Thursday, 25 March 2021

02 HUKUNCE HUKUNCEN TA'AZIYYA A MUSULUNCI

HUKUNCE-HUKUNCEN TA'AZIYYA A MUSULUNCI

DARASI NA BIYU (002)

📒ABU NA BIYU: YIWA IYALAN MAMACI TA'AZIYYA DA KUMA LAFUZZAN DA AKE AMFANI DASU📒

Ana yiwa iyalan mamaci ta'aziyya da duk wadansu kalamai da ake sa ran zasu lallashe su, su rage masu radadi da damuwar wannan rashi tare da sanya su yarda da hukuncin Allah da kuma hakuri, musamman ma lafuzzan da Annabi Muhammad SALAL LAHU ALAIHI WA SALLAM yayi amfani da su, idan mutum ya san su, idan kuwa mutum bai san su ba, to, sai yayi amfani da kyakkyawar kalma domin cimma wannan manufa, kuma kada su sabawa Shari'ah. Dangane da wannan akwai hadithai kamar haka:

📌1. Hadithin Usama bin Zayd (R.A) yace:..... Wata diyar Manzon Allah SALLAL ALAIHI WA SALLAM ta aika masa cewa danta na dab da mutuwa sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata gare sa ya aika mata cewa: Yana yi mata sallama kuma yace: "DUK ABINDA ALLAH YA KARBA NASA NE KUMA ABINDA YA BAYAR NASA NE, KO WANE ABU A WURIN SA YANA DA IYAKANTACCEN LOKACI, TAYI HAKURI TA NEMI LADA (a wurin Allah)."  [Bukhariy da Muslim suka ruwaito sa] .

📌2. Hadithin Buraidah bin Husaib (R.A) inda ya nuna cewa:....... Manzon Allah SALLAL ALAIHI WA SALLAM ya je yiwa wata mata daga cikin matan Madina ta'aziyya sai ya ce mata:" BABU WANI MUTUM KO MACE MUSULMA DAKE DA 'YA' YA UKU (da suka rassu) FACE ALLAH YA SHIGAR DA SU ALJANNA SANADIYAR 'YA' YAN" Sayyidina Umar (R.A) yana gafen dama da Annabi SALLAL LAHU ALAIHI WA SALLAM, sai yace koda 'ya' ya biyu?, sai Annabi yace: "KODA BIYU" [Bazzar da Hakim suka ruwaito sa, kuma Hadithi ne ingantcce] 

📌3. Ta'aziyyar da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata gare sa ya yiwa Ummu Salamah a lokacin da mijin ta abu-Salamah ya rassu, sai Annabi SALLAL LAHU ALAIHI WA SALLAM ya ce: "YA ALLAH KA GAFARTAWA ABU SALAMAH KA DAUKAKA DARAJAR SA A CIKIN SHIRYAYYU, KA MAYE BAYAN SA, KA GAFARTA MUNA TARE DA SHI, YA UBANGIJIN HALITTU, KA YILWATA MASA KABARIN SA KA HASKAKA MASA". [Muslim ne ya ruwaito sa] 

📌4. Ta'aziyyar da Manzon Allah SALLAL ALAIHI WA SALLAM yayiwa Abdullahi bin Ja'afar sai Manzon Allah ya ce:.... "YA ALLAH KA MAYEWA JA'AFAR A CIKIN IYALAN SA, KA SANYA ALBARKA GA DANSA ABDULLAHI (dansa) KUMA KA (Sanya Albarka ga) KASUWANCI" ya fadi haka sau uku. [Ahmad ya ruwaito sa, kuma hadithi ne ingantcce] 

💡Wasu kenan daga cikin lafuzzan da Annabi Muhammad SALAL LAHU ALAIHI WA SALLAM yayi amfani dasu wurin yiwa Sahabban sa ta'aziyya. 

Wallahu a'alamu bissawab. 

Mu hadu a darasi na uku (003)

✍️Nasiru Bala Bungudu. 
(Chief Imam Salih bin Abdul Aziz Juma'at Mosque Bungudu)

No comments: