🌺🌺🌸🌺🌸🌸🌺🌺🌸🌺
```ABUBUWA GUDA (20) DUK WANDA ALLAH YA ALBARKACE SHI DA RAYUWA TARE DA DAYAN MAHAIFANSHI KO DUKAN SU YA KAMATA YA KIYAYE...!!!
🌺🌺🌸🌸🌺🌸🌸🌺🌺🌺
Dukkan yabo da jin jina da girmamawa sun tabbata ga Allah (S.W.T) wanda ya gwama/hada kadaitashi da biyyaya ga iyaye. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta wanda yace “Yardar Allah na tare da yardar iyaye, fushin Allah na tare da fushin iyaye”, da iyalan gidansa da Sahabbansa da wadanda suka biyo su da kyautatawa har zuwa ranar karshe.
1⃣Yi masu biyayya da da’a ga duk abinda suke so ko suka yi umurni in bai saba ma shari’a ba.
2⃣Nisantar duk abinda zai fusata su ko ya tunzura su.
3⃣Ka tsare mutuncin su da girmama su a idon jama’a.
4⃣Yi kokari ka yi duk abinda ka san yana faranta ransu koda basu saka ba.
5⃣Ka karba kiransu cikin murmushi, kaje zuwa aikin da suka sanya ka cikin nishadi.
6⃣Kada kayi jayayya dasu ko da a cikin maganar su basu da gaskiya (a maimakon haka ka samu wani lokaci na musamman na lurar dasu kuskuren su a cikin hikima).
7⃣Ka saurare su idan suna Magana kuma kada ka daga masu murya.
8⃣Ka taya su aiki ko da basu neme ka ba.
9⃣Idan dayansu baya da lafiya ka himmatu wajen jinyarsa da kanka.
🔟Bayyana ladabi garesu ko a wurin zama ko tafiya (kada ka saki jiki ko ka mike kafafu ko ka haura sama da su ko kayi tafiya gabansu ta yadda za su ji lallai basu da wani matsayi na girmamawa a gurin ka).
1⃣1⃣Kada ka taba damuwa ko jin ciwon bayyana cewa iyayenka ne (kayi alfahari dasu koda basu da wata daukaka wadda ake kuri da ita).
1⃣2⃣Kada ka bari bukata ta kamasu har su kai ga rokon ka. Ka wadatasu da gwargwado abinda zasu ji dadin rayuwa har su taimaki wani matukar kana da iko.
1⃣3⃣Nuna kulawa da su ta fuskar ziyara koda a wuri daya kuke, idan kuma ba a wuri daya kuke ba to ka ware wani lokaci da zaka rinka tuntubar su, kana samun lokacin fira das u, kana sauraren kokensu da biyan bukatar su.
1⃣4⃣Rinka nuna musu godiya, da cewa duk abinda ka yi musu baka biyasu ba a kan renonka da sukayi.
1⃣5⃣Kada ka bukacesu da abinda basu son baka.
1⃣6⃣Kada ka fifita iyalanka ko ‘ya’yanka akan su.
1⃣7⃣Ka boye masu mafi yawan kyautatawar da ke tsakaninka da iyalanka domin gudun shedan ya sa masu kishi a kan wannan.
1⃣8⃣Idan rashin jituwa ta shiga tsakanin su da iyalinka kada ka taba goyon bayan iyalanka a fili koda su keda gaskiya.
1⃣9⃣Rinka neman addu’arsu kana fada masu bukatunka tare da sanar dasu cewa, addu’arsu tafi ta kowa kima da saurin karbuwa.
2⃣0⃣Yawaita neman sa albarkarsu a koda yaushe.
COURTESY:
Shababu Ahlissunnah Waljama’ah Tsafe
ZAMFARA STATE
08064607294, 08139348898
P.R.O SHABABUS-SUNNAH TSAFE```
No comments:
Post a Comment