🍉🍉🥭🍑🍎🍊🍋🍌🍉🍉
*BARKA DA SHAN RUWA*
🍉🍉🥭🍑🍎🍊🍋🍌🍉🍉
_003_
8⃣ *KO YANA HALASTA IN DOGARA GA KIRAN SALLAH DA AKE YADAWA A GIDAJEN RADIO A WURIN YIN BUDA BAKI KO SHIGAR ALFIJIR?*
_AMSA_
Yana halasta, musamman idan an tabbatar kafafen masu inganci ne a wurin ayyukansu, ko kuma musulmi ke jagorantarsu, wannan itace fatawar *SHEIKH MUHAMMAD BN UTHAIMIN RAHIMAHULLAH*
9⃣ *MINENE HUKUNCIN SAHUR GA WANDA YAYI NUFIN YIN AZUMI?*
_AMSA_
Yin sahur mustahabbi ne kamar yadda *sheikh muhammad bn salih al-uthaimin RAHIMAHULLAH* ya tabbatar da hakan, kamar yadda yake sunnah ne yin sahur din a daya bisa ukun karshen dare, saboda fadar *ZAID BN THABIT (RA)* _"MUNYI SAHUR TARE DA MANZON ALLAH S.A.W, SAI MUKA TASHI DOMIN MUYI SALLAH, SAI AKA TAMBAYI ZAID, NA WANE TAZARA TSAKANIN KIRAN SALLAH DA SAHUR? SAI YACE: KAMAR KWATANKWACIN KA KARANTA AYA HAMSIN(50)."_ [Bukhari da muslim]
Da kuma fadar manzon Allah s.a.w cewa: _"AL'UMMATA BA ZASU GUSHE SUNA SAMUN ALKHAIRI BA MATUKAR SUNA GAGGAUTA BUDA BAKI, SUNA JINKIRTA SAHUR"_ [Imamu Ahmad ya ruwaito]
🔟 *DAME AKE SON MAI AZUMI YAYI BUDA BAKI?*
_AMSA_
Anason fara buda baki da *DABINO,* idan bai samu ba sai ya fara da *RUWA* Dalili akan haka shine hadisin da yazo daga salman bn Aamir (RA) yace, Manzon Allah s.a.w yace: _"idan dayanku ya kasance yana azumi yayi buda baki da *DABINO,* Idan bai samu ba sai yayi da *RUWA,* Saboda su ruwa tsarkakakku ne"._ [Maruwaita biyar suka ruwaito shi ] thirmidhi yace hadisi ne HASAN SAHIH
*ALLAHUMMA TAQABBAL SIYAMANA* 👏👏👏👏
#ABU_SINAN
+2348064734911
No comments:
Post a Comment