GAREMU MATA,SHAWARA CE KAWAI!!!.
Duba da yanda Allah ya halicce mu ,yasa nake ganin ya kamata mu Dan nutsu kadan mu gane muna da tawaya da kuma matsaloli a tare damu.
Duk inda aka duba koda Asibiti ko wurin magani za a tarar mata munfi maza damuwa da kuma yawan lalurori.
Haka bangaren shedanci mata munfi yawa.
Sannan bangare tsafi da tsubbu mune a gaba.
Wani Malami Yace "Idan Namiji ya zama Ustaz za a ga abin kamar wani abu gama gari,amma kafin mace ta zama ustaziya completely sai anci baqar wuya,zaka ganta dai kamar Ustaziya amma daga shedan ya Dan hura ta sai kaga ta zama wata qaramar shaidaniya ko 'Yar bori,amma Duk barnar 'ya mace indai akwai tsoron Allah a tare da ita da kuma ilimi kana fara Mata nasiha da wa'azi zata nutsu sa6anin wacce ta rasa wannan abubuwa guda 2,ita mace dole sai kayi haquri da wasu dabi ah NATA".Kuma na yarda da wannan maganar tasa,haka muke.
Hakan yasa naga ya kamata mudan riqe wannan domin samun nutsuwa a rayuwar mu ta yau da gobe,saboda yanda zamu ga mun zama abubuwan wasan shaidanu,su shiga jikinmu sanda suka so su kuma fita sanda suka ga dama,Allah ya qare mu da lafiya baki daya.
Ki Tabbatar kina wadannan abubuwan koda kina da lalura ko baki da ita don Allah na roqeki.
*Karanta koda Rabin izu ne na Qur'ani kullum duk kasalarki ko simini 1 ki daure kiyi,a hankali zakiji kina qara yawan karatun idan kika saba,ko kinji kamar kin dauki dala da gwuron dutse idan za kiyi karatun ki fadawa zuciyar taki dole sai kinyi,don wata tace min " idan zata karanta Qur ani ji take kamar zata mutu".
*ki nemi (hisnul Muslim) Littafi ne,ki ajiye akusa dake ki duba a hankali akwai Azkar Wanda za kiyi da safe da kuma Wanda za kiyi da yamma,ko unguwa zaki je kidan saka shi a jaka idan lokacin yi yayi ki dakko kiyi.
*Idan kika kama ruwa bayan fitsari ki Dan daure kiyi alwala ko ba ko da yaushe ba amma kidan dinga kokartawa kina yi.Zama da alwalan yana da kyau koda kina Haidha kiyi.
*Yar uwa kina sallame sallar farilla ki karanta ayatul,kursiyyu,falaqi,Naasi,Qul huwal lahu(ikhlas)ko wacce 3,ki Dora da amanar rasul,barinma ki qara da subhanallahi 33,Alhamdulillah33,Allahu akbar33 ,ki yima Annabi (SAW)salati ,nan take zaki ji wani sanyi da nutsuwa aranki.
*Kin farka daga bacci kinyi Addu ah,zaki shiga ban daki kinyi addu'ah,zaki fito kinyi addu ah,zaki zauna kince Bismillah,zaki ci Abinci kinyi addu ah,kin gama ci kinyi Addu ah,zaki sanya tufafi koda bismillah kice,zaki cire Ki ambaci hakan,zaki fita daga gida kinyi addu ah,kin dawo zaki shiga gida kinyi addu ah,komai zaki yi na aiki ko baki iya addu arba,kawai ambaci "Bismillah".
*Ki Dan dinga zama kina Nazarin abubuwan da Ki kasan Haram ne ki kudirce fara ragewa,a hankali sai Allah ya dafa mana,kamar jin kada kada-kade,kallo mara amfani,sai fa muna ragewa Nasan muna son nishadi amma Reduction yayi a rayuwa,kamar zama ba dan kwali duk sai mun dinga kula ,Idan muna zaune bama komai muyi ta istigfari,hailala,salati da sauransu.
Guarantee na baki idan bakya yi ki fara daga yau zaki ji wani chanji na musamman acikin Duniyar ki.Allah yasa mu dace baki daya Ameen.
✍ummu juraij
No comments:
Post a Comment