Thursday, 25 March 2021

001 HUKUNCE HUKUNCEN TA'AZIYYA A MUSULUNCI

HUKUNCE-HUKUNCEN TA'AZIYYA A MUSULUNCI.

DARASI NA FARKO (001)

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai jinkai, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah. 

Bisa ga la'akari da muhimmancin ta'aziyya da kuma bukatuwar musulmi ga sanin yadda take a Sunnar Manzon Allah SALLAL ALAIHI WA SALLAM, domin kaucewa bidi'o'i naga ya dace in tunatar da kaina game da takaitaccen bayani akan ta'aziyya wanda ya kunshi abubuwa guda shidda (6) kamar haka:
👉1. Shar'antuwar Ta'aziyya a Musulunci
👉2. Yiwa iyalan mamaci ta'aziyya da kuma lafuzzan da ake amfani dasu.
👉3. Ba'a iyakance ta'aziyya da kwana uku ba kamar yadda wasu suke riyawa.
👉4. Abubuwa biyu (2) da ya kamata a nisanta a lokacin mutuwa.
👉5. Sunnah ne dangin mamaci da makwabtan sa suyi abincin da zai kosar da iyalan mamacin su aika masu.
👉6. Mustahabbancin shafa kan maraya da tausaya masa.

📒NA FARKO: SHAR'ANTUWAR TA'AZIYYA A MUSULUNCI:📒

An Shar'anta yin ta'aziyya ga iyalai da dangin mamaci, saboda hadithai da suka yi bayanin haka:

📌 1. Hadithin Qurra Al-Muzanniy (R.A), cewa: a lokacin da Manzon Allah SALLAL ALAIHI WA SALLAM ya samu labarin rassuwar dandan wani daga cikin Sahabban sa, ya je yayi masa ta'aziyya har ma yace masa "MINENE YAFI SOYUWA A GAREKA? SHIN KAJI DADIN RAYUWAR KA TARE DA WANNAN YARO? KO (kafi son) KA ISKO SHI BAKIN KOFAR ALJANNA YANA JIRAN KA, YA BUDE MAKA (don ka shiga)?" sai yace: ya Annabin Allah!, nafi son ya riga ni ya bude mani. Wannan Hadithi [[Nasa'iy ya ruwaito shi da wannan siyaqi, haka kuma ibn Hibban da Hakim da Ahmad duka sun ruwaito sa. Kuma hadithin Sahihi ne.]]

📌 2. Hadithin Anas dan Malik (R.A), yace: Manzon Allah SALLAL ALAIHI WA SALLAM yace: "DUK WANDA YAYIWA DAN UWAN SA MUMINI TA'AZIYYA AKAN WATA MUSIBA, (da ta same sa) ALLAH ZAI TUFATAR DA SHI CIKAKKUN TUFAFI A RANAR ALKIYAMA WADANDA MUTANE ZASU YI FATAR SAMUN IRINSU" [Khadeeb Al-Baghdadiy ya fitar da shi da bin Asakir da kuma bin Adiy. Hadithi ne ingantcce] 

Wallahu a'alamu bissawab. 

Mu hadu a darasi na biyu (002) insha'allah. 

✍️ Nasiru Bala Bungudu. 
(Chief Imam Salih bin Abdul Aziz Juma'at Mosque Bungudu)

No comments: