Sunday, 9 February 2020

SUJADAR SAHU A SALLAH

*LIMAN NE YAKE SALLAH DA MUTANE, SALLAH MAI RAKA'A HUDU, BAYAN YA DAGO DAGA SUJADA TA BIYU A RAKA'A TA UKU SAI YA ZAUNA YANA ZATON A RAKA'A TA HUDU YAKE, SAI MAMU SUKAYI MASHI TASBIHI DA SAURI, SAI YA TASHI ZUWA RAKA'A TA HUDU DA SAURI, BAYAN WANCAN ZAMAN DA YAYI DAN KADAN(KAMAR ZAMAN JALSATIL ISTIRAHAH) ZAIYI SUJUDUS SAHAWY NE KO KUWA?*

*_AMSA_*

Idan liman ya zauna a Raka'a ta uku da mantuwa, zaiyi sujada biyu(kafin sallama). Saboda fadar Manzon Allah S.A.W cewa:
لكل سهو سجدتان
Ko wace mantuwa tana da sujada biyu, *Imamu Ahmad da Abu Daud suka fitar da hadisin*

Ibn Qudama Al-maqadisy(RH) a cikin *AL-MUGNY* yace: _Idan Liman ya zauna ba a wurin da ake tahiya ba kwatankwacin *JALSATIL ISTIRAHAH,* zaiyi sujada (kafin Sallama), duka dayane, koda zamu fadi cewa jalsatil istirahah Sunnah ce a cikin Sallah,(ko bamu ce ba) domin shi Mai sallar baiyi nufin cewa jalsatil istirahah yayi ba, yayi nufin waninta(zaton cewa Yana tahiya ta karshe ne) kenan ta zama mantuwa, koda bai yi sujada biyu kafin Sallama ba, sallar shi tayi, domin wani aiki ne yayi Dan kadan a cikin Sallah, shi Kuma aiki Dan kadan bai bata Sallah...._

Haka idan kuka duba a cikin:
كشاف القناع (1/395)
Ya kawo kwatankwacin wannan maganar, ya Kara da hadisin Abdullahi Dan Masa'ud dake cikin Muslim cewa:
فإذا زاد الرجل أو نقص في صلاته فليسجد سجدتين
Idan mutum yayi Qari ko ragi a cikin Sallah zaiyi sujada guda biyu.

Ash-Sheikh Muhammad bin Salih Almunajjid(Hafizahullah) yake cewa:
لكن إذا لم يسجد الإمام للسهو، ظنا منه أنه لا يلزمه السجود، أو نسيانا منه للسجود، فصلاته صحيحة.
Sai dai, idan Liman baiyi sujadar sahawun ba, ko yayi tunanin cewa ba dole bane sai yayi sujadar, ko Kuma ya manta, sallar shi ingantatta ce.

Wannan shine abin da yake na dai dai.

Allah yayi Mana muwafaqa a cikin Kyawawan ayyukan mu

#ABBAN_SINAN
+2348064734911
+2349030201868

No comments: