*HUKUNCI FADAR INA KWANA KO INA WUNI KO BARKA DA DARE KO BARKA DA WARHAKA*
*_FADHILATUSH-SHEIKH ABDULAZIZ BN ABDULLAHI BN BAZ HAFIZAHULLAH_*
*TAMBAYA:* wasu daga cikin Mutane suna wadatuwa da fadar INA KWANA KO INA WUNI da sauransu, suka watsar da ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH WABARATUHU, sallamar musulunci, ko akwai wani bayani game da hakan???
*AMSA:*
```Eh baya halasta gabatar da wannan, abunda ke wajibi shine farawa da sallama ASSALAMU ALAIKUM, kafin fadar INA KWANA KO INA WUNI, idan kuma ka kara WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU, ka kammala kuma hakan yafi falala, sannan bayan sallama sai INA KWANA KO INA WUNI YAYA KUKE, YA YAYANKU, YA IYALANKU, da sauransu gaishe gaishe masu kyau, sai dai a fara da ASSALAMU ALAIKUM wannan shine karanci, idan kuma ka kara da WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU, ka hada duka kenan, Annabi Muhammad s.a.w ya kasance yana tare da sahabbansa, sai ga wani ya shigo yace: ASSALAMU ALAIKUM, sai Manzon Allah s.a.w yace(goma) ma'ana yana da lada goma, sai ga wani ya shigo yace; ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH, sai manzon Allah s.a.w yace;(Ashirin) ma'ana: Lada ashirin, sai ga wani mutum ya kara shigowa yace: ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU, sai Annabi Muhammad s.a.w yace;(Talatin) ma'ana; lada talatin.
Wannan shine falalar hadewa duka.
Allah yayi mana jagora.```
Copyright©
*_ABU-SINAN_*
*Hashim Sirajo Uba Tsamiya*
atstsamawy@gmail.com
hashimtsamiya.blogspot.com
http://www.binbaz.org.sa/mat/17636
No comments:
Post a Comment