🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI*
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Wallafar: *Ash-Sheikh Muhammad Sani Liman Tsafe (ABU HURAIRAH)*
_004_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
✅ *SABUBBAN DA KE JANYO YANKE ZUMUNTA.*
Idan kayi nazari akan sabubban dake janyo yanke zumunta zaka samu cewa akwai sabubba masu yawa. Ga kadan daga cikinsu
1. *JAHILCI:* Jahiltar mummunan sakamakon da mai yanke zumunta yake samu anan duniya da lahira, ko kuma rashin yin aiki da abin da mutum ya sani. An karbo daga Umar (R) ya kasance akan mimbari yana cewa: ku nemi sanin dangantakarku, sannan ku sadar da zumuntarku wallahi! Lallai zai kasance tsakanin mutum da dan uwansa wata rigima ta hadasu saboda rashin sanin juna, da yasan akwai zumunta tsakaninsu da wannan dalilin na alakar zumunta ya hanashi cin mutuncinsa *(Bukhari, Adabul mufrad 73)*
2. *KARANCIN TSORON ALLAH;*
Idan tsoron Allah yayi rauni sannan addini yayi saku-saku ba zai damu ba idan ya yanke abin da Allah yayi umarnin asadar, kuma baya kwadayin ladar da ake samu idan an sadar da zumunta kuma baya tsoran mummunan sakamakon da zai same shi a dalilin yanke zumunta.
An karbo daga sa’id bn sam’an, yace: Naji Abu Hurairah yana neman tsarin Allah daga shugabancin yara da wawaye (jahilai) sai aka ce masa mine ne alamar yin haka? sai yace dan za’a dinga yanke zumunta a kuma dinga yin da’a ga mai halakarwa a saba ma mai shiryarwa *(Adabul-mufad 66)*
3. *GIRMAN KAI;*
Sashen mutane idan mutum ya samu wani matsayi babba ko ya samu wata daukaka ko kuma ya zama babban dan kasuwa sai yayi girman kai ga yan'uwanshi, ya kyamaci ziyartarsu, kuma ya kyamaci zuwa garesu, yana ganin shi ke kan gaskiya kuma shi ya can-canta a ziyarta.
4. *YANKEWA MAI TSAWO;*
A nan akwai wanda yake yanke ma yan'uwansa lokaci mai tsawo al’amarin ya dore akan haka har ya kai ga yanke zumuntarshi dasu gaba daya, har ya saba da yankewa sai yayi nesa dasu. An karbo daga Mikdam, lallai yaji manzon Allah (SAW) yana cewa lallai Allah yana maku wasiyya da iyayenku mata sannan yana maku wasiyya da iyayenku maza, sannan yana maku wasiyya da yan'uwanku *(Adabul mufrad 60)*
5. *AIBANTAWA MAI TSANANI;*
Sashen wasu mutane idan dan'uwansu ya ziyarcesu bayan a baya ya yanke zumuntarshi dasu lokaci mai tsawo sai su yawaita zar ginshi har zargin yayi tsanani wanda wannan sai yasa shi kaurace masu saboda tsoron mummunan zargi da suke mashi.
6. *DORA MA RAI NAUYIN DAYA WUCE QA’IDA;*
A nan akwai wanda idan dan'uwansu ya ziyarcesu sai su dora ma kansu yin hidindimu da suka wuce karfinsu domin su ga cewa sun karrama dan'uwan nasu sama da karfinsu ko karancin abun hannunsu, wannan shi ke sanya yan'uwan nasu su dinga takaitawa da ziyartarsu domin tsoron kada su dora masu ire-iren wadannan nauye-nauyen. Saboda Annabi yace mafi karancin sadar da zumunci shine sallama mafi girman zumunta shine sadarma wanda ya yanke maka.
7. *KARANCIN KULA DA WADANDA SUKA KAWO MAKA ZIYARA;*
Akwai daga cikin mutane wanda idan yan'uwanshi suka ziyarceshi baya bayyanar da farin cikinsa akan ziyarar, bai tsayawa ya tattauna dasu ko ya sakar masu fuska, sai dai za ka ga yana bata rai yana kyamarsu, wannan yana zama sanadin yan'uwa ba zasu kara ziyartarshi ba dan tsoron irin wannan wulakancin.
Manzon Allah yace, kada ku wulakanta wani abu na alkhairi ko da sakin fuskane idan ka hadu da dan'uwanka.
8. *TSANANIN ROWA;*
Wasu daga cikin mutane idan Allah ya azurtasu da dukiya mai yawa ko wani matsayi zaka same su suna gudun yan'uwansu, ba wai dan girman kai ba a'ah! Domin jin tsoron kada yan'uwan suyi amfani da wannan damar domin bayyanar da bukatunsu zuwa garesu, ko kuma domin kada ya temakesu. Maimakon ya basu dama idan sun ziyarceshi yakarbi bakuncinsu, ya yalwata masu, yayi masu hidima gwargwadon halinsa,ko kuma ya basu uzuri akan abin da ba ya da ikon yi masu amma sai kaga yana kauda kansa, yana kaurace masu domin kada su rokeshi kamar yadda yake riyawa. Mine ne amfanin dukiya ko matsayi da mutum zai samu idan har zai haramta ma yan'uwansa amfana da ita.
9. *JINKIRIN RABON GADO;*
Hakika zaka samu wasu daga cikin mutane suna jinkirta rabon gado kodai domin kasala, ko kuma wani daga cikin magadan yana da wani mummunan kuduri game da yan'uwansa ko makamacin haka.
Duk lokacin da aka jinkirta rabon gado to kiyayya da adawa zata watsu tsakaninsu domin idan wannan yana da hali ko yafi karfin gadon wani shi kuma yana bukatar raba gadon domin bashi na shi kason ya samu ya bude kasuwanci ko makamanci haka.
10. *MUTUWAR AUREN ZUMUNCI;*
Hakika mutuwar auren zumunci yana haifar da matsaloli a tsakanin yan'uwa na bangaren miji dana bangaren mata musamman in akwai 'ya'ya a tsakaninsu ko kuma saboda wasu matsaloli da suka shafi sakin auren.
A NAN ZAMU DAKATA SAI A LOKACI NA GABA INDA ZAKUJI CIGABAN *SABUBBAN DAKE JANYO YANKE ZUMUNTA*
DOMIN CIGABA DA SAMUN WANNAN RUBUTU KUNA IYA AIKEWA DA SAQON WHATSAPP ZUWA GA: +2349030201868 DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA*
#ABBAN_SINAN
https://fb.me/abbansinan
No comments:
Post a Comment