Wednesday, 19 April 2017

LAA'ILAHA ILALLAH

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*BAYANIN MA'ANAR LAA'ILAHA IL-LALLAHU!!!*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*_001_*

_Rubutawa:_ *Hashim Suraj Uba Tsamiya(ABU SINÃN)*

*بسم الله الرحمن الر حيم*

*الحمد لله رب العالمين، وصلى الله وسلم وبارك على نبينا محمد وعلى آله وصحبه أجمعين.*

```Da farko ya kamata musan cewa ita wannan Kalmar itace ke rabewa tsakanin musulmi da wanda ba musulmi ba!
Wannan Kalmar akan ta aka aiko dukkan Annabawa!
Itace Kalmar dake tabbatar da tsoron Allah na hakika!
Itace igiyar nan mai karfi, wacce duk Wanda ya riketa zata kaishi Aljanna!

Abin lura: Wannan Kalmar ba fadarta a baki ko da halshe tare da jahiltar ma'anarta ke sanya musuluncinka ya inganta ba!

Domin kuwa munafukai suna fadarta a bakunansu, amma kuma Allah yace" suna chan kasan wuta" a suratun nisa'i aya ta 145, tare da cewa suna Sallah suna sadaka, watakila har wurin wa'azi suna halarta.

Abunda ya kamata ga duk wanda ya fadeta, toh ya san ma'anarta har a zuciya ya kudurceta(ma'anarta, sharuddanta, falalarta, da abunda ta kunsa na tauhidi da akeeda) dole ne kaso Kalmar, kaso mai son Kalmar, dole ne ka yaki duk mai adawa da Kalmar ko mai saba mata.

Ita Kalmar LAA'ILAHA- IL-LALLAH! korewa ne da kuma tabbatarwa. Kore ilahantaka ga duk wani wanda ba Allah ba! Koda kuwa Manzo ne, ko Annabi, ko Mala'ika, ko wani mutumin kirki, ko gausi ko waliyyi koma Waye!  Tare da tabbatar da ilahantaka ga Allah shi kadai.

Na daga cikin mas'alolin jahiliyya wanda Annabi Muhammad s.a.w ya saba musu; Bautar mutanen kwarai ta Hanyar Neman biyan bukatunsu da nufin su nema musu ceto a wurin Allah, saboda zatonsu akan cewa Allah na son hakan. Kamar yadda Allah s.w.t yake cewa;
*ويعبدون من دون الله ما لا يضرهم ولا ينفعهم ويقولون هؤلاء شفعؤنا عند الله.* {يونس ١٨}

Ma'ana: "Suna bautar wani wanda ba Allah ba, Wanda bai iya cutar dasu, kuma bai iya amfanar dasu, har ma zakuji suna fada cewa wadancan sune masu cetonmu a wurin Allah"

Wannan ayar in muka lura zatayi aiki ga masu Dariku da yan shi'ah! Saboda suma zakuji suna fadar irin wadannan kalmomin, bari ma, wani lokaci nasu sunfi muni da hadari.

Muna rokon Allah s.w.t ya tabbatar damu akan tauhidi da akeeda Allah ka kara mana Ikhlasi.

Wannan mukaddima ce, amma bayanin zaizo a fitowa ta gaba insha Allahu.

Copyright©
Hashim Suraj Uba Tsamiya(ABU SINÃN)
08064734911```

http://abbansinan.WordPress.com

http://hashimtsamiya.blogspot.com

http://abusinan.blogspot.com

atstsamawy@gmail.com

No comments: