Friday, 10 January 2020

022 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_022_

*LADDUBAN ZIYARAR MARA LAFIYA DA ABIN DA KE KAN MAI JINYA DA LIKITA DA AN GUWAR ZOMA.*

Kamar yadda muka gani a baya cewa ciwo daga Allah yake kuma ciwo kaffara ne na zunubai, kuma mun ga cewa hatta
manya-manya daga cikin bayin Allah
sun yi ciwo. Musulunci ya koyar da komai domin hatta yadda a ke zuwa ziyarar/gaida mara lafiya manzon sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya koyar da mu ladubban zuwa ziyarar/gaida da mara lafiya. Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa aihi wa sallam ya kasance yakan je gaida mara lafiya kuma hadisi ya tabbata daga manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam da ya ke nuna mana idan mutun ba shi da lafiya yana da haqqi a kanka na ka je ka gaishe shi, muddin ba ka je ba ka tauye masa haqqinsa. *[Muslim]* Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Ku gaishe da mara lafiya Musulmi, ku ciyar da abinci,ku ‘yanta wuyaye.” *[Bukhari]*
Hakqin Musulmi ga Musulmi guda shida ne: Idan ya haxu da shi ya yi masa Sallama, idan ya kira ka ka amsa ma shi, in ya nemi ka yi masa nasiha ka yi ma shi, in ya yi atishawa ya kuma ce Alhamdu lil Lah, ka gasshe shi, in ya yi rashin lafiya ka je ka gasshe shi. Ya ce mai gaida Mara lafiya yana tafiya a gavar
Aljanna ne har ya je ya dawo. *[Bukhari]*

Ga ladubban kamar haka;

*NIYYA  KYAKKYAWA:*

Domin dukkan ayukka ba sa ingantuwa sai da niyya. Ana so niyyar ta zamanto kyakkyawa koda yaushe, mai zuwa ziyarar mara lafiya ana so ya yi niyyar zuwa gasshe da mara lafiya domin Allah ba wai don wani abu ba, a’a ya je ne domin samun lada wajen Allah, haka Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ambaci lada mai yawa ga wanda ya je gasshe da mara lafiya domin Allah. *[Muslim 268 da Abu Daud 3569]*

*NEMAN IZINI:*
Ana so ka nemi izinin mara lafiyan kafin ka shiga wajensa kamar yadda ya zo cikin Sahihul Bukhari Ibn Abbas ya nemi izinin shiga wajen Nana A’isha Allah ya qara mata yarda lokacin da ba ta da lafiya kafin ya shiga.  *_(Yana da kyau ‘yan‘uwa su kiyaye shiga gidajen jama’a, wannan bala’i ne kuma laifi ne shiga gidajen jama’a ba tare da izini ba, ko da ka yi sallama sai ka jira an ba ka izini kafin ka shiga, haka Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya koyar da mu. Haka nan ma haramun ne qanin miji ya shiga xakin matar wansa sai da izinin yayan nasa, idan kuma baya nan to haramun ne kai qaninsa ka shiga xakin matar. Allah ya ba mu ikon gyarawa amin)._*
Kai ma ana so ka nemi izinin mara lafiya kafin ka shiga wajensa ko da kuwa a asibiti, yayin da Ibn Abbas ya je gaishe da Nana A’ishatu Allah ya qara mata yarda, da ya je ya nemi izinin shiga sai ta ce kada ya shigo, sai aka gaya mata Ibn Abbas ne fa dan baffan Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam, sai ta ce kada dai ya shigo, da aka matsa mata sai ta ce, “Ina tsoron in ya shigo zai yabe ni, amma ya shigo. Da ya shigo sai ya ce mata, “yaya jiki?” kamar dai yadda a ka koyar da su, sai ta amsa da cewa, “Muna fatar rahamar Allah kuma muna tsoron azabarsa.” Sai Ibn Abbas ya ce, Haba ke da kike matar Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam! Ke ce fa wadda Annabi ya fi so, kuma ke ce wadda aka saukar da aya kaza da kaza saboda ita.” Ya yi ta gaya mata kyawawan ayyukanta. sai ta ce, “Da ma abin da na ke tsoro ke nan na ce kada ka shigo, da ma na san sai ka yabe ni sai ka yi ma ni Kirari.” *[Bukhari]*
Shi Ibn Abbas ya yi abin da Annabi
sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi umurni ne da a yi wa mara lafiya, ita kuma ta yi tawali’u ne kuma da ma tawali’u hali ne na mutanen kirki, don haka babu kyau a rinqa tuna wa mara lafiya munanan ayyukansa, haramun ne a je ziyarar mara lafiya kana a riqa tuna masa munanan ayyukansa.
Abdullahi ibn Umar lokacin da ya ke ciwon ajali Hajjaj ibn Yusuf As Saqafi ya nemi izinin ya shiga ya gaishe shi, sai
Abdullahi ibn Umar ya ce a ce masa ba ya so, ya taqura sai ya shiga, da ya shiga ya yi sallama Abdullahi bn Umar ya yi banza da shi. *_(Hajjaj bn Yusuf saqafi shi ne ya sa aka soki Sahabi mai daraja Abdullahi bn Umar Allah ya qara masa yarda da wani masoki mai dafi, ba don komai ba sai don zalunci da mugunta, Abdullahi bn Umar ya yi wa Hajjaj magana ne ranar juma’a a kan ya tsananta wa jama'a wajen huduba har la’asar, sai ya sa aka soke shi. Wannan sukar ce ta zama sanadiyyar Rasuwar sa. Bayan an soke shi ne daga baya ya zo gaishe shi don yaudara, sai shi kuma Abdullahi bn Umar ya ce ba ya so, shi ya sanya Shamsudden Zahabi a cikin littafinsa Siyar ya fadi miyagun maganganu a kansa ba don komai ba sai don ya kashe sahabai da bayin Allah nagari har a qarshe yake cewa, “Muna qin sa ne saboda Allah ya ce ’’ mugu dan ta’adda azzalumi dan kama karya jabberi’’ ya dai sossoke shi. Mai karatu yana da kyau ya karanta tarihinsa a cikin SIYAR A’ALAMUN NUBALA shafi 343/4)._*
Bukhari ma ya kawo magana mai kama da wannan da ke nuna ladabin zuwa
ziyarar mara lafiya.
Dattijon arziqi mafifici mai daraja a bayan qasa bayan manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam
Abubakar Siddiq, shi ma ya nemi izinin shiga ya gaishe da Nana Fatimatu Allah ya qara ma ta yarda lokacin da ba ta da lafiya, ya yi sallama Sayyina Ali dan Abi Dalib Allah ya qara ma sa yarda ya fito sai ya ce masa ya nema ma sa izinin shiga ya gaishe da Nana Fatimah, sai Ali ya shiga ya gaya ma ta Abubakar yana neman izinin ya shigo ya gaishe ta, sai ta ce ya shigo, shi kuma ya shiga ya gasshe ta.
Ana so mai zuwa ziyarar mara lafiya ya nemi izinin shiga kafin ya shiga wajen mara lafiya.

ANAN ZAMU DAKATA, A GABA ZAMU CIGABA DA BAYANI AKAN LADDUBAN ZIYARAR MARA LAFIYA INSHA ALLAHU.

Wannan duka yana zuwa maku ne a cikin littafin: *HUKUNCE HUKUNCEN JANAZA A MUSULUNCI* Wallafar: _Malam Haruna Abubakar Shika_

MASU BUKATAR SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA* SAI SU TURA CIKAKKEN SUNA DA GARI ZUWA GA +23430201868 A WHATSAPP

https://fb.me/abbansinan

No comments: