🍉🍉🥭🍑🍎🍊🍋🍌🍉🍉
*BARKA DA SHAN RUWA*
🍉🍉🥭🍑🍎🍊🍋🍌🍉🍉
_002_
4⃣ *MINENE HUKUNCIN AZUMIN RAMADAN?*
_AMSA_
Azumin ramadan farilla ne, Allah s.w.t ya farlantashi ga bayinshi, Qur'ani da sunnah da ijma'i duk sun tabbatar da hakan, Qur'ani shine fadar Allah s.w.t : *_"YAA KU WADANDA SUKAYI IMANI, AN WAJABTA MUKU AZUMI, KAMAR YADDA AKA WAJABTAMA WADANDA SUKA GABACEKU, DOMIN KU SAMU TSORON ALLAH"_*
A sunnah kuma shine, bukhari ya ruwaito hadisi da muslim a cikin sahihan littafansu, daga Abdullahi dan umar r.a, Manzon Allah s.a.w yace: *_"AN GINA MUSULUNCI AKAN GINSHIKAI BIYAR, KALMAR SHAHADA, TSAYAR DA SALLAH, BADA ZAKKAH, AIKIN HAJJI, AZUMIN RAMADAN"_*
duk wanda yayi inkarin farlancinshi yayi ridda
5⃣ *MINENE SHARADIN YIN AZUMI?*
_AMSA_
Azumi na wajabta ga dukkanin musulmi, baligi, mai hankali, mai lafiyar da zai iya yin azumin
6⃣ *YAUSHE ZAN KUDURCE NIYYAR YIN AZUMIN RAMADAN?*
_AMSA_
wajibi ne ka kudurce niyyar yin azumin ramadana kafin fitowar alfijr, idan bakayi niyyar yin azumi ba sai bayan alfjr ya fito, azuminka baiyi ba, amma a azumin nafila ya inganta zaka iya yin niyya da rana tsaka, saboda hadisin aisha r.a dake nuni akan hakan.
7⃣ *ZAN IYA YIN NIYYA GUDA DAYA A RAMADANA BAKI DAYA?*
_AMSA_
Abunda yake dai dai shine niyya a farkon watan ta wadar har zuwa karshe, babu bukatuwar chanja niyya a kowane dare, kuma ita niyya ba'a furuci da ita, muhallinta shine zuciya.
#ABU_SINAN
+2348064734911
No comments:
Post a Comment