🎤🎤🎤🎤🎤🎤🎤
*NASIHARMU TA YAU DAGA GROUP DIN MUKYAUTATA NIYYA!!!*
🎙🎙🎙🎙🎙🎙🎙
*WANDON MUMINI RABIN KWABRI NE!!!*
```Hadissai masu tarin yawa sun tabbata daga Manzon Allah s.a.w dangane da dangale tufafi ga maza. Zamu kawo kadan daga cikinsu domin fadakar da Al'umma.```
*عن ابن عمر رضى الله عنهما أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: "من جر ثوبه خيلاء لم ينظر الله يوم القيامة(متفق عليه)*
*_Daga ibn umar (Allah ya yadda dasu) manzon Allah s.a.w yace; duk Wanda ya saki tufafinsa yana jansu a kasa saboda German kai! Allah bazai kalleshi ba a ranar gobe kiyama._*
*وعن أبي هريرة رضى الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: ما أسفل من الكعبين من الإزار ففي النار. (رواه البخاري)*
```Daga Abi hurairah(R.A) daga Annabi Muhammad s.a.w yace sashen tufafin da aka saki ya wuce idon sawu to zai shiga wuta. Har ila yau akwai wani hadisin Na Abi hurairah(R.A) yace: manzon Allah (s.a.w) yace;...Allah (s.w.t) ba ya amsar sallar mutumin da ya saki tufafinsa kasa.```
*Saboda haka duk Wanda ya karyata wadannan hadissan ko kuma yayi izgili ga masu dage tufafinsu, Dan fodio yace kafiri ne! Kuma wallahi yana da hujja. Shi kuwa imam Ahmad bin hambal(imamu Ahlus Sunnah waljama'ah) cewa yayi;*
*من رد حديث رسول الله صلى الله عليه وسلم فهو شفا هلكة*
*wato duk Wanda kaga yana Raddi ga hadissan Manzon Allah s.a.w! Toh yana gefen halaka.*
```Saboda haka yan uwa yan dariku kuyi hattara da izgilanci ga hadissan Manzon Allah s. a.w.
Manzon Allah s.a.w yayi bayani yadda ya kamata musulmi ya sanya tufafinsa inda yace; Tufafin musulmi wando ko Riga ya tsaya tsakanin kwabrinsa na kafa ko kuma tsakanin idon sawu da gwiwar kabrinsa na kafa. Ko kuma yace "can kasan idon sawu an kaddara mashi shiga wuta. Wani wurin yace; Allah bazai kalli mutumin da ya saki tufafinsa ba don German kai.
Wadannan hadissai na sama sunyi nuni a fili cewa irin dinkin da samari keyi a wannan zamani Wanda rigarsu ko wandonsu ya wuce idon sawu, musulunci ya haramta irin wannan dinkin.! Har ma idan Anyi sallah da irinshi sallar mutum Rana da rauni, saboda haka yana da matukar muhimmanci muyi kokarin gyarawa don mu samu Rahamar ubangiji.```
*_Abdullahi bn umar(R.A) yace; wata rana na wuce gaban Manzon Allah s.a.w Alhali tufafi na suna reto(Jan kasa) sai Manzon Allah s.a.w yace" Abdullahi ka ja tufafinka sama! Sai na ja tufar sama kadan. Sai Manzon Allah s.a.w yace; ka kara jawo tufar ka sama kadan! Sai na kara Jan tufar sama kadan. Abdullahi bn umar yace tun daga Ranar na rinka sanya tufafi sama. Wani daga cikin kabilarsa(Abdullahi) ya tambayeshi sama kamar ya? Sai nace tsakanin idon sawu da gwiwar kafa. Saboda haka duk Wanda keson muwafaka da sunnah shine wando ko Rigarsa kada su wuce idon sawu._*
*Allah muke roko ya tabbatar damu akan sunnar Annabi Muhammad s.a.w*
Ga masu bukatar shiga group din *MUKYAUTATA NIYYA* kai tsaye zasu iya danna wannan link dake kasa domin shiga, sai dai duk Wanda ya karya dokar group, Admins zasuyi waje dashi.
https://chat.whatsapp.com/2dm86OqUUNB69euFNsdOjM
Allah ya bada ikon kiyayewa.
Copyright©
```Hashim Surajo Uba Tsamiya
08064734911```
No comments:
Post a Comment