FASSARAR KHUDBAR JUMU'AH DAGA MASJID ABI HURAIRA AREA 2 TSAFE JIHAR ZAMFARA
#SHIRKA_DA_NAU'O'INTA
BAYAN mukaddimah.....
Yan uwa musulmi masu albarka hakika banban abunda ALLAH yafi kauna shine riko da tauhidi, Kuma babban abunda ALLAH yafi kin shine shirka!!
ALLAH madaukakin na cewa "KU BAUTA MA ALLAH KADA KU HADA SHI DA KOWA"
lallai yan uwa musulmi mafi girman zunubi shine yin shirka da Allah....
ALLAH madaukakin na cewa yayi "DUK WANDA YAYI SHIRKA DA ALLAH MAKOMAR SHI WUTA (idan ya mutu bai tuba ba)"
Sannan kuma Allah na cewa "LALLAI ALLAH BAYA GAFARTAWA IDAN AKAYI SHIRKA DASHI AMMA YANA GAFARTA WANI LAIFIN WANDA BA SHIRKA BA GA WANDA YASO"
Yan uwa musulmi hakika Allah ya tsoratar da dukkan annabawan da ya aiko game da Shirka, ALLAH yana cewa "MUNYI WAHAYI GAREKA DA WADANDA SUKA GABACE KA IDAN KAYI SHIRKA LALLAI DUK AYYUKAN KA SUN LALACE"
Yan uwa musulmi mu duba girman Annabawa amma Allah yace masu idan suka yi shirka ayyukan su sun lalace balle mu, Wannan kiran fa ba Allah yana nufin Annabawa ba!!
A'a ana nufin mu, Domin annabawa basu yin shirka...
Yan uwa musulmi idan muka diba musulmi fa yawa sun fadawa shirka da sanin su wasu kuma bada sanin su ba!!
ALLAH madaukakin sarki na cewa "DA YAWAN SUNYI IMANI AMMA SUN HADA ALLAH DA WANI"
Manzo sallal lahu alaihi wassalam ya gargade mu gargadi mai tsauri yana cewa "lallai abunda nafi tsoratar maku a rayuwar Ku shine shirka karama"
Wata rana Abubakar assidiq radiyyallahu anhu yaje wajen Manzon Allah sai Manzo Allah yace mashi lallai shirka tana nan cikin musulmi, Lallai shirka tafi boyuwa a cikin Ku Sama da tururuwa a saman bakin dutse cikin dare "
Amma ga wata addua da zaka rika karanta wa domin neman kariya kace" YA ALLAH INA ROKONKA KA GAFARTA MANI KA KARENI DAGA SHIRKA "
NAU'OIN SHIRKA
*Rokon kabari, Sau da yawa zaka ga wasu masu karancin islamiyya suna zuwa rokon kabari, Ko aljanu ko waliyai ko annbawa Alaihis salam
Alhalin Allah madaukakin sarki ya haramta hakan har ma ya fada cikin suratul ahkaf cewa" BABU BATACCE IRIN MAI KIRAN WANIN WANIN ALLAH "
Kuma duk musulmi mai imani ya amince cewa kiran WANIN Allah shirka ne, Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace" Roko ibada ne " Dan haka duk wanda ya roki WANIN Allah dan neman biyan wata bukata ko neman kariya hakika yayi shirka!!
* Kudurta cewa wani na cutar wa...
Sau da yawa idan wani abu yafaru da dan Adam sai ya dora laifin bisa wani abu, Ko dora shi ga wani dalili ko kuma cewa ai wane ne dalili da sauran su...
ALLAH madaukakin sarki yace "IDAN ALLAH YA KAWO MAKA CUTA BABU MAI IYA DEBE MAKA ITA SAI SHI"
*SHIRKA TA HANYAR YIN MAGANA...
sau da dama wasu na fadar wasu maganganu alhalin shirka ce, Kamar cewa 'Taya Allah kiwo yafi Allah na nan'!
Kamar cewa Idan Allah ya yarda tare da wane, Ba' a cewa hakan nan cewa ake yi idan Allah ya yarda sannan wane ya yarda, Kaga dole sai ka fara sanya Allah farko.
Sannan masu cewa mun dogara ga Allah mun dogara gareka, Huzaifa ya ruwaito cewa Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace "Kada Kuce abunda ALLAH yaso da abunda wane yaso"
* JINGINA NI'IMAH GA WANI ABU....
jjngina samuwar Ni'ima ga wani abu kamar aiki, Ko sana'a ko, Alhali yin haka sanya wa Allah kishiya ne, Allah kuma yace "KADA KU SANYA MA ALLAH KISHIYA"
* SIHIRI...
Yanzu yawan yin sihiri ya yawaita cikin musulmi, A yanzu yadda sihiri yazama ruwan dare ya koma wa wasu kamar jini, Saboda yawan yin sihiri har sanya wasu anan Zamfara na Jefa Alqur'ani Mai tsarki cikin makewayi (Toilet) subhannallah...
Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace "Duk wanda yaje wurin boka ko dan sihiri ya karyata abunda aka saukar wa Manzo Allah (Alqur'ani)"
* YIN RANTSUWA DA WANIN ALLAH...
wasu nada tabi'ar yin rantsuwa da, kaddara ko lokachi ko iyaye da sauran su, Har munzo zamanin da akafi yarda da rantsuwar da akayi ba Allah a ciki...
* IZGILI DA WANI ABUN ADDINI....
wasu kuma nada tabi'ar yin izgili da Abubuwan addini kamar, Gemu hijabi, aswaki, Yawaita sallama da sauran su.
* RATAYA LAYA KO KARHU
Daga cikin musulmi akwai masu tabi'ar daura laya ko karhu ko guru ko qaho da sauran su, Da sunan samun kariya ko wani abu, Wannan duk shirka ne.
*JIBINTAR KAFURAI
wasu nada tabi'ar jibintar kafurai fiye da musulmai, Alhali basu son Allah kuma basu son Manzon Allah.
Tabbas duk wanda ya fada shirka tabbas ya halaka, Duniya da Lahira.
ABUBUWAN DAKE SAMUWAR MAI YIN SHIRKA
- Rayuwar mai shirka tana lala cewa.
- Kullum cikin tashin hankali mai shirka ke kasancewa.
-Cirewar natsuwa daga rayuwa.
- shiga cikin batattu domin Allah yace "DUK WANDA YAYI SHIRKA YA BACE"
-Rosa ayyukan bawa, Duk wanda yayi shirka ya roza ayyukan shi. ALLAH madaukakin sarki ya cewa Manzo Allah cewa "DUK WANDA YAYI SHIRKA YA LALATA AYYUKAN SHI"
-DUSHE HASKE.
duk mai yin shirka Allah zai sanya wa rayuwar shi duhu, Baya taba ganin hasken alkahri.!!
Yan uwa musulmi hakika shirka tana tauye imani, Lallai yazama wajibi garemu muyi watsi da duk abunda zai kowa mana tangarda a cikin imanin mu, Domin samun tsira gobe Kiyama mu da iyalan mu da yan uwan mu baki daya.
. Allah ka albarkaci rayuwar mu baki daya.
Allah kayi mana kariya daga shirka, Ka biya mana bukatun mu na alkhairi, Ya Allah Muna tawasuli da sunayen ka ka biya mana bukatun mu na alkhairi baki daya, Ya Allah kara albarka ga garuruwan mu kabamu lafiya da cikakken zama lahiya ameen.
©®Ibrahim Rabilu Tsafe Alzamfari. 07064282182
Jumu'ah 01-5-1439
Friday 19-January - 2018 AB
No comments:
Post a Comment