FASSARAR KHUDBAR JUMU'AH DAGA MASJID ABI HURAIRA AREA 2 TSAFE JIHAR ZAMFARA
#DUKIYA_DA_FITINONIN_DAKE_TARE_DA_ITA
DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE
BAYAN mukaddimah.....
Yan uwa musulmi masu albarka lallai mu sani fitunun dake cikin dukiya suna da matukar yawa, Kamar yadda Allah madaukakin sarki ya fada.
Yan uwa musulmi muji tsoron Allah mu tuna lallai kudin dake hannu mu yabamu su ne matsayin Jarabawa!! ALLAH Ya fada cikin suratul anfal cewa "YAYAN KU DA DUKIYOYIN KU FITINA NE GAREKU"
Hakama Allah madaukakin sarki ya fada cikin suratul Tagabun cewa "LALLAI DUKIYOYIN DA YAYA FITINA NE GAREKU"
Yan uwa musulmi idan akace dukiya ana nufin kudi ko wata kadara...
Saboda falalar Allah garemu ya halasta mana hanyar samun dukiya, Allah ya bamu hanyoyin samun dukiya da matukar yawa, Hanyoyin samun dukiya ta halal kashi 99% ne saura kashi daya kuma ne na haram!!
Kunga Allah yayi mana adalci...
Akwai kashe kashen neman halal -
Akwai mutane masu dagewa wajen neman halal, Suna nema tsakanin su da Allah, To wannan Allah yasanya albarka a ciki.
Akwai wanda kuma bayan kyautata neman shi babu ruwan shi da halal da haram, To wannan shine dukiyar ke zaman mashi bala'i, Koda anyi Sadaka ko hajjji ko umrah babu lada..
IDAN AN SAMU DUKIYAR to yaya zaka kashe ta??
Yan uwa musulmi akwai wanda ke zama abokin shi itace dukiya, Ya maida zancen shi kudi mafarkin ki shi kudi, Komai dai maganar kudi...
Alhali abunda ake bukata idan ka rike kudi ka dauke su a hannun ka ba'a zuciyar ka ba, Idan har kasanya kudi a zuciyar ka to lallai ka kama hanyar yin asara...
Yan uwa musulmi masu albarka hakika musulmi na kwarai shine wanda kudi basu hana shi bin Allah basu hana shi neman ilmi ko yin ibada.
Yan uwa musulmi hakika ranar kiyama kafin kowa ya shiga aljannah sai an tambaye shi game da dukiya!
Ina kasamo??
Ina ka aje??
Ina ka kashe??
Wallahi tallahi sai anyi mana wannan tambayoyin 😰😰
Hakika Allah madaukakin sarki ya halicce mu dan mu bauta mashi, Neman halal ne amma ba ido rufe ba 😇😇
Akwai wadanda suke da dukiyar mai yawa, Basu taimakon kowa basu taimakon addinin musulunci, Duk shelar da za'a yi na neman taimako ga addini amma babu ruwan shi...
Babu taimakon addini babu taimakon yan uwa ko makwabta kai wasu ma har iyalin su 😴
Akwai kuma masu almubazaranci da kudi, Komai suka samu nan take zasu kashe, Sai dai duk inda ake neman raya wata bidi'ah to zai bada gudunmuwa!!
Ire iren wannan duk makomar su wuta...
Akwai kuma masu riya, Wato zasu bada Kyauta da Sadaka amma ba dan Allah ba dan kawai ace wane yana da kokari!!
Yan uwa musulmi masu albarka hakika babu wanda zai tsira daga sharrin shaitan sai wanda ya nema ta halal kuma ya kashe ta halal, aka taimaki addini aka taimaki jama'a da marar sa galihu da marayu da sauran mabukata...
Lallai wadannan mutanen Allah yana son su jama'a ma suna son su kamar yadda Allah yake fada cewa cikin suratul furqan "SUNE IDAN ZASU CIYAR BASU TUNANIN KOMAI BASU HAUFI SUNA CIYARWA DAGA ABUNDA ALLAH YA AZURTA SU"
Yan uwa musulmi masu albarka hakika mu sani dukiyar nan aro ce Allah ya bamu, Duk abunda muka samu anan wallahi duk anan Zamu barshi!!
Dama munzo babu ko sisi babu kaciya babu riga babu wando, Haka kuma Zamu koma.
Yan uwa musulmi kada mu bari abunda ke karewa ya rude mu, Har muyi asara...
Shaitan yakan rudemu da aikata abunda ALLAH ya haramta, Kamar cha cha, Kamar zalunci kamar sata kamar cin hanci da rashawa, Yanzu ma'aikatan gwamnati sun lalace sun kowa yafi son inda ake kwasar dukiyar kasa!!
Yan kasuwa sun lalace sun koma mayaudara kasuwanci ya koma kamar na jahiliya.
Yan uwa musulmi Allah fa ya haramta mana cin dukiyar mutane ya haramta mana zubar da jini da cin mutuncin musulmi!!
Manzo sallal lahu alaihi wassalam ya barranta da masu zalunci "BAYA TARE DAMU MAI YIN ALGUSU"
Yan uwa musulmi wajibi ne Mumini ya kaucewa zaluntar dan uwa musulmi kamar yadda baka son a cuce ka!!
Shi zalunci bai takaita ba kan yan kasuwa ko barayi, A'a akwai wanda ake ba rance bai biya ko kuma kasuwanci da yaudara.
Akwai wadanda kudi ke sanyawa girman kai da fankama, Inda Allah ya sanya kowa ya zam mai arziki da mun zama masu girman kai.
Da yawa wadanda Allah yaba dukiya tana zama sanadin hakalar shi.
Yan uwa musulmi duk wasu kudi da motoci da gidaje abun tambaya ne,
Kada mu manta fadar Allah garemu cewa "KUDI DA YAYA FITINA NE GAREKU"
ALLAH Ya gafarta mana yayi mana rahama, Ya ubangiji ya bamu dukiya mai albarka ta halal, Ya ubangiji ka biya mana bukatun mu na alkhairi ka yafe mana kurakuren mu ka gafarta wa mamatan mu, Ameen ya rabb.
©®Ibrahim Rabilu Tsafe Alzamfari. 07064282182
Jumu'ah 7-5-1439
Friday 26-January - 2018 AB
No comments:
Post a Comment