Friday, 22 December 2017

HUDUBAR JUMU'AH MAI TAKEN, HUKUNCIN BIKIN KIRSIMETI DA SABUWAR SHEKARA A MUSULUNCI.

FASSARAR KHUDBAR JUMU'AH DAGA MASJID ABI HURAIRA AREA 2 TSAFE JIHAR ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

Bayan mukaddimah........

Yan uwa musulmi masu albarka a yau khudbar mu zata yi magana ne game da hukuncin #BIKIN_KIRISMETI_DA_SABUWAR_SHEKARA_GA_MUSULMI

Yan uwa musulmi masu albarka mu girmama ubangiji Allah kuma mu gode masa game da ni'imar shi garemu ta musulunci, Kuma mu gode masa bisa ga alkawarin sa na kare addinin musulunci daga duk wani sharri!

Yan uwa musulmi masu albarka hakika riko da addini dole kuma wajibi haka ma dole rokon ALLAH mutun ya zama musulunci shine addinin shi har zuwa karshen rayuwar shi.

Hakika Allah madaukakin sarki ya zaba mana musulunci ya zama addinin mu kamar yadda yake fada cewa "NA ZABA MASU MUSULUNCI YA ZAMA ADDININ KU"

Hakika shi addinin musulunci ya cika kuma ya kammalo kuma ta tanadi dokoki da ka'idodi, Babu wani bangaren rayuwar mu da musulunci ya kyale, Kama daga

- mu'amula 'Musulunci ya tsara yadda za' a yi mu'amula.

-Siyasa hatta ita ma musulunci ya tsara yadda za'a yi ta a cikin tsafta.

-Ibadah tabbas musulunci ya tsara yadda za'a Ibadah baki daya.

Da sauransu.

Shi musulunci addini ne wayyaye wamda yake dai dai da kowane irin zamani, Kamar yadda Allah madaukakin sarki ke cewa "MUN SAUKAR MAKA DA LITTAFI NE DAN BAYANI GAME DA KOMAI"

Yan uwa musulmi masu albarka kada mu yadda muyi wani abu da zai kaskantar da addinin mu, Ko yaya abun yake komai yadda muke kallo shi karami!!

Yan uwa musulmi a yanzu wani abun takaici da ban tsoro dake faruwa tsakanin musulmi shine yadda zaka ga wai musulmi na bikin kirismeti, Har yana zuwa wuraren su yana taya su murna yana nishadi da annashuwa.

Har takai ga wasu jahilai daga cikin musulmi na cewa 'Ai babu banbanci tsakanin musulmi da kirista !!!

Har suna cewa ai duniya yanzu ta waye, Kai har masu cewa wai ai duk Allah ne ya saukar da musulunci da kiristanci  Subhannallah!!!

To fadin wannan maganar fa kafirci ne, Allah ne yace "ALLAH YA KAFIRTA MASU CEWA ALLAH UKU NE"

A wani Wuri kuma yace "WALLAHI ALLAH YA KAFIRTA MASU CEWA ISAH (ALAIHIS SALAM) DAN ALLAH NE!!"

ALLAH madaukakin sarki ya gargade mu da so da kaunar kafurai tun daga yahudawa na nasarawa wato kirista...

Yana cewa "YAKU WADANDA SUKAYI IMANI KADA KU RIKI  YAHUDU DA NASARA A MATSAYIN MAJIBINTA DUK WANDA YA RIKE SU (MAJIBINTA)  TO YANA TARE DASU LALLAI ALLAH BAYA SHIRYAR DA AZZALUMAI"

Hakama Allah madaukakin sarki yana kara cewa "KAI MUSULMI YAHUDU KO NASARA BASU TABA YARDA DA DA KAI HAR SAI KA ZAMO DAGA CIKIN SU (wato ka koyi dabi'unsu)"

Yan uwa musulmi ana samun wasu musulmi na zuwa wajen kafurai har suna cewa murnar haihuwar Annabi Isah Alaihis salam, Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace "Duk wanda yayi kama da kiristoci to yana cikin su"

Zama da kiristoci a lalura babu laifi sai dai dole ne a kiyaye duk wata alaka wadda data danganci addinin ka.

Yan uwa musulmi Ibn taimiyah yana cewa 'Abunda kiristoci keyi a addinin Annabi Isah Alaihis salam haramun ne!!!

Yan uwa musulmi masu albarka ma' abota ilmi sunyi gargadi game da taya kafurai murna.

Umar bn Khaddab khalifan Manzo sallal lahu alaihi wassalam na biyu yana cewa 'Kada musulmi su kuskura yaje wajen da kiristoci ke bukukuwan su domin Allah yana saukar da fushin sa a nan to idan musulmi yaje wurin abun na iya faruwa dashi "

Kada ka kuskura wani ya jaka ko ya rude ka cewa wai ai duk ana tare ko kuma kasa daya jama'a daya wallahi kada ko sau daya kaje wajen da kafurai ke yin bukukuwan su!

Su kafurai basu son Allah basu son Manzo sallal lahu alaihi wassalam duk abunda zasu fada maka karya ne kuma adawar ka tana cikin jinin su da rayuwar su

SABUWAR SHEKARA  (NEW YEAR)

Bayan kwana ki kuma kiristoci na bikin sabuwar shekara, Kuma abun takaici kaga musulmi na murna da annashuwa cewa sabuwar shekara ta kama!!

Har zakaga musulmi na turawa a yanar gizo cewa happy new year

Wannan abun takaici ne matuka!!

Shin musulmi sun manta da ainihin shekarar su??

Wai har ana samun musulmi wanda zaka tambaya yau naga ga watan musulunci ya kasa fada??

Wannan abun takaici ne!!!

Lallai wajibi mu fifita amfani da kwanan watan musulunci fiye da nasu, Watanni musulunci a bayyane suke kuma akwai dalilin saukar dasu Allah madaukakin sarki yana cewa "SUNA TAMBAYAR KA GAME DA JINJIRIN WATA MUN SANYA WANNAN NE DAN SANIN LOKACHIN IBADAH DA AIKIN HAJJI"

hakama madaukakin sarki na cewa "ADADIN WATANNI A WURIN ALLAH SUNE GUDA GOMA SHA BIYU AKWAI HUDU MAFI FALALA A CIKIN SU"

kenan ga manu Zamu dauki na wasu??

Amfani da watan ni kafurai sai lalura da kuma dole!!

Kada mu dauka cewa amfani da watan musulunci al'ada ne...... A'a addini ne.

Muna tawasuli da sunayen Allah dari ba daya ya shiryar damu hanya madaidaiciya ya biya bukatun mu na alkhairi.

Allah ka taimaki yan uwa musulmi dake zirin gaza ka kaskantar da yahudawa da masu goya masu Baya.

Allah ka amintar damu Kabamu lafiya d zama lafiya ya ubangiji kayi rahama ga mamatan mu.

Ya ubangiji kayi albarka da bunkasa kasashen mu da jahar mu da garin mu baki daya.

©®Ibrahim Rabilu Tsafe  Alzamfari. 07064282182
Jumu'ah 2-Rabi'ul thani-1439
Friday 22-December - 2017 AB

No comments: