🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
*GIDAN NI'IMA*
🏠🏠🏠🏠🏠🏠🏠🏠🏠🏠
Gabatarwa; *BABAN-SINAN*
_Fitowa Na Farko 001_
🔴 *ZABEN ABOKI/ABOKIYAR ZAMA NA KWARAI*
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah shi kadai Wanda yake cewa;
*وَاللَّهُ جَعَلَ لَكُمْ مِنْ بُيُوتِكُمْ سَكَنًا...(النحل ٨٠)*
Tsira da aminci su kara tabbata ga farin jekada Annabi Muhammad s.a.w, da iyalan gidansa da sahabbansa da duk wanda yabi bayansu da kyautatawa har zuwa ranar addini.
_Bayan haka:_
Allah madaukakin sarki a cikin Qur'ani yana cewa;
*وَأَنْكِحُوا الْأَيَامَى مِنْكُمْ وَالصَّالِحِينَ مِنْ عِبَادِكُمْ وَإِمَائِكُمْ إِنْ يَكُونُوا فُقَرَاءَ يُغْنِهِمُ اللَّهُ مِنْ فَضْلِهِ وَاللَّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ*
Ma'ana;
*_Ku Aurar da ayama(namiji ko mace wadanda basu da aure) daga cikin Ku, da mutanen kwarai daga cikin bayinku maza da bayi mata, idan kuna tsoron talauci Allah zai wadata Ku daga cikin falalarsa, Allah mai yalwataccen falala ne kuma masani._*
Babu makawa ga namiji ko mace akan wajibi ne su zabi abokin zama na kwarai, saboda hadisin Annabin rahama s.a.w da yake cewa;
*_Ana auren mace don Abu hudu; Saboda dukiyarta, ko don dagantakarta, ko don kyau, ko don addini, sai Annabi yace na horeka da ma'abociyar addini._* (bukhari da Muslim)
Haka a wani hadisin da Muslim ya ruwaito manzon Allah s.a.w cewa yayi;
*_Duniya wani jin dadi ne, mafi alkhairin jin dadin duniya shine ka samu mace ta gari._*
A wani wurin kuma sai Manzon Allah s.a.w yake ba samari shawara akan cewa;
*_Ku auri yan mata kuma masu haihuwa, saboda inyi alfahari daku a ranar kiyama._*
Kenan a wannan hadisi na karashe manzon Allah s.a.w baya goyon family planning, Allah ya kiyaye.
Daga karshe zan rufe da zancen Magabata cewa:
*الرجل الصالح مع المرأة الصالحة يبنيان بيتا صالحا لأن البلد الطيب يخرج نباته بإذن ربه، والذي خبث لايخرج إلا نكدا.*
*_Mutumin kwarai idan ya hadu da mata ta kwarai suna Gina gida na kwarai, saboda gari tsaftatacce yana fitar da tsirrai da izinin ubangiji, Wanda ya lalace babu abunda zai fitar sai lalatattun tsirrai._*
ZAMU DAKATA A NAN SAI WANI LOKACI IDAN ALLAH YA KAIMU
_SUBHANAKAL-LAHUMMA WABI HAMDIKHA, ASH-HADU AN LAA'ILAHA ILLA ANTA, ASTAGFIRUKA WA'ATUBU ILAIHI_
✍🏻 Hashim Siraj Uba Tsamiya ( ABU-SINAN )
+2349030201868
https://hashimtsamiya.blogspot.com
atstsamawy@yahoo.com
No comments:
Post a Comment