📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUPS DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
_Fitowa Na sha takwas 018_
Gabatarwa: *UMMU SINAN*
*MUSTAHABBAN ALWALA:*
Wannan shi ke biye da mataki na sunnoni, kenan sunnoni sun fi mustahabbai karfi,
wadanda suke dukansu biyun farillai na gabansu, babu daya daga cikin sunnoni ko
mustahabbai da mutum zai yi sakaci da su, domin kowannen mu so yake ya yi ibada
cikakkiya kammalalla, to kuwa tunda hakane bai kamata kace ai wannan mustahabbi ne ka daukeshi kamar wani karamin abu. Su mustahabban alwala suna da yawa, amma yanzu ga kadan daga cikinsu:
1⃣ Ambaton Allah kace *Bismillah* a daidai lokacin da zaka fara alwala, amma idan mutum
ya manta saida yake tsakiyar alwalar ya tuna
ba komai sai kayi a lokacin.
2⃣ Addu'a bayan kammala alwala, itace kuma kamar haka:
*ﺃَﺷْﻬَﺪُ ﺃَﻥْ ﻻَ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺍَﻟﻠﻪُ ﻭَﺣْﺪَﻩُ ﻻَ ﺷَﺮِﻳﻚَ ﻟَﻪُ، ﻭَﺃَﺷْﻬَﺪُ ﺃَﻥَّ ﻣُﺤَﻤَّﺪًﺍ ﻋَﺒْﺪُﻩُ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟُﻪُ، ﺍَﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺍَﺟْﻌَﻠْﻨِﻲ ﻣِﻦَ ﺍَﻟﺘَّﻮَّﺍﺑِﻴﻦَ، ﻭَﺍﺟْﻌَﻠْﻨِﻲ ﻣِﻦَ ﺍَﻟْﻤُﺘَﻄَﻬِّﺮِﻳﻦَ.*
_Ma'ana:_ ```Ina shaidawa da babu abun bauta da
cancanta sai Allah, kuma shi kadai yake bashi da
abokin tarayya, kuma ina shaidawa lalle (Annabi)
Muhammad bawan Allah ne kuma manzonsa ne,
Ya Allah ! ka sanya ni daga cikin masu yawan tuba, kuma ka sanya ni daga masu neman
tsarkaka.```
3⃣ 'Karanta Ruwa;
Bawai ana nufin mai alwala ya shashshafa gabbansa bane, a'a, ana bukatar yayi amfani da ruwa amma kada ya malalar dasu, domin yana daga cikin tsarin musulunci
tattali da tsimi da tanadi.
4⃣ Gabatar Da Asuwaki:
Bayani kuma dama ya gabata akan asuwaki, ana yi da danye ko da
busasshe, idan bai samu ba sai ayi da yatsa, amma mu sani asuwaki daban kuskurar baki ma
daban. Hakanan kuma ko da mutum lokacin sallah yayi amma yana da alwala to abinda ake so shine ya yi asuwaki.
5⃣ Wuri Mai Tsarki:
An so inda zaka yi alwala ya zama wurine mai tsarki.
6⃣ Dama Kafin Hagu:
Abun nufi shine ka fara wanke hannun dama kafin hannun hagu, hakanan ka fara wanke kafar hagu kafin ta
dama.
7⃣ Jerantawa:
Wato jeranta kowacce sunnah
tare da 'yar-uwarta, kamar fara gabatar da kuskurar baki kafin shaka ruwa.
8⃣ Wankewa Sau Uku:
Ma'ana wanke wuraren da ake wankewa sau uku, mu sani wankewa sau uku zai zama mustahabbine idan wankewar farko ta game ko ina, amma idan ta farko bata
game ba to ta biyu tananan amatsayin wajibi, haka idan ta biyun bata game ba
to ta uku tana nan a matsayin wajibi. Ya zama wajibi mai alwala mace ko namiji ya kula sosai
ya cuccuda inda ya kamata ya sa ruwa ba tare da barna ba.
Amma shi kai sau daya ake shafarsa, ba'a shafar kai sau biyu ko uku. Sannan kuma mutum ya tabbata a wadannan wankewa da akace yayi sau uku bai kara akan hakan ba, yayi iya kokarinsa ya ga guda ukun sun kammala.
Wadannan kadan kenan daga cikin
mustahabban alwala, kuma wadannan bayanai
sun shafi mata kamar yadda suka shafi maza, sai dai
mata su sani gashin kansu al'aurane, saboda haka bai
halatta su bayyanar dasu ga maza ba, kenan idan zaki yi alwala sai ki sami wuri ki kebance
kanki.
Wadannan bayanai da suka gabata zasu haskaka mana yadda alwala take, amma hanya mafi sauki shi ne a yi maka ita a aikace ka gani domin haka sahabban ma'aikin Allah suka yi, an
tambayi Usman dan Affan dan gane da alwala sai yasa aka kawo mishi butar alawala yayi musu ita a aikace, yace kuma irinta manzon Allah s.a.w yayi.
A nan nake kira ga dukkanin limamai na juma'a dana sauran masallatai da kuma malamai a
jami'oi da kwalejin ilimi da kuma malamai a sakandare da firamare da malaman islamiyyu da malamai masu karantarwa a masallatai da
masu wa'azi da sauran wadanda abin ya shafa kamar kungiyoyin addini
dasu karantar da mutane alwala a
aikace, yadda kowa zai gani ya kuma yi tambaya, kada kaga kamar kowa ya gane da zarar ka yi ta a aikace zaka ga abin mamaki, ni na taba gwada
hakan a *Federal university birnin kebbi,* ita ibada sai an koyawa mutum ba wai daka akeyi ba, kai da ganin
alwalar wani kasan bai je makaranta ba, Allah ya karba mana ibadummu.
A NAN MUKA KAWO KARSHE DANGANE DA BAYANI AKAN ABUNDA YA SHAFI ALWALA, A GABA ZAMU BAYANIN ABUBUWAN DAKE KARYA ALWALA INSHA ALLAHU.
WANDA YAYI BITAR RUBUTUN;
✍ *Hashim Siraj Uba atstsamawy ( _ABU-SINAN_ )*
DOMIN SHIGA GROUPS DIN;
*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911
*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613
No comments:
Post a Comment