Monday, 19 March 2018

AZUMIN WATAN RAJAB(SUNNAH KO BIDI'AH)?

🌺🍇🍏🌹🌷🌼🌸💐🌺
*AZUMIN WATAN RAJAB(AZUMIN TSOFAFFI) SUNNAH NE KO BIDI'AH???*
🌺💐🌸🌼🍇🌷🌹🍏🌺

Rubutawa: *_Hashim Surajo Uba Tsamiya(ABU SINÃN)_*

بسم الله الرحمن الر حيم

```Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya chanchanci a bauta masa shi kadai kuma ya hanemu da shirkah, Tsira da Aminci su tabbata ga farin jekada Annabi Muhammad s.a.w wanda ya tsoratar damu daga aikata bidi'ah.

Bayan haka; Nayi nufin yin wannan rubutu ne saboda ganin ya dace mu fadakar da yan uwa musamman iyaye da kakanni da ake zalunta da hadissan karya, dangane da falalar azumin watan Rajab.

Da farko dai shi watan Rajab yana daya daga watanni masu alfarma wanda aya ta 36 a suratu taubah tayi bayani.

✏✏✏✏✏✏✏✏
MAGANGANUN MAGABATA AKAN AZUMIN WATAN RAJAB(AZUMIN TSOFAFFI)
✏✏✏✏✏✏✏✏

kai tsaye yanzu ga Wata tambaya da akayi ma sheikh bin baaz(R.H) dangane da azumin Rajab(azumin tsofaffi).

An tambayi sheikh bin baaz(R.H) akan cewa shin ko yana halatta azumtar watan Rajab (AZUMIN TSOFAFFI) gaba dayansa? Domin wasu Malamai suna fadar cewa: duk wanda ya azumci Rajab, an gafarta mashi zunubbansa koda sun kai yawan kumfar teku, wasu kuma malaman sunyi hani da azumtar watan suna cewa; duk da zamanshi cikin watanni masu alfarma baya halatta a azumceshi gaba daya???

Ga amsar da bin baaz ya bada, yana cewa; " Abun sani kawai shine ba'a shar'anta azumtar watan Rajab ba! Bari ma an karhantashi, abunda ya tabbata shine an shar'anta azumin sha'aban, manzon Allah s.a.w ya kasance yana yin azumin sha'aban, yana azumtar sha'aban sai kadan yake  ragewa, amma Rajab an karhanta yin azumi a cikinsa, azumi a cikinsa yana daga cikin aikin jahiliyya, saboda masu azumtar basu da dalilin azumtar watan!!! Hadisan da ake yawo dasu akan falalar watan Rajab basu da asali, bari ma na karya ne wadanda basu inganta ba, abunda shari'ah ta shar'anta ga musulmai shine suci susha a watan Rajab, sai dai idan ya kasance kana yin azumin nafila tun kafin zuwan watan wanda su dama shari'ah ta tabbatar dasu, kamar; litinin da Alhamis, Ayyamul-beedh da sauransu, wannan yana da kyau kuma babu laifi, amma azumtar watan gaba dayansa, ko kuma baka saba yin azumin nafila ba sai da watan ya shigo sai ka fake da azumin nafila ka gabatar da na Rajab wannan shari'ah bata yadda dashi ba.
Wannan itace amsar da sheikh bin Baaz ya bada dangane da azumin tsofaffi na Rajab.

Hadisi ya tabbata daga Aisha matar Annabi Muhammad s.a.w tana cewa:كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يصوم حتى نقول لايفطر، ويفطر حتى نقول لايصوم، وما رأيته أكثر صياما منه في شعبان.
[صحيح أخرجه البحاري(١٩٦٩)، و مسلم(١١٥٦)].

Ma'ana; Aisha R.A take cewa; "Manzon Allah s.a.w ya kasance yana yin azumi har sai nace bai cin abinci! Yana cin abinci har sai nace bai yin azumi(ma'ana yana yin azumi da yawa, haka kuma yana aje azumi ya huta sosai) ban taba ganin Manzon Allah s.a.w yana cika azumin wata daya ba sai dai idan ramadhan ne, ban taba ganin watan da yafi azumi a cikinsa ba face sha'aban.
[Bukhari da Muslim].

ﻗﺎﻝ ﺷﻴﺦ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ
" ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ " ‏( 25/290 ‏) :
" ﻭﺃﻣﺎ ﺻﻮﻡ ﺭﺟﺐ ﺑﺨﺼﻮﺻﻪ ﻓﺄﺣﺎﺩﻳﺜﻪ ﻛﻠﻬﺎ
ﺿﻌﻴﻔﺔ ، ﺑﻞ ﻣﻮﺿﻮﻋﺔ ، ﻻ ﻳﻌﺘﻤﺪ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻋﻠﻰ
ﺷﻲﺀ ﻣﻨﻬﺎ ، ﻭﻟﻴﺴﺖ ﻣﻦ ﺍﻟﻀﻌﻴﻒ ﺍﻟﺬﻱ ﻳﺮﻭﻯ ﻓﻲ
ﺍﻟﻔﻀﺎﺋﻞ ، ﺑﻞ ﻋﺎﻣﺘﻬﺎ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻮﺿﻮﻋﺎﺕ ﺍﻟﻤﻜﺬﻭﺑﺎﺕ...

Shaikhul Islam Ibn taimiyyah (RH) y
ace: “Kebance watan rajab da yin azumi,
dukkan hadisan
da su ka zo akan haka da’ifai ne (masu
rauni), bari
ma hadisan karya ne, masu ilimi
basu amfani dasu, domin basu
cikin hadisan
da ake amfani dasu don nuna falalar
aikata abu,  bari ma dukkan su ma
hadisai ne
na karya..”
Duba Majmu’u Fatawa (25/290).

ﻭﻗﺎﻝ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﻘﻴﻢ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :
" ﻛﻞ ﺣﺪﻳﺚ ﻓﻲ ﺫﻛﺮ ﺻﻴﺎﻡ ﺭﺟﺐ ﻭﺻﻼﺓ ﺑﻌﺾ
ﺍﻟﻠﻴﺎﻟﻲ ﻓﻴﻪ ﻓﻬﻮ ﻛﺬﺏ ﻣﻔﺘﺮﻯ " ﺍﻧﺘﻬﻰ ﻣﻦ " ﺍﻟﻤﻨﺎﺭ
ﺍﻟﻤﻨﻴﻒ " ‏(ﺹ 96 ‏)

Imam Ibnul Qayyim (RH) yace;
“Dukkan hadisan 
da suka ambaci azumin watan rajab da
sallatar wasu
darare a cikin sa, hadisai ne na karya kuma 
kirkirarru”.
Duba Almanarul Muniif (shafi 96).

ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺤﺎﻓﻆ ﺍﺑﻦ ﺣﺠﺮ ﻓﻲ " ﺗﺒﻴﻴﻦ
ﺍﻟﻌﺠﺐ " ‏(ﺹ 11 ‏) :
" ﻟﻢ ﻳﺮﺩ ﻓﻲ ﻓﻀﻞ ﺷﻬﺮ ﺭﺟﺐ , ﻭﻻ ﻓﻲ ﺻﻴﺎﻣﻪ
ﻭﻻ ﺻﻴﺎﻡ ﺷﻲﺀ ﻣﻨﻪ ﻣﻌﻴﻦ , ﻭﻻ ﻓﻲ ﻗﻴﺎﻡ ﻟﻴﻠﺔ
ﻣﺨﺼﻮﺻﺔ ﻓﻴﻪ ﺣﺪﻳﺚ ﺻﺤﻴﺢ ﻳﺼﻠﺢ ﻟﻠﺤﺠﺔ "
ﺍﻧﺘﻬﻰ.

Alhafiz Ibn Hajar Al-Asqalani yake
cewa; “Babu
wani abu da aka ruwaito na falalar
watan Rajab,
ko yin azumi a cikin sa, ko azumtar
wasu adadin
kwanaki ayyanannu, ko tsayuwar
wasu darare
kebantattu”.
Duba Tabyinul ujub (shafi 11).

ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﺳﻴﺪ ﺳﺎﺑﻖ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ " ﻓﻘﻪ
ﺍﻟﺴﻨﺔ " ‏( 1/383 ‏) :
" ﻭﺻﻴﺎﻡ ﺭﺟﺐ ﻟﻴﺲ ﻟﻪ ﻓﻀﻞ ﺯﺍﺋﺪ ﻋﻠﻰ ﻏﻴﺮﻩ ﻣﻦ
ﺍﻟﺸﻬﻮﺭ , ﺇﻻ ﺃﻧﻪ ﻣﻦ ﺍﻷﺷﻬﺮ ﺍﻟﺤﺮﻡ , ﻭﻟﻢ ﻳﺮﺩ ﻓﻲ
ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ ﺃﻥ ﻟﻠﺼﻴﺎﻡ ﻓﻀﻴﻠﺔ ﺑﺨﺼﻮﺻﻪ ,
ﻭﺃﻥ ﻣﺎ ﺟﺎﺀ ﻓﻲ ﺫﻟﻚ ﻣﻤﺎ ﻻ ﻳﻨﺘﻬﺾ ﻟﻼﺣﺘﺠﺎﺝ ﺑﻪ
" ﺍﻧﺘﻬﻰ

Imam Sayyid Sabiq (RA) yake cewa;
“Azumin
watan rajab bashi da wani fifiko na
falala akan
waninsa cikin watanni, sai dai shi
yana daga cikin
watanni (guda hudu) ma su alfarma,
kuma ba a
samu a cikin sunnah ingatacciya ba cewa
yin azumi a
cikin sa yana da falala kebantacciya,
abunda ya zo
akan haka (ma’ana hadisan da suka
zo) ba a kafa
hujja dasu (domin da’ifai ne)”
Duba Fiqhus-Sunnah (1/383).

ﻭﺳﺌﻞ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﺍﺑﻦ ﻋﺜﻴﻤﻴﻦ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻦ ﺻﻴﺎﻡ
ﺍﻟﺴﺎﺑﻊ ﻭﺍﻟﻌﺸﺮﻳﻦ ﻣﻦ ﺭﺟﺐ ﻭﻗﻴﺎﻡ ﻟﻴﻠﺘﻪ .
ﻓﺄﺟﺎﺏ :
" ﺻﻴﺎﻡ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻟﺴﺎﺑﻊ ﺍﻟﻌﺸﺮﻳﻦ ﻣﻦ ﺭﺟﺐ ﻭﻗﻴﺎﻡ
ﻟﻴﻠﺘﻪ ﻭﺗﺨﺼﻴﺺ ﺫﻟﻚ ﺑﺪﻋﺔ , ﻭﻛﻞ ﺑﺪﻋﺔ ﺿﻼﻟﺔ "
ﺍﻧﺘﻬﻰ .
" ﻣﺠﻤﻮﻉ ﻓﺘﺎﻭﻯ ﺍﺑﻦ ﻋﺜﻴﻤﻴﻦ " ‏( 20/440 ‏)

An tambayi sheikh Muhammad Salihul Usaimeen
(RH)
dangane da azumi ranar 27 ga watan
rajab da
kuma tsayuwar dararen sa.
Sai ya amsa da cewa:
“Yin azumi ranar 27 ga watan Rajab
da tsayuwar
darensa kebance shi da haka bidi’a
ne, dukkan
bidi’a kuma batace”
Duba Majmu’u fatawa na Usaimeen
(20/440).

   Haka zalika Sayyidina umar R.A ya kasance yana bulala akan wadanda ke kamewa akan azumin Rajab, yana ce musu kuci abinci, wannan watane da ya kasance ake girmamawa a lokacin jahiliyya. [Ibn Abi shaibah ya fitar 3/102] da ibn kathir a cikin musnadil- faruk 1/285]

Haka zalika ibn umar R.A ya kasance idan yaga mutane suna wuce gona da iri akan Rajab, yana kyamar hakan!
[Sahih: ibn abi shaibah ya fitar 3/102]

Ibn Abbas ya kasance yana hani akan azumin Rajab gaba dayansa, saboda kada a maida shi ya zama abunda za'a rinka yi duk shekara, wato a maidashi ya zama idi.
[Sahih; Abdulrazak ya fitar 7854].

✏✏✏✏✏✏✏✏
HADISAN DA SUKA INGANTA AKAN WATAN RAJAB!
✏✏✏✏✏✏✏✏
=  "kuyi axumi a cikinshi kuma kuci abinci a cikinshi.
[Sahih irwa'ul galeel 958]

= Sha'aban yana tsakanin Rajab da Ramadhan, ana shagaltar da mutane akanshi(domin samun saukin Ramadan) a cikin sha'aban ake daukar ayukkan bayi, ina kwadayin/inason kada a daga ayyukana face ina azumi.
[Isnadinsa mai kyau ne, silsilatus-sahiha 1898]

✏✏✏✏✏✏✏✏
HADISSAI DA'IFAI WADANDA MASU AZUMIN RAJAB KE KAFA HUJJA DASU.!!!
✏✏✏✏✏✏✏✏

= A cikin Aljanna akwai wani gulbi, ana kiransa Rajab, ruwansa suna da fari wanda farin yafi na nono, duk wanda yayi azumin Rajab na rana daya, Allah zai shayar dashi daga wannan gulbin.[Silsilatu-dha'ifah 1898]

= Rajab watan Allah, Sha'aban wata na(manzon Allah), Ramadan watan Al'umma ta. 
Da'ifi ne, silsilatu-dha'ifah 4400]

= Darare guda biyar ba'a maida Addu'ah: 1. Farkon Daren Rajab

2. Daren Rabin watan sha'aban

3. Daren jumu'ah

 4. Daren karamar sallah

5. Daren babbar sallah

[Maudu'i ne, silsilatu-dha'ifah 1452]

= Rajab watane mai girma, Allah na lunka lada idan kayi aikin Alkhairi a cikinsa, duk wanda yayi azumin Rajab na kwana daya,kamar yayi azumin shekara. Duk wanda yayi na kwana bakwai, za'a rufe mashi kofofin wutar jahannama bakwai. wanda yayi na kwana takwas, za'a bude mashi kofofin Aljanna takwas. Wanda yayi na kwana sha biyar, mai kira zaiyi kira a sama yace; an gafarta maka abunda ya gabata na laifuka...[maudu'i ne, silsilatu-dha'ifah 5413]

✏✏✏✏✏✏✏✏
RUBABBUN HADISSAN DA YAN SHI'AH KE KAFA HUJJA DASU AKAN FALALAR WATAN RAJAB.
✏✏✏✏✏✏✏✏
Daga Baban hassan (A.S) yace; Annabi Nuhu (A.S) ya tuka jirgin ruwa a farkon watan Rajab, sai ya umurci wadanda ke tare dashi da su azumci wannan ranar, yace; "duk wanda ya azumci wannan ranar Allah zai nisanta shi da wuta na tsawon tafiyar shekara daya.

=Daga Abi Ja'afar, Muhammad ibn Aliyu(A.S) yace; duk wanda yayi azumi a Rajab na rana daya, a farkon Rajab ko tsakiyarsa ko karshensa, Allah ya wajabta mashi shiga Aljanna, kuma Allah zai sanya shi a tare damu a cikin darajojinmu na Ahlul baiti a ranar kiyama, wanda yayi na kwana biyu, Allah zai gafarta mashi duk zunubbanshi da suka gabata, wanda yayi na kwana uku, Allah zai gafarta mashi abunda ya gabatar na zunubi da wanda zaiyi a gaba sannan za'a bashi damar ceton yan uwanshi ma'abota zunubi...

= As-sadik Ja'afar  ibn Muhammad yace; "kada ka bari ranar ashirin da bakwai ga Rajab ta wuce ba tare da ka azumceta ba! Domin a ranar ne aka saukar wa Annabi Muhammad s.a.w Annabta...

Duka wadannan zaka samesu a cikin littafi mai suna FALALAR WATANNI UKU, wanda gingimemen malamin Shi'ah mai suna MUHAMMAD IBN ALIYU IBN HUSSAIN IBN MUSA AL-QUMMY ya rubuta.
Allah ka la'anci qummy.

  A takaice wadannan sune hujjoji na dangane da rashin ingancin azumin Rajab(azumin tsofaffi), duk wanda yake ganin akwai Gyara matukar gyaran nashi ya inganta hadisi ne ko aya ina maraba dashi kwarai da gaske.

Allah ya hadamu dani daku da sauran musulmai a cikin Aljannah.

ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH...```

Copyright©
Dalibinku
*_Hashim Suraj Uba Tsamiya {ABU SINÃN}_*

☎08064734911
📞09030201868 
    08116194214

http://hashimtsamiya.blogspot.com

atstsamawy@gmail.com

17-07-1438AH
15-04-2017AC

No comments: