Friday, 17 February 2017

Malamai

DUK WANDA YA CUTAR DA MALAMAI; TO MANZON ALLAAH YA CUTAR.   Babban malami daga cikin Tabi'ai mai suna Ikrimah (rahimahullaah) yana cewa:   إيّاكم أن تؤذوا أحدًا من العلماء، فإن مَن آذى عالمًا فقد آذى رسول الله – صلى الله عليه وآله وسلم – لأنهم حملة كلام الرسول – صلى الله عليه وآله وسلم – الذائدون عن حياضه، المنافحون عن كلامه، رحمهم الله تعالى أجمعين”  Kashejinku! Kada ku cutar da wani daga cikin malamai, domin duk wanda ya cutar da malami to tabbas ya cutar da Manzon Allaah(s.a.w), domin malamai sune ke 'dauke da maganganun Manzon Allaah, masu kore duk wata shubha da bid'a daga tafkinsa, masu kare maganarsa(Rahimahumullaahu).   Sannan yana daga cikin cutar da malami: - Ambatonsa da sharri.  - Fadi ko yayata abunda yike tattare dashi wanda bayaso.  - Zaginsa kaitsaye ko a fakaice.  - Bid'antar dashi ba tareda dalili da shari'a ta amince dashi ba.  - Kuskusrantar dashi ba tareda dalili 'kwa'kkwara a shar'ance ba.  - Yin masa 'kage, 'karya ko 'kazafi.  - Sakin baki akansa.  - Fitar dashi daga da'irar sunnah ko musulunci bakidaya ba tareda dalilin a shar'ance ko wanda bai 'daukan tawili ba. D.s.   Shi yasa yakamata mutane su kame bakinsu da harsunansu daga fadin munanan maganganu akan malamai, domin duk mai 'bacin malami to gubace yike sha, kuma ana ji masa tsoron muguwar 'karshe, sannan kuma bashine yike ci wanda zai biyashi anan duniya, idan kuma akaje lahira a kwashi ladansa aba wannan malamin, ko a dauki zunuban malamin a dan'ka masa, karshe kuma a jefa shi a wutar Jahannama.  MUNA ROKON ALLAAH YA KAREMU YAKUMA 'KARA TABBATAR DAMU AKAN HANYA MADAIDAICIYA.  Dan'uwanku: Abdullahi Almadeeniy K

No comments: