin likitanci ko na gargajiya ba. Idan ka afkawa wanda baka san zurfin iliminsa na magani ba, yana iya jawo maka hasarar dukiya da ta rai da ma ta imani. Domin kana iya fadawa hannun boka ko dan sihiri ko dan tsibbu. Allah (S.W.T) yana cewa Kada ku kashe kawunanku. Lalle Allah ya kasance mai jin kai gareku
Littafan da zaa duba
Zadul Maad, Dibbin Nabawi na Ibn Kayyim Al Jauziyya, babban likitan Musulunci.
   WADANNE ABUBUWA NE KE FITAR DA MUTUM MUSULUNCI
Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) wanda yace Duk wanda yayi ridda ya bar addininsa ya mutu yana kafiri wadancan ayyukansu sun ruguje duniya da lahira kuma su sahabban wuta ne masu dauwama ne cikinta (Suratul Bakara 217). Tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah (S.A.W.)  wanbda yace; "Duk wanda ya bar addininsa ku kasheshi (Bukhari).
Ya ku yan uwa musulmai sanin abin da ke fitar da mutum daga musulunci abu ne mai matukar muhimmanci, don haka ya zama wajibi ga dukkan musulmi namiji da mace su sansu don karsu fada ciki.
Kamar yadda Khuzaifa bin Yaman R.A yake fada cewa kasan sharri ba don kayi shi ba sai don ka kare kanka daga gareshi. Wannan ne ya jawo hankalinmu damu fadakar da musulmi hadarin da suke ciki na jahiltar wadannan abubuwa
ABUBUWAN DAKE FITAR DA MUTUM MUSULUNCI SUNA DA YAWA GA GOMA SHA BIYAR DAGA CIKINSU
Akwai musulmin da yake aikin musulunci, amma duk da haka yana zuwa wurin bokaye da malamn duba dana tsibbu yana tambayarsu kan alamarinsa na duniya, kuma yana gasgantasu. Sheikh Usman yace wannan kafirci ne. Manzon Allah (S.A.W.) yace duk wanda yaje wajen boka ko malamin duba ya gasgatashi ga abun daya fada, hakika ya kafirce ma abun da aka saukarma Annabi Muhammad (S.A.W.) . Ahmad ya fitar da hadisin da Muslim da Hakeem.
Akwai musulmi dake daawar shi musulmi ne kuma yana aikin musulunci amma kuma yana zuwa kabarin wani waliyyi ko malami ko wani mai ibada yana aje riga ko abinci da nufin cika wani alwashi da yayi ko neman tubarraki, wanna shima kafiri ne inji Sheikh Usman bin Fodiyo.
Zagin Allah ko zagin Manzon Allah (S.A.W.)  yin wanna shima kafircine.
Wanda ya zagi sahabban Manzon Allah (S.A.W.)  ko yima Aisha RA kazafi shima kafirine inji Imam Malik. Saboda karshen ayar dake cikin Suratul Fatahi Allah (S.W.T) ya ke cewa ya fitar da sahabbai ne don ya fusatar da kafirai dasu.
Wanda ya sanya wani tsakaninsa da Allah kamar waliyyi yana rokon bukatunsa wurinsa don ya yaye mashi damuwa ko neman arziki yana dogara garesu kuma yana rokon cetonsu, shima wannan kafiri ne. Allah (S.W.T) yace kada ka kirayi wani koma bayan Allah wanda bai iya amfanar da kai da komi kuma bai iya cutar da kai. Lallai inka aikata haka to kana cikin azzalumai (kafirai) (Suratul Yunus 106).
Duk wanda yaki wani abun da Manzon Allah (S.A.W.)  yazo da shi ko yaki aiki da shi ya kafirta.  Allah (S.W.T) yana cewa wanda suka kafirta halaka ta tabbata akansu kuma Allah ya bata aikinsu, domin sun kyamaci abun da Allah ya saukar (Suratul Muhammad 8)
Wanda yayi izgili ko yayi wasa da wasu alamomi na musulunci kamar aibata gemu ko dage wando ko mata masu hijabi, ko izgili ga masu waazi ko aibanta Shariar Musulunci, shima ya kafirta. Allah ya ce "shin da Allah da ayoyinsa da Manzonsa kuke izgili, babu wai kun kafirta bayan imaninku (Suratu Tauba 65).
Taimakawa kafirai akan su yaki Musulmai ko su cutar dasu shima wannan kafirci ne. Allah (S.W.T) yace: Wanda ya jibinci kafirai daga cikin ku lalle yana tare da su. Lallai Allah (S.W.T) baya shiryar da azzalumai (kafirai)(Suratul Maidah 51).
Duk wanda ya kauda kai daga addinin Allah bai neman ya sanshi kuma bai neman yayi aiki da shi ya kafirta. Allah (S.W.T) yace Wadanda suka kafirta daga abun da akai masu gargadi masu kauda kai ne (Surah Ahkaf 3).
Wanda ya dauki wata laya ko wasu kulle-kulle ya jefa mahadar hanya ko karkashin itace ko kasan duwatsu ko cikin rijiya ko cikin ruwa ko makabarta Sheikh Usman yace shima kafiri ne.
Duk wanda yace yasan gaibi wannan kafiri ne inji Sheikh Usman. Allah (S.W.T) yace “Babu wanda yasan gaibi a cikin sammai da kassai sai Allah (S.W.T)”.
Wanda ke buga ganga yana janyo ayoyin Alqurani ko Hadissan Manzon Allah (S.A.W.) shima Sheikh Usman yace kafiri ne.
Wanda ya rubuta Al-qurani ko sunayen Allah da najasa ko jini ko ya jefa cikin masai shima Sheikh Usman yace kafiri ne.
Hakama wanda yayi addua da sunayen Aljanu ko wasu sunayen da baa sansu ba ko ya rataya kambu ko wuri da manufar ya tsareshi shima kafirci ne. Manzon Allah (S.A.W.) yace “Lallai addua da sunayen wasu da baa sani ba ko rataya kambu ko wuri hakika shirka ne”.
Duk wanda ke aiwatar da shirka ko sihiri shima kafiri ne. muna rokon Allah yasa mu mutu musulmi ya karemu daga hadarin fita daga cikin musulunci.
Domin Karin bayani a duba wadannan littafai:-
Nurul Albab na Sheikh Usman Ibn Fodiyo
Nawaqidul Islam na Sheikh Muhammad Ibn Abdulwahab
Sahihul Fiqhussunnah na Sheikh Kamalu Bin Sayeed.
Jawahili Ikilit Sharhin Muktasar na Sheikh Khalil.

38                     TSARIN SUNAYEN ALLAH INGANTATTU
Sunayen Allah dari ba daya wadanda aka tace domin wadancan da aka saba karantawa akwai wadanda basu inganta ba. Domin hadisin da yazo dasu tirmizine ya ruwaito sa, shida ya rubuto hadisin ya raunana shi da sauran malaman hadisi nada da yanzu. Shiyasa muka kawo maku wadanda suka inganta. Domin nasiha ga musulmi, an daukosune daga cikin alqur’ani da hadisai ingatattu:

*الله  *الأحد *الأعلى *الأكرم  *الإله *الأول *والأخر *والظاهر * والباطن * البارئ *البر *البصير *التواب *الجبار *الحافظ *الحفيظ *الحسيب *الحفي *الحق *المبين *الحكيم *الحليم *الحميد *الحي *القيوم *الخبير *الخالق *الخلآق *الرؤف * الرحمن * الرحيم *الرزاق *الرقيب *السلام *السميع *الشاكر *الشكور *الشهيد *الصمد *العالم *العزيز *العظيم *العفو *العليم *العلي * الغفار *الغفور * الغني * الفتاح * القادر *القاهر * القدوس *القدير *القريب *القوي *القهار *الكبير *الكريم *اللطيف * المؤمن *المتعالى *المتكبر *المتين *المجيب *المجيد *المحيط *المصور *المقتدر *المقيت *الملك *المليك *المولى *المهيمن *النصير *الواحد * الوارث *الواسع *الودود *الوكيل *الولى *الوهاب *الجميل *الجواد * الحكم *الحيي *الرب *الرقيق *السبوح *السيد *الشافي *الطيب *القابض *الباسط *المقدم *المؤخر *المحسن *المعطى *المنان *الوتر0   

Saturday, 21 December 2019

ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI

ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI

NA

SANI LIMAN TSAFE
(ABU HURAIRA)
07059593000

    BUGU NA FARKO

WANDA YA DAUKI NAUYIN BUGAWA
Alh. Tambaya Tsafe
(ALLAH YA GAFARTA MASHI)

17 /11/1438

ABUBUWAN DA KE CIKI

    GABATARWA
MECE CE ZUMUNTA

DA WANE ABU AKE SADAR DA ZUMUNTA

FALALAR SADAR DA ZUMUNTA

HADARIN DA KE CIKIN YANKE ZUMUNTA

SABUBBAN DA KE JANYO YANKE ZUMUNTA

ABUBUWAN DA KE TAIMAKAWA WAJAN SADAR DA ZUMUNTA

FALALAR SADAR DA ZUMUNTA GA ABOKAN IYAYE

YAYA ZA`A MAGANCE MATSALAR YANKE ZUMUNTA

YANKE ZUMUNCI YANA DAGA CIKIN ALAMOMIN TASHIN AL-QIYAMA

بسم الله الرحمن الرجيم
                          
                             GABATARWA

Godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata'ala wanda ya fitar da sunan zumunta daga sunanshi, kuma ya tsoratar da al'umma daga yanketa, kuma na shaida babu wanda ya cancanta a bautamawa da gaskiya sai Allah(subhanahu wata'la) shi kadai yake ba shi da abokin tarayya.
Kuma na shaida Annabi Muhammad (salallahu alaihi wasallam) bawan Allah ne kuma manzonsa ne, kuma shine wanda yafi kowa sadar da zumunta a duniya. Tsira da amincin Allah su tabbata gareshi da alayensa da kuma sahabbansa da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka dalilin da yasa na rubuta wannan littafi kasantuwar samar da kwamitin zumunta da akayi a gidan LIMAN DAN BAWA TSAFE shi yasa na wallafa wannan littafi domin yan'uwana su amfana da sauran al'ummar musulmi baki daya. Duk abin da aka gani na dai dai cikin wannan littafi, datarwa ce ta Allah(subhanahu wata'ala), abin da kuma aka samu na kuskure daga gareni ne saboda karancin ilimi, muna rokon Allah(subhanahu wata'ala) ya yafe mana.

                                                          MAWALLAFI:
                                                              SANI LIMAN TSAFE
                                                               (Abu Hurairah)
                                                           Zamfara State
                                                          16/03/1441AH
                                                            14/11/2019

MECE CE ZUMUNTA 
IBN ATHEER yana cewa: Zumunta tana nufin taimakawa yan uwa na bangaren dangantaka da sarakuta da kula da halayen su koda kuwa suna zaune a wurare masu nisa koda kuma suna munana maka (a daya bangaren kuma yanke zumunta yana nufin kishiyar abubuwan da aka ambata a baya)
DA WANE ABU AKE SADAR  DA ZUMUNTA  
       Ana sadar da zumunta da al’amura masu yawa kamar ziyartarsu,                                                 bibiyar halayansu, tambaya game dasu, aika masu da kyaututtuka da kuma saukar da kowannensu a matsayin da ya dace dashi, da bada sadaka ga fakirai daga cikinsu, da tausasa ma mawadatansu(Binsu a hankali) da girmama manyansu, da kuma tausaya ma kananansu, da masu rauninsu, da yawan tambayar halin da suke ciki, da kuma ziyartarsu da kanka ko ka aika wasika ko kayi amfani da wayar salula.
Mafi girman abin da ake sadar da zumunta da shi shine yin wa'azi garesu, kamar yadda Allah madaukakin sarki yake fada wa manzonshi cewa: (KAYI GARGADI GA DANGINKA MAKUSANTA) [shu'araa 214]
   Haka kuma Manzon Allah (salallahu alaihi wasallam) ya rinka kiran danginsa domin ganin sun shigo addinin musulunci.
Saboda haka mutum yayi kwadayin kiran yan uwansa zuwa ga shiriya ya umurce su da aiki mai kyau, ya kuma hane su da aikata miyagun ayyuka.
Zumunta tana bambanta gwargwadon  kusanci da matsayi na wadanda ake sadar da zumunta zuwa garesu,  zumunci da yake tsakanin uba da dan-dansa yana da bambanci da dan-dan dan uwa na nesa. 
Bugu da kari, zumunta tana bambanta gwargwadon halayen wadanda za’a sadarmawa suke ciki kamar sadar da zumunta ga marar lafiya da mabukaci ta bambanta da sadarwa ga waninsu. Haka ma sadarwa ga babba ta bambanta da ta karami.
Haka sadar da zumunta yana bambanta ta fuskar bigire, wanda yake zaune a cikin gari ya bambanta da wanda yake zaune a wani gari wajen ziyartar shi, tambayar halin da yake ciki, da yi masa sallama ko aika mashi da sakonni.

FALALAR SADA ZUMUNTA
  Sadar da zumunta yana da tarin falala mai yawa kadan daga ciki sun hada da: 
Sadar da zumunta alama ce dake nuna cewar bawa yayi imani da Allah da kuma ranar lahira.  kamar yadda hadithin  da Abu Huraira ya riwaito daga manzon Allah (SAW) yace: ''Duk wanda  yayi imani da Allah da kuma Ranar Lahira to ya  Karrama Bakonsa, haka nan wanda yayi imani da Allah da ranar lahira to ya sadar da zumuntarsa (Buhari ya riwaito shi 6138”).
Lallai sadar da zumunta sababine na yalwar arziki da kuma tsawon rayuwar dan adam da kuma samun albarka a cikin su.
         An karbo hadithi daga Anas (R) yace manzon Allah, yace:''Duk wanda yake so a shimfida arzikinsa a kuma jinkirta masa rayuwarsa to ya sadar da zumuntarsa'' (Buhari 5986- Muslim 2557)”.
Abdullahi dan Umar (R) yace ''Duk wanda ya kiyaye  ubangijinsa , ya sadar da zumuntarsa  to za’a jinkirata masa ajalinsa, kuma dukiyarsa zata yalwata, sannan iyalansa zasu so shi.” (Tirmizi-1979- Buhari  adabul mufrad-58).
3. Sadar da zumunta yana janyo sadarwar Allah ga wanda ya sadar da ita.
      Abu Huraira ya ruwaito hadithi daga manzon Allah (SWA) yace ''Lallai Allah ya hallicci dukkan halitta bayan ya kammala sai zumunta ta tashi sai tace nan ne matsayin da zan nemi tsari daga wanda ya yanke ni?  Sai Allah (SWA) yace eh; shin ko kin yarda in sadar ma wanda ya sadar dake in kuma  yanke ma wanda ya yanke ki?  Sai tace eh, sai Allah yace haka zai kasance gareki''. (Bukhari -5987- muslim 2554).
4.  Sadar da zumunta yana daya daga cikin manyan sabubban da ke shigar da mutun Aljanna. Abu Ayubal Ansari yace ''Lallai wani mutum; yace  ya manzon Allah ka ba ni labarin aikin da zai shigar dani aljanna kuma ya nisanta ni daga shiga wuta, sai manzon  Allah yace ''ka bauta ma Allah kada ka hadashi da komai a wajan bauta, ka tsaida  sallah, ka bada zakka, ka sadar da zumunta. (Bukhari 1396-muslim 13)
5. sadar da zumunta yin da'a ne  ga Allah da Manzonsa,  Allah (SWA) ya fada a cikin Alqur’ani yana mai yabon masu sadarda zumunta  “sune wadanda suke sadar da abin da Allah yace a sadar dashi (Zumunci) suna jin tsoron ubanginsu kuma suna tsoron mummunan hisabi ”
  (Suratul Ra’ad 21)
An karbo hadisi daga Abu sufyan a cikin hadisinsa mai tsawo a cikin kissar Hirkala yace ma Abu sufyan mine ne Manzon Allah yake umurtar ku dashi sai Abu sufyan yace: yana cewa ku bauta ma Allah shi kadai kada ku hadashi da komai a wajen bauta, kubar ababen da iyayenku ke fada,kuma yana umartarmu da yin Sallah da riko da gaskiya da kamewa, da kuma sadar da zumunta (Muslim 1883)
6. Sadar da zumunta yana daya daga cikin kyawawan ayyuka a cikin addinin musulunci, Allah (SWT) yana cewa: ''kuba ma’aboci kusanci hakkinsa (ana nufin dan'uwa) (Isra’i 26)
Hakanan a wani wurin yace, kuji tsoron Allah wanda kuke rokon juna dashi kuma ku sadar da zumunta (Suratul Nisa’i 1). Ya kuma kara cewa ku bauta ma Allah kada ku hadashi da komai a wajen bauta, ku kyautatama iyayenku da makusantanku (yan'uwanku na zumunta) da marayu da miskinai da makwabci na kusa.
HADARIN  DA KE CIKIN YANKE ZUMUNTA
Hakika Allah (SWT) da manzonsa (SAW) sun tsoratar dangane da hadarin yanke zumunci, suka sanya matsayin yanke zumunci dai dai da Fasadi/barna a bayan kasa.
Allah (SWT) yace to shin kuna fatan idan kun juya daga (umarnin) zakuyi barna a cikin kasa, kuma ku yanke zumuntarku? Wadannan sune wadanda Allah ya la'anesu, kuma ya kurmantar dasu, kuma ya makantar da ganinsu. (Suratu Muhammad 22-23)
An karbo hadisi daga Aisha (R) manzon Allah (SAW) yace zumunta tana rataye da al’arshin Allah. Tana cewa wanda ya sadar dani Allah ya sadar dashi, wanda ya yanke ni Allah ya yankeshi (Muslim 2555)
An karbo daga MUD’IM (R) manzon Allah (SWA) yace mai yanke zumunta baya shiga Aljanna (Muslim 2556)
Haka nan kuma, an karbo  daga Abubakrata, Manzon Allah yace, Babu wani laifi daya can-canta Allah ya gaggauta ma ma'abocin sa uquba tun anan duniya tare da  cewa yayi mashi tanadin uqubar a lahira kamar wanda ya yanke zumunta da kuma azzalimi (Bukhari adabul mufrad 67)
An karbo daga Abu Huraira; lallai wani mutum yace ya manzon Allah lallai ni ina da yan'uwa kuma ina sadar da zumuntarsu amman suna yanke mani, ina kyautata masu amma suna munana mani, ina yin hakuri dasu amma suna jahiltata? Sai Annabi yace, idan har ka kasance kamar yadda ka fada to lallai kamar kana zuba masu toka ce mai zafi, Allah ba zai gushe ba yana taimakonka akansu matukar ka dauwwama akan haka (Muslim 2558) Ma’ana: kamar kana ciyar dasu toka mai zafi saboda abin da suke haduwa dashi na laifi.
Haka nan kuma an karbo daga Abdullahi ibn Amru binul As, Manzon Allah (SAW) yace, bai zama mai sadar da zumunta ba wanda yake so aranka mashi, sai dai mai sadar da zumunta shine wanda idan an yanke mashi, shi yana sadarwa (Bukhari 541)
An karbo daga salmanu ibn Amir, Manzon Allah yace, yin sadaka ga miskinai sadakace kamar sauran sadakoki, amma yin sadaka ga dan'uwa tana da darajoji biyu (2) ladar sadaka da kuma ladar sadar da zumunci (Abu Dawud 2555-Tirmidhi 658)
An karbo daga Abu Hurairah yace, lokacin da wannan ayar ta sauka,,, kayi gargadi ga yan'uwanka makusanta, Annabi (SAW) ya kira Quraishawa, suka hadu gaba dayansu, yayi musu wa’azi gaba dayansu kuma yayi ma dai-dai kunsu yace ya Fatima ki tsamar da kanki daga wuta, lallai ni bani wadatar daku a wurin Allah da komai sai dai lallai kuna da wata zumunta da sannu zan sadar da ita (Muslim)

8. SABUBBAN DA KE JANYO YANKE ZUMUNTA.
Idan kayi nazari akan sabubban dake janyo yanke zumunta zaka samu cewa akwai sabubba masu yawa. Ga kadan daga cikinsu
1. JAHILCI: Jahiltar mummunan sakamakon da mai yanke zumunta yake samu anan duniya da lahira, ko kuma rashin yin aiki da abin da mutum ya sani. An karbo daga Umar (R) ya kasance akan mimbari yana cewa: ku nemi sanin dangantakarku, sannan ku sadar da zumuntarku wallahi! Lallai zai kasance tsakanin mutum da dan uwansa wata rigima ta hadasu saboda rashin sanin juna, da yasan akwai zumunta tsakaninsu da wannan dalilin na alakar zumunta ya hanashi cin mutuncinsa (Bukhari, Adabul mufrad 73)
2. KARANCIN TSORON ALLAH; Idan tsoron Allah yayi rauni sannan addini yayi saku-saku ba zai damu ba idan ya yanke abin da Allah yayi umarnin asadar, kuma baya kwadayin ladar da ake samu idan an sadar da zumunta kuma baya tsoran mummunan sakamakon da zai same shi a dalilin yanke zumunta.
An karbo daga sa’id bn sam’an, yace: Naji Abu Hurairah yana neman tsarin Allah daga shugabancin yara da wawaye (jahilai) sai aka ce masa mine ne alamar yin haka? sai yace dan za’a dinga yanke zumunta a kuma dinga yin da’a ga mai halakarwa a saba ma mai shiryarwa (Adabul-mufad 66)
3. GIRMAN KAI; Sashen mutane idan mutum ya samu wani matsayi babba ko ya samu wata daukaka ko kuma ya zama babban dan kasuwa sai yayi girman kai ga yan'uwanshi, ya kyamaci ziyartarsu, kuma ya kyamaci zuwa garesu, yana ganin shi ke kan gaskiya kuma shi ya can-canta a ziyarta.
4. YANKEWA MAI TSAWO; A nan akwai wanda yake yanke ma yan'uwansa lokaci mai tsawo al’amarin ya dore akan haka har ya kai ga yanke zumuntarshi dasu gaba daya, har ya saba da yankewa sai yayi nesa dasu. An karbo daga Mikdam, lallai yaji manzon Allah (SAW) yana cewa lallai Allah yana maku wasiyya da iyayenku mata sannan yana maku wasiyya da iyayenku maza, sannan yana maku wasiyya da yan'uwanku (Adabul mufrad 60).
5. AIBANTAWA MAI TSANANI; Sashen wasu mutane idan dan'uwansu ya ziyarcesu bayan a baya ya yanke zumuntarshi dasu lokaci mai tsawo sai su yawaita zar ginshi har zargin yayi tsanani wanda wannan sai yasa shi kaurace masu saboda tsoron mummunan zargi da suke mashi.
6. DORA MA RAI NAUYIN DAYA WUCE QA’IDA; A nan akwai wanda idan dan'uwansu ya ziyarcesu sai su dora ma kansu yin hidindimu da suka wuce karfinsu domin su ga cewa sun karrama dan'uwan nasu sama da karfinsu ko karancin abun hannunsu, wannan shi ke sanya yan'uwan nasu su dinga takaitawa da ziyartarsu domin tsoron kada su dora masu ire-iren wadannan nauye-nauyen. Saboda Annabi yace mafi karancin sadar da zumunci shine sallama mafi girman zumunta shine  sadarma wanda ya yanke maka.
7. KARANCIN KULA DA WADANDA SUKA KAWO MAKA ZIYARA; Akwai daga cikin mutane wanda idan yan'uwanshi suka ziyarceshi baya bayyanar da farin cikinsa akan ziyarar, bai tsayawa ya tattauna dasu ko ya sakar masu fuska, sai dai za ka ga yana bata rai yana kyamarsu, wannan yana zama sanadin yan'uwa ba zasu kara ziyartarshi ba dan tsoron irin wannan wulakancin.
Manzon Allah yace, kada ku wulakanta wani abu na alkhairi ko da sakin fuskane idan ka hadu da dan'uwanka.
8. TSANANIN ROWA; Wasu daga cikin mutane idan Allah ya azurtasu da dukiya mai yawa ko wani matsayi zaka same su suna gudun yan'uwansu, ba wai dan girman kai ba a'ah! Domin jin tsoron kada yan'uwan suyi amfani da wannan damar domin bayyanar da bukatunsu zuwa garesu, ko kuma domin kada ya temakesu. Maimakon ya basu dama idan sun ziyarceshi yakarbi bakuncinsu, ya yalwata masu, yayi masu hidima gwargwadon halinsa,ko kuma ya basu uzuri akan abin da ba ya da ikon yi masu amma sai kaga yana kauda kansa, yana kaurace masu domin kada su rokeshi kamar yadda yake riyawa. Mine ne amfanin dukiya ko matsayi da mutum zai samu idan har zai haramta ma yan'uwansa amfana da ita.
9. JINKIRIN RABON GADO; Hakika zaka samu wasu daga cikin mutane suna jinkirta rabon gado kodai  domin kasala, ko kuma wani daga cikin magadan yana da wani mummunan kuduri game da yan'uwansa ko makamacin haka.
Duk lokacin da aka jinkirta rabon gado to kiyayya da adawa zata watsu tsakaninsu domin idan wannan yana da hali ko yafi karfin gadon wani shi kuma yana bukatar raba gadon domin bashi na shi kason ya samu ya bude kasuwanci ko makamanci haka.
10. MUTUWAR AUREN ZUMUNCI; Hakika mutuwar auren zumunci yana haifar da matsaloli a tsakanin yan'uwa na bangaren miji dana bangaren mata musamman in akwai 'ya'ya a tsakaninsu ko kuma saboda wasu matsaloli da suka shafi sakin auren.
11. NISAN WURIN ZAMA DA KUMA KASALAR ZUWA ZIYARA; Akwai daga cikin mutane wadanda idan gidan su ko garin su yana nesa sai a dinga jin kasalar zuwa ziyartarsu, wanda wannan sai ya nisantasu da yan'uwansu.
Nisan wuri bai kamata ba ya zama dalili na yanke zumunta, musamman wannan zamanin da ake da hanyoyin sadarwa daban daban, Allah ya bamu ikon kulawa da zumunta.
12. MAKWABTAKA A TSAKANIN YAN UWA
Da yawa Makwabtaka tana gadar da yankewar zumunta a tsakanin yan'uwa. Umar Dan khaddab yace ku umurci yan'uwanku su dinga ziyartar yan'uwansu amma kada suyi makwabtaka da juna a gidajensu, sannan sau dayawa kusanci a tsakanin gidajen yan'uwa yana haifar da sashen wasu matsaloli wadanda suke haifar da fada a tsakanin 'ya'yansu wanda wannan yakan zarce har zuwa ga iyayensu sai wannan ya haifar da gaba da yanke zumunci a tsakaninsu.
13. KARANCIN KAUDA KAI DA HAKURI A KANSU:
Sashen wasu mutane suna da karancin kauda kai da kuma hakuri akan abin da yan'uwansu suka yi masu. Wasu yan'uwan da an samu sabani tsakaninsu ko wani kuskure da ya afku sai su yanke zumunta, su kaurace ma yan'uwansu.
14. HASSADA:
     Akwai daga cikin yan’uwa wanda Allah yake azirtawa da ilimi ko wani babban matsayi ko dukiya mai yawa sai ka same shi yana yima yan'uwansa hidima yana kyautata ma su, sannan ka samu sashen yan'uwansa suna nuna masa hassada da kiyayya da haifar da rikici tsakanin shi da su, suna cewa duk abin da yake yi masu ba domin Allah yake yi ba.
15. YAWAN WASA:
    Lallai yawan wasa (da sunan wai abokin wasa) yana haifar da mummunan abu a tsakanin yan'uwa domin wani yana iya fadar kalma mai muni ga dan'uwansa ba tare da ya kula da hadarinta ba agare shi, wannan sai ya gadar da kiyayya da gaba a tsakaninsu a sanadiyyar wannan Kalmar.
16. ANNAMIMANCI DA KARBAR GULMA:
    Akwai da yawa daga cikin yan'uwa wadanda dabi'arsu shine yawo da annamimanci a tsakanin yan'uwa domin su kawo rabuwar kai da gurbata tsakanin yan’uwa wanda wannan yana gadar da yanke zumunta, sai dai abu mafi muni shine karbar gulma da yadda da ita shi ke haifar da yankewar zumunta.
17. SHAGALTUWA DA DUNIYA: Shagaltuwa da duniya da son yawan tara abin duniya yana hana mutun sadar da zumunta, da kuma samun lokacin ziyartar yan'uwansa da nuna soyayyar shi zuwa gare su.
18 MIYAGUN HALAYE NA MATAR SHI: wasu daga cikin mutane ana jarabtarsu da muguwar mata mai mummunan dabi’a mai yawan sukar yan'uwansa, bata son yayi mu’amala da yan'uwansa ko wasu, tana dogewa wajan ganin ta raba shi da yan'uwansa tana hana shi ziyartarsu, da sadar da zumunta zuwa garesu, idan yan uwan sa suka ziyarceshi sai tayi ta fushi tana murtike fuska. Bugu da kari akwai mazajen da suke mika ragamar zumuncinsu ga matarsu sai wanda ta yarda dashi yake sadarmawa, wanda bata yarda da shi ba sai ya yanke ma sa.
19. MANTAWA DA WASU YAN'UWA A LOKACIN WALIMA KO WATA HIDIMA:               Hakika wani daga cikin yan'uwa yakan shirya walima ko wata hidima ya gayyaci yan'uwansa sai ya manta da wani ko wasu, sai su da ba’a gayyata ba su munana masa zato, su nuna kamar an wulakantasu an zabi wasu wadanda suka fisu, wannan  nasa ya kaurace masu da yanke zumunta a tsakaninsu.
      Wadannan sune  kadan daga cikin abubuwan dake janyo kauracewa juna da kuma yanke zumunta. Ya kamata a basu kulawa ta musamman da hattara da fadawa cikinsu.
6. ABUBUWAN DA SUKE TAIMAKAWA WAJAN SADAR DA ZUMUNTA
   Akwai abubuwa da yawa da suke taimakawa mutum wajan sadar da zumunta. Ga kadan daga cikinsu kamar haka:
Yin tunanin manya-manyan darajoji da suka tabbata ga mai sadar da zumunta: Lallai sanin kyakykyawan sakamakon aiki da kuma hango kyakykyawan karshe dake samun mai sadar da zumunta yana taimaka maka wajen sadar da zumunta.
Nazari akan mummunan karshe ga mai yanke zumunta: kula da abin da yanke zumunci yake janyowa na bakin ciki da damuwa da hasara, da nadama da sauransu, yana taimakawa mutun ya nisanci yanke zumunta ya kuma sadar da ita.
Neman taimakon Allah: Wannan yana tabbata ne ta hanyar rokon Allah ya datar da kai ya kuma taimake ka bisa sadar da zumunta ga yan uwanka.
Maida mummuna da kyakykyawa: Yana daga cikin abin da yake wanzar da soyayya da kuma kiyaye zumuncin dake tsakin yan'uwa shine musanya mummuna da kyakykyawa. Karbar uzurunsu idan sun yi kuskure da kuma basu uzuri. Yana daga mafi kyawan abin da zan fada acikin wannan shine abin da ya gudana tsakanin Annabi Yusuf da yan'uwansa, hakika sun aikata abin da suka aikata amma yayin da suka bada uzuri ya karbi uzurinsu ya musu rangwame mai kyau, bama wannan kadai ba, har addu’a yayi musu kuma ya roki Allah ya gafarta musu.
Yi musu rangwame da kauda kai daga aibobansu koda basu baka uzuri ba: Wannan yana daga cikin abin da yake nuna karamcin mutum da kuma girman himmarsa, mai hankali tatacce yana yin rangwame da kau da kai daga ambaton aiboban yan'uwansa, baya ambaton laifukan su ko da kuwa basu bada uziri ba.
Kan-kan dakai da saukin ma’amala: Wannan yana daya daga cikin abubuwan da suke sanya soyayyar yan uwa ga dan uwansu kuma su kusance shi.
Nisantar husuma da yawan jayayya da jidali ko fada da yan uwa.
Barin yi masu gori da neman sai sun ran kamaka: ya zama dole mutun ya bar yima yan'uwansa gori idan ya basu wani abu ko ya ziyarcesu, ko ya basu wata kyauta da dai sauransu.
Juriya da daukar duk wani aibantawa daga yan'uwa: Lallai wannan yana daga cikin abubuwa mafi kyau, shine mutun ya kauda kai yayi hakuri da duk wata suka ko tsegumi da yan’uwansa suke mashi, saboda shedan na shige da fice don ganin ya haifar da matsala a tsakanin yan'wa.
Gaugawar aikawa da kyauta idan aka samu sabani a tsakanin yan’uwa: Kyauta tana janyo Soyayya da kaunar juna, sannan kuma tana hana mummunan zato. Saboda Annabi (SAW) yace; ''KUYI KYAUTA KU SO JUNA''
Kwadayin kawo gyara da sulhu a tsakanin yan'uwa idan an samu sabani: Yana daga cikin abin da ya kamata ga duk masu hankali da natsuwa shine su yi sauri su kawo gyara da sulhu idan wata matsala ta taso a tsakanin yan'uwa, domin idan ba’ayi haka ba sharrin yana iya game kowa.
Gaggauta rabon gado: Yakamata idan aka samu rasa rai a gida na uba ko na uwa a gaggauta raba gado domin kowa ya amshi rabonshi, wannan yana kawar da rigima da yawan neman sai anraba kuma wannan yana kara dankon zumunci a tsakain yan’uwa.
Shirya taro na wata-wata ko shekara-shekara: Lallai ire-iren wadannan tarukka suna dauke da alherai masu yawa domin a nan ne za’a san juna asadar da zumunta ga juna, ayima juna wassiya da dai sauransu.
Kaddamar da gidauniya ko kafa asusu: Yana daga cikin abin da ke karfafa zumunta, shine samar da gidauniya ko wani asusu da za'a rika tara kudi duk wata ko shekara domin tallafawa yan'uwa. Da wannan gudunmawa da aka bada za'a iya tallafawa yan'uwa idan wasu matsaloli sun tunkaresu.
Kwamitin masu bada shawara: Yana da kyau a samar da kwamitota wadanda zasu rika bada shawara a karkashin kwamitin zumunta, kamar kwamitin ilimi, Kwamitin sulhu, da sauransu. Ta haka ne kowa zai san hakkinsa da kuma hakkin yan'uwansa a kansa.
Kula da halayansu da ba kowa matsayinsa: Akwai daga cikin yan'uwa wanda yake yarda da kadan daga sadarwar da akayi masa, koda a shekara za’a ziyarceshi sau daya, koda ta wayar salulane, wani ma ko da sakin fuskane da kuma Magana. Akwai wanda bai yarda da komai sai ziyara ako da yaushe. Duka wadannan a kula dasu saboda zumunta ta tabbata.
Sadar da zumunta don Allah: Zumunta Ibada ce mai girma don haka ana sadar da ita ne don Allah shi kadai bashi da abokin tarayya, kamar yadda Allah (SWT) yake fada: ''KUJI TSORON ALLAH DA KUKE ROQON JUNA DASHI, KUMA KU KIYAYE ZUMUNTA. [Nisa'i aya ta 1]
Hakikanin mai sadar da zumunta don Allah shine mai sadar da zumuntar sa ga yan uwanshi ko sun sadar mashi ko basu sadar mashi ba, kamar yadda Bukhari ya ruwaito cikin sahihin littafinsa, manzon Allah (SAW) yana cewa: ''BAI ZAMA MAI SADAR DA ZUMUNTA BA, WANDA SAI AN SADAR MASHI SANNAN YA SADAR, HAKIKANIN MAI SADAR DA ZUMUNTA SHINE WANDA IDAN AN YANKE MASHI SAI YAYI KOKARIN SADARWA''.  [Bukhari 5991]
7. FALALAR SADAR DA ZUMUNTA GA ABOKAN MAHAIFI DA MAHAIFIYA DA YAN'UWAN MATA KO MIJI
An karbo daga Abdullahi dan Umar yace Manzon Allah (SAW) yace: “Lallai mafi kyakykyawan biyayya shine mutun ya sadar da zumunta ga abokan mahaifinsa” (muslim-2552)
An karbo Daga Aisha (R) tace: ''Ban taba kishi da matan Manzon Allah (SAW) ba irin yadda nike kishi da khadija (R), ban taba Ganinta ba, sai dai Annabi yana yawan ambatonta. Sau da yawa yakan yanka akuya ya raba ya aikawa abokanta, da yawa nikan ce masa kamar babu wata mace a duniya sai khadija! Sai yace “lallai Khadija ta kasance kaza-kaza (ya lissafa abubuwan kirki na ta da yawa) sannan diyana gaba daya duka ita ta haifesu”. (Buhari 3818-muslim 2435).
8. YAYA ZA’A MAGANCE MATSALAR YANKE ZUMUNCI
     Bayanai sun gabata a baya dangane da matsayin yanke zumunta da cutarwarsa ga mutun da irin sabubban da ke janyo yanke zumunta idan abin ya kasance haka lallai ya zama wajibi ga mai hankali ya tsoraci hadarin yanke zumunta, kuma ya nisanci dukkan sabubban da zasu ja shi zuwa ga yanke zumunta.
Abin da ya cancanta a gare shi shine ya sadar da ita dukkan sadarwa, ya kuma san girman sha'anin zumunta yayi kirdadon sabubban da zasu sa shi sadar da ita, ya kiyaye dukkan ladubban da ya kamata ya kiyaye, tare da yan'uwansa.
YANKE ZUMUNTA YANA DAGA CIKIN ALAMOMIN TASHIN ALKIYAMA.
An karbo daga Abdullahi ibn Amru bn As, Yace Manzon Allah (SAW) yace: ''kiyama ba zata tsaya ba har sai alfasha, da neman aikata Alfashar ya bayyana da yanke zumunta da mummunar makwabtaka”. (Ahmad ya ruwaito)
Hakika labarin da Annabi ya bada ya tabbata, domin Alfasha ta watsu a tsakanin mafi yawa daga cikin mutane, ba tare da sun damu da tattauna abubuwan da suke aikatawa na laifukka ba, basu kuma damu da mummunan sakamakon da zasu hadu dashi ba a dalilin yanke zumunta.
Zaka ga dan'uwa ba ya sadarwa ga dan'uwansa sai yankewa da juya baya. Watanni da shekaru suna shudewa alhali suna zaune cikin gari guda basu ziyartar juna, basu sadarma juna, lallai babu shakka wannan yana nuna raunin imanin mutane.
KAMMALAWA
Muna godiya ga Allah (subhanahu wata`ala) wanda daga cikin ni`imominsa ne ya bamu damar kammala wannan littafi mai albarka, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad(salallahu alaihi wasallam) wanda yayi addu`ah da cewa wanda ya sadar da zumunta Allah ya sadar dashi da rahamarsa, wanda kuma ya yanke zumunta ka yankeshi daga samun rahama. ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU

07059593000

Thursday, 12 December 2019

TASBIHIN MAMU IDAN LIMAN YA KARANTA SURATUL A'ALA A CIKIN SALLAH

📚📚📚📚📚📚📚📚📚📚
*KO YANA HALASTA MAMU YAYI TASBIHI A LOKACIN DA LIMAN YA KARANTA SURATUL A'ALA A CIKIN SALLAH???*
📚📚📚📚📚📚📚📚📚📚

Rubutawa: *Abu Hussain, Abdulhameed As-safrawy*

Fassarawa: *ABU-SINAN ATS~TSAMAWY*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da aminci su kara tabbata ga farin jekada, Annabi Muhammad S.AW, da iyalan gidansa da sahabbansa baki daya.
Bayan haka:

Bayan tambaya da mutane suka yawaita akan wannan matsalar naga ya dace in fassara wannan amsa da babban Malami ABU HUSSAIN ya ba wani Wanda yayi mashi irin wannan tambayar amsa a 04/09/2011 kusan shekaru tara kenan da suka gabata.
Kai tsaye ga hujjojin da malam ya kawo akan halascin hakan Daga bakin magabata
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

*IMAMUS SUYUDY (RH) A CIKIN*
الدر المنثور
Ya kawo hadisi Wanda imamu Ahmad da Abu daud da ibn Murdawaihy da imamul Baihaqy a cikin سنن nashi, Daga ibn Abbas(R.A): Manzon Allah s.a.w ya kasance idan ya karanta سبح اسم ربك الأعلى yana cewa: سبحان ربي الأعلى

Haka Abdurrazak ya fitar a Musnad nashi, da ibn Abi Shaibah, da Abd bn Humaid, da ibn jarir, Daga ibn Abbas: ya kasance idan ya karanta: سبح اسم ربك الأعلى yana cewa: سبحان ربي الأعلى

Haka ibn Abi Shaibah da Abd bn Humaid sun fitar Daga Aliyu bn Abi Dalib (R.A) ya kasance idan ya karanta سبح اسم ربك الأعلى sai yace: سبحان ربي الأعلى Alhali yana cikin Sallah, sai aka tambayeshi: shin anyi kari ne a cikin Qur'ani? Sai yace: A'a, mun kasance ana umurtarmu da fadar hakan, sai muke fada.

Haka Sa'eed bn Mansur da Abi Shaibah da Abd bn Humaid da Imamul Munzary sun fitar Daga  Abi Musa Al-Ash'ary(R.A) cewa Abi Musa Al-Ash'ary ya karanta سبح اسم ربك الأعلى a sallar Juma'ah sai yace: سبحان ربي الأعلى

Haka Nan Sa'eed bn Mansur da Abd bn Humaid da ibn Jarir da ibnul Munzary da imamul Hakim(kuma ya inganta) Daga Sa'eed bn Jubair yace: Naji Ibn Umar yana karanta: سبح اسم ربك الأعلى sai yace: سبحان ربي الأعلى sai yace: wannan itace Qira'ar Ubayyu ibn Ka'ab

Haka ibn Abi Shaibah da Abd bn Humaid Daga Abdullahi bn Zubair, cewa: Abdullahi bn Zubair ya karanta سبح اسم ربك الأعلى sai yace سبحان ربي الأعلى Alhali yana cikin Sallah.
Haka Nan Abd bn Humaid ya fitar da wani hadisin Daga Dhahhak cewa: yana karanta SURATUL A'ALA, Sannan yana cewa duk Wanda ya karanta ta ya fadi: سبحان ربي الأعلى

Haka Nan Abd bn Humaid ya fitar Daga Qatada, yace: Manzon Allah S.A.W ya kasance idan ya karanta SURATUL A'ALA yana cewa: سبحان ربي الأعلى

Haka Nan Ibn Abi Shaibah ya fitar daga Umar, ya kasance idan ya karanta: سبح اسم ربك الأعلى yana cewa سبحان ربي الأعلى

Ibn Katheer a cikin Tafsirinsa yake cewa:
Imamu Ahmad yace, Waqee' ya bashi labari, Isra'il ya bashi labari, Daga Abi Ishaq, Daga Muslim Al-bad'een, Daga Sa'eed bn Jubair, Daga ibn Abbas: Manzon Allah S.A.W ya kasance idan ya karanta سبح اسم ربك الأعلى yana cewa: سبحان ربي الأعلى

Ibn jarir Ad-dabary(R.H) yace: ibn Humaid ya bani labari, Hakam ya bani labari, Daga Anbasah, Daga Abi Ishaq Al-hamdany: Ibn Abbas ya kasance idan ya karanta: سبح اسم ربك الأعلى yana cewa: سبحان ربي الأعلى
Haka idan ya karanta: لا أقسم بيوم القيامة idan ya Kai karshen ta أليس ذلك بقادر على أن يحيي الموتى
Sai yace: سبحانك وبلى

Bayan wadannan akwai wasu manyan malaman musulunci da dama da suka kasance suna aikata wannan Sunnah

Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albany(R.H) a cikin Sahih Abi daud(4/39)
Daga ibn Abbas: Manzon Allah S.A.W ya kasance idan ya karanta سبح اسم ربك الأعلى yana cewa: سبحان ربي الأعلى

Albany yace: Hadisi ne ingantacce, imamul Hakim ma ya inganta shi akan sharadin Buhari da Muslim.

Da wannan zamu fahimci kenan ba laifi bane don liman ya karanta SURATUL A'ALA mamu suyi Tasbihin da ya tabbata, kamar yadda hadisi ya tabbata akan hakan Daga bakin Manzon Allah S.A.W , kuma sahabbai suka kasance suna aikata wannan Sunnah.

Allah ya kara fahimtar damu sunnar Annabi Muhammad S.A.W, ya bamu ikon aiki da ita.

*Hashim Siraj Uba Ats~tsamawy (ABU-SINAN)*
+2349030201868

15/04/1441H
12/12/2019

https://fb.me/abbansinan

Saturday, 7 December 2019

010 KARATUN HADISI...

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*KARATUN HADISI DA AIKI DASHI SHIKE KAWO ZAMAN LAFIYA GA MUSULMI*
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲

DAGA ZAUREN: *MU KYAUTATA NIYYA*

_Fitowa Na farko 010_

*SUNNONIN ALWALA*

🔸 *SALLAH RAKA'A BIYU BAYAN ALWALA*

Manzon Allah S.A.W yace: *_((Duk Wanda yayi alwala irin wannan alwalar tawa, sannan yayi sallah raka'a biyu ba kayi tunanin komai ban cikin zuciyarka, an gafarta mashi abunda ya gabatar na zunubinshi))._*
[Bukhari 539, Muslim 159: Daga Humraan maula Uthman R.A]

DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA* NA MAZA KO NA MATA SAI A TUNTUBI WADANNAN NUMBERS:
+2348064734911
+2349030201868

https://fb.me/abbansinan

009 KARATUN HADISI

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*KARATUN HADISI DA AIKI DASHI SHIKE KAWO ZAMAN LAFIYA GA MUSULMI*
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲

DAGA ZAUREN: *MU KYAUTATA NIYYA*

_Fitowa Na farko 009_

*SUNNONIN ALWALA*

🔸 *TAKAITA RUWA*

*_Daga Anas (R.A) yace: ((Manzon Allah S.A.W ya kasance yana wanka da sa'i daya ko mudu  5, yana alwala da mudu daya))._*
[Bukhari 737, Muslim 201]

DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA* NA MAZA KO NA MATA SAI A TUNTUBI WADANNAN NUMBERS:
+2348064734911
+2349030201868

https://fb.me/abbansinan