⛔ *HUKUNCIN TAHIYYATUL MASJID* ⛔
💬TAMBAYA🔻
➖ Raka'o'i guda biyu da akeyi lokacin shiga masallaci wajibi ne akan duk Wanda ya shiga masallaci???
➖ Menene akan Wanda ya shigo sai ya tarar za'a tada ikama, zaiyi nafilolin biyu ko kuwa zaiyi sallar farillar bayan an kare sai ya ranka???
🌷 *_FADHILATUSH SHEIKH AL-ALLAMA SALIH AL-FAUZANY HAFIZAHULLAH_*
✍🏻 *AMSA*
🔻 ```Manzon Allah s.a.w yace;
🗯(idan dayanku ya shiga masallaci, yayi raka'a biyu kafin ya zauna)
[Imamul-bukhari ya ruwaito shi a cikin sahihinsa 1/114. Daga hadisin Abi Qatadha Assulamy R.A].
✋ Wanda ya shiga masallaci kuma yayi nufin zama a ciki, toh yayi nafila raka'a biyu kafin ya zauna, amma Wanda ya shiga ba tare da yayi nufin zama ba(wato ya shiga ya tarar da za'a tada sallah ko ya shiga ne kawai ya karbi wani Abu ya fita).
🔻 Wannan babu Tahiyyatul-masjid a gareshi
🔻 Hakanan kuma idan ka shiga da niyyar yin sallar farilla, kuma ka iske an tayar da sallar wacce take farilla, toh zakayi sallar farilla a cikin jama'a.
sallar farillar ta wadatar maka akan Tahiyyatul-masjid.
ALLAH YAYI MANA JAGORA
📚Madogara:
المنتقى من فتاوى الشيخ الفوزان
س/54باب الصلاة
DAN UWANKU A MUSULUNCI:```
*ABU-SINAN*
_HASHIM SIRAJ UBA TSAMIYA_
+2348064734911
atstsamawy@gmail.com
hashimtsamiya.blogspot.com
No comments:
Post a Comment