Sunday, 24 December 2017

AN GABATAR DA DAURA KASHI NA FARKO MAI TAKEN; BAYYANA KIRKIRARRUN KARYA DA AKE JINGINAWA IBN TAIMIYYA AKAN HALASCIN MAULUDI.

🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌
*MASJID ABU-HURAIRAH YAR YARA TSAFE*
🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌

```AN GABATAR DA DAURA KASHI NA FARKO MAI TAKEN; BAYYANA KIRKIRARRUN KARAI-RAYI DA AKA JINGINA GA SHEIKHUL ISLAM IBN TAIMIYYA AKAN HALASCIN MAULUDI...

   Daurar wadda Sheikh Sani Liman (ABU HURAIRAH) Tsafe ya gabatar,  bayan Malam yayi khudubatul haaja, yayi sallama ga Yan uwa musulmai da suka taru a wajen.

  Sheikh sani Liman ya cigaba da cewa; abunda ya hada mu a wannan waje shine domin mu tattauna abunda ya shafi bukukuwan maulidi, muna yima Yan uwa musulmi maraba da karba wannan kira da sukayi, suka nuna cewa su lallai su mazajen sunnah ne, masu jira ace Sunnah tayi kira domin su amsa kiran.

  Sheikh Sani ya cigaba da cewa; Yan uwa kafin mu shiga cikin wannan littafin akwai wata shimfida da nikeson in gabatar, domin ta zamo mana haske a tafiyarmu ta Sunnah...

   Yan uwa musulmi ahlus-sunnah da muka taru a wannan masallaci bisa wannan muna saba ya kamata mu San cewa shi Ahlus-sunnah duk inda ya samu kansa to wajibi ne gareshi yayi fada da Bidi'ah!

Sheikh yace, shi fada da Bidi'ah ana yinsa ne ta hanyoyi guda biyu.

*HANYA TA FARKO:*
Fadakar da al'umma akan Bidi'ah a kowane lokaci, a kowane zamani, yadda dan Bidi'ah baiji kunyar jajircewa wajen dabbaka bidi'ashi ba, toh ai mu yafi cancanta ace mun jajirce wajen tabbatar da Sunnah, kada mu dauka cewa bidi'ar mauludi ita kadai ce zamu tsaya akanta! A'a Na daga cikin bidi'oin da ya kamata muyi fada dasu; Fadar ''SADAKHALLAHUL-AZEEM" bayan kammala karatun Qur'ani! Wannan Bidi'ah ne!!!   Na gaba shine; Fadar "AMIIN WA'ALAIKUMUS-SALAM" a wajen maida sallama, kara AMIIN Bidi'ah ne!!! da wasu daga cikin bidi'oin da basu da bambanci da bidi'ar mauludi.

Sheikh Liman yace ya kamata mu zauna mu zakulo wadannan bidi'oin domin a bayyanawa al'umma, kamar yadda babban Malami Sheikh Usman bin fodiyo ya rubuta littafi akan irin wadannan bidi'oin.

Sheikh Sani Liman ya cigaba da cewa; ba wai dole sai a irin wannan zaman bane zamu rika yakar Bidi'ah! Muna da masallatai, da makarantun islamiyyu da sauran wurare, idan ya zamana cewa ana yima bidi'ah tsirara a irin wadannan wurare a koda yaushe, babu shakka ma'abota Bidi'ah zasu ji tsoron  bayyana bidi'arsu, kuma zasu rikice.

*HANYA TA BIYU:*
hanya ta biyu da ake yakar bidi'ah shine riko da Sunnah, da dabbaka Sunnah, saboda idan Ahlus-sunnah mukayi rauni wurin riko da Sunnar Manzon Allah s.a.w, bamu koyi dashi a wajen maganganunmu da mu'amalarmu da wajen sutura da kasuwanci da sauransu, toh an samu matsala!  Ashe kenan yana daya daga cikin hanyoyin fada da bidi'ah raya Sunnah, saboda Annabi ya kira raya Sunnah a matsayin raya addini ne, saboda haka ya zama wajibi akan Ahlus-sunnah ya raya Sunnah! Abar jin kunyar aje gemu ko dage wando da sauransu.

Sheikh Liman yace, wannan ita ce wasiyya ta gareku...


   Sai Malam ya shilla akan maganar abunda ya taramu a wajen, Malam ya sukwane akan maganar bidi'ah, har ya kawo hadissai dake nuna cewa wajibi ne mu kyamaci bidi'ah, sannan ya kawo mana ayoyi dake nuna wajabcin biyayya ga manzon Allah s.a.w, ya kuma kawo mana manyan malaman musulunci da sukayi suka akan mauludi suka ce ba addini bane.

Bayan Malam ya gama wannan jawabin sai yace kai tsaye sunan littafin da zamu karanta;
تبيين كذب المفتري بما نسب إلى شيخ الإسلام ابن تيمية من استحسان الاحتفال بالمولد النبوي صلى الله عليه وسلم.
Wanda babban malaminmu na jahar zamfara Sheikh Muhammad kabir ibn umar Al-marwy(ABU SUMAYYA) ya rubuta.

Daga nan sai sheikh Sani Liman yayi mana bayanin irin kokarin da marubucin littafin yakeyi wajen baiwa sunnar Annabi kariya, da wasu ayyukan da yake yima Sunnah, malam yayi mana bayanin marubucin littafin sosai, inda har ya fada mana wasu daga cikin littafan da ya rubuta.  Na daga cikin littafan da malamin ya rubuta wanda sheikh sani ya ambata akwai;

√ TUHUFATUL AKHYAAR, BIMA'ARIFATI MALA ASLA LAHU MINAL-AKHBAR.

√ MASHAYIKHIS-SUFIYYA YAKULUNA ALLAHU FISSAMÃ(malaman sufaye sun tabbatar da cewa Allah yana sama)

√ ITTIHAFIL MU'UMININA BIT-TAKHRIJI AHADISI BUGYATUL MUSLIMEENA.

√ AHSANUL-AQAWEEL FI ISBATIS- SUNNIYATI LUBSIS-SARAWEEL, WAR-RADDU ALA MAN ZA'AMA ANNAHU BIDI'AH(wannan raddi ne ga katon dan Bidi'ah Abduljabbar akan littafin da ya rubuta ya nuna cewa sa wando Bidi'ah ne).

√ KASHFUZ-ZUNUN FI TAFSIRI QAULIHI TA'ALA;  ﻗُﻞْ ﺑِﻔَﻀْﻞِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَﺑِﺮَﺣْﻤَﺘِﻪِ ﻓَﺒِﺬَٰﻟِﻚَ ﻓَﻠْﻴَﻔْﺮَﺣُﻮﺍ ﻫُﻮَ ﺧَﻴْﺮٌ
ﻣِّﻤَّﺎ ﻳَﺠْﻤَﻌُﻮﻥ

Da wasu littafai kusan sha uku da Malam ya ambata kuma ya ba daliban ilimi shawarar su nemesu domin amfanuwa.
Daga nan ne Sheikh yaja burki saboda lokaci da yayi halinsa, malam yace a kashi na biyu zamu shiga cikin littafin ne kai tsaye.```

Ga masu bukatar audio Na wannan Daura suna iya garzayawa a dandalin sunnah Na darulfikr.com a folder Malam zasu sameshi a cikin muhadara insha Allahu.

Allah ya sakawa marubucin wannan littafi da Alkhairi dashi da Sheikh Sani Liman da ya zakulo littafin domin fadakar da al'umma.

Sai mun hadu a fitowa Na gaba insha Allahu.



*MASJID ABU HURAIRAH TSAFE SOCIAL MEDIA COMMITTEE*
+2348064734911

05-04-1439AH
24-12-2017AC

No comments: