📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
_021_
RASHIN LAFIYA (CIWO)
Ciwo daga Allah ya ke babu wanda ya fi qarfin Allah ya jarrabe shi da ciwo ko wane iri ne, in muka bibiyi tarihi za mu ga bayin Allah da dama sun yi fama da rashin lafiya ba don kome ba sai dai don Allah ya daukaka darajarsu da kuma kankare ma su zunubansu. Gwargwadon imanin mutum gwargwadon yadda Allah zai jarraba shi. Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya gaya mana cewa girman lada na tare da girman jarrabawar da Allah ya jarrabe ka da ita, haqiqa idan Allah ya so wasu mutane sai ya jarraba su (da wata cuta), wanda ya yarda da hukuncin Allah to yana da yarda, wanda ya yi hushi to yana da sakamakon fushinsa.
[Tirmidhi ya ruwaito]
Don haka ciwo ba abin zargi ba ne domin akwai wani sakamako wanda Allah ya ke bai wa wanda ya yi ciwo,
haka ma’aiki sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya fada mana a wani hadisi da aka samo daga Anas Allah ya qara masa yarda ya ce, “Manzon Allah sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam ya ce, ‘Idan Allah ya so bawansa da alheri sai ya sa masa wata cuta (uquba) a nan duniya, amma idan Allah ya nufi bawansa da sharri sai ya qyale shi da zunubinsa har ya cika masa da shi ranar qiyama.’”
[Tirmidhi ya ruwaito]
Wannan magana ta manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ta nuna mana ashe duk wanda ciwo ya same shi ya yi haquri ba kansa ne farau ba, manyan mutane su ma sun yi ciwo na tsawon lokaci mai tsawo, misali kamar Annabi Ayyub da Allah ya gaya mana ya yi ciwo na tsawon lokaci wanda har ya kai na shekara 18 ba ya fita saboda ciwo, wanda har ya kai ga gaba dayan dukiyarsa ta qare ‘ya’yansa duk suka mutu baki dayansu saboda tsananin ciwo, sai da ta kai gaba dayan jikinsa ba ya amfani sai zuciyarsa kawai, wasu malaman tafsirin ma cewa suka yi sai da ya kai jikinsa ya kasance yana yankewa yana faduwa qasa. Wata rana matarsa ta ce masa ya roqi Allah ya ba shi lafiya mana, sai ya ce shekarata saba’in lafiyata lau amma in kasa haquri da rashin lafiya ta shekara sha bakwai? [IBN KATHER]
ﺍﻟﻠﻪ ﺃَﻛْﺒَﺮُ
Bayin Allah ke nan shekara da shekaru suna fama da rashin lafiya amma suka yi haquri, haka aka san bayin Allah cikin haquri ko da yaushe.
Kusan idan muka bibiyi tarihi zamu ga yadda Allah Ya ke jarraba bayinsa da cututtuka ba don komai ba sai don Ya qara masu daraja da daukaka. Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa salam ya yi ciwo, haka shi ma babban sahabinsa Abubakar shi ma haka, haka shi ma Imam Malik ya yi rashin lafiya har ya kai ba ya zuwa masallaci sai a gidansa yake yin sallah,haka ya mutu cikin wannan rashin lafiya. Allah Ya rahamshe shi amin. Shi ma dalibinsa Imamu Shafi’i ya yi rashin lafiyar da ta kai in ya hau doki jini na zuba a duburarsa, har ya cika masa huffinsa (takalminsa). A qarshe dai ina mai cewa ciwo ko rashin lafiya daga Allah ne kuma ba abin zargi ba (ba aibu ba ne) ne domin jarrabawa ce daga Allah, kuma akwai sakamako mai yawa ga wanda ya yi haquri kuma ya miqa al’amarinsa ga Allah. Imam Ahmad shi ma ya yi ciwo mai tsanani har ta kai ga yana nishi da qyar, kuma a cikin wannan ciwon ya rasu Allah Ya rahamshe shi amin.
Ana so mara lafiya ya yi haquri da cutar da ta same shi ya miqa lamarinsa ga Allah kuma ya yi haquri, babu abu mafi tsada fiye da Allah Ya ba ka haquri, kuma Allah Ya yabi masu haquri a cikin littafinsa kuma Ya yi ma su bushara da lada mai yawa kuma Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya fadi irin falalar haquri, shi mumini duk abin da ya same shi lada ne.
Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Abin sha’awa ga al’amarin mumini komai nashi lada ne. Idan abin farin ciki ya same shi ya gode wa Allah alkhairi ne a gare shi, in kuma abin baqin ciki ko damuwa ya same shi ko ciwo ne ya yi haquri alkhairi ne a gare shi.” [Muslim]
Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce wanda Allah ya nufe shi da alkhairi sai ya sanya ma shi wata cuta. [Bukhari da Muslim]
Babu wata damuwa ko baqin ciki ko ciwo ko wani abu mai cuta da zai sami mumini face lada ne a gare shi. Har qaya idan ya taka face Allah Ya kankare masa kurakuransa. [Bukhari da Muslim]
Ibn Mas’ud ya shiga wajen Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya taras da shi yana zazzabi, sai ya ce ma shi, “ Ashe kai ma kana zazzabi zazzabi mai tsanani haka?” Sai Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce, “Haka ne abin yake, ni ciwon mutane biyu nake yi.” Sai Ibn Mas’ud ya ce, “Kana nufin kana da lada biyu ke nan?” Sai Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce, “Na’am.” Sannan
sai ya ce, “Babu wani ciwo ko qaya da zai sami musulmi face Allah ya kankare masa munanan ayyukansa kamar yadda itaciya take kakkabe ganyayen ta. [Bukhari da Muslim]
Zamu dakata anan, idan Allah ya kaimu wani sati zamu cigaba Insha Allahu.
Wannan duka yana zuwa muku ne a cikin littafin: *HUKUNCE HUKUNCEN JANAZA A MUSULUNCI* Wallafar: _Malam Haruna Abubakar Shika._
MASU BUKATAR SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA* SAI SU TURA CIKAKKEN SUNA DA GARI ZUWA GA
+2349030201868 A WHATSAPP
Https://fb.me/abbansinan
No comments:
Post a Comment