Monday, 2 October 2017

FACEBOOK SECURITY

YAYA ZAN KARE FACEBOOK ACCOUNT DINA
DAGA BLOCKIN KO HACKERS??

Daga Dan uwa: Basheer Journalist Sharfadi Kano.


Assalamu Alaikum warahmatullah,
Kamar yadda muka tattauna jiya kan wadannan
matsalolin da suke faruwa na yunkurin yin awon
gaba da rayukan facebook, to cikin ikon Allah
yau zamu tattauna ne akan wancan take da na
bayar a sama, inda zan kawokadan daga
abubuwan da ya kamata mu sani kuma mu
kiyaye game da account din mu, sai a biyo mu,
1. Yana da kyau ka dinga canja password din ka
akalla bayan sati daya (1) zuwa sati biyu,
sannan wajen canjawar a guji sanya 123456 ko
sunan ka, ko kuma lambar wayarka, sunan
budurwar ka, ko unguwar ka, a’a yana da kyau ka
sanya harufa da kuma lambobi, kai harma da
symbols kamar @”-+, sannan kada ka yarda ka
sanar da wani wannan password din naka,
Sannan a kula kada kayi amfani da password
guda daya a dukkan abubuwanka misali a Email
dinka da kuma facebook din ka da sauran abinda
kake budewa duk su zama iri daya domin hakan
zai baiwa wasu damar yin awon gaba da account
dinka,
2. sanya Karin email akan account dinka a kalla
ina bada shawarar kayi adding email kamar guda
uku (3) akan account dinka kaga kana da
cikakken iko akan account dinka duk wani motsi
ko wani yunkuri da akayi kai tsaye zaka gani,
Sannan a setting na email din ka mayar dashi
babu wanda zai iya ganin su sai kai kadai “only
me” a yaren facebook,
3. Sannan lambar wayarka ta zamo tana aiki
kana samun sakonni acikin ta da yawan mu
lambobin da muka bude facebook dasu mun rasa
layukan, amman har yanzu mun gaza cire lambar
daga kan fb din mu canza ta da lambar da muke
da ita a yanzu, rashin yin hakan zai bamu
matsala don haka idan kasan ka rasa layin ka to
ka canza lambar layin ka na yanzu domin ka
cigaba da samun sakonnin facebook,
4. Ka sanya “Login Approval” a account din ka
yadda zaka sanya shine ka bi wannan hanyar
kaje :Home -> Account Settings -> Security ->
Login Notification sai ka mai da shi “Enable”
Wannan zai baka damar jin duk wani motsi na
account din ka sannan idan zakayi login dole sai
an turo maka da code ko kuma kayi approving ta
wayarka idan android ce, sannan anan bangaren
zaka iya samar da “code generator” ta yadda
zaka samar da wani code wanda kai ka dai ne ka
sanshi idan kazo yin login bayan password to shi
ma zaka saka shi,
5. Sannan zaka iya zabar wasu amintattu daga
friend dinka kamar Grantor kenan ka sanya su,
suma zasu iya baiwa account din ka kariya,
6. Ka samar da tsayayyiyar browser da kake
hawa facebook, kada ka zama yau ka ari wayar
wancan ka hau gobe ka ari ta wancan, sannan a
daina yin saving din password a browser saboda
zaka iya yadda wayar ka, ko kuma a dauke maka
ita, mu samman a wannan lokacin da ake yawan
kwace kaga wani zai iya hawa, sannan facebook
zasu iya yi maka blocking saboda yawan yin
hakan,
7. Ka dinga yin log out duk sanda ka hau idan
zaka sauka,
8. Kada ka baiwa wani ko wata bayanan ka na
yin login a account din ka ko wani web site,
9. Kayi tunani kafin ka danna link, zaka ga ance
ka danna link, to ka fara yin tunani kafin ka
shiga, misali ace ka danna kaga abinda zai faru
ko makamantan hakan, ko idan ka shiga sai kaga
ance ka saka password dinka to duk irin wannan
sai a kiyaye,
10. Kayi login a www.facebook.com ka wai
www.fb.com kada kayi login a facebook ta kan
wani site daban ba wannan ba, ko application
wanda ba ingantacce ba,
11. Ka dinga yin updating din browser din ka ko
application din ka,
12. ka dina installing anti virus a wayar ka ko a
computer da kake amfani da ita,
13. ka daina yawan tura Requesting ko yawan
yin accepting ka kula wajen karbar wanda baka
san shi ba, yana da kyau ka duba propile din sa
kafin kayi accepting din sa,
14. Ka daina yawan yin sharing na wani link da
baka tantance shi ba,
15. ka daina hade facebook account dinka da ko
wane shafukan internet, zaka ga da yawa daga
website ana yin register din su ta facebook mai
makon kayi da email sai kayi da facebook shima
wannan ya kamata ayi tunani sosai kafin
aiwatarwa,
16. Kada ka yi wani psoting wanda ya sabawa
wadansu to idan suka yi ta yin reporting din sag
a facebook su ma zasu yi blockin din account din
ka,
Bara na dakata anan naga rubutun zaiyi tsayi da
yawa,
Naku: Basheer Journalist Sharfadi
Domin bada shawara ko Karin haske za’a iya
tuntuba ta a:
www.facebook.com/journalistsharfadi
Phone: 09035830253
Email: bjournalist55
# BasheerSharfadi #Facebook # SocialMedia

No comments: